Halysaah Page 189 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 189…Aunty ta kasa ce ma Kilishi komai tsabar shock din da ta shiga, har sai da Kilishi tace “Hello kina ji na Fulani? Ko network ne” Aunty ta kalli Walid dake kwance ta mike ta nufi kofa ta fita ta kullo dakin don bata son ya ji abinda Kilishi ke gaya mata, Da kyar Aunty tace “Kika ce Junaid bai mutu ba Kilishi?” Kilishi tace “Wallahi kuwa, yana nan da ransa cikin koshin lafiya, gashi nan har ya dawo cikin mu” Aunty tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…..” Kilishi tace “Innalillahi kuma? Ke da zaki yi hamdala Fulani, tare fa mu ka yi ta koke koken rashin sa shekarun baya” Aunty ta kasa cewa komai taji ƙafafuwanta sun kasa ci gaba da daukarta har sai da ta samu waje ta zauna kawai ta katse wayar, ta dafe kanta don har wani dishi dishi ta soma gani, Ajay ya dawo da ransa?? Amma me yasa su Maryam da Khadijah basu kira sun gaya mata ba, tunawa tayi ta kashe wayarta tun jiya saboda damuwan Walid da yayi mata yawa, kilan suna ta nemanta basu sameta ba, amma kuma ai tun daxu ta kunna wayar, kuka ta fara yi sosai tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Walid ya cuci kansa, ya cuci kansa, gashi wanda ya nakasa kansa ta dalilinsa bai mutu ba, ta ina zan fara ni Hafsat” Babban abinda ya kara daga mata hankali bai wuce ganin hatta Mai martaba bai kirata ya sanar mata dawowar Ajay ba, a duk watannin nan ta rasa gane kansa gaba daya duk ya canza mata, wani lokacin sai yayi kwana biyu bai kira yaji jikin Walid ba sai in ita ce ta kirasa, iyaka kawai kudi yake tura masu isassu, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita tana tunanin menene mafita a yanxu, ta yaya ɗan ta na fari kuma only son dinta ace ya zama gurgu just like that, a maimakon ma a samu waraka duk uban kudaden da aka kashe sai tabarbarewa al’amarin ya kara yi matsalar spinal cord din ya ma fi na da, ta ina zata fara? ta ci kukanta ta koshi ta share hawayenta ta mike ta koma cikin dakin. Bayan kwana uku Ajay ya dawo stable suka fara shirin dawowa gida daga asibitin da aka yi admitting dinsa, a wannan kwanaki ukun Khaleesat sai dai su je asibiti su dawo tare da Mami bata samu isasshen time tare da shi ba, duk da an maidasa asibiti saboda mutane masu zuwa dubasa a masarauta but still akwai manyan mutanen da dole sai an kai su hospital din wajensa, a asibitin ma sai ya kasance ba shi da wani privacy, Jay da Mukhtar ne tare da shi a asibitin har ranan da aka yi discharging din su, suna cikin mota da daddare za su koma gida Jay ya kalli Mukhtar dake gaban motar yace “How did Walid’s Surgery went Mukhtar, na mance ban tambaye ka ba” Ajay dai kallon Mukhtar kawai yake yana zaune back seat together with Jay, Mukhtar yace “Doctors ba daya ba, ba biyu ba sun sanar ma Aunty a hakura da further Surgery don bazai tashi ba, aikin gama ya riga ya gama don ya riga ya nakasa amma taki ji ta kuma hanani gaya ma Mai martaba abinda likitocin suka ce, ita lallai sai anyi masa Surgery din karshe bata yarda Walid bazai mike ba, haka ta sa Mai martaba ya kara tura makudan kudi aka sake last Surgery din da aka yi some days ago, to wannan Surgery da aka yi na karshe kara complicating issues kawai yayi, yanxu kwata kwata baya iya motsa kafafuwansa unlike before da yake iya motsi mikewa ne kawai bazai iya ba, she just ruined everything completely ta karasa nakasa shi, ace har likitoci su bata shawara ta hakura amma taki, Surgery har hudu fa aka yi babu nasara sai more complications….” Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace “To amma me yasa ka dawo Mukhtar? Naga kamar babu kowa wajensu ai” Mukhtar yace “Dole in dawo, sai ka ga rashin mutuncin da Walid ke min kamar ni na dora masa laluran, idan bai gode min ba ai bazai min rashin mutunci ba, kana basa shawaran da zai amfanesa ya dingi kunduma maka zagi kenan yana maka hauka” Jay yace “That is because he frustrated Mukhtar da kayi considering hakan, babu abinda Frustration baya jawowa” Mukhtar yace “Sai ma kaga yanda ya koma yanxu, duk ya zama wani iri, ya rame yayi baƙi, yaki sa ma zuciyarsa tauhidi yanda kasan arne, dama babu batun sallah a lamarinsa yanxu, gashi fa yana kwance babu kafa amma a haka yake sa a kawo masa kwayoyi asibitin kuma uwar na gani bata cewa komai, da na mata maganar hakan bai dace ba saboda condition dinsa cewa tayi baya iya bacci ne shi yasa yake sha, ko kuma idan ya zageni yayi min rashin mutunci sai ta fara basa hakuri maimakon ni da yayi ma ta bani hakuri, naga kawai bazan iya ba na tattara na dawo, ashe abun farin ciki zan dawo in tarar a masarauta….” Jay ya girgiza kai yace “Allah ya kyauta, yanxu yaushe za su dawo Nigeria?” Mukhtar yace “In few days time, Ina jin ana gobe zaku tafi Amurka za su dawo” Jay yace “Nan da 6 days za mu tafi ai” Mukhtar yace “Eh su kuma in 5 days time za su dawo” Jay yace “Allah ya dawo da su lafiya” Mukhtar yace “Ameen” Shi dai Ajay babu abinda yace a conversation din nasu, har suka isa gida daga karshe, nan suka tarar da duk yan gidan an taru ana ta jiran isowar su, Ajay is still yet to understand the meaning of the caring he is seeing from each and everyone in the Emirate, wani irin mamaki ya dinga yi, sai yake ga kamar dai wani abu daban suke ma farin ciki amma ba dawowarsa ba…. Bayan isha’i Ajay na zaune parlon Mai martaba, daga gefensa Jay ne zaune sai Mukhtar dake kusa da Jay, sun fi minti bakwai zaune cikin parlon Sarki bai ce komai ba, ko ina yayi tsit a babban parlon, babu wanda baya cikin parlon a wannan lokacin tun daga su Gimbiya Firdausi, Kilishi, Hajiya Shafa’atu, Hajiya Sumayya, har da ‘ya yansu gaba daya, kowa na jiran jin abinda Mai martaba zai ce, Hajja na zaune kan kujera tana ta kallon Ajay a ranta tana kara gode ma Allah, ji take kamar an zare mata duk cutar da take yi akan rashin Ajay, ga kuma ciwon Walid, amma bayyanar Ajay yanxu taji kamar an dauke mata cuta, Ummi ma na zaune gefen Hajiya A’isha, Khaleesat dake kusa da Mami lokaci lokaci take daga ido a hankali ta kalli Ajay su hada ido don shi ma kallonta yake, har sannan gata nan gata nan dai ne kawai, don bata samu lokaci da mijinta ba for 3 days now, sai dai su je asibiti da Mami su dawo tare, daga daya bangaren Mami Hadiyah ce zaune sai Khadijah a gefenta, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Ajay calmly yace “Ahmad….” Daga Jay har Ajay suka daga kai suna kallon Mai martaba, Sarki yace “Junaid….” Hakan yasa Jay ya sauke idonsa kasa, Ajay yace “Ranka shi dade….” Mai martaba yace “Where have you been for 2 years Ahmad?” Ajay ya sunkuyar da kansa yayi shiru, kowa na parlon kallonsa yake yana jiran yaji abinda zai ce barin Khaleesat dake kallonsa babu ko kiftawa, Hajja ta girgiza kai tana share hawayen da suka fara zuba idonta, after some seconds Ajay ya dago kansa a hankali yana kallon Mai martaba yaga idonsa na kansa baya ko kiftawa, Ajay ya girgiza kai cikin sanyin murya yace “I can’t tell ur highness, I only remembered opening my eyes to a man from the riverine area, and he was taking care of me, kawai abinda na sani kenan” Kowa na parlon kallonsa yake da alhini a fuska, Mai martaba ya mike tsaye yace “A ina mutumin yake?” Ajay yace “Yana Benue ranka shi dade, amma ban tuna sunan garin ba, It’s a riverine area” Mai martaba yace “Zaka iya gane garin yanxu?” Ajay yace “Zan gane….” Mai martaba ya kalli Jay yace “Make arrangement Jawwad, za mu koma Makurdi gobe in sha Allah…” Gimbiya Firdausi tace “Allah ya ja da ran sarki, Amma nake ga da sa wa kayi a je a dauko mutumin a kawo sa har nan, da ace kaje da kanka, kaga yace riverine area ne” Mai martaba yace “A’a, da kaina zan je Gimbiya, da kaina ya kamata in je wajen wannan mutumi in gansa” Ummi tace “To amma ranka shi dade ai da an bari Junaid ya kara warwarewa gaba daya kafin a je….” Hajja tace “Gaskiya ne wannan, ka bari ko nan da wasu kwanaki ne kafin dai tafiyarsu America sai a tafi Benue din ya kai ku har garin, amma yanxu a bar sa ya huta, bangarensa ma a hakura da zuwa, a bari matarsa ta ci gaba da kulawa da shi” Jay ya daga kai ya kalli Hajja, Mai martaba yace “Nan da kwanaki uku za mu koma Makurdi din in sha Allah….” Sarki ne ya fara barin parlon, jiki ba kwari Hajja ta mike ta fita daga parlon, Mami na kallon Khaleesat tace “Tashi mu je Halysaah” Khaleesat ta kasa ce ma Mami komai, ji tayi kamar ta fara kuka don bin Ajay take son yi part dinsa, amma bata yi musu ba ta mike ta bi Mami suka nufi kofa tana jin hawaye na taruwa idonta, Ajay ya bi ta da kallo…. Suna komawa part din Mami, Mami ta sa Khaleesat ta gyara mata dakin baƙi dake part din don akwai visitors dinta da zasu kwana dakin, Khaleesat ta shiga dakin cikin sanyin jiki don yin abinda Mami ta sakata, har zuciyarta take son kasancewa tare da mijinta, Mami ta shiga kitchen zata wanke fruits, sai ga Hajiya Shafa’atu ta shigo bangaren da sallama, Mami ta fito daga kitchen tana amsa sallaman, Hajiya Shafa’atu tace “Gida zan tafi yanxu Fulani, sai gobe zan dawo in sha Allah” Mami tace “To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, ke da Gimbiya za ku wuce?” Hajiya Shafa’atu tace “Ehh tare za mu tafi, tana bangaren Hajja taje sallamanta” Karasawa Hajiya Shafa’atu tayi kusa da Mami tace “Halysaan ta tafi bangaren mijinta ne?” Mami tace “A’a tana daki” Hajiya Shafa’atu tace “To dai ya kamata ayi mata gyara me kyau Fulani tunda kinga all this while wajenmu take ba wajen iyayenta ba, zuwa gobe zan mata order din kayan gyara masu kyau, if possible she should stay in ur part har a gyarata, sai dai ta dinga zuwa dubasa tunda naga Jawwad na wajensa…” Mami ta ɗan yi murmushi tace “Haka ne Hajiya, nima nayi mata order daxu da yamman nan, amma dai bai kamata in bar ta a nan ba gaskiya don akwai shiga hakki, zuwa anjima kadan zata shirya ta tafi bangarenta ai ba wai yaji sauki bane har yanxu Junaid din, in taje can din zata taimaka masa da wasu abubuwan, he still can’t lift heavy things….” Hajiya Shafa’atu tace “Yanxun ma daga ɓangaren Junaid din nake, amma kuma ni sai naga kamar jikin nasa yayi sauki sosai” Mami tace “Kinsan har yanxu fa ba a cire fragments din bullets dake jikinsa ba Hajiya, shi ne ma dalilin tafiyar da za su yi…” Hajiya Shafa’atu tace “Gaskiya ne, kuma dole surgery za ayi….” Mami tace “To kin ga” Hajiya Shafa’atu tace “Amma da Halysaar za ayi tafiyar ai?” Mami tace “Eh tare za su je, Sarki da kansa yace a je da ita, su uku za su yi tafiyar” Wayar Hajiya Shafa’atu ne ya fara ringing ta duba taga Gimbiya Firdausi ke kiranta, tace “To Fulani bari in je sai gobe in sha Allah….” Mami tace “To Allah ya kai mu lafiya Hajiya” Daga haka Hajiya Shafa’atu ta juya ta bar parlon, Mami ta koma kitchen ta ci gaba da wanke fruits din da take. Khaleesat na gama gyaran dakin da Mami ta sakata ta fito parlor ta tarar da Mami zaune tana cin Apple, Mami tace “Kinyi wanka ne Halysaah?” Khaleesat tace “Da yamma nayi wanka…” Mami tace “To ki je ki kara yi ko?” Khaleesat ta juya ta koma bedroom din da wani lokaci take kwana in dai tana part din Mami, har kayanta akwai a dakin, Mami ta dau wayarta ta kira Jay, yana fara ringing ya daga tace “Where are you Jawwad?” Jay da fitowarsa daga part din Ajay kenan yace “In zo ne Mami?” Mami tace “Eh zo” katse wayar tayi ta mike ta tafi bedroom dinta zata dauko ma Khaleesat tsadaddun turarurrukan ta, Jay na kusa da bangaren Mami ya hango Hadiyah that is also coming towards Mami’s part, tana ganinsa ta juya zata canza hanya ya bi ta da sauri ya fixgota ta fado jikinsa tun kan tayi corner, ta zaro ido tana kokarin kwace kanta tace “A’a.. meye haka kuma” Yaki saketa yana kallonta yace “Ni kike canza ma hanya idan kika ganni a gidan nan?” Ta fara tura baki tana turasa tace “Don Allah ka sakeni kar wani ya zo wucewa, meye haka kuma?” Ganin yaki saketa sai ma mannata da yayi da bango ta gatsa masa cizo a hannu, ba shiri ya saketa ta ruga da gudu zuwa parlon Mami ta bude kofar ta shiga kamar an korata ciki, Mami na kallonta da mamaki tace “Lafiya ke kuma?” Yake Hadiyah tayi tana sosa keya tace “A’a Mami, dama Hajja ce tace in zo in ce maki ki dama mata fura da Nono” Mami ta kalli Jay da ya shigo parlon, tsayawa yayi bakin kofar bai yarda su hada ido da Mami ba, don da yasan tana zaune parlor bazai shigo ba a lokacin, Hadiyah ta nufi kitchen da sauri ta shiga, ya sauke kansa ya karaso cikin parlon, Mami dai kallonsa kawai take, ya zauna yace “Gani Mami” Mami tace “Na gan ka ai, in ji yau ba bangaren Junaid zaka kwana ba dai?” Jay yace “Mami ai saboda jikinsa ne yasa nake zama part din, kuma kin ga yau aka yi discharging dinsa fa” Mami tace “To wai Ajayn nan ance maka ba shi da macen da zata kula da shi ne sai kai? Ko ka manta yana da mata ne?” Jay ya ɗan yi murmushi yace “Da gaske mancewa nake Mami…” Mami tace “To na tuna maka yanxu, zan tura ta taje ta kula da mijinta idan zaka tafi sashin ka ka kwanta to gwara ka je ka kwanta, kai baka ga alamar jikinsa da sauki bane?” Jay yace “Haka ne Mami, amma idan da wani abu ki ce mata ta zo ta fada” Mami tace “Ba ma sai an ce mata ba in dai Halysaah ce” Tana kai wa nan ta mike ta shiga dakin da Khaleesat ke ciki don ganin ko ta fito wankan, Jay ya kalli hanyar kitchen din Mami, mikewa yayi ya nufi kitchen din ya shiga ya kulle kofar. Khaleesat na sanye da hijab dinta har kasa ta nufi part din Ajay wajen karfe tara da rabi na dare, slowly take tafiya ta bude kofar parlonsa ta shiga, ta karasa ta bude kofar bedroom dinsa dai dai sanda ya fito daga bandaki yana goge gashin kansa da karamin towel ya daga kai yana kallonta, sauke ido tayi ta shiga cikin dakin ta kulle kofa, ya karasa har gabanta yana kallonta babu ko kiftawa, murya can kasa yace “Jeeddah” a hankali ta kwantar da kanta a kirjinsa that is wet, ta lumshe ido bata ce komai ba, ya dago hijab din jikinta ya cire ya ajiye gefen gado, ya zame hulan kanta, kallon gashinta ya dinga yi, wanda yanzu iyakarsa shoulder dinta, ya dago kanta da mamaki yace “What happened to your hair Jeeddah?” Kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, lokaci daya hawaye suka cika idonta, rufe fuskarta tayi a jikinsa tana kuka a hankali.



