Kimiya da Fasaha

Manyan dalilan da suke sawa a rufe Number ka ta WhatsApp Da kuma yadda zaka gyara bayan an dakatar da kai.

Manyan dalilan da suke sawa a rufe Number ka ta WhatsApp

Assalamu alaikum warahmatullah, ƴan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan sabon bidiyon.

A sau da yawa akan rufewa mutane WhatsApp ɗinsu suma rasa akan wani dalili ne hakan ta faru.

A don haka yau zamu zayyano manyan dalilan da ke sawa a rufe maka Number ka WhatsApp.

 

Na Farko (Amfani da WhatsApp GB ko Gold)

Kamar yanda aka sani kalolin wannan Whatsapp ɗin ba halastattu bane,ma’ana babu su a cikin Google playstore, wato yayin amfani dasu bazasu iya kare maka sirrukan ka ba, da kuma bayananka ta yanda mamallaka waɗannan Manhajojin zasu iya satar bayananka kuma bazasu iya kare su ba daga farmakin da Kamfini Google ke kaimusu ba, a don haka da zaran hackers sun kai musu hari suke iya samun nasara a kanka saboda rashin kariyar da mamallakan wannan Applications ɗin suka basu, a don haka duk wani App wanda ba daga Google playstore aka ɗauko shiba akwai yiwuwar yabada damar a satar maka bayananka na waya ta hanyarsa.

 

Na Biyu (Yawan Reporting)

Kamar yanda aka sani a komai na dunyi kai harma da rayuwa akwai tsari, sannan komai a kwai Kotu, adon haka yayi da mutane suka haɗu suka takai ƙarar Number ka ta hanyar yin report a WhatsApp,yana matuƙar taimakawa wajan a rufe maka Number a don haka se mu kiyaye sakin number mu da kuma yawan laifi a groups gudun kada ai refort na lambobin mu.

 

Na Uku (Yawan ana Blocking naka)

Sau da yawa zakaga mutum ya kasa gano meke faruwa ne ake ta rufe masa number, to haƙiƙa kamfani WhatsApp suna kula da yawan Blocking naka da ake yayin aikata wani laifi a groups na daga Mutane da suke yawan yi a don haka suke saka wani adadi na idan kawuce suma zasui Blocking numberka domin sun gano kana aikata laifukan da mutane basa so.

 

ƴan uwa wannnan sune taƙaitattun hanyoyin da suke sawa ana rufe maka WhatsApp wanda ya kamata a ce ka sansu kuma ka kiyaye domin gudun faruwar hakan.

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

 

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

 

Wannan shine link dinsu

 

Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan

 

Wannan shine abinda zaka rubuta musu

Hello WhatsApp Team!
My WhatsApp account is banned. I’m sorry I installed third party app by mistake, please unbanned my WhatsApp account immediately.

Thank you.

 

Waslam alaikum na gode…dafatan an ilimantu da wannan rubutun.

Back to top button