Harijin Sarki Page 6 Romantic Hausa Novel
Taɓe baki tayi tana gwada yanda taga yana wani bubbuɗawa yana tafiya cikin iko ta juya zata fita taji an kira sunanta ta tsaya cik ya tako cikin sabuwar shiga yace “Zaki dubani ki faɗamin matsala ta” juyowa tayi tace “Ranka ya daɗe zuwa dare Zaifi dacewa da lokacin bincike” zuba mata sihirtattun idanunsa yayi wannan ta sanyata yin ƙasa da nata cikin izza ya tako gabanta yace “Tun yanzu kince zakiyi iyakar ƙoƙarinki, Iya inda ƙoƙarin naki ya tsaya kenan” sake rusunar da kanta tayi jikinta na kyarma tunda take bata taɓa ganin mutum me kwarjinin wannan mutumi ba, da wannan ya kama hannunta ya ɗora bisa wandonsa ya haɗeshi da dick ɗinsa ta ɗago da mugun sauri cike da razani taga yanda ya kafeta da idanunsa yace “Wannan shekarar ta biyu da watanni shida bata kwanta ba kuma an tabbatar min da ke kaɗai zaki iya kwantar da ita ina so yau ta kwanta” cike da tsoro tace “Meye amfanin sai na taɓa sannan zanyi abinda ya dace” sake matse mata hannu yayi a jiki yace “Ina samun nutsuwa da ɗumin hannunki Likita Samha a matuƙar buƙace nake yanzu haka, kuma inason nayi release ko zan samu ta kwanta kiyi wani abu akai an tabbatarmin da warakata tana hannunki har yanzu ruhin sirri yana bani tabbas akan zan samu waraka ne ta hannunki”Janye hannunta tayi tace “Akwai buƙatar gwaje gwajen jini da ƙwayoyin halitta, aikin yazomin bakatatan ina buƙatar zurfafa bincike Yallaɓai, alamun tsoron da yagani a yanayinta shine ya sashi rabuwa da ita yace “yanzu meye solution?” Zama ta nemi guri tayi ta buɗe system ɗinta ta fara bincikenta ta ɗago tace “Inason wasu magunguna da allurai zasu taimaka maka wajen samun bacci me kyau. Juyawa yayi ba tare da yace mata komai ba ya fice daga parlourn zuwa inda ya tarar da Yadam ya miƙe cikin ladabi suka fice ta bi bayansu da kallo tana jinjina girman wannan mutumi saikace ragowar jinsin samudawa, ita a tarihin rayuwarta bata taɓa ganin mutum mai tsayi da faɗinsa ba, damƙe hannunta tayi har yanzu tanajin ɗumin wannan abu nasa da ya sanya mata a hannunta, Lumshe idanunta tayi tsigar jikinta tana tashi tana tunano matan da suke kwance yanzu haka cikin rashin hayyaci kuma duk ta’annatin wannan abar ne, ji tayi ance mata “Sultan ya bada umarnin a kaiki ɓangarenki” da sauri ta kalli mai maganar tace “Inane ɓangarena?” Sunkuyar dakai tayi tace “Yace a kaiki ɓangaren mai rasuwa Nataj” zubawa hadimar ido tayi daga bisani tace “Muje” fita sukayi suka nufi wani katafaren dake masu gadin sun san da zuwansu suka buɗe musu ƙaramar ƙofa suka shiga, haske fetal kamar rana ko ina sai walwali yakeyi sashin yanada maƙotaka da sashin Sultan ta kusa, ƙofar parlourn suka buɗe suka shiga ta rinƙa kallon gurin da irin ƙawa da alatun dake wannan sashi, ta sauke ajiyar zuciya ta ɗago ta kalli Hadimar tace “Nan ɓangaren baiyi kama da Aikina ba” ƙasa tayi da kanta tace “Nidai haka aka umarceni” nuna mata ko ina tayi ƙarshe ta barta a wani ɗaki da kallon haɗuwarsa ta shagaltar da ita har Hadimar ta fita bata sani ba” Rage kayan jikinta tayi ta shiga inda aka faɗa mata bathroom ne tayi wanka cike da tsoro wannan ƙawa da alatun ya koma firgitata, alwala tayi ta fito tayi sallah tana shirin kwanciya wata Hadima tazo ta ƙwanƙwasa mata ƙofa tace “Ranki ya daɗe me kike da bukatar ci ko sha?” Ɗan jim tayi kafin tace a bata Tea kawai haka wannan Hadima ta fita babu jimawa ta dawo ta haɗa mata tea ɗin ta gama ta tashi tayi mata sallama, zama tayi tana research ɗinta tana save abubuwan da zasuyi mata amfani, har biyun dare bata kwanta ba, ji tayi iskar ɗakin ta sauya mata da ɗumi da wani ƙamshi me ratsa zuciya, tanajin kamar wani idanu yana Kallonta, nan ta fara dube dube tanajin idanun ruhi na yawo a jikinta babu kuma kowa a gurin.Tsoro ne ya shiga Zuciyarta ta maza ta rufe system ɗinta ta ja duvet ta kwanta tanajin wani razani na shigarta, da haka wani bacci me nauyi ya ɗauketa cikin baccin taji wayarta tana ruri ta tashi firgigit ta lalubo wayar tana jin haushin dalilin daya hanata kashe wayar ganin number an rubuta (Sultan Al Zirkan) yasata tashi zaune ta kara a kunnenta, “Kizo” iya abinda aka faɗa kenan aka kashe wayar ta fara rarraba idanun tana maimaita kalmar “Kizo! Kizo!!” Allah ya jarabceta da tsoron dare musamman a wannan gidan data fahimci kamar akwai motsin wasu ruhika saɓanin wanda take gani.Ji tayi wayar ta ƙara ɗaukan ruri ta miƙe da sauri cikin rashin sanin abinyi ya yayumi rigar saman rigar baccin jikinta ta fice domin tasan dole wannan kiran zai zama kiran ujula ne, bata samu matsala da duk masu gadin gidan ba tun daga inda ta fito har inda ta shiga babu wanda yace mata ƙala hasali ma janyewa suke suna bata hanya, shiga tayi har parlourn da suka tsaya ɗazun bata ishe kowa ba ta shiga wanda ya isheshi a ciki ta tarar da Basrah tsaye tana kaiwa da komowa, ta kalleta tace “Likita me kikazo yi da daren nan?” Cikin tsoro tace “Uhm… Dama na samu kira ne ance nazo” kallon ƙofar shiga turakar Sultan tayi tace “Kira daga wannan sashin?” Jinjina kai tayi tana me duba wayarta Basrah ta kalli number tace “Hakane amma yanzu yana kan ganawa da matansa ne saidai ki jira ya gama sai ki shiga….” Sake kiran wayar hannun nata akayi ta kalli Basrah ta kalli wayar tace “Yana kirana kina cewa kuma na jira idan wata ujular ce tasa ya nemeni a wannan lokacin fah?”……………


