Mejo Najeeb Page 52 By Autar Alheri
“Da kallon mamaki sukabishi ganin yadda yazube ƙasa yana rusar kuka wanda, kafin wani yasamu zarafin yin magana suka yaran sunfara fitowa daga ɗakin mama salmu somai somai kamar ansaka kaza acikin ruwan zafi, kowannensu kallo ɗaya zakamishi kasan abinda ya aikata sabida yadda suke a hargitse, yah balah dagashi se boxes beko sakashi dedeba, hafizu kuwa jallabiyar daya shiga da ita ya ɗauro a ƙugunshi…anty hawwa da anty bilki kuwa babu me kayan kirki dukkanku tsinannun kayan bacci ne ajikinsu babu na albarka kuma rashin natsuwa yahanasu saka kayan dede, ga mama salmu acikin ɗakin taƙi fitowa daga ita se zane ɗaura gaba.. “innalillahi wa’innailaihi raji’un shine abinda ya fito daga bakin mama bintu, iyya hassi kuwa wuyan anty hawwa ta shaƙo tana faɗar ke dan ubanki mikukeyi aɗakinnan dukkanku acikin wannan tsohon faren? Tatambeta arikice gabanta na dukan tara tara. Mamansu ya balah kuwa kafesu kawai tayi da ido suda anty bilki tanamusu kallo kwaƙwab.. “bazakiyimun bayaniba Sena kasheki ahidannan iyee hawwa, mikuke aikatawa nace? Muryar iyya hassi ta hargitsa wurin gaya acikin dare. Kuka anty hawwa tasaki amma taƙi cewa komai..Nlm Musa kuwa seda yayi kukan sosai kana yamiƙe yana share hawayenshi yace “hassi kidainamin ihu acikin gida yanzu darene tun baki taramin jama’aba, miye na tambayar abinda suka aikata baya gaya kina gani da idonki, yau takai takawo ƴaƴan cikina suna neman junansu hadda matata kuma acikin gidana, innalillahi wa’innailaihi raji’un, haƙiƙa zancen Allah baya faɗuwa ga ayanan ta bayya acikin gidana dukkanku kungani. Shiru yaɗanyi kafin yaɗago yana kallon iyya hassi yace “hassi kunyiwa Maryama ƙazafin neman maza har kuna ikirarin zata ɓata muku yara, Humm yau gashi yaran naku suna neman junansu Bama awajeba, abinda kukaso gani ga ƴar wani yau gashi akan ƴaƴanku kunso tozaltarda ita amma gaya yaƙare akan ƴaƴanku, kukane yaƙara kuɓuce Mishi cikin kukan yake faɗar “kunsaka nakireta a tsakiyar dare saboda makircinku yau ga ƴaƴanku nan na aikata abu mafi muni atsakiyar daren ya zakuce ayi dasu sukuwa? Ko baki Berufeba, ɗaya daga cikin samarin gidan yataso ƙeyar juwaira agaba dawani ƙanenshi yana faɗar “Abba basu kaɗai ba gasuwa fasiƙannan suma iskancinsu ne ya tadani daga bacci, yafaɗa yana turosu gaban Abba.. duka wurin kowa yayi tsit masu kuka nayi masu salati nayi. Abba kuwa bedamu dasu zubaida domin abinda ya gani da idonshi yafi wanda aka gaya Mishi rashin hankali…wlh kuncuceni kuncuci tarbiyar dana baku kun zalunci rayuwarku, kuma kisani kema salmu bani kikayiwa ba kanki kikayiwa kin tozaltarda kanki a idon ƙananun yara ƴaƴan mijinki dakika rena kamar ƴaƴanki yau sune abokan taɓewarki, wlh kuda Allah shine zesakamin wannan cin zarafin da kukayimun, yaƙarasa zancen yana ƙara fashewada matsanancin kuka. “Cikin baƙin cikin wannan al’amarin mama bintu tace”dan Allah mlm kayi haƙuri karkayi musu baki wannan abin kaɗai yafi baki Bala’i sabida hakan shima kawai ya’ishesu yanzu addu’a kawai zamuyi musu Allah ya shiryardasu, dagasu har uwar tasu, domin salmu bakiyiwa kanki Adilci ba, farin cikina ɗaya dayakasance a yau ɗinnan jidda batanan da tana gidannan taga wannan mummunan abu da kinkashe yarinya da ƙyrciyarta, kinyaga mata rigar mutunci, abu ɗaya zance Miki anan shine kiyi gaggawar tuba kinemi tafiyar uban giji akan wannan mummunan aikin. Sekuma tajuya gunsu iyya hassi dasuka zube akan ƙafafunsu suna rusar kukanda bayada anfani ayanzu, seda ta ƙare musu kallo kana tace “faɗar Allah ne da manzonsa, duk wanda tayiwa ɗan wata mummunar fata ko mummunar addu’a to tasani ko bakinta bazata rufeba mala’iku zasuce Amin walaka, idan mummunan firucine ma kayi zeƙare akanka ne,Abinda kukayiwa Maryama yau gashi tun ba’aje lahira ba Allah yasaka mata yanuna muku shine sarki kuma aje lahira yayi muku hisabi akan hakkinta, abinda kukaso akanta Allah yakareta kuma abun yadawo akan ƴaƴanku, Allah yaganarda masu hali irinnaku gaskiya kusan cewar tabbas (khama tudinu,tudanah) in Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama duk abinda kayi se anyima makamancin shi. Allah yasa mufi ƙarfin zukatanmu…tunda mama bintu tafara magana jikinsu yayi tabbas sun cutarda Maryama kuma sunso hakan akanta amma ga yadda Allah yayi nashi iko, atake suka fara neman tuba dafatar Allah yasa isseta tayafe musu harcikin ranta kamar yadda mahaifiyarta tace domin kuwa inbata yafe musuba sunsan tabbas basuga Komaiba..”kuwuce dakinku Allah yashiryeku dan alfarman Annabi. Muryar mama bintu tadoki kunnuwan yaran..cikin kuka suka zube gaban mahaifinsu da iyayensu mata suna hasu haƙuri tare da yimusu alƙawarin bazasu ƙara maimaita hakanba in sha Allah, domin sosai sukaji kunyar abinda suka aikata kuma jikinsu yayi mugun sanyi…mlm Musa kuwa ko kallon inda suke beyiba yace “abu ɗaya zan gaya muku duk wadda take da mijin aure tafitar dashi acikin satinnan harku mazan idan kuma bakuda zanbawa duk wanda naga dama sadakarku, alhmdllh haryanzu ina yiwa Allah godiya daya kasance bakece najeebullah yazaɓa hawwa’u dakin cuci yaron mutane kinkaimai gaibu agida ina me matuƙar tayashi murnar samun nagar tacciyar mace kamar Maryama…sudai basuce Komaiba se kuka. Mama Binta ce tace “mlm aure bazeyuba acikin satinnan kodai kabari Allah kawo musu mazajen tukkunnah ayi auren ko kuwa kabari suyi bara’a domin aure baze ɗauru agaresu yanzuba muddin auren mutunci za’ayi.Shiri yaɗanyi yana sauraren ta tabbas zancenta gaskiya ne babu zancen aure ga macen da tayi zina muddin batayi bara’a ba, nisawa yayi kana yace wlh iya bara’a zanbari kuyi agidannan amma bazan barku hallaka min gidaba,,,,sekuma yajuya ga mama salmu dake rakuɓe kamar muna fuka yace “kekuwa kije zaki gani domin Allah ne kawai ze iya zakamin abinda kimanin bawai mutunba sabida bawani hukunci dazeyi aiki agareki yawanke laifin zunubinki, babu duka babu zaki balle saki amma duk abinda kikayi Allah shine yasan yadda zeyi dake, yana gama faɗar hakan yawuce ɗakinshi cikin ƙunar rai. Itama mama bintu wucewarta tayi nata ɗakin aranta tana jinjina girman wannan al’amarin…..hakan aka barsu sukaɗai se iyayen nasu atsakar gidan suna rusar kukan danasani wanda bayada anfani, daga ƙarshe kuwa yakama gabanshi zuciya acunkushe😥 *ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUKANTANMU ALLAH YABAMU IKON SOWA ƳAƳAN WASU ABINDA MUKA SOWA NAMU ALLAH YABAMU IKON YIWA DUK WANI MUSULMI FATAN ALHERI DA ADDU’A TAGARI ALFARMAN MUHAMMAD DA ALQUR’ANI*Washe gari misalin ƙarfe 11:00am kowa ya fito agidan amma banda isseta da mejo Ammi ta tambayi nazeer ko ina najeeb domin taga yakoro mata yaranta yariƙe mata ƴarta amma har yanzu basu fitoba…. Murmushi kawai nazeer yayi yace “zasu fito gwaggo ayi haƙuri. Ƙwafa tayi kana tace aizezo yasameni ne baze kara ganintaba balle yahana tafitowa cikin mutane yajira harseta koma gidanshi tukkunna….shidai nazeer murmushi kawai yakeyi Amma bece komai, hakan Ammi taƙaraci faɗanta harta dena…abu wasa wasa har azahar babu su mejo babu dalilinsu. Haka Hajiya Hannah tace aje akirasu akace basu buɗe ƙofa har akayi la’asar wuraren 5:00mp ne Alhaji abdussalam yadawo gidan, ananne yasamu Ammi bata zuhurta faɗa, yatambaya miyafaru aka gaya Mishi. Seyace to Allah dai yasa lafiya, Sapwan yace yagani imma basu buɗe ba yabuɗe dakin yaga miyahanasu fitowa Allah dai yasa lafiya…hakan kuwa akayi Sapwan yaje yayita nocking amma basu buɗeba sekawai yabuɗe yashiga, sedai abin mamaki wayam yagani bakowa a ɗakin cikin mamaki yafito yana tambayar ma aikatan gidan, ananne wani security yace wlh sunbar gidan tun ƙarfe 6:00am. Ido yawaro cikin mugun mamaki yazaro wayarshi yashiga kiran Layin mejo na Nigeria, aiko sega kiran yashiga, alokacin mejo da Isseta suna gidansu inda a Lagos inda isseta tafara zama suna kwance maƙale da juna sun gama shagalinsu cikin farin ciki da ƙaunar juna. Hannu yasaka yaɗauki wayar dake kan bedside ta ruri, yaɗaga ahankali tareda karata a kunnenshi yana mannawa isseta kiss a kunne, ƙanƙameshi tayi dasauri tareda faɗar “washhh yah najeeb nidai kaƙaramin uhm,uhm taƙarasa zancen cikin shagwaɓa. Shiko batareda yatankawa me kiranshi awayana yayi saurin ajiye wayar gefe, yace “ohhh my god sweet babyy Nima ban ƙoshiba wlh yafaɗa yana ƙara janyota jikinshi atake suka koma ruwa….da sauri Sapwan yajanye wayar akunnenshi yana dariya Aranshi yace “tab ɗijam waƴannan anyi jara babbu kullun suna maƙale da juna, da wannan mamakin yanufi cikin gidan inda yake sanarwar iyayen mejo fa yaɗauke matarshi sun gudu yanzu hakan suna Nigeria….ido duk suka wato har nazeer dake wurin, shikam Alhaji abdussalam dariya kawai tayi kana tace “to Maryama kema sekishirya komawa dakinki domin gobe Alhaji khamis zezo asabunta aurenku kibi mijinki…..shiru wurin ya ɗauka sosai anrasa mecewa komai se mamakin rashin kunyar najeeb sukeyi.Washe gari dasafe Abba yakira mejo yace zeje Niger idan yanazuwa yazo sutafi yaɗauko matarshi…buɗar bakinshi se cewa yayi “Abba kaje kawai Allah yatsare dominni naɗauko tawa saura kai ka ɗauko taka daga hakan yayanke wayar.Sororo Abba yayi yana kallon wayar kafin yasaki murmushi kawai ya girgiza kanshi, yarasa ina mejo yakoyi rashin kunya yaronda keda tsananin kunya amma yanzu san idonshi abuɗe suke.Hajiya umma kuwa gabaki ɗaya hankalinta atashe yake domin tayi kiran tsijuju harta gaji yaƙi zuwa, gaya Alhaji khamis har yanzu beyiwa kowa daga cikinsu zancen Maryama ba, ɗaya ɓangaren kuma bata samun nomber mejo tanimu, gaya wani irin feeling takeji akan najeeb kamar zatayi hauka abin duniya duk ya isheta tarasa yadda zatayi da rayuwarta……..aɓangaren Alhaji khamis kuwa tuni yanufi Niger gun ɗauko matarsa. Kwananshi ɗaya washe garin na biyu aka ɗaura aurenshi da Ammi yaɗauko matarshi tare da jidda da halima tunda isseta tagudo tabarsu.GombeGidan su isseta kuwa gabaki ɗaya abin duniya ya ishe mama salmu tayi danasanin abinda ta aikata babu adadi tayi kuka harta gode Allah, Abba yajuya mata baya ko kallo bata isheshi ba, hakama matan gidan babu mesakawa da ita balle fiddawa duk wannan tsoron nata dasukeji takaice, mama bintu ce kawai ketemakawa wani lokacin tana ɗan kulata tare da yimata nasiha akan rayuwa….hakan yasa Takoma ga Allah kullun cikin neman tuba take da yafiyar uban gijinta….afannin ƴammatan gidan ma hakan abin yake domin babu ruwan kowa dasu gaba ɗaya rayuwa tayi musu ƙunci.LagosWai ina labarin mansura?? Mansura tun lokacinda tabar gidansu mejo mahaifinta yasakata kullin dole, bata fita ko ina har school acewar shi dama bada son ranshi tarayu ahannun Jamila ba, hakan yasa makonta biyu da koma gidan ya ɗaura mata aure da wani cousin brother ɗinta… alokacinda taji ɗaurin auren bata wani damuba domin da wannan kullin na bala’i Gara tarungumi auren tunda wanda takeso dai basamu zatayiba, ahakan aka tattara mansura aka kaita gidan mijin Kaduna state, babi mamsura yarufe semuce Allah ya bada zama lafiya..Banana islandCikin sauri sauri yake takonshi har yafito harabar gidan, kaitsaye yanufi inda dandazon mutocinshi suke..dasauru garadan sojojin nan suka taso cikin sauri sauri suka buɗe mai mota yashiga, suna suka shiga nasu, Captain jameel yaja motar suka bar gidan cikin aza babban gudu,,,seda suka danyi nisa da tafiya kana mejo yaga sun nufi wata hanyar daban kamar bata inda suka dosaba cikin mamaki yace “miyasa za’abi nann? “Sorry Sr Hajiya umma ce takirani yanzu tace idan mufito musameta anan tana neman ka.. rass gaban mejo yafaɗi amma yadake bece komaiba gudun kar Captain jameel yagane wani abun……danugun sauri tafito daga bedroom ɗinta kamar zata tashi sama hakan tafito tsakiyar gidan tanufi get…cikin sauri su Captain Umar dake gadin gida sukabiyota suna faɗar “lafiya dai Madam? Amma ina kafin suzo harta fice daga get ɗin, koda suka ƙaraso suka suka fito farfajiyar gidan taɓacewa ganinsu sam basuga ko me Kamada ita ba kamar wata aljana…arikice Captain Umar yaɗauki waya yana kiran mejo amma bugun duniya yaƙi ɗagawa hakan yasa yanayarda kiran gun general Aliyu, yana ɗagawa cikin tashin hankali Captain Umar kegaya Mishi abinda ke faruwa…arazane yamiƙe tsaye yana faɗar whatt?…!



