Sirrin Rike Miji

Ko Kinsan Ta Yaya Al’adar Mace Ke Rikiciwa?

KO KINSAN TAYAYA AL’ADAR MACE KE RIKICEWA?

Mace tun tana shekara 13 ko 14 take zama daya daga cikin masu jinin al ada har zuwa shekara 50 to daga nan malamai sun tabbatar hukunci jinin haila ya sauka akanta koda tanayi.

kowacce mace da lokacin yin al’adarta amma mafi yawan mata sunayi afarkon wata kuma yanda ya saba zuwa idan ya canja ya zama na cuta kuma ya zama babu hukunci akansa.

wani lokacin jini yana daukewa mace amma bayan ta sadu da mijinta sai taga jinin ya dawo to irin wannan ya kamata mace tarinka amfanida auduga ko farin kyalle wajen ganewa ko akwai saura domin akwai macenda koda ya dauke ba aso tayi gaggawar saduwa da mijinta anaso A kalla asamu sa’o,i ashirin da hudu (24hours) sannan tayi wanka,

lokacinda mace tasamu ciki shi wannan jinin yana daukewa ya zama abincin wannan jaririn shiyasa idan mace tanada ciki bata ganin jini saidai idan na cutane shima wannan bashida hukuncin jinin al’ada saidai duk lokacinda mace zatayi sallah saita sake alwala.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

 

CIWON MARA
Mata musamman wadanda basuda aure suna ciwon mara irin wannan kuma dattin maniyi ne domin ita mace maniyinta yana kasan nononta lokacinda sha awa tayi mata yawa zai dawo mararta idan be fitaba lokacin al ada saiya dinga mata ciwo.

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Kanki Kafin Aure Da Bayan Aure

 

RIKICEWAR AL’ADA
Koda yake ana samun canjawar lokacin zuwan al’ada kwanaki uku zuwa biyar to amma rikicewar sa alamune na matsala kuma ciwon sanyi (infection) shine kan gaba wajen kawo matsalar rikicewar al’adar mace,
Ana samun matsalar aljanu suma sukan jawo matsalar rikicewar al’ada don haka me fama da wannan matsala ta nemi magani.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

 

WASU DAGA CIKIN MAGUNGUNAN

Ga wadanda ciwon sanyi ya jawo musu matsalar sai a samu habbatussauda cokali 3 sai garin kustul hindi cokali 7 garin shazabu cokali 3 sai asamu zuma kofi biyu azubasu agauraya ana shansa safe da yamma saikuma a samu garin albanuna ana zuba cokali daya acikin ruwa kina wanka dashi.

su kuwa wadanda suke fama da matsalar aljanu saisu garzaya wajen masu rukiya sannan a samu Garin Kustul Hindi kamar cokali guda Garin Hulba ma haka. Ki rika tafasawa kina sha In sha Allahu al’ada zata daidai tu.

Sannan ‘Ya’yan Habbatus sauda idan ana taunawa ana hadiyewa in sha Allahu za’a samu sauki.

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

Back to top button