Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 59 Hausa Novel

Duk yanda yake jin zai samu Khadeeja ta saurareshi ya gagara, gashi kuma sai a yanzu Allah ya jarrabeshi da kaunarta.Kusan kullum sai yayi mata waya, idan ta ga dama ta dauka idan kuma ba ta ga dama ba taki dauka. Ya mayarwa kansa duk Juma’a da yamma sai ya je gidan duba Hammad, sai dai hakan bai bashi damar ganinta ba. Domin idan yaje ko da yayi mata waya haka zata saka a bude masa parlor din baki ta turo masa Hammad, har ya gama hirarsa da Hammad ya tafi ba zata fito ba. Don haka wasu lokutan sai kawai ya rutsata a office inda dole ta zauna su gaisa har su dan yi hira.Abu daya ne yake hanashi zakewa a kan maganarta saboda har yanzu yana jin kunyar Baffanta, baisan da wane bakin zai je yace masa ya sake bashi auren Khadeeja ba. Shi yasa ya dage yake kokarin ganin ya gamsar da Khadeejan ta jewa Baffan da maganar da kanta.Kwanci tashi har shekara ta zagayo.Tun da ya gama hada takardun yake cike da farin ciki, haka ya kwana cike da zakuwa sabodan yanda yake son gari ya waye ya jr ya sami Khadeeja yayi mata albishir. Yana fita office dinta ya fara tsayawa, yayi sa’a kuwa ta riga ta zo.Kamar yanda ya saba a cikin office din ya sameta tana zaune tana editing script din da zata yi amfani da shi wajen gabatar da show dinta.Yana shiga ya tura kofar sannan ya yiwa kansa mazauni a kujerar gabanta cike da walwala. Bayan sun gaisa yace ‘Kina jin dadinki fa, kin ga yanda kike sheki kuwa.’Tayi dariya tace ‘Don Allah ka bari, haba. Ko waya ma baka yi min ba kace min zaka zo to da ka zo na riga na shiga studio fa?’Shima dariyar yayi yace ‘Sai na jiraki mana. Ai idan kina son na daina zuwa wajen nan to ki yarda mu mayar da auren mu mu huta, in ba haka ba dole kullum na zo nan nayi attendance don duk masu shirin yi min shigar sauri su ganni su san ina nan ba fashi.’Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce masa ba, amma dai yawana zuwan nashi office din ya fara gundurarta. Ba wai don bata so a ganshi bane kuma ba wai tana jin ya isa ya hanata kula wanda take son kulawa ba; kawai dai tana so ya dana bata space tunda ita dai ta gama magana a kan lallai ba zata koma gidansa ba kuma har yanzu hakane a ranta.Muryarsa ce ta katse mata tunanin da ya kirawo sunanta, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kai.Yace ‘Ki sauwake mana wahala ki yarda mu mayar da aurenmu, duk wani abu da ya bata miki rai a baya nayi miki alkawarin ba zaki sake gamuwa da shi ba a zamanmu.’Ta jijjiga kai ‘Na fahimceka Mustapha, amma dai kayi hakuri. Ba wai kaine ba zan aura ba, auren ne gaba daya ba zan yi ba. Don allah ka daina wannan maganar, ka mayar da hankali wajen kula da iyalinka. Ka ga yanzu ni babu aurenka a kaina, idan taji kana zuwa wajena zaku iya samun matsala. Kazo kai baka sami natsuwa da ta gidan ba kuma ni ba aurenka zan sake yi ba.’Ya jijjiga kai don baya son wannan maganar, shi yana ji a jikinsa Khadeeja matarsa ce shi kadai don haka duk tsawon lokacin da zata dauka tana yi masa yanda zai jure. Ya zaro envelope daga aljihunsa ya dora a kan tebur din ya tura mata gabanta yana murmushi yana cewa ‘Wannan na zo kawo miki daman.’Ta dauko tana dubawa tana cewa ‘Me na samu.’Ta zaro takardun daga envelop ta fara dubawa; kujerar Hajji Mustapha ya bata. Tana dubawa tana murmushi saboda yanda tunanin zata je Hajji ya faranta mata zuciya. Ta ninke takardu ta fara mayarwa cikin envelop din a daidai lokacin da murmushinta ya ragu. Ta tura masa gabansa tace ‘Na ji dadi Abban Hammad, na gode Allah ya kara arziki da rufin asiri. Amma kayi hakuri ba zan iya karba ba, ba wai don na raina ba ko wani abu. Na gaya maka ba zan sake aurenka ba so kaga babu wani dalili da zai sa na karbar maka kujerar Hajji. Kuma ko na karba ma Baffa ba zai taba barina naje ba sai dai a daura mana aure kafin na tafi; kuma wannan ba zai yiwu ba. Please kayi hakuri! Amma na gode sosai.’Kafin ta gama bayanin fuskarsa ta canza gaba daya, ba tare da ya dauki takardun ba yace ‘To ki karba mana Khadeeja ki bari a daura mana auren, please ki daina guduna haka.’Ta sunkuyar da kanta cikin damuwa tace ‘Ba gudunka nake ba, amma dai ba zan iya karaba ba.’Suka yi shiru na dan lokaci. Jimawa kadan yace ‘To yanzu ya kike so ayi? Ni da sunanki na biya wannan kujera.’‘Kayi hakuri ba zan iya karba ba.’Suka sake yin shiru na dan lokaci.Kafin suyi magana aka kwankwasa kofar, ta amsa ta bada izini aka shiga. Wata mace ce abokiyar aikinta ta dan leko tace ‘Anti Khadeeja yallabi yace ke ake jira a studio za a fara.’‘Yanzu zan shigo.’ Ta fada tana shirin mikewa.Ta dubu Mustapha tace ‘Bari naje kada ka sa a koreni aiki.’Yayi dariya shima ya mike, sai dai tana kula dashi bai dauki takardun ba. Ta mika hannu ta dauka sannan ta zagayo ta tsaya a gabanshi, ta mika masa takardun tana murmushi tana cewa ‘Kayi hakuri ka tafi da wannan, wallahi ba zan iya karba ba. Idan na karba ba zan iya da rigimar Baffa ba tunda na san ba zan aureka ba. Kayi hakuri please.’Ya mika hannu ya karbi takardun yana tsareta da ido kamar mai binciken wani abun a idonta, har sai da ta kawar da nata idon. Ta wuce ya biyota a baya suka fito daga office din, suka jero har zuwa reception sannan tayi masa sallama ya fice ita kuma ta mike ta nufi studio din. Tana fatan Allah ya sa dai kada ta kwafsa saboda yanda Mustapha ya jagula mata lissafi; me zata yi da kujerar makansa? Wato ma shi har yanzu tunani yake saboda kujerar Makka yasa ta ki komawa gidansa? Bai ma san wacece ita ba kenan, zaman da suka yi tare bai sa ya fahimceta ba. Ba ta bukatar kujerarsa kuma ta san tabbas idan ba aurensa ta kuma yi ba ko kashi ta kai gida tace shi ya bata sai sun yi rigima da Baffa, kuma bata shirya karya ba saboda Mustapha wanda take so ya rabuda ita ya daina damun rayuwarta.……..Tana tashi daga waje aiki ta wuce gidan Yaya Mama, tayi sa a yaran duk sun tafi islamiyya don haka ta sami Yaya Mama ita kadai. Bayan sun gaisa Yaya Mama tace ‘Bari na samo miki ruwa ko lemo.’Ta dafe cinyarta tace ‘Barshi kawai sai da na tsaya na ci abinci sannan na karaso.’Ba tare da bata lokaci ba ta fara bata labarin kujerar Makkan da Mustapha ya kawo mata dazu.Sai da ta gama bata labarin suka sheke da dariya a lokaci guda sannan tace ‘Wai ni zai saya da kujerar Makka dan rainin hankali.’Yaya Mama tace ‘Ai kuwa dan rainin hankali lamba daya, wato tunda ki ce ya sakeki saboda kujerar Makka bari ya biyaki sai ki yarada ya mayar da aurenku.’‘Ashe kin gane.’Suka cigaba da hira suna tuna abubuwan da Mustaphan yayi a baya.Sai da Magriba ta fara kawo jiki sannan Khadeeja ta fara shirin tafiya.‘Bari na wuce kada magriba tayi min a nan.’Yaya Mama ta dafa hannunta tace ‘Khadeeja, idan fa zaki koma gidan Mustapha kin san babu wanda zai hanaki ko? Don ni ina ganin ma gara ki koma can din tunda kin ga ko babu komai ga Hammad. Kuma naga har yanzu baki da wani manemin; duk da ma duk wanda zaki aura mijn wata ne don haka kin ga dole ki zauna da kishiya. Ni ina ga gara gidan Mustaphan tunda dai yayi nadama har yana kokarin ya faranta miki.’Nan take ta bata rai, ta zare hannunta ta dan matsa daga kusa da ita sannan tace ‘Ba zan taba komawa gidan Mustapha ba, aure kuma baya gabana balle na fara damuwa da rashin manemi. Idan Allah ya saka ina da rabon aure a gaba to duk wanda Allah ya sa shine mijina zan aura amma fa in sha Allahu ba zan sake auren Mustapha ba. Mutumin da ya daukeni ne kawai a matsayin solution to his problem. Ko yanzun ma da yake ta kokarin na koma gani yayi kirikiri matar tasa ta kasa kula masa da gidan da yara kamar yanda nayi. Shi yasa ya lallabo ya mayar da ni cikin wahalar da Allah ya rabani da ita. Ba zan koma na, can su karata.’Ta mike ta dauki jakarta, don haka itama Yaya Maman ta mike. Ta san idan ta fiya takurawa da maganar yanzu zasu yi fada don haka sai ta kyaleta suka yi sallama ta kama hanya._____Wunin ranar gaba daya bai yi masa dadi ba. Ko da dai bai sa ran Khadeeja zata karbi kujerar ba tare da an kai ruwa rana ba amma kuma bai sa ran zata ki karba haka gaba daya ba ba tare da wata kofa ta sulhu ba. Haka ya wuni a office din babu walwala. Sai da yamma tayi sannan ya kwashi kayansa ya koma gida.Yana shiga dakinsa ya ajiye takardun hannunsa a kan mudubi; takardar kujerar da ya bawa Khadeeja ce a sama tare da wasu takardun na office.Tunda ya je sallar magriba masallaci ya dawo yayi zamansa a kasa shi da yara. Da farko ta dan zauna a wajensu ana hira gaba daya, daga baya kuma sai ta tashi ta haye sama ta barsu.Dakinsa ta shiga don ta samu ta huta domin nan ne kawai idan ta rufo kofar Rukayya ba zata so ta buga ta tasheta ba. Har ta wuce mudubin sai kuma ta koma da baya, ta sa hannu ta dauki envelope din da ta ja hankalinta. A bude take don haka sai kawai ta zaro takardun ta fara karantawa.Nan da nan kanta ya kulle; tabbas wannan sunan Khadeeja ne. To me hakan yake nufi? Suna tare kenan yanzu ta zama bazawararsa ko me? Tunda idan ba wata alaka ce tsakaninsu ba me zai saka har ya biya mata kujerar Makka? Kenan ma ita Mustapha zai rainawa hankali, ya saki matar sannan ya koma yama binta? Gaskiya ba zata yarda ba.’Ta daga kanta ta hango wayarsa tana chaji a kan bedside durowa; nan da nan ta ajiye takardun ta karasa ta dauki wayar. Ta riga ta san PIN din don haka kai tsaye ta bude ta fara duba whatsapp; sai dai har ta gama dubawa bata ga sunan Khadeeja ba. Tana duba calls taga sunan ‘Sweetheart’ shine sunan da yayi saving lambarta tun yana zuwa zance kuma bai taba canzawa ba. Bayan rabuwarsu Najan ta goge ta saka maman Hammad amma bata san yanda aka yi ya mayar ba. Ta mayar da wayar ta ajiye cike da damuwa da takaici…

Back to top button