Fentin Zina Page 14 Hausa Novel
****Da madaukakin mamaki inna da fateema suka bita da kallo, inna ta tabe baki tace Allah ya baki lafiya.Fateema bata amsa ba ta bi addanta daki ta sameta zaune gefen gado ta hade kai da gwiwa tana risgar kuka.Adda wai meke faruwa ne? Duk menene wannan? Na kasa gane komai, meya kawo wannan shirgegen mayaudarin gidan mu? Kuma……Ta hadiye maganar sakamakon wani irin kallo da Ameenan ta mata da idanunta da suka rine tace cikin muryar dake nuna tasha kuka, kada ki kara danganta shi da mayaudari domin shi din wanda nake sone kuma zan aura.Adda kina Lafiya kuwa? Ko dai wani abu na damun ki? Dan Allah ki daina irin wannan maganar baki ji me inna tace bane? So kike ranta ya baci akan ki kenan.Ta zauna a gefenta ta cigaba da cewa, ki bari abi komai a hankali kada kiyi gaggawar yanke hukunci.Girgiza kai Ameena tayi hawaye na zuba daga idanunta tace fateema baza ki fahimci daci da kunar da nike ji bane a cikin raina, soyayya gaskiyace fateema mutuwa zanyi idan ba’a aura mun Ahmad ba, shi kadai nake so idan na rasa shi sai dai in kare rayuwata ba tare da aure ba, bazan iya auren wanin shi ba ki taya ni rokon su inna da baba malam kada su hana mun auren shi.Aiko sai dai ki mutu babu aure tunda haka kika zaba, inna ta fada tana shigowa dakin don duk abunda suke cewa tana ji, tsayawa tayi a kanta tace ashe baki da hankali Ameenatu? Har yaushe zakiyi wannan sakarcin? Wato idan kika rasa shi baza kiyi aure ba shi ga dan gwal ko? Yaron da kowa ya shaida takadari ne manemin mata iyayensa sun daure masa gindi yana abunda yaga dama irin shi zaki nacewa? Ina hankalin ki ya tafi? Toh bari kiji idan na kara jin kin ambaci sunansa cikin gidan nan zanyi mugun saba miki wawuyar yarinya kawai.Shiru dukkansu sukayi daga Ameena har fateema saida inna ta karaci fadanta ta fita Fateema ta hau sharewa addanta hawaye tana fadin, kinga abunda nike gudar miki daga gurin inna ko? Kinsan ta bata iya fushi ba dan Allah ki bar kukan haka nan kada kan ki yayi ciwo kinji.Batace komai ba ta kwanta yayinda soyayyar Ahmad ke dada ruruwa a cikin zuciyarta tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba.Washe gari da rana wani yaro ya shigo gidan da sallama, aka amsa masa fateema ce da Ameena inna ta tafi makwabta suna, yaron yace wai ana sallama da Ameena.Wuf Ameena ta tashi dama bata rabo da hijabi a cikin gidan don haka tayi gaba ko bawa yaron amsa bata yi ba.Yana ganinta ya saki ajiyar zuciya tace dashi dawo daga nan ta nuna masa zauren ya shigo fateema ta taho ta dube shi tace.Dan Allah ka rabu da ita kada ka ja mata samun matsala a gida, ka tafi yanzu dan Allah kuma kada ka sake zuwa domin manufar ka ta riga ta bayyana mana.Fateema…..Ameena ta kira sunanta a kausashe, kallonta fateeman tayi.Zo ki wuce ki koma ciki bana son jaraba kada ki sake mun katsalandan a cikin al’amurana.Wucewa Fateeman tayi ta koma ciki tana mamakin addanta a kasan ranta sai take jin kamar an canja musu ita ne.Ameena ta maida kallonta kan Ahmad tace kayi hakuri da abunda tayi kada ranka ya baci.Murmushi ya saki yace babu komai ban dauka da zafi ba saidai na tsorata sannan naji fargaba ta shigeni.Ta dan zaro ido waje tace fargaba da tsoro kuma? Na meye toh?Hum Ameena da zaki taba zuciyata kiji yadda take bugawa da karfi tana neman fasa kirjina ta fito waje duk akan soyayyarki da zaki san girman abunda nike fuskanta ina tsoron abunda zai rabani dake Ameena, ina fargabar rasaki.Ahmad! Kada ka damu babu abunda zai rabani da kai said mutuwa, ita kadaice zata daukeni ta dakatar da aure tsakani na da kai amma sabanin ita ka kwantar da hankalin ka Ameena tana son ka tana matukar sonka bazata bari wani abu ya raba ku ba.Ki rike mun alkawari, sannan ki unblocking dina a wayarki in dinga jin muryar ki data zame mun tamkar sinadirin ji.Shikenan zanyi yadda kace.Ok ni zan tafi kada inyi dare sai munyi waya ko.Hi nake kamar kada ka tafi, zan fiso muyi ta tsayuwa a haka muna kallon juna ba tare da wani abu ya gitta ba.Turo kofar akayi a razane dukkansu suka kalli kofar.Inna ce ta shigo batayi wata wata ba ta isa gun Ameena ta tsinka mata mari bata bari ta dawo hayyacinta ba ta kara daura mata wani marin sannan ta juyo kan Ahmad tace ka bace mun daga nan kada kuma na sake ganin kafar ka a gidan nan.Sum sum yaja kafar shi ya fita ita kuma ta tusa keyar Ameena zuwa cikin gida ta dau wani itace ta hau bugunta dashi, fateema tazo tana son tarewa inna tace cikin tsananin fushi idan kika kuskura kika zo nan saina hada duka na fasa jikunan ku.Komawa tayi ta zauna a dakalin kofar dakin su tana kuka.Ita kam Ameena dake zuciyarta ta riga ta bushe ta kangare a shirye take data dauki ko wani irin hukunci zasu yi mata muddin daga karshe zasu gaji su aura mata Ahmad, ko digon hawaye babu a fuskarta wannan karon kamar ba ita inna ke bugu ba saida inna ta gaji don kanta ta kyale ta tana sauke numfashi.Ameena tama kasa tashi don ba karamin duka tasha ba, dama haka inna take indai ranta ya baci, da ja da gindi ta shiga dakinsu sai sannan ta fashe da kuka mai ban tausayi tana yi tana karkarwa, fateema tazo ta dafa ta tana lallashin ta da bata baki.A hankali ta kwanta anan kasan tiles din zazzabi mai zafi ya rufeta.Fateema ta taba wuyanta da sauri ta cire hannunta tace Adda jikin ki zafi sosai akwai zazzabi barin sa miki ruwa in taya ki gasa jikinki sai kiyi wanka in kawo miki magani kisha.Kai kawai ta iya gyadawa idanunta a lumshe don itama abunda tafi bukata kenan tayi wankan, har fateema ta fita a dakin tana kallonta hawaye na tsiyayowa daga idanunta tana mai tausayin addanta da kuma mamakin abunda ya shiga ranta har yake kokarin sauya tarbiyyarta a dan kankanin lokaci.Haka ta taimaka mata ta gasa jikinta ta fito ta barta tayi wanka data gama ta bata magani tasha tace adda kiyi bacci zaki danji dadin jikin idan kin tashi.Bani wayata fateema.Dauko wayar fateema tayi ta mika mata tace barin je in kama ma inna aiki.Gyada kai Ameena tayi dama tana Allah Allah idan ta bata wayar ta fita.Bayan fateema ta fita ta shiga contacts dinta tayi unblocking dinshi kana tayi dialing number sin shi tasa a kunne ba’a dau lokaci ba ya daga yana cewa na shiga rudani sweetheart zuciyata ta karye da yadda mahaifiyar ki ta tarbeni bansan yaya zanyi ba idan suka rabani dake basu san irin girman son da nike miki bane da sun sani da sunyi gaggawar mallaka mun ke ba tare da jinkiri ba ina tsoron rasa ki domin nasan bazan moru ba.Ka daina fadin haka kana dada karya mun zuciya ne kawai, ban taba son kowa ba a rayuwata sai kai kadai kuma bana jin zan iya son wani koda rabin son da nike maka ne insha Allah babu abunda zai raba mu nayi maka wannan alkawarin.Kin tabbata sweetheart? Kin tabbata zakiyi yaki akan soyayyar mu? Kin tabbata zaki dage tsayin daka wajen fadin cewar ni kike so kada a raba mu?.wannan lissafin duk ka bar shi iya abunda na sani kawai ina son ka kuma bazan yadda a raba mu ba.Nagode! Nagode nima na miki alkawarin zaki sameni da cika alkawari da rikon gaskiya da amana kuma zan shayar dake soyayya irin wacce zata dawwama a kwakwalwar ki ina sonki fiye da yadda nike son kaina.Na sani nasan yadda kake sona amma ka sani son da nike maka yafi wadda kai kake mun.Haka kike gani dai.Motsi taji alamun za’a shigo yasa tace zan kira ka anjima ta kashe wayar ta ajiye a karkashin pillow.Fateema ce ta shigo tana binta da kallon tuhuma ta zauna kusa da ita tace adda nasan me kikeyi ba sai kin boye mun ba ni mai rufa miki asirice a ko wani irin hali, sai dai gaskiya daci gareta wacce nasan baki son jinta a yanzu kuma ko an fada bazata hau kanki ba tunda kina cikin soyayya irin wacce ake kira makauniya amma duk da haka ni ‘yar uwar kice bazan gaji da son nusar dake munin abunda kike kokarin aikatawa ba, sau tari kakan so abu sai ya zamto ba shine alkhairi ba kuma kakan iya kin abunda zai zama shine alkhairin ka.Ta numfasa kana ta cigaba.Bazanso ki bata alakar dake tsakaninki da iyayen mu ba saboda wani can da bai san darajar kiba kuma yake son amfani dake na wucin gadi shawara zan baki kiyi kokarin koyawa zuciyarki kinsa kota yaya domin idan kika dage kika nace lallai hakan bazata haifar da da mai ido ba dan Allah adda sau daya dai ki gwada.Hmm fateema kenan duk wani kwantarda kaida kike yi da wannan make muryar da kikeyi ba fahimtar su nakeyi ba da ace inada iko da zuciyata dana yakice Ahmad a cikinta ko domin ran inna yayi fari sai dai kash kaddara ta riga fata soyayyar shi a raina bazan iya yakiceta ba kuma nasan dai karshe zasu gaji su barni in auri wanda nike so.Kenan adda kinfi martaba soyayyar Ahmad a ranki fiye data iyayenki da suka haife ki? Suka sha wahalar renon ki, suka tarbiyyantar dake suka inganta ki babu kalma a duk fadin duniyar nan da take da girman kalmar iyaye idan kika cire Allah da manzon sa, babu wadanda Allah ya umurta da a musu biyayya kada a saba musu sai iyaye, kina nufin ke Ahmad kika baiwa wannan matsayin?



