Hausa novels

NIHAAD Chapter 50 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

50

Nihad ta ki yarda su hada ido da shi, ya dinga kallonta don duk a tsorace take, ya kamo hannunta zai yi magana aka bude kofa Mami tayi ta fito daga dakinta, Khalil yayi saurin tashi daga kusa da ita ya nufi kujera, Mami ta kallesa ta kalleta, ita dai Nihad kanta na kasa, Mami tace “Ya ciwon kan? Kin sha magani?” Nihad still bata dago kanta ba tace “Na sha” Mami tace “Toh Allah ya sauwake, je kiyi kwanciyarki kawai….” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, Mami na kallon Khalil fuska daure tace “Ban gane ma’anar shisshige ma yarinyar nan da kake ba Khalil?” Ya zaro ido da sauri, sai kuma ya xauna yace “Mami shisshige mata kuma? I just saw she is sick and….” Mami ta katse sa rai bace tace “If she is sick ni baxan iya mata abinda ya kamata ba sai kai? Sannan who did she tell she is sick? i see no reason da xai sa kana shiga dakin da take at the first place ita ba muharramarka ba, meye ma’anar hakan? to gaskiya bana so, don’t ever try it again, idan wani abu ya dameta ta zo ta gaya min bana son wannan shige matan da kake we are not pagans” Khalil ya mike yace “Mami ai baki taɓa gani na….” Dakatar da shi tayi tace “Bana son jin komai, na dai gaya maka abinda xan gaya maka, khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, ta juya tayi komawarta cikin dakinta, a hankali ya koma ya zauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, kansa bai taɓa kullewa yanda ya kulle ba yanzu, ya ga alama it’s not going to be easy, it doesn’t look Mami will take things easy kafin aje ga Abbansa, sai a sannan ya fara tunanin he wished bai boye ma Aunty Maryam komai ba tun farkon dawowarsu, may be she will have understood him, yasan yanzu its too late ita kanta baxata fahimcesa ba yanxu, it’s just too late, bayan wani lokaci Mami ta fito daga dakinta ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofa zata fita, ya jima bai ga ta hade masa rai haka ba, wannan yasa jikinsa yayi sanyi, he don’t think she will ever support him in any way, Mami xata bude kofar parlon aka bude before her, hakan yasa ta daga kai suka yi ido hudu da shi, da fara’a tace “Aa, Aliyu yaushe ka dawo?” Yace “Not too long Mami” Khalil ya wani murtuke fuska yana danna wayarsa, Mami ta koma ta zauna tana kallon Aliyu tace “Sannu da zuwa, ai ban san ka dawo ba wallahi” Ya zauna saman kujera yace “Ina yini Mami” Tace “Alhamdulillah, ka dawo lafiya?” yace “Lafiya lau Alhamdulillah” Mami tace “To maa sha Allah, gaskiya ka dade sosai wannan karan” ya ɗan yi murmushi da iyakarsa baki yace “Na shigo ne in gaisheki dama….” Tace “Toh Nagode Aliyu, i will be coming downstairs later, you are welcome dear” Yace “Alright” Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Mami ta kalli Khalil da damuwa tace “Why didn’t u speak to him Khalil?” Khalil kamar jira yake yace “Why will i speak to him Mami?” Mami ta girgiza kai tace “No…. gaskiya bana son haka, tunda ya shigo har nan ya gaisheni menene a ciki don ka gaisa da shi? Me yake yi som” Khalil yace “Am i his mate da xan fara gaishesa Mami? or da can ya saba shigowa gaisheki a nan idan ba hypocrisy ba, look Mami i am begging you to stop forcing me do what isn’t necessary, babu abinda ya hadani da su” Mami tace “No Khalil, me yasa kake daukan komai da zafi a rayuwarka ne? ko kaki ko ka so ɗan uwanka ne fa” Khalil ya mike yace “Ba ɗan uwana bane ban hada komai da shi ba…” Mami ta daure fuska tace “Kace min ba ɗan uwanka bane” Yace “I want to excuse my self plss” Kallonsa Mami ta dinga yi, yace “I said i want to excuse my self Mami” Mami ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “Ohk” Juyawa yayi ya fice daga parlon a fusace, Mami ta girgiza kai irin zuciyar Khalil na damunta, he is the one always causing problem for himself, sai yace baya tsoron kowa, hatta mahaifinsa tasan yanda duk suke shakkarsa shi baya yi, shi yasa yana ce masa ya bar masa gida ko minti goma bai kara ba a gidan yayi gaba, bayan few minutes ta girgiza kai ta mike ta fita daga parlorn ta nufi dakin da Nihad take don ce mata ta hada kayanta, Khalil yayi stiff a bakin kofar dakin don zai fito kenan sai ga Mami, Kallonsa Mami take babu ko kiftawa ta ma kasa ce masa komai, confidently yace “I left my phone in here, so i came to pick it up” Daga haka ya bar ta tsaye bakin kofar without waiting for her reply, ta bi sa da kallo, Can ta shiga cikin dakin, Nihad na kwance ta rufe ido kamar me bacci, Mami ta dinga kallonta for some seconds, sai kuma ta karasa kusa da gadon, Nihad ta bude ido da sauri, ganin Mamin ta mike ta zauna tana murza idonta, Mami tace “Are you feeling better now?” Nihad tace “Alhamdulillah” Mami stood for almost a minute looking at her, Sai kuma ta juya ta fita daga dakin. Khalil na komawa bedroom dinsa yaga miss calls din Farooq, zaunawa yayi gefen gado yayi dialing number, yana fara ring Farooq ya daga, suka gaisa sannan farooq yace “I think Nihal will be going to kano for the weekend don dazu Umma ta kirani tace in tura mata Tp ta ce mata ta taho Kano, after exams ai xata iya zuwa Abujan ko?” Da sauri khalil yace “Sure ba damuwa, i think that will even be better” Farooq yace “Toh maa sha Allah” Daga haka suka yi sallama khalil ya katse wayar. Mimi na dawowa makaranta Mami ta shigo dakinta, Mimi dakw goge jikinta da towel tace “Mami good afternoon” Mami tace “Afternoon dear, kina ji na” Mimi ta kalli Mami tace “Ina ji Mami” Mami tace “Za ku je gidansu Nadeeyah ke da Nihad ku yi 2 days a can” Da mamaki Mimi tace “Why Mami? Me ake yi a gidan?” Mami tace “Ba komai, but you have to do as i say” Mimi tace “Ohk” Mami tace “Idan kin huta kin ci abinci anjima sai kice mata ta shirya kayanta, kema ki shirya naki” Mimi tace “Toh” Juyawa Mami tayi ta fita daga dakin. Nihad na kallon Mimi dake zaune gefenta a kan gado tace “Ina za mu je?” Mimi ta wara ido tace “Somewhere, gidan sister din Mami” Nihad felt a bit relieve jin haka, don dama har cikin ranta ta gaji da gidan nan, and har zuciyarta taji bata son tana ganin Khalil don wani tsoronsa take ji, da ta tuna abinda yayi mata sae taji hawaye ya zubo mata, ita duk tunaninta ae ya santa fa, a hankali Mimi tace “But pls tell me Neehad, why are u always unhappy, ur eyes are often swollen, u are always silent, ko baki son gidanmu ne?” Nihad ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Mimi tace “Or are you not comfortable here? Am i not nice to you? Kinga ai bakya haduwa da cousins dina da step sister dita Hanan, basa shigowa part din nan so it’s rear ku hadu, and idan kika saki jiki da Noor xa ki ga she is also nice, u misunderstood her ne kawai from the beginning” Nihad dai ta kasa ce mata komai she wish she can tell her abinda khalil yyi mata ko zata samu saukin abinda ke damunta a zuciya, Ganin haka Mimi ta sauke ajiyar zuciya tace “So now kawai ki hada kayanki, nasan you won’t get boring gidan da za muje cause they are not strict, we will be having enough freedom there to go anywhere unlike here, and i will be taking u out to many places in Abuja” A hankali Nihad tace “Okay thank you” daga haka ta sauka daga saman gadon ta tafi wajen kayanta, Mimi ta bi ta da kallo, seeing how she is walking tace “Are you injured?” Da sauri Nihad ta kalleta tace “I am getting better now” Mimi tace “Ohk”

Umma na jera kayanta da Isiya me wanki da guga ya kawo mata dazu a Press aka bude kofar dakinta, daga kai tayi tana kallon kofar ganin Amina tace “Wai baki tafi islamiyyar ba?” Amina tace “Umma, Aunty Nihal ta dawo” Umma ta ajiye kayanta da sauri tace “Kai haba, oyoyo oyoyo” Daga haka ta fice daga dakin da sauri ta tafi can bangaren Mumy ta shiga dakin Nihal, Kwance ta ganta Mumy na zaune gefenta, cike da farin ciki Umma tace “Oyoyo autana, sannu da zuwa, sannu da zuwa” Sai kuma ta karasa bakin gadon tace “Aa baki da lafiya ne?” Nihal ta girgiza kai tace “Aa lafiyata qlau” Mumy tace “Nima tambayar da nayi mata kenan, ina jin gajiyar hanya ce kawai” Umma tace “To taso mu je, ga favourite dinki can na maki” Nihal tace “Umma bana jin yunwa sai anjima” Umma tace “Ni dallah taso, dubi yanda kika rame kamar baki cin abinci a makarantar, ni wallahi wannan jarabbaben makarantar ya isheni Allah ya so shekaran karshe kike ki huta mu ma mu huta” Mumy tace “Tashi kije Nihal” Nihal ta sauka daga kan gadon ta bi bayan Umma suka fita daga dakin, Mumy dai ta bi su da kallo, at times ganin Nihal na sa ta mance duk wani damuwarta, yana rage mata kewar Nihad da take, tana jin Nihal kamar Nihad a zuciyarta, sannan tun bayan da Farooq ya kirata ya sanar mata yaje har inda Nihad take a Abuja, Mumy ta samu rest of mind, duk da yace sauran bayanan sai ya shigo Kano zai mata amma ta kwantar da hankalinta Nihad is fine and comfortable where she is. Umma ta cika ma Nihal abinci a gabanta, ita dai Nihal ta daura chin dinta a saman gwiwarta tana kallon abincin, Umma ta dawo ta zauna tace “Toh deba ki ci mana” A hankali Nihal ta jawo plate ta fara zuba abincin, Umma dai sai kallonta take don ta rame sosai ba kadan, sannan ba lively Nihal dinta take gani a nan ba, Umma tace “Nihal” Da sauri Nihal ta dago ta kalleta, da damuwa Umma tace “Did you have any problem?” Nihal ta girgiza kai da sauri tace “Aa Umma, i am okay” Umma tace “Na ganki a sanyaye kamar kina da damuwa daughter” Nihal ta girgiza mata kai kawai tace “Ba komai Umma” daga haka ta ci gaba da dibar abincin da take, Umma na ta kallonta tace “Ko dai Nihad kike tunani har yanzu Auta?” Lokaci daya taga hawaye ya kawo idon Nihal, nan da nan hankalin Umma ya tashi, ta mike don a duniya babban tashin hankalinta kukan Nihal ko kuma damuwar Nihal, Umma tace “Yanzu meye abun kuka? Wallahi in dai Nihad ce ni sai in sa duk inda take a samota in hakan ne xai sa ki daina damuwa, in ma kauyen xaki je ki masu kwana biyu sai kije in dai wannan ne damuwarki Nihal” Nihal dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, nan Umma ta hau lallashinta tana jin kukan nata har cikin ranta. Da yamma Umma ta dau makullin mota ta fita sai gidan Hajiya Turai, bayan sun gaisa Umma tace “Anya turai baxa ki sake rakani gidan malamin nan ba a sassauta abin nan da yayi” da mamaki Hajiya Turai tace “Saboda me?” Da damuwa Umma tace “Toh Nihal ce har yanzu na rasa gane kanta wallahi, duk ta sukurkurce, kinsan sun shaku sosai da er uwar, wallahi daxu da naga test script dinta sai da hankalina yayi mugun tashi, Nihal da bata taɓa faduwa a makaranta ba, gashi shekaran karshe take, a’a gaskiya mu je a sassauta abin nan Turai” Hajiya Turai tace “A karya asirin kenan nufin ki?” Umma tace “Aa, a karya kuma?? Cewa nayi fa a sassauta yanda dai Uban zai bar Nihad din ta shigo gidan amma babu yabo babu fallasa sannan ko sisinsa baxai shiga hannunta ba balle na dreban, kin dai gane ai, ni dai in samu hankalin ‘ya ta ya kwanta, ta ci gaba da karatunta cikin aminci” Hajiya Turai tace “Amma abun da mamaki, tun da can bata daga hankali haka da abun ya faru yana zafi zafi ba sai yanxu?” Umma tace “Ke kuwa sabo, nima dai farko naga bata yi haka ba duk da ta damu gaskiya, amma wai daga zuwa makaranta shkkn abu ya lalace, Sai ma kiyi ta kiranta a waya bata son dagawa, gaba daya tayi sanyi yanda kika san an zare mata laka, wallahi abun na damuna, kuma nasan saboda er uwarta ne, gashi yanzu naga uban ma yana jan ta jiki tunda ba Nihad din, ko Shekaranjiya ce min yayi xai canxa mata laptop, to taki kwantar da hankali” Hajiya Turai tace “Toh sai mu koma gobe” Umma tace “Yauwa Hajiya turai, sannan ita ma Kamila ina son a kara aiki akan mijinta, don suna ta samun matsala kwanan nan, ita kuma Nihal wani da minister ya fito yana sonta shi ma sai ayi aiki a kai” Hajiya Turai tace “Duk Allah ya kai mu goben” Umma bata jima a gidan ba tayi mata sallama ta kama hanyar gida.
Dab da magrib Nihad ta gama shiryawa tana tsaye gaban mirror tana daura Nikab dinta sai ga Mimi ta shigo ita ma ta shirya, Mimi ta wani ɓata fuska tace “C’mon plss where r u going with this mask, ba fa school xa mu je ba” Bata jira me Nihad xata ce ba ta kwace Nikab din, Nihad ta juya tana kallonta don khalil ne yace ta sa Nikab din, da tayi niyyar baxata sa ba amma kuma kawai ta dauko daga karshe, Mimi na girgiza kai tace “Don Allah ki dau mayafi ki yafa mu fita, we are not going to school fa, beside this is evening” Nihad tace “I am more comfortable with the Nikab Mimi” Mimi tayi shiru tana kallonta, Nihad ta mata murmushi ta amshe Nikab din a hannunta ta shiga daurawa, Mimi ta daga kafada ta fita daga dakin xuwa parlon Mami, ganin Khalil zaune parlon tace “Yauwa yayanmu pls ka kai mu mana since u are around, i don’t want to be escorted” Ya kalleta sai kuma yayi kasa da murya yace “Tell Mami so” Da sauri ta shiga daki wajen Mami tace “Mami since yayanmu yana nan ya kai mu can gidan mana” Mami tace “Ohk” Mimi tayi murmushi ta juya ta fita ta kulle mata kofa, Tana kallon Khalil tace “She said ohk” Daga haka ta fice daga parlon. Mimi ta sauka downstairs tare da Nihad bayan Bilkisu ta kai masu kayansu waje, dai dai stairs din karshe Nihad ta makale jikin rail din staircase din tana kallon wanda ta gani zaune parlor ko kiftawa babu, yana tare da 3 of his frnds ga drinks da kaza with small chops a gabansu, they were all gisting suna dariya, Mimi ta kalleta ganin kamar she is shock tace “What happen Nihad?” Nihad tayi backing parlon da sauri kamar xata koma sama tana zaro ido ta cikin Nikab din fuskarta, Mimi ta kama hannun Nihad da mamaki tace “Are you alright?” Nihad ta kasa cewa komai xuciyarta na heaving, Mimi na rike da hannunta tace “Nihad” Da sauri Nihad ta kalleta, with confusion Mimi tace “What happen?” Nihad tayi karfin halin cewa “Nothing, nothing” Mimi ta kama hannunta suka sauka daga stairs din, kin kallon inda su Aliyu suke tayi tana makale da hannun Mimi tana shige mata kamar xata harde ta fadi, gaba daya mamaki ya cika Mimi, Can dai Mimi ta kalli su Aliyu da suka bi su da kallo tace “Yaya sai mun dawo” Yana kallonta yace “Ohk” Daga haka suka fita daga parlon tana rike da hannun Nihad, Mimi ta kulle kofa tana kallonta tace “Kin san wani a cikinsu ne?” Nihad ta hadiye wani abu da kyar ta girgiza mata kai, Mimi dai ta dinga kallonta, Nihad tayi karfin halin cewa “Who is the guy in white?” Mimi tace “He is my cousin brother, did u know him?” Nihad ta kasa ce mata komai tana kallonta babu ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata ga wani jiri da ke dibanta, ta dinga nanata kalmar cousin da Mimi ta furta mata a zuciyarta, Can Nihad tayi karfin halin cewa “Can i know his name pls??” Mimi tace “Aliyu, his name is Aliyu Iliya, yayansu Sajida and Farhana” a hankali Nihad ta dinga gyada mata kai amma ta kasa cewa komai, Mimi tace “But don Allah ki gaya min, kin san sa ne? U reacted as if kin ta6a saninsa” Da sauri Nihad ta girgiza kai amma ta kasa cewa komai har sannan, bayan few seconds tayi karfin halin cewa “What is his relationship with ur brother?” Mimi tace “Of course they are cousins, my brother is Ibrahim Khalil Jikamshi, while he is Aliyu Iliya, mum dinsa ita ce Aunty Hassana ai kin santa….” Nihad was Baffled, taji zuciyarta na wani irin bugawa tace “Jikamshi?” Mimi tace “Yeah, that’s my father” Mimi ta wara ido tace “You mean all this while baki san gidan da kike ba?” sunkuyar da kai Nihad tayi a hankali tana jin jikinta kamar an zare mata laka, Mimi dai sai kallonta take, can dai Mimi tayi murmushi ta kama hannunta suka bar wajen, Har suka isa mota Nihad jan kafa take tana ganin komai kamar a mafarki, a ranta kuwa ta fadi Aliyu Iliya ya fi sau goma, for the first time she felt life had never been nice to her, she’s been deceived in so many ways by so many people, Umma, her frnds, and now Aliyu, nothing was in her favor during her pass, a yan kwanaki kadan taga abubuwan da bata ta6a zato ba a lkcn da bata ta6a tunani ba, a yan kwanakin nan ta fahimci not everything is as it seems, she felt so stupid of her self at this point, tayi da ta sanin abubuwa da yawa na rayuwarta a baya, she wish she can amend things, but how will that be possible, Mimi ta dinga kallonta bayan ta bude mata back seat amma taga bata shiga ba alamar tayi nisa tunanin da take, kamar ma bata san sun kai parking space din ba, a hankali Mimi ta dafata, firgit Nihad ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, Mimi ta nuna mata motar, Nihad ta shiga da sauri trying all possible best kar ta bar hawaye ya taru idonta balle har ya kai ga zubowa, why she?? Why is all this happening to her?? Mimi ta zaga ta shiga gaban motar, sai a sannan Nihad ta daga kai suka hada ido da khalil dake kallonta ta madubi, sosai gabanta ya fadi, kuma bata taɓa jin kunyar duk abubuwan da tayi masa ba sai yau, she felt so ashame of her self, yau ne taji kunyarsa na gaske, a kwanakin baya tana jin guilt a xuciyarta na abubuwan da suka faru amma na yau ya wuce misali, and she remembered vividly ranan da ya kai ta Wellcare wajen Aliyu da abinda ya faru, yanda ta cakumesa a wuyar riga raining all sort of insult on him, bata san sanda ta hade kai da gwiwa ba wasu hawaye masu zafi suna sauka idonta, many things are not as they seem, truly not everything is as it’s seems, ta yaudari kanta sosai a baya, Khalil ya tada motar suka bar gidan, sai da suka yi nisa ya kalli Mimi yace “Ba ki bukatan komai?” Mimi ta ɗan buda ido tace “In dai expenses din na kanka” Ya ɗan yi murmushi yace “Ohk, where are we going now?” Ta kira masa wajen wani shopping, nan ya dau hanyar zuwa wajen, suna isa yayi parking ya ciro Atm card dinsa ya mika mata, ta amsa tace “I thought tare xa mu shiga” Yace “Nahh, ke kadai za ki shiga, i have done my part by giving u my card” tace “Can i shop for two?” Ya gyada mata kai, kulle motar tayi ta juya ta bar wajen yana ganin ta shiga ciki ya sauka ya shiga bayan motar, shi da yake bai biyo ta main parlor ba bai san su Aliyu na parlon ba ma, Nihad taji wani kukan ya taho mata jin ya shigo bayan motar, ya dago kanta a hankali yace “Now tell me what’s ur problem” ta kasa kallonsa tana shesshekan kuka sosai, she wish many things didn’t happen, she wish she was so kind to everyone back then, bata taɓa sanin Umma bata sonta ba sai da Aunty Maryam ta ganar da ita, she encouraged her to be mean to everyone, ya cire nikab din fuskarta yana kallonta, ta boye fuskarta da sauri wani kuka ya taho mata, kunyar hada ido da shi take, ya jawota jikinsa ya rungumeta a hankali yana kokarin kai hannunsa in between her legs yace “Does it hurts har yanzu?” Bata san sanda ta zaro ido ba ta rike hannunsa da sauri, closing her leg tightly tace “Aa” Yace “Then what?” Shiru tayi bata ce komai ba tana sauke ajiyar zuciya a jikinsa, she felt a bit relieved, tana jin breathing dinsa a fuskarta kamar me rada yace “You need the phone?” Shiru tayi Idonta a rufe bata ce komai ba tayi lamo a jikinsa, Shi ma bai kuma ce mata komai ba ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali, Nihad ta bude ido tayi karfin halin cewa “Me ya kawoka gidanmu?” Bai bude ido ba still yana taɓa kafarta yace “We should ask Habibu that” Da sauri ta daga kai ta kallesa, da sauri Khalil ya saketa ganin Mimi ta fito daga mall din rike da just er leda, ya bude motar ya sauka ya koma front seat, tana karasowa ta shiga gaban motar ta ajiye ledan hannunta tana Murmushi tace “just 2 perfumes” Yace “You are not serious” Dariya tayi, ya tada motar suka bar wajen. Har suka isa anguwansu Nadeeyah Nihad bata daina tunanin abinda yace mata ba wai they should ask Habibu, how did he know Habibu, gari yayi duhu suka iso gidansu Nadeeyah don har an idar da magrib, bayan yayi parking ya sauka motar, Mimi ta sauka ita ma tana rike da ledan turaren da ta siyan ma ita da Nihad, Nihad ta sauka daga cikin motar, Mimi tace “Bari in kira me aiki ta dau mana kaya” Daga haka ta wuce ciki, Nihad ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Khalil taga kallonta yake da sauri ta sunkuyar da kai ta juya zata bar wajen ya fizgota ya hadeta da mota yana kallon lips dinta, gaba daya ta rikice don mai gadi na zaune kusa da gate, ta fara turasa zata bar wajen sai ga Mimi ta fito tare da Nadeeyah, da sauri ya saketa ya bude driver seat kamar zai dau wani abu.

Kika karanta min littafi baki biya ba bashin dari biyar a kanki har duniya ta nade. Ehe 😌

 

Click Here To Read Nihaad Chapter 51 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

 

Nihaad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

 

Back to top button