Karfe A Wuta Chapter 20 By Ayshercool
Abbu kuwa hatta ɗinkin da Al’amin zai saka, ya yi masa, sai dai tun ranar da ya gaya masa, bai sake saka shi a idonsa ba.Yana zaune yana ta mitar rashin ganinsa rahila ta ce “Ba fa zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka je ka nemo shi duk in da yake, kar ya kunyataka a idon duniya.Kana kallo yanzu na sauke mayafina daga gidansu amaryar, sun yi walima, duk sun gama shiri, na kai musu mukullin gida, har jere sun yi, fita zaka yi ka nemo shi ai”Haka Abbu ya shuri takalama ya bazama, aka sanar da shi, su na can wata unguwar, suna walimar aurensa.Ya bazama ya tafi, yana zuwa ya tarar da labarin ƴan sanda sun kama su duk sun tafi da su.Hankalin Abbu ya tashi, ya tafi division ɗin nan unguwar aka masa a station ɗin ma artabu aka yi da su, an kwashe su an kai su anti daba, ya ce wallahi ba za shi anti daba a daren nan ba saboda shi.Da ya koma gida kuwa, rahila kamar ta ari baki saboda mitar, meyasa bai je ba a sake shi, kar ya basu kunya, ya ce idan za ta iya, ta tafi.Jauhar kuwa su mama suka sakata a ɗaki, suna yi mata nasiha, fuskokinsu ɗauke da fara’a da jin daɗi, da nanata mata ba zasu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba.Ita dai ta damu sosai ta ga waye wannan mijin, da har suka ga ya dace da ita? Har a ranar idonta da kwanciyar jinin jifan da mama ta yi mata da takalmi.Washegari ranar juma’a, za a ɗaura aure a babban masallacin juma’a, amma Al’amin yana tsare.Sha ɗayan rana, sai ga P.A ɗin Honorable indabo a anti daba da kansa, ya je belin Al’amin, wanda ya yi hakan ne, saboda aikinsa da yake son ya ƙarasa masa.Suka din ga sara masa, suka gaisa ya gaya musu wurin wanda ya zo, yake son ya yi beli, da wanda ya aiko shi””Gaskiya malam yaron nan ba zai ci bulus ba, state CID zamu kai shi”P.Aya ce “Ayi haƙuri, in anjima za a ɗaura masa aure, ko dan albarkacin wannan a sake shi mana””Wai ka san me ya yi kuwa?””Eh, an ce sun yi shaye-shaye sun tayar da tarzoma ko?”.”Ai da wannan ne da sauƙi, ya saba zuwa wurin nan a kan haka, jiya ƴan sandanmu sun kamo su, saboda sun sha tana gaya musu gaibu, a tsakiyar harabar station ya ɗaga ɗan sanda ya buga da ƙasa, saboda yana ganin ya isa, ya na ji da ƙarfi. Kuma ya din ga yi wa mutane wani shegen kallo kamar kumurci, zai gane kurensa, CID zamu kai shi”Ana haka shugaban kula da sashen ya shigo da shi da wani matashin ɗan sanda, suka ƙame suna sara masa, ya kalli P.A ya ce “Lafiya kuwa?”.Suka gaisa sannan ya ce “Honorable ne dai ya kuma aikoni ayi ban baki, a saki Mai dogon zamani “”Ba su gaya maka laifin da yayi ba? Jami’inmu fa ya daka, ba ya ji yaron nan ko kaɗan””Sun gaya mini, amma kamar yadda aka saba, honorable ya bayar da saƙo”Ya numfasa ya ce “A fito da shi da sauran yaran da ku ka kama” aka buɗe Al’amin, da yaransa, ya fito yana ɗan jirga ƙafarsa a hankali, saboda taron dangin da suka yi masa jiya, suka yi masa dukan tsiya, daga jami’in ya tankaɗa ƙeyarsa, ya waiwayo a fusace ya saka ƙafa ya kwashe shi a wurin.Daga shugaban, har PA ɗin babu wanda ya kalla, ya kama hanyar ficewa daga cikin station ɗin.Ya girgiza kai ya ce “VIPER kenan, Allah ya shirya”.PA ya ce “Viper kuma?””Eh sunansa kenan a gidan nan, sunan da suka saka masa kenan, ban san sau adadin da muka kama shi ba, ban taɓa ganin mutum mai bala’in taurin kansa ba, mu daka mu daka wallahi ko gezau ba ya yi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi wa mutane, kai ka ce kumurci ne zai kai sara, shiyasa nake yi masa sha’awar hakar tsaro, yana da girma da kwarjini na gaske, amma shi ba a saka shi ba a hana shi”.P.A yayi murmushi ya ce “Ai tun da ka ga honorable ya riƙe masa wuta, ba ya wasa da lamarin sa, kai ka san ba ƙaramin mara ji ba ne”.”Eh ai ku ne ke goya musu baya””Ai sabgar tamu ce dole sai da su”. Kafin PA ya gama sallamar su ya fito, tuni su Viper sun ɓace.Har gida walid ya je ya sanar da Abbu, an sako su, amma yayi yayi da shi, ya taho gida yayi shirin ɗaurin auren yaƙi.Abbu ya bi walid, har in da Al’amin yake, ya mimmiƙe yana bacci, jikinsa duk shaidar dukan da ya sha a station.Maganar duniya Abbu yayi, amma yayi burus ya ƙi tashi, sai da ya cire takalmi ya hau ƙwala masa, sannan ya tashi da ƙyar yana muzurai, Abbu ya tasa shi a gaba zuwa gida.Ba ƙaramin kyau manyan kayan suka yi masa ba, yayi wani irin kyau na mussaman, kwarjinin da Allah ya yi masa ya fito sosai da sosai.Bayan sallar juma’a aka ɗaura masa aure, bayan an saukko daga masallaci, babu wanda ya sake ganinsa.Jauhar kuwa gabanta sai tsananta faɗuwa yake yi, ƴan ƙawayenta na makaranta, suna ta tsokanarta, suna yi mata raha, amma ta kasa sakewa.Mama ta hau ta da zagi a gaban mutane, wai sai ta saka an ce aure dole za ayi mata, taƙi walwala ko wanka ba ta yi ta shirya ba.Jiki babu ƙwari, jauhar ta yi wanka, aka yi mata kwalliya.Tayi kyau sosai da sosai, dama dai-dai gwargwado tana da hasken fata da kyanta na fulani.Baba ne ya fara dawowa gida, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye, ana ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.Ya saka aka kira masa jauhar, zuwa ɗakinsa.Cikin tsananin tashin hankali da damuwa, Saifu ya shigo gidan, yana ƙwalawa baba kira.Mama ta ce “Saifu lafiyarka ka ke yi wa mahaifinka irin wannan kiran haka?”Bai saurareta ba, ya shiga ɗakin baban, mama da anty suka bi bayansa, ‘yan biki kuma suka yi cirko-cirko.”Baba wane irin miji ka aurawa jauhar? Tun a masallaci nake nemanka ban ganka ba”Baba yayi shiru, ya ƙi bashi amsa.”Baba magana nake yi fa kayi mini shiru yanzu zaka yi alfahari da wannan zaɓin da ka yi mata?marainiyar Allah, ka rasa wa zaka aura mata sai tantirin ɗan daba? Laifin me tayi maka har haka, mutumin arziki ya fito yana sonta, amma ka hana shi ka bawa mutumin banza, yanzu wane mutumin kirkin ne zai so haɗa zuriya da mai dogon zamani”A gigice jauhar ta ɗago idonta, gabanta ya shiga faɗuwa, tana jin yadda sunansa ya karaɗe arear unguwannin, duk da ba ta taɓa ganinsa ba, amma ya shahara da rigima da ‘yan unguwar su, da shi da madaki tana jin sunayensu, ta san dai madaki, tun da cikin unguwar su yake.Cikin zafin rai saifu ya sake cewa “Baba ka yi mini bayani, menene dalilinka na yin haka?””Saifu, kai ma ka fara shaye-shayen ne? Uban naka ka ke gaya wa haka? Shi ka ke tuhuma? Ba ‘yar sa ba ce? Zai zaɓa mata abun da zai cutar da ita ne?”Ya ce “Zai yi mana mama, ke da wannan matar menene ba zaku iya aikatawa ba, kuma na san ku kuka ƙulla komai, akwai Allah”Jauhar kuwa kuka ta fara, amma ta kasa magana, jikinta ya din ga tsuma, Hafsa kuwa fita tayi, ta kira yaya tijjani, wai ga saifu can yana yi wa baba rashin kunya.Aikuwa ya shigo cikin gidan da sauri, zuwa ɗakin baba, sai faɗi in faɗa yake da mama, baba kuma ya ƙi magana.Yana zuwa ya ɗauke saifu da mari, sai dai yana sauke hannunsa shi ma ya rama, take dambe ya kaure, sai dai jin hayaniya a waje ne, ya sanya suka yi saroro.Bushe-bushen ‘yan tauri ne yake tashi daga ƙofar gidan, nan da nan warin wiwi ya din ga shigowa gidan, yaran Aminu sun cika layin, suka din ga busar ‘yan tauri, suna yi wa Aminu kirari, sai dai babu shi a wurin.Su maman ma waje suka yi, domin zuwa su ga abun da yake faruwa.Nan ‘yan biki suka dare, wasu kuma suka tafi kallo.Baba ya riƙo hannun jauhar, da take ta uban kuka, kamar shi ma zai fashe da kuka ya ce “Fatima, na yi miki laifi, ban san yaya aka yi wasu abubuwan suka faru ba, dan Allah ki yafe mini, in sha Allah ba zaki wulaƙanta ba, zaki yi alfahari da hakan, na san na daɗe ina zaluntar rayuwarki, ina cutar da ke, dan Allah ki yafewa baba jauhar, kar ki yi fushi da ni, in sha Allah sai auren nan ya zame miki alkhairi”Ta share hawayenta ta jinjina masa kai ta ce “In sha Allah Baba””Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka ya kare ki daga dukkanin sharri da abun ƙi, Allah ya kula mini da ke a duk in da ki ke.Na san dama ke mai haƙuri ce, zaki ci riba in sha Allah” ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake ƙoƙarin ciwota.Ba a rabu da bukar ba an haifi habu, ta san wannan auren wani sabon ƙalubalen ne a rayuwarta.Ƙawayenta tuni suka gudu gida, ‘yan biki ma duk sun watse, ta samu wuri ta ƙule a ɗakinta, ta din ga kuka, tana neman agajin Ubangiji.Kwatsam! Yaran madaki suma suka taho layin, da niyyar tarwatsa yaran Aminu, dan kuwa ba sa jituwar da za su bari su shigo musu layi, su yi musu wannan budurin.Ba a jiyo komai, sai karafkiyar makamai, da zage-zage tamkar ana yaƙi.Suna daga cikin gidan, suka jiyo ana cewa tun da aka aurar da ƴar gidan ga maƙiyinsu, idan ta bar unguwar ta bar ta kenan, idan suka kuma ganin ta, sai sun sassarata.Mama ta ce “Zakiyya, kin ga wata tijara, ni fa hankalina ya tashi, ji kamar ana yaƙi”.”To ke ina ruwanki, da an kaita ba shikenan ba, can su je su ƙarata ba”Suna cikin maganar, sai ga gwangwanin tiya gas, a tsakiyar cikin gidan ƴan sanda sun sake dira, su tarwatsa su.Jauhar ta ƙara takurewa tana kuka, saboda tsananin tsoro da tashin hankali, dan a kunnenta ta ji ana cewa, idan aka ƙara ganinta a unguwar ma, sai an sassarata.Unguwar ba ta yi dai-dai ba, sai bayan sallar la’asar, hatta sallar la’asar a gida aka yi ta a unguwar, saboda tashin hankali.Bayan Baba ya yi sallar la’asar, ya kira mama ya ce, ya shirya masa jauhar, ya kaita da kansa, tun kan yaran nan marasa ji su ce za su yi mata illa.Idanun jauhar duk sun kumbura, sun jawur saboda azabar kukan da ta sha.Mama tana dariya take cewa “Haba Jauhar, kowa da haka yake kafa nasa iyalin, da haka kowa ya saba”Jauhar ta kalli mama, iya wannan tashin hankalin bai isa ya sanya su gane sun jefa rayuwarta a garari ba, amma take yi mata wannan surutan? Haka ta yi alwala ta yi sallar la’asar, sai dai ta kasa addu’a ma.Ko kaya ba ta canza ba, mama ta ɗaukko mayafi, ta ce tare za su kaita ɗakin miji.Sun fito waje, Saifu ya kawo kai, yayi turus ya ce “Baba, yanzu wannan tashin hankalin da aka yi a unguwar nan, duk a kan auren nan, bai sanya ka saduda ba, ka haƙura? Baba ya yi masa shiru, ya yi gaba hannunsa riƙe da na jauhar, ya buɗe mata mota ta shiga baya, suka ja suka tafi.A can suka tarar da wasu daga danginsu Al’amin, a gidan suka din ga rangaɗa guɗa, da aka ce an kawo amarya, dan sun baro can gidan su Al’amin, a kan Abbu zai aika da motocin ɗaukko amarya, sai dai suna ganin Baba suka nutsu suka yi shiru.Har kan gado ya kaita ya zaunar da ita, ya riƙe hannunta, ya din ga yi mata addu’a, sannan ya sunkuya ya yi ƙasa da murya ya din ga yi mata nasiha, yana yi tana kuka, sai da ya gama ya din ga saka mata albarka ya ce mama ta wuce su tafi.Angon kuwa yana can dabar su, ban da bushe-bushen sigari, babu abun da yake yi, hatta dambarwar da aka yi a gidan su amaryar bai sani ba, shi dai ya san Walid ya ce za su gayyato ‘yan gangi da ‘yan tauri, ayi nishaɗi.Bai ma san a ina aka ya ba, balle ya san abun da ya faru.Sai wajen ƙarfe takwas na dare, Walid ya dawo, ya din ga ba shi labarin, abubuwan da suka faru, da yadda suka yi da ‘yan sanda. A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar yana zuba, yana bawa Al’amin labari, amma bai tanka ba.Ya gaji ya ce “Maza, ka tashi mu shirya, mu raka ka gidan amarya”.Sai a yanzu ya ɗago ya kalleshi, amma ya yi tsaki ya koma ya kashingiɗa.Walid ya ce “Wallahi ba ka isa ba, wai so ka ke sai Abbu ya yi fushi da kai? Dama na haɗa maka kayanka jiya, yau sai ka bar gidan nan, kai Allah ya ɗaga darajar ka, kana wasa da damar ka” walid ya cigaba da mita, yana ƙara haɗawa Al’amin kayansa a ghana must go, da masu dauɗa, da wankakku, har da takalma da brush, haka ya din ga danna su.’yan uwan su Al’amin, babu yadda ba su yi ba, su ga fuskarta, amma fafur ta ƙi, ta din ga ƙudundunewa, suna nan tare da ita har tara na dare, suka gaji ga dare, masu zuwa ganin gida, duk suka gama, suka din ga tafiya, har ya rage saura itakaɗai aka bari.Nan hankalinta ya fara tashi, daga ita sai farar fitila mai batir, tana ta addu’a a cikin zuciyarta cike da fargaba da tsoro. Tana ta tunanin kar ‘yan daba su lallaɓo su zo su kasheta.Ta gaji da zaman wuri ɗaya, ta ga ledar pure water, a ajiye a falo, da ‘yan ganin gida suka zo da ita, ta ɗauka ta yi alwala, ta yi sallolin da suke kanta, ta zauna zaman dirshen tana tuna ƙalubalen rayuwa da ta haɗu da su kashi-kashi yanzu kuma ga ta kuma a wani mataki, mai hatsarin gaske.Har bayan sha ɗayan dare, sai itakaɗai a gidan.Fargaba da tsoron da take ciki, ya ninku a zuciyarta. Kasancewar bacci ɓarawo ne, haka ya yi awon gaba da ita daga nan in da take a zaune kusa da gado.Sai dai ba ta san adadin lokacin da ta shafe tana baccin ba, ta farka a razane, taga hasken wutar lantarki an kawo wuta. Ji ta yi kamar motsi a falon, ta lallaɓa ta leƙa cikin tsoro da tashin hankali bakinta ɗauke da addu’a.Wani dogon mutum ta gani a kwance a kan doguwar kujera, ya juya bayansa, ya duƙunƙune da babbar riga, da alama sauro ne ya dame shi, ya lulluɓa.Gabanta ya faɗi, ta koma ta zauna tana tunanin, wannan shi ne angon ko kuwa? Iya ƙoƙarinta ta dage kar ta kuma komawa bacci, saboda tsoron da take ciki.Al’amin kuwa, Walid ne ya taso shi a gaba, ya kai shi har gidan, daga shi sai shi, da ƙullin kayansa a ghana must go wajen sha ɗaya da rabi na dare.Suna tafe yana lallaɓa shi, sai da ya tabbatar ya shiga, sannan ya tafi.Ya shiga yana ƙarewa gidan kallo, shi dai ya san gidan kango ne, amma yadda aka jera masa kaya, yayi kyau.Yana shiga falon, bai bi ta kan ina amaryar take ba, ya tuntsurar da ƙullin kayansa ya haye kujera ya mimmiƙe kamar gawar sababi.An fara kiraye-kirayen sallar asuba, ta shiga banɗakin cikin ɗakin, tayi alwala ta din ga nafilfili, har aka yi sallar asuba.Bayan ta idar tana cikin azkar, wani irin nannauyan bacci, ya kwashe ta a wurin.Sai da gari ya yi haske, sannan ta farka, ta tashi tana salati, ta tashi tana ƙarewa ɗakin kallo. Yayi kyau sosai da sosai, duk ko fenti babu amma furnitures ɗin sun yi kyau.Ta fita falon gabanta na faɗuwa, domin gaida mai gidan da no nemanta bai yi ba, sai dai ba ta gan shi ba, ta leƙa ɗaya ɗakin, amma baya nan, sai ghana must go a falo.Ta fito tana ta lelleƙa gidan, abun ya burgeta, duk da ba ƙerarren gida bane, amma ta ji daɗin cewar gidanta ne ita ke da iko da shi, amma da ta tuna haryanzu ba ta yi ido huɗu da angon ba, sai gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shi ma auren dolen aka yi masa da ita.Tunawa ta yi, da ‘yan dabar Unguwar su, sun ce idan suka kuma ganinta a unguwar su, sai sun sassarata. Gaba ɗaya ranta ya ƙara dugunzuma.Ta zauna shiru a falo, tana ta jira, ko wani zai zo mata daga gida, amma shiru babu wanda ta gani, ga yunwa tana ji, dan wunin jiya ba abun da ta ci, gashi ta kwana ta wayi gari ba ta saka komai a cikinta ba.Can kuwa, Rahila kuwa kamar ta taka rawa, ta rabu da ƙaya, Aminu ya bar mata gida, ta ƙara sakewa da ita da yaranta yadda take so, fargabar ta zata ragu sosai da sosai, ta san yanzu dole zai tattara ya bar unguwar ya ƙara gaba.Dangin mahaifiyar Aminu da suka zo, daga can ƙauyen tofa, ta din ga wulaƙanta su, dan sai da ta yi wa Abbu masifar dan me za a gayyato su, sai dai a hakan gudunmuwar dubu ɗari biyu suka bawa Abbu na auren.Ban da uban kayan abinci da suka taho da shi, suka ce a ƙara a kan na biki. Sai dai har suka yi kwana biyun, ko sau ɗaya ba su ga Al’amin ba, sai kwasar takaicin rahila, yadda take wulaƙanta su, tare da aibata shi, tana an mutu an bar mata riƙon masifa da tsiya.Washegari da safe, waɗanda ba su je ganin gidan ba, suka ce za su je su ga gidansa, daga nan za su wuce su koma tofa. Da Abbu suka yi sallama, Rahila kuwa ko kallo ba su isheta ba.Har wajen sha ɗaya da rabi na safe, jauhar na zaune na rarraba ido, ta ji sallma a tsakar gidan.Amsawa tayi, tana jiran ƙarasowar masu sallamar.Mata ne wasu ‘yan dattijai, da matasan ‘yan mata.Jauhar ta karɓe su hannu bibbiyu, suka shigo falon suka zazzauna, hannunsu da kaya.Suka gaisa da jauhar, ɗaya daga cikinsu ta ce “Tubarkallah, Aminullahi ya mori ‘yar kyakykyawar yarinya Tubarkallah, ya sunanki?”Jin abun da suka ce, ya sanya ta gane ‘yan uwansa ne, ta ce “Jauhar”Suka din ga maimaita sunan nata, suna cewa sunanta na ‘yan birni.”Ina Aminullahin ne? Tun da mu ka zo, bamu ganshi ba, gashi daga nan can gida zamu koma” cewat wata dattijuwar.Jauhar ta ce “Ya fita””Ohh, ji soko, daga kawo masa amaryar jiya, har ya saka ƙafa ya fice, to Allah ya kyauta. Kin ganni ni kakarsa ce, ga yayar gyatuma tasa, nan duk ‘yan uwan mahaifiyarsa ne, amma ba ya zuwa in da muke. Dan Allah kya ɗan din ga saita shi a hanya, ki yi ta haƙuri kin ji, Allah ya baku zaman lafiya”Kunya ta saka jauhar kasa amsa musu.Suka yi ta yi mata hira, amma ta kasa amsa musu, saboda nauyinsu da ta din ga ji, sai dai kakartasa mace ce mai barkwanci, suka ba ta kayan da suka zo da su, su tsintsiyar laushi da ta kwakwa, kaskon turaren wuta, kayan miya har da kuɗi.Jauhar ta yi tayi musu godiya, sai dai ranta duk babu daɗi, ga baƙi amma babu abun da za ta basu.Zuwa azahar, suka yi mata sallama suka tafi.Har la’asar babu wanda ya sake zuwa, ta ji babu daɗi sosai, rashin ganin wani daga gidansu ko mutum ɗaya.Yaran maƙwabta suka ɗan shisshigo mata, shigowar ta su tayi mata daɗi, ta basu kuɗi, ta ce su sayo musu buredi.Suka sayo, suka zauna, suka ci tare da su, ta ajiye wani da niyyar idan mai gidan ya zo ta bashi.Mama kuwa bayan sun koma gida daga kai jauhar, duk ‘yan biki sun watse, kowa tayi ta kanta.Suka ƙule a ɗaki ita da zakiyya ta ce “Zakiyya duk da gidan yarinyar nan babu gyara, amma yayi kyau sosai da sosai””Eh ai hakan yayi, ma rage wani surutun, har ku ka taho kuwa kun ganshi ya je gidan shi angon?”Mama ta ce “Ina fa, itakaɗai muka baro, sai wasu ‘yan uwan babarsa, su ma na san ba zasu jima ba zasu tafi ba. Nifa sunansa kawai nake ji, ban taɓa ganin sa ba”.”Zaki ganshi ne, ba dai ya zama sirikinku ba? Ni na san shi, amma lokacin yana yaro, ai kin san daga baya suka dawo ƙofar na’isa da ba a nan suke ba, ni tsoro nake ji ma kar yaran nan su cigaba da kawo mana farmaki”Mama ta ce “Babu abun da za su dawo su yi mana, mun yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda, yanzu menene abun yi?””Abun yi, shi ne mu jira dawowar wannan Alhajin, mu ga yadda za a ɓullowa lamarin ya haƙura gaba ɗaya da batun ta””Haka ne, to Allah ya dawo da shi lafiya, sai ayi ta ta ƙare, jauhar dai an aurar da ita, sai mu jira mu ga yaya zai kasance da namu ‘ya’yan.Gidan jauhar magariba na yi, yara suka watse suka bar ta itakaɗai kamar tsohuwar mayya. Sai fitila ta kunna, ta saka mayafinta ta din ga korra sauro daga ɗakunan, saboda yadda suke ambaliya kamar a barikin su.Ta rurrufe ko ina, tana jiran ta ga ta ina ango zai shigo, amma shiru.Har bacci ya kuma cin ƙarfinta ya kwashe ta.Wunin ranar kuwa, Al’amin zarya ya din ga yi, sai da aka sakar masa yaransa da aka kama a unguwar su madaki, har suka sanar masa iƙrarin da ‘yan unguwar da suka yi, na idan suka kuma ganinta a unguwar sai sun sassarata.A ransa ya ce Allah ya ƙara, maganinsu kenan, da suka ga babu wanda ya dace su bawa ‘yar su sai shi.Tare da su ya wuni yana shaye-shaye, Walid ya na son ya yi masa magana, amma ya san yana yi za su yi faɗa, dan haka sai dare ya sake lallaɓa shi, daga can unguwar ya goya shi a babur ya kai shi gidansa na ɗorayi chiranci.Sai dai kamar jiya, kafin gari ya yi haske, ya sake barin gidan, gashi ko brush ba ta da shi, ba ta da kayan girki, haka ta kuskure baki ta cinye biredin jiya, gashi ba ta son cigaba da taɓa kuɗin da aka bata, yakamata ta nuna masa kayan da aka bata, saboda ‘yan uwan sa ne suka bata.Ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana tunanin yanzu haka za ta rayu, wanda ya ajiye ta baya ko ƙaunar ganinta, kwana na biyu kenan haryanzu ba ta ga kalarsa ba ma.Tana son yin wanka da sauran buƙatu, amma ba hali, babu ruwa, ga rijiya a gidan amma babu guga, babu sauran kayan masarufi.Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ya dawo da ita hayyacinta, ta tashi ta ɗaukko mayafi ta saka, ta buɗe a hankali.Saifu ta gani a tsaye, hannunsa riƙe da kaya.Ta washe baki ta ce “Yaya saifu” yayi murmushi ya ce “Na’am Waliyiyya”Ta bashi hanya ta ce ya shigo, ta karɓi kayan hannunsa, suka shiga har falo.Ya kalleta ya ce “Yaya babu wata matsala dai ko?”Ta girgiza kai ta ce “Babu””Ina mijin naki yake?””Baya nan, ya su baba? Ya su mama?””Suna nan ƙalau, gida yaƙi kyau ba kya nan, duk ‘yan matan nan an rasa wadda za ta yi aikin da ki ke yi” tayi shiru tana murmushi.”Ga sauran kayanki na kawo miki, na harhaɗo da na ɗakinki duk na kawo miki, muddin ki ga ya yi miki wani abu da baki gamsu ba, ki gudo gida kin ji ko?” Ta jinjina masa kai alamar to.Ya ce “Kina buƙatar wani abun ne?”Ta ce “A’a”Ya miƙe ya ce “Na san ba zaki faɗa ba ai” ya shiga kitchen ɗin ta yana dubawa, babu alamar an dafa wani abu.Ya ɗauki gas ɗin ta, ya fita da shi, ya yo mata refilling, ya yi mata sayayyar kayan shayi da ‘yan kayan abinci, ya dawo ya kawo mata.Ya ce “Ki yi haƙuri jauhar, bani da kuɗi, amma zan sake dawowa in sha Allah, kar ki yadda da wani haƙuri, na san zaman aure haƙuri ne, amma kar ki zauna ana zaluntarki, ko ya ce zai dake ki, zan sake dawowa in sha Allah kin ji ko” ta ɗaga masa kai alamar eh, ya sayo mata guga, ya janyo mata ruwa ya tara mata, ta din ga yi masa godiya suka yi sallama.Bayan tafiyar sa, tayi wanka ta canza kaya, yaran maƙwabtanta da suka shgo, ta dafa musu taliya, suka ci ba ta gaza ba, ta ɗebarwa maigidan nasa ta ajiye.Sai dai yaran da wuri suka tafi yau, ta samu wuri tana wanke-wanke, ta ji kamar an wuce ta bayanta.Tashi ta yi a firgice, tana addu’a da tunanin ko gane-gane ta fara yi.Sai dai ta ga takalmi a ƙofar falon, kasancewar gidan akwai gate, kuma akwai ƙaramar ƙofa, ƙofar a buɗe take.Ta lallaɓa ta leƙa, ba ta ga kowa ba, ta shiga falon tana tambayar waye?.Fitowa ya yi daga ɗaya ɗakin, hannunsa riƙe da baƙar leda, kallo ɗaya ta yi masa ta gane shi, ƙwala ihu ta yi, ta ruga da gudu ɗakin da gadonta yake, ta rufe ƙofar ɗakin.
Ayshercool 08081012143
