Uncategorized

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 52 Complete Novel

   

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

  FIFTY-TWO📍

     Murza idonsa Deen yayi dan ya tabbatar su din yake gani, daidai lokacin baby tee data juyo zata karbi jakarta hannun khaleel idonta ya sauka akan Deen, ai ba shiri ta kwasa a guje tayi ciki, tana shiga tayi sama a guje bata tsaya ko ina ba sai bedroom din mami, mami na zaune kawai taji kamar an jeho mutum akanta, kankameta baby tee tayi cikin tashin hankali tace;

     “Ki rufe kofar mami, dan Allah ki rufe pleassssse”…..

Girgizata mami tayi ganin duk ta rude tace;

     “Nitsu daughter, nitsu ki gayamin abinda ke faruwa, babu kowa a bakin kofar, menene?”….

     “Mami dan Allah ki rufe, ki rufe kawaiiiiii”….

Da sauri Deen ya karaso gurin da khaleel yake a tsaye kamar gunki ya kasa gane meke faruwa, chakumo wuyar rigarshi Deen yayi cikin matsanaicin bacin rai yace;

     “Daga gidan uban wa kuke?!”….

Sakin baki khaleel yayi yana kallonsa dan sam be gane abinda yake yiwa fada ba….

Kara shakeshi Deen yayi cikin hargowa ya sake fadin;

      “Nace daga gidan uban wa kuke! Ka tsaya kana kallo na kamar robot! Ina ka kaita tun dazu? Yaushe ka dauketa? Waya cire mata jacket din danasa mata? Answer me!!”….

A nitse khaleel da har lokacin be bar mamaki ba yace;

      “Bani na cire mata jacket ba sannan babu inda….”

Deen be jira jin karashan zancen ba tinda yace bashi ya cire jacket ba ya cillar dashi a kasa yabi bayanta dan dama ita yakeso ya hukunta din saboda da kafarta tafita taje ta sameshi ai……

Dakin Umm ya fara shiga ko sallama babu, Umm na zaune kan sallaya kawai taji an bankado kofa, dagowa tayi taga deen ne, tana ganinshi ta nuna masa kofa tace;

     “Out!”…..

Ko kulata beyiba ya hau dube dube, yana ganin be ganta ba ya fita, tabe baki umm tayi ta cigaba da abinda take……

Dakin mami yayi hango kofar a bude, yana shiga ko ya tarar da mami da baby tee rungume a jikinta sai cewa mami take ta tashi ta rufe kofa, ta saketa ta rufe kofan kuma taki sai kara kankameta take……

Wani irin ihu baby tee ta fasa tana fadin;

     “Mami kinga ya shigo ko, sai da nace ki rufe kofar, mami dukana zeyi”…..

Dago kai mami tayi taga deen yana nufosu fuskarnan ta hada ja tsabar bacin rai…..

      “Karka kuskura ka karaso!!!”….

Mami ta fada tana daka masa tsawa….

Ko jinta beyi ba ya cigaba da nufosu, hannunsa ya mika da niyar  chapkota tayi saurin juyar da mami ta koma daya gefenta, be fasa ba ya koma daya gefen, nan ma ta sake juyawa, haka suka dinga juye juye da mami suna zagayeta sai musu magana take sunki kulata, shi deen dama bayajin abinda take cewa abinda yasa a gaba kawai shine, ita kuma baby tee gani take idan ta tsaya kamata zeyi, gwara idan ya juyo ze chapkota sai yaji mami ce, shi kuma ya dage sai ya dankota, karshe dayaga bata mishi lokaci zatayi kawai ya hauro gadon, ganin haka ita kuma ta dira ta dayan gefen ta shige toilet a guje, zata sa key kenan kuma ya banko toilet din, ganin ba sarki sai Allah kawai ta shige cikin bath basin ta kunna ruwa sannan ta kwanta ruwan na sauka a jikinta gabadaya ta lumshe ido tana saddakarwa…..

Tsayuwa yayi akanta yana kallon yanda ruwan ke sauka a jikinta saidai sam yaki yarda ya kalleta yana jin yanda zuciyarsa ke tafarfasa har lokacin, saida ya bari ta nitse ruwan ya gama dukanta sannan ya zira hannu ya tsamota kamar kifi ya fito da ita, mami na zaune tayi tagumi abun duniya ya isheta na wannan masifa data kasa ganewa taga an fito da baby tee a jike ruwa sai diga yake a jikinta  tayi tsilli tsilli da ido kamar yaron da aka kama yana wasan ruwa, baki a sake mami tace;

     “Tsomata kayi a ruwa? Wani irin mugunta ne wannan bakada hankali ne deeni?”….

Daidai nan Umm data keta jin hayaniya daga daki ta shigo, kallonsu ta shigayi daya bayan daya tana mamakin me kuma ya faru, ga Deen rike da baby tee da take a jike jagap…… Dawo da kallonta kan mami tayi tace;

      “What’s going on here?”…..

Cikin jimami mami tace;

     “Wallahi bansani ba kawai gani nayi sunata guje guje suna zagayeni nayi magana sunki kulani”…..

Deen be sauke taba cikin fushi yace;

     “Wannan yarinyar bata da hankali, kunnen kashi gareta kuma wallahi sai na saita ta yau, daga yau bazata sake renawa wani hankali ba”….

     “Wani irin renewa wani hankali, kayi mana bayani mana sai wani surutan banza kake”….

Cewar mami rai a bace…..

Be bata amsa ba sai ma wata maganar daya sake sako musu da basu gane kanta ba….

     “Fisabilillahi sai ta cire jacket saboda batasan ciwon kanta ba? Toh in bata sani ba nina sani”….

Yana fadin haka ya nufi kofa, mami na ganin haka tayi nufi tareshi Umm tayi saurin kamo hannunta tace;

      “Barshi! Yayi mata duk abinda zeyi sun fi kusa!”……

Insisting mami tayi da fadin;

      “A’a kinsan fa saif ba hankaline dashi ba, karya cutar da ita”…..

     “Kome ya mata ai ya isa da ita, alamu sun nuna bata da gaskiya itama tinda ta kasa cewa komai”….

Ba karamin tashi hankalin baby tee yayi ba jin wannan magana ta Umm, yanzu su duk a tunaninsu rashin gaskiya ne ya hanata magana meanwhile ruwan daya cika cikinta ne yada ta kasa magana, tanajin dadi ta samu masu taimakonta shine za’ace ya tafi da ita, wato ya kasheta ma ba ruwansu, kawai ji tayi an wurgar da ita akan katifa sai a lokacin tagane duk maganar zucin da take sunma bar wajensu mami….. 

Bata kara dawowa hayyacinta ba saida taji ana rufe kofa, tanaji tana gani ya rufeta yayi tafiyarsa……

     Tinda ya tawo da ita yake tunani hukuncin daze mata ya wuce saidai duk abinda ya tunano sai yaga yayi kadan, hakan yasa ya yanke shawarar rufe ta a boys quarters har sai ya yanke hukuncin abinda ze mata, part dinsa ya koma yana jin yanda zuciya ke dibarsa daya koma ya kakkarya mata kasusuwa saidai sam hakan be masa ba dan yanaso yayi mata abinda har abada bazata manta ba yanda ko gate yace kar taje bazata jeba, sai kawai yayiwa kansa allurar bacci saboda ya dan samu relieve kafin anjima……

    Bayan sallahr isha mami  da abun ya dameta ganin har lokacin deen be dawo da baby tee ba ta ninke sallaya ta nufi dakin umm, akan sallaya ta sameta kamar yanda tayi tsammani, cike da damuwa tace;

      “Anya baza muje mu dubo halin da yarinyar nan take ciki ba? Hankalina ya kasa kwanciya wallahi”….

Murmushi umm tayi tace;

      “Karki damu, mu barshi muga gudun ruwanshi, I know why am saying this!”…..

     “Amma fa kinsan saif besan gatse ba karya cutar min da yarinya”….

     “Ni ko nasan be san gatse ba mami, so nake kawai inga karshen abinda ze iya mata tinda sun maida mana gida kamar wasu kaji, kullum cikin fada kamar wasu marasa hankali”….

     “To ai saif ne babban mara hankalin shida yake babba, ita baby tee meta sani”….

      “Karkiyi shedarta mami, idan bera na sata daddawa ma da warinta, amma na kusa kawo karshen komai”…..

     “Toh Allah ya kyauta yasa mu dace”…..

Numfasa umm tayi tace;  

     “Ameen, ni gwara ma ayi aurenta da khaleel din kowa ya huta”….

 Cikin jimami mami tace;

      “Amma bakya tunanin it’s too early? Ni dai nafiso ta kara sanin kanta sosai kafin ayi auren nan”…. 

     “Eh zan tafi da ita UK soon, I’ll take care of all that, ya zamana muna dawowa za’a daura auren”….. 

Cikin rashin jindadi mami tace;

     “Yanzu bazaki barmin ita ba dan Allah? Karatun nata fa? Kuma kinsan nafiki time, gwara ki barmin ita in koya mata duk abinda ya dace”….

     “Yes naso in bar miki ita sis, but from the look of things idan na bar miki ita taruwa zasuyi susa miki hawan jini, ni ko bazasu min  asarar yar uwa daya tilo ba”….

Murmushi mami tayi tace;

     “Sai in masa iyaka da zuwa gidannan dama gulma ce ta zaunar dashi, da ko kwana bayayi”…

    “Hmmmm”…

Kawai umm tace ta sako wata hirar daban…..

    Da farko baby tee bata damu ba dadi ma ta dinga ji ya tafi ya barta ita kadai ko banza ta huta da masifarsa, kawai saita fara rawar sanyi saboda jikekken kayan dake jikinta har lokacin, kallon dakin tayi ko Allah zesa taga abinda zata rufe jiki saidai babu komai a dakin illa katifa ko curtains na window babu, haka ta kankame jikinta tana rawar sanyi gwanin tausayi, tanajin kiran sallar magariba amma ba damar yi saboda babu sutura babu hijabi, a haka har wani baccin wahala ya kwasheta tana rawar dari, bata gane shayi ruwan bane saida ta farka gurin karfe tara taga ko ina dulum babu haske, ashe anyi disconnecting wutar part din saboda babu kowa a ciki, da lulebe ta karasa bakin kofa ta gwada budewa saidai ina deen ya riga ya garkame da mukulli, wani irin kukan nadama ta fashe sai ihun kiran sunansu take amma babu me jinta, sai sambatu take tana fadin:

         “Mami! Umm! Dan Allah kuzo ku taimakeni! Wayyo Allahna! Yaya saif na tuba dan Allah kayi hakuri bazan sake ba”….. 

Haka ta karaci kukanta da kiraye kirayen sunansu babu wanda yasan tanayi…. 

Karshe durkushewa tayi a kasa ta saki wani kuka me cin rai tana kara jin tsanar deen a ranta……. 

      Yanda Mami taga rana haka taga dare dan kwana tayi akan sallaya tana yi musu addu’ar shiriya, hakama umm batayi bacci ba itama kuma ba karamin dumawa tayi ba, duk yanda takesan nuna abun be dameta ba amma deep down ya bala’in damunta, saidai babban damuwarta shine rashin jituwarsu suna yan’uwa na kusa….

        Deen be tashi farkawa ba sai asuba, duk a tunaninsa befi yayi baccin two hours ba tinda ya saba yiwa kansa allura mara karfi irin wannan baya hour daya ma sai ya tashi, sai gashi ya share sama da hour takwas yana bacci, hakan kuma baya rasa nasaba da rashin baccin da be samu yayi ba a yawon nemansu, daya gansu ma still be wuta ba, shine allurar tasashi ya zarce, saidai wasai yake jinsa kamar be taba shiga damuwa ba……

Da sauri ya mike tuno da halin daya barta a ciki dukda tarin sallolin dake kansa dan yasan dole hankalinta ze tashi tinda babu connection a part din, be taba tinanin ze barta a ciki for two hours ba daya ajye mata spare key a dakin….. 

    Mukullin ya zira yana kokarin bude dakin gabansa sai faduwa yakeyi, murda kofar yayi yaji alamun mutum a bakin kofar, ahankali cikin cool voice irin na wanda ya tashi daga bacci yace;

        “Zahrah tashi in bude kofar”….

Shiru yaji bata motsa ba sai yayi tunanin bacci takeyi, sai ya hau tura kofar a hankali yana budeta kadan kadan yanda bazeyi hurting dinta ba….. 

Tsugunawa yayi a gabanta ya dora hannunsa a kasan hancinta bayan ya shigo ciki, ba karamin tashi hankalinsa yayi ba jin ko numfashi batayi ga jikinta yayi zafi kamar garwashi, rikicewa yayi ya shiga jijjigata yana fadin;

      “Dan Allah ki tashi zahrahta! I’m so sorry pls, wallahi bazan kara rufe ki ba, ki yafemin dan Allah!”….

Sai kuma ya ciccibeta yayi part dinsa da ita da sauri, yana zuwa ya kwantar da ita a bedroom dinsa, saurin dauko first aid box dinsa yayi tare  da ruwan roba, shafa mata yayi kusan sau bakwai amma ko motsi batayi ba, taba cikinta  yayi yajishi a cike, sai a lokacin ya tuna da ruwan da tasha a cikin jacuzzi, option daya kawai yake dashi shine ya mata mouth to mouth resuscitation ya bata oxygen, without second thought ya dago kanta gently ya dafe goshinta sannan yasa dayan hannunsa ya matse hancinta, numfashi ya sauke ya dora bakinsa akan nata softly, a hankali ya shiga wura mata iskar bakinsa yana kara tallafo kanta, sai da ya mata transfering enough oxygen kafin ya fara zuko nata numfashin, ba’ayi five minutes ba ta dan fara tari a cikin bakinsa, janye bakinsa yayi kadan sai kuma yaji ta dena tarin, bakinsa ya sake maidawa akan nata amma be matse mata hacin ba saima harshensa dayasa yana lashe lips dinta daya bushe, yafi 5mins yana haka kawai yaji tayi wani irin tari hade da zubo da ruwan datasha, sai jin ruwa kawai yayi a bakinsa, be damu ba ya dagota zaune yana mammatsa mata ciki har tagama zubo da ruwan…..

Bude jajayen idanunwanta tayi batareda tasan wanda ke kanta ba tace;

        “Yaya saif dan Allah kayi hakuri bazan sake ba”…

Rungumeta yayi cikin wani mugun tausayinta daya taso masa, da kuma jindadin yayan datace masa yace;

       “Nima bazan sake ba anty zahrah, kiyi hakuri na kulleki na tsawon wannan lokacin, it wasn’t intentional wallahi”…….

Zamewa tayi jin muryarsa wani haushinsa na taso masa, saidai batace komai ba dan bata shirya neman wata fitinar ba, saidai ta hada rai sosai…. 

Kamo hannunta yayi murya chan kasa yace;

      “Ina kika je kika barni a salon ina jiranki, sai fitowa nayi naga jacket din dana sa miki a yashe a kasa”….

Tarin karya ta hau yi, nan da nan ya rikice yayita mata sannu, karshe kuma ta mike tace mishi ita zata gurin su mami, cikin lallashi yace;

      “Dan Allah ki zauna inyi treating dinki kinga temperature dinki is still very hot”……

Kada kai tayi a shagwape tace;

      “Ni gaskiya bazan zauna ba, na fa warke”….

Murmushi yayi yace;

       “Alright baby girl, amma dan Allah karki fadawa umm da mami rufeki nayi”…. 

      “Toh me zance musu?”….

      “kice musu a bedroom din kasa kika kwana dama ban tafi dake ba” …

A hankali tace;

      “Toh”….

Cikin shakku yace;

      “Kin yarda kuwa?” ….

      “Eh!”…. 

Ta bashi amsa approvingly …

 Murmushi yayi ya ja hancinta yace;

       “Thank you beautiful! Muje in rakaki”…..

Fita sukayi ya rakata har part din su mami, luckily for him babu kowa a parlon, bedroom din kasa ya kaita ya fito da allurar daya tawo dashi dan ya mata saboda hankalinsa be kwanta da zafin jikinta ba amma kememe ta hana, karshe ma cewa tayi idan ya mata allura saita fadawa umm da mami rufeta yayi ta kwana a boys quarters, yanaji yana gani ya tafi ya barta bayan ya hadata da Allah da annabi tashiga tayi wanka ta chanja kaya karsu umm su ganta da wannan kayan data jike dasu tun jiya, saida yaga tashiga toilet sannan ya fita…….. 

Sai da ta bada tazarar  10 minutes sannan ta fito daga toilet din batareda ko ruwa tasa a hannunta ba, tsaki taja tana ayyana yanda ya rena mata hankali, wai tace musu babu abinda ya mata saboda gata shashasha, duk wahalar datasha sai ya tafi a dadin baki, harda wani ce mata anty zahrah na munafurci, besan kallonsa kawai takeyi ba, sama ta haura ta zauna a daidai passage din da dakuna suke ta fasa wani uban ihu tana fashewa da kuka yanda tasan mami da umm zasu jita, ba’ayi 1min ba ko suka fito da sauri, rige rigen isa gareta sukayi ko kafin su karasa tayi suman karya, da sauri mami ta dauko ruwa suka shafa mata, bude ido tayi jikinta na rawa dama kuma jikinta da zafi, sai abun ya daga musu hankali, dagota mami tayi sai salati take tana tambayarta meya mata…..

        “Daureni yayi a boys quarters ya dukeni sannan ya tafi ya barni a ciki sai yanzu ya budeni”…..

Ta fada tana shesshekar kuka…… 

Ba mami kadai ba har umm da take kare deen sai da abun ya daketa, ta kumayi dana sanin kin bari suje..

Kwafa mami tayi tace;

      “Karki damu wallahi sai na rama miki, he’ll surely pay for it!”…..

Sannan ta taimaka mata ta shiga da ita dakinta, towel ta bata tace tashiga tayi wanka, ta juyo ta kalli umm cikin hada fuska tace;

       “Yanzu kinga gudun ruwan nasa ai ko? Zaki bata taimako irin naku na likitoci ko shima bazaki iya ba in dauketa in tafi da ita asibiti dan yanzu na dena jira”…..

Girgiza kai kawai umm tayi ta fita daga dakin, dawowa tayi wata maid biye da ita hannunta dauke da tea me kauri da umm tasa a hado, karba umm tayi ta ajye akan bedside drawer tana jiran baby tee ta idar da sallah ta bata tasha ta mata allura….. 

Tana idarwa ta mika mata shayin har lokacin batace komai ba dan dagaske she was speechless, ba musu baby tee ta karba tasha dan duk kin ta da abinci ranar saida taji yunwar wahala, da hannun ta mata alamun tazo bayan ta gama shan tea din, zaunar da ita a gefenta tayi ta dora hannu akan goshinta, mai da hannu tayi wuyarta nan ma taji jikinta da wani mugun zafi, batace komai ba ta mata allura, ba musu ta tsaya saboda tasan hannun umm bashida zafi, suna zaune ita da mami sun yi shiru har bacci ya kwashe baby tee, sai a lokacin umm ta tashi ta koma kusa da mami, hannunta ta ruko tana murmushi tace;

        “My sweet yaya!”….

    “Ba wani your sweet yaya kawai kinsa ya wahalar min da yarinya”….. 

Murmushi tayi tace;

      “Allah yasa karshen wahalarta kenan! Allah yasa ta nitsu su dena rigima daga wannan”….

Wani irin kallo mami ta mata tace;

        “Kina nufin yaci bulus kenan? Wato itace ma me lefi, toh be isa ba wallahi”…..  

       “Bance miki yaci bulus ba, kin fa san halina yaya, everyone will be served right!”…..

     “Koma dai menene zan hukuntasa personally wallahi”…..

Umm zatayi magana kenan kiran abby ya shigo wayarta, dauka tayi suka gaisa cikin mutunci ya mata bayanin yanata kiran baby tee tun bayan tabar gurinsa jiya baya samunta, ce masa kawai tayi bata jindadi yanzu ma ta gama mata allura, har yace ko a daga test din da zasu ita da khaleel tace kawai ya aiko a karbi blood sample dinta, gwara ma suyi abun isu isu basai anje da yaran ba, sosai yaji dadin shawararta dan dama bayaso ayi a gaban deen dan yaga alamun yanaso ya kawo musu cikas, sallama sukayi tace ya aiko yanzu ma…..

Tana sauke wayar ta dauko syringe, needle da test tube tayi taking blood sample na baby tee ta ajye….

Ba’a jima ba abby ya aiko ta bayar aka kai masa, sake kiranta yayi ya mata bayanin yasa khaleel ya kawo nashi shima har an kaiwa personal Doctor dinsa ya fara yin tests din……. 

         Sai gurin sha biyun rana ta farka, wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga na atamfa dataga an ajye akan bedside drawer ta kuma san dan ita aka ajye, har mamakin wanda yake siyo mata kaya a gidan take dan saidai kawai taga an bata kaya tasa, har tazo bakin kofa taga wani note an turashi jikin kofar, zarowa tayi ta bude ta karanta content din……

     “Make sure you eat before you come downstairs! I love you my angel!” …..

Murmushi tayi tana tunanin wanda ya rubuta tsakanin mami da umm, komawa tayi ta zauna akan couch tashiga bin abinci da aka jera akan center table da kallo, bubbudesu tayi taci wanda zata iya ci sannan ta sauka kasa……..

   Tun kafin ta karasa cikin parlourn  takejin muryoyi kala kala, tana zuwa taga ashe eesha da billy ne sukazo, da sauri suka taso suka rungumeta suna hada baki gurin fadin;

      “Ya jiki!” ….

Meaning su umm sun fada musu bata da lafiya……

     “Da sauki”….

Ta basu amsa ba yabo ba fallasa tana zama …..

Sata a tsakiya sukayi, eesha ta kalli umm tace;

     “Wallahi kuna kama sosai umm”….

Murmushi umm tayi tace;

    “Allah ko?”…..

Dariya eesha tayi tace;

      “Sosai ma, amma da yaya saif ta fara min kama farko dana fara ganinta”…..

      “Eh suna dibar kama ai”….

Umm ta bata amsa……

Turo baki baby tee tayi tace; 

      “Ni dai bana kama da wanchan mutumin”….

Zaro ido eesha tayi tace;

       “Haba kiji dadi mana kina kama dashi bakiga yanada kyau sosai ba”…. 

Tashi umm da mami sukayi dan su basu guri suyi hirarsu….

Bata rai baby tee tayi tace;

      “Bawani kyan dayake dashi, ke baki ma san menene kyau ba kawai zakizo kina hadani dashi, wallahi kin cuceni”……

Wannan magana a daidai kunnen deen dayake shigowa a lokacin….

Kallonta billy tayi tana jin kamar ta hadiyeta, har wani lumshe ido take jin yanda sautin zazzakar muryar baby tee ze sauka a kunnenta, a take taji duk wani gabobi na jikinta sun motsa, babu abinda take bukata illa kasancewa da ita kota wani hali a kuma lokacin……

Deen har zeyi magana kawai ya bita da harara dan bayasan wani abu ya hadasu yau tace zata tona masa asiri….. 

Da sauri eesha da billy suka hau gaishesa, be kulasu ba yacewa eesha;

      “Taso muje, ina son magana dake!”…..

Jiki na rawa eesha ta tabi bayanshi , garden suka je, ya nuna mata guri yace;

      “Zauna!”…..

Suna fita baby tee taja wani tsaki ta kalli billy tace;

      “Ko wani irin magana ne da ba za’a iyayi a gabanmu ba?”…..

Murmushin yake billy tayi tana danne yanayin da take ciki tace;

      “Ke kuwa ai dole su kebe a matsayinsu na masoya, nima gani nida ke a kebe” …

Bata gane abinda take nufi ba tace;

      “Koda yake hakane, nima in zamuyi zance da darling khal na fiso inga mun kebe”….. 

        “Toh kingani? Dan Allah kuna da paracetamol ki dauko min? Kaina ke dan min ciwo”…..

Mikewa tayi tace;

      “Eh ba za’a rasa ba, bari na tambayar miki umm” …

        “Thank you love”….

Billy ta fada tana bin bayanta da kallo har wani hadiyar yawu take……

Tana ganin ta haura sama tayi saurin bude jakarta ta zaro wani magani ta zuba a kofi biyu sannan ta zuba exotic drink din da aka kawo musu a ciki, murmushin farin ciki tayi tana godewa Allah data tawo da maganin, bata saba fita dashi ba ashe alheri ne ke kiranta ta tawo dashi yau…..

Dawow baby tee tayi hannunta dauke da paracetamol harda tawo da wani ruwan, mika mata tayi ta karba ta shanye kamar dagaske kan nata na ciwo …….

Batafi five minutes dasha ba tace;

       “Kinga har kan nawa ya dena ciwo”….

Gyada mata kai kawai baby tee tayi…..

Dauko juice din tayi ta mikawa baby tee cup daya tace;

      “Gashi nan na zuba mana kisha”…..

Girgiza kai tayi tace;

      “No ki barma kawarki in tazo sai tasha”…..

         “Ai ta riga tasha, wannan mu na zubawa munasha muna hirarmu tinda sun tafi sun barmu”…… 

      “Hakane!”….

Ta fada tana karban cup din, kaiwa bakinta tayi ta fara sha a hankali, zuka take tana tuno da rayuwarta na codeine, abun mamaki kwana biyu ko sha’awar sha batayi, harta shanye bata sani ba, ajye kofinta keda wuya taji kanta na sara mata ga wani irin yaji yaji da takeji a idonta……

Kallonta billy tayi tayi murmushi tace;

        “Ko zaki iya kaini bedroom a kasan nan, skirt dina zan gyara”…..

Cikin wani irin yanayi me cike da kasala da weakness tace;

      “Mu je”……

Tafiya take a hankali billy na biye da ita har suka karasa dakin, ita ta fara shiga sannan billy ta shiga, billy na shiga ta sawa dakin key sannan ta hankadata kan gado tabi bayanta….

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button