Uncategorized

Illolin da shan kwayoyin hana daukar ciki ke haifarwa don Allah a kiyaye

 

Barazanar da mata mai shan kwayoyin hana daukar ciki take ciki

Assalamu alaikum jama’a barkan ku da sake saduwa da mu a yau kai tsaye zan yi bayani ne akan illolin da shan kwayoyin zubar da ciki ke haifarwa don haka sai a biyo mu dan jin wadannan illoli kamar haka;

1. Illar ta farko ita ce Irregular Period wato suna rikita al’ada ga mafi yawan mata, musamman masu shekara 35 zuwa sama. (Alal misali idan al’adar ki tana zuwa farkon wata to shan irin magungunan nan na iya sawa ta dawo zuwa tsakiyar wata ko kuma karshen wata ma)

2. Matsala ta biyu ita ce Vaginal Discharge, yawan amfani da magungunan zubar da ciki yana haddasa wa mace zubar farin ruwa daga gabanta, wanda shi wannan ruwan yana da kauri, sannan yana da ɗoyin kwarai da gaske wanda ka iya sa mijinki ya tsane ki, kada wajen neman gira a rasa idanu. Allah Ya kyauta 

3. A cikin illolin da shan kwayoyin hana daukar ciki akwai Blurred Vision, duk mace mai shan kwayoyin birth control ba ta tsufa da idanunta. Dr Helen George likita ce a bangaren idanu ta ce “Adadin mata masu matsalar idanu tana ƙaruwa saboda amfani da kwayoyin hana daukar ciki”.

4. Matsala ta huɗu ita ce Intense Headache, wato matsanancin ciwon kai, wanda shi wannan ciwon kan yana haifar da migraine wato ciwon kai mai tsayawa cak! Yakan yi awa 8-9 bai sauka ba 

5. Akwai Weight Gain ma’ana kashe kwayoyin halitta masu daidaita nauyin jiki. Ta yadda suna iya sako maka nauyin jiki, wani lokacin kuma ya dauke nauyin… Ka jika sam babu kwari.

6. Illa ta karshe da za mu yi bayani ita ce yana kashe kwayoyin haihuwa. Sannan suna haifar da wasu cututtukan kamar haka:

  • Infection
  • Siphlis
  • Xion homorn

Dukkannin waɗannan cututtuka suna da cikar ga lafiyar mace Allah Ya kyauta.

Back to top button