Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 76 By Hafsat Bature Complete Novel

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

Cigaban page 76

“Nifa lafiyata qalou, Nagode da kulawar ku agare ni, nayi missing ɗinku sosai,” Cikin sanyin murya ya furta hakan, A hanzarce Batul ta miƙa hannu ta kunna fanfo ruwa ya soma zubowa, tarba tafin hannayen ta tayi Ruwa ya taru a cikinsu ta wanke mashi fuskar shi tare da zuba mashi ruwan a bakin shi Ya kuskure shi, Bayan ta kammala ta ruƙo hannun shi “Mu koma ɗaki Mubeen” Sai da suka taimaka mashi tukunna Ya iya miƙewa, fitowa su ka yi daga Cikin toilet zuwa ɗaki, A saman gadon Shi Ya kwanta Yana faman sauke ajiyar zuciya, kewaye da gadon shi suka tsaya suna tottafa mashi addu’o’i, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, bayan sun samu komai ya lafa suna shirin komawa su zauna Kwatsam Gabriel Ya farka Hananyen shi biyu daddafe da kanshi Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara da ta janyo hankulan su Gare shi, Jikin shi sai kerma yake yi musamman la66ansa, Sambatu ya ke yi na fitar hayyaci, A hankali Su ka soma tafiya suna tunkarar gadon shi, A kewaye da gadon shi suka ja burki suna ambaton sunan shi Muryoyin su a tsorace

“Gabriel! Meke damun ka? Faɗa mana ina ke yi maka ciwo,” Shiru bai tanka masu ba, Hankalin Azeeza duk yafi tashi don tuni tafara sharar ƙwalla, tsananin tausayin shi ne ya kama su, musamman da ya daddafe kanshi sai ya tuna masu da Danish, duk idan ciwon shi ya tashi haka ya ke yi masu ya dinga fasa ƙara,

“Gabriel are u okey? Kan ka yana maka ciwo ne”? Azeeza ce ta ke tambayar shi, Deeja tace “Ku ɗan jira in jaraba yi mashi Karatu kamar yarda Angel ta ta6a Yima Danish wata’ƙil shima yaji sauƙi, ta ƙarasa maganar tare da hawa saman gadon ta matsa kusa dashi ta tallabo kanshi da yatsun hannayenta tare da ɗago dashi, Saitin kunnan shi na dama ta kai bakinta, Kafin a tsanake ta soma Yi mashi karatun qur’ani, surorin da ta haddace akanta, fatiha, iklas, Falak da nasi, da wasu ayoyi irinsu Ayatul kursiyyu, Amanar rasulu da sauransu, A nutse Deeja take karanta mashi su cikin kunnan shi, su Parveen duk suna a tsaye bakin gadon suna kallon shi azeeza tana zaune daga gefen shi, ga dukkan alamu natsuwa ta fara shigar shi, don tun da ta fara Jikin shi ya daina kakarwa, natsuwa ta fara shigar shi, A hankali ta zame Hannayenta daga saman kanshi,

“Da sauƙi jikin naka”? Tayi maganar tana kallon fuskar shi, sai faman lumshe idanuwan shi ya ke yi, daƙyar ya iya buɗe baki Ya amsa mata da cewa “Am ok, Ina fata mun same ku lafiya,” har suna haɗa baki wurin furta mashi “Muna Lafiya” parveen tace “faɗa mana su wanene mu, don ni ban yarda ka dawo dai dai ba,” A hankali ya ke kallon fuskokin su ɗaya bayan ɗaya Ya soma faɗa masu sunayen su

Hannah Hibba Deeja, Parveen, Eve, Yasmin, Batool, Rubina, Aziza, Sarah, Jamima…….” tunkan ya rufe baki yaga suna ta murna ganin ya dawo dai dai, haƙiƙa Yaji daɗin kulawar su gare shi, Sai dai abu ɗaya daya faɗar mashi da gaba rashin mutun ɗaya acikin su, Yarinyar da ya ƙwallafa rai akan son ganinta, don su dasa daga inda su ka tsaya

“Where’s ANGEL”? Ras gabansu Ya faɗi Jin tambayar da ya yi masu, Nan fa suka fara kallon kallon a tsakanin su fuskokinsu ɗauke da matsananciyar damuwa

“Inna lillahi..! Mun manta da Angel! Tun ɗazu da safe ta shiga toilet ta datse, Ba irin bugun da bamuyi ma ƙofar ba amma ta ƙi buɗewa, bamusan me ta ke yi a ciki ba”

Muryar Haris ce ya janyo hankalin su ga kallon shi, Farkawar shi kenan daga bacci Yana ji suna zancen Babu Angel, Jikin shi A raunane Ya yunƙura Ya miƙe zaune, Da sauri Deeja ta nufi gadon shi ta haye sama ta zauna tana kallon shi,

“Haris Sannu Ya jikin Naka? Ina fata ba inda ke yi maka ciwo” murmushi ya sakar mata yayin da ya ke bin ta da kallo, daga gani ba ƙaramar kewar ta yayi ba,

“Deeja lafiyata qalou, Jiki na da sauƙi, Naji ana zancen babu Angel me ya faru da ita? Ko sun zo sun ɗauke ta ne”?

Girgiza mashi kai tayi alamar a’a “Ɗazu da safe ta shiga toilet yin wanka, bamusan meya faru da ita ba, mun jira ta buɗe mana ƙofa amma shiru, mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wurin ganin mun 6alle ƙofar amma taƙi buɗuwa,’ deeja na kai ƙarshen maganar ta, Batul ta jefa masu tambaya “Haris Ina Danish ɗinmu”! Ɗago wa yai da idon shi tare da kallonta, Mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi

“Kamar batul nake gani! Yaushe aka dawo da ke?” Murmushi ta sakar mashi tare da cewa “Tuntuni na dawo, Na yi kewar ku sosai,” Jinjina kan shi ya yi kafin yaci gaba da magana “Bansan inda Danish ya ke ba, saboda ba’a tare mu ke dashi ba, tsawon lokacin nan bamu ta6a Yin tozali da shi ba,” Idon Gabriel akan Batul Sai yanzu da ya dawo hayyacin shi ya gane ta, Yasan cewa ƴar uwar su ce da suke ta nema, kuma itace Yarinyar da ya gani a kwanakin baya saman Third floor Tana gudun ceton Rai! Baisan ya akai ta dawo ba, Sai dai yaji daɗin ganin ta da ranta da lafiyarta.

“Ƴar uwar mu ce Batul, nasan baka santa ba” Azeeza ce tayi mashi magana ganin yana kallonta, Numfasawa ya yi tare da saukowa daga saman gadon kamar zai kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikin shi

“Ina zaka je”? Atare su Hibba su ka haɗa baki wurin yi mashi magana

“Inason ganin Angel, ku nuna mini ƙopar toilet ɗin da ta shiga, zan yi ƙoƙari in 6alle ta”

“Kana fama da kanka Gabriel taya zaka iya 6alle ƙofa, tafiyar ma daƙyar ka ke yinta, Pls Ka koma ka zauna bazamu bari ka Ƙara raunata kan ka ba, ” Hannah ce tayi maganar tare da ruƙo hannun shi, ba don ya so ba ya koma ya zauna daga gefen gadon shi.

Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, sun gama murnar dawowar su Haris damuwar rashin Angel ta hana su sakat ga dare har ya gabato amma babu ita, Jamimah sai kuka take yi masu akan Su Je su buɗe ƙofa su ɗauko Mata Genie ɗinta Idan suna son zaman Lafiya, Sun saba atare su ke kwaciya bacci, kwanakin nan ita ke yi masu shimfiɗa a saman floor.

Komawa Cikin sashen toilet ɗin su ka yi, Don su ƙara jaraba ƙarfi ko sun samu ƙofar ta buɗe masu, Gabriel da haris sun so su taimaka masu Wurin buɗe ƙofar sai dai sun hanasu yin hakan saboda babu ƙoshin lafiya a jikin su.

Kukan Jamimah Ya karaɗe Cikin ɗakin su, Hatta Javed da Naufal sai da su ka farka daga bacci saboda sautin kukanta daya cika kunnuwan su, Taƙi samun wuri ta zauna, Ga uban bargon data zumbula a jikinta, Angel ta rufe mata uniform a cikin toilet shiyasa take ta yin zarya da bargo, Kanta har ya fara sara mata, Gabriel ne ya miƙa mata hannu tare da ambaton sunanta, Kamar jira ta ke yi da gudu ta nufi gadon shi ya ɗauketa saman jikin shi yana lallashinta, cikin shesshesƙar kuka take ce mashi “Dan Allah kaje ka ɗauko mini Genie ɗita, tun ɗazu tana a cikin toilet, ƙofa ta rufe da ita sunƙi su taimaka mata, Uniform ɗina ma suna a ciki itace ta yi mini wanka tace zata Wanke mani su, in sun bushe sai in saka su a jiki na….” duk ta cika shi da surutun ta, shi kanshi hankalin shi ba a kwance ya ke ba, Kowa da abunda yake saƙawa a ranshi dangane da rashin Angel gani su ke kamar fa an ɗauke ta shiyasa taƙi buɗe ƙofar, saboda babu alamun mutun acikin toilet ɗin, Ko motsi wannan baka Ji.

Ina Angel ta shiga meya faru da ita?

abunda ya faru Lokacin da Angel ta zuƙunna a gaban tukunyar fulawar nan, Hankalinta ba’a kwance ya ke ba, tun da ta fahimci Furen Danish, Azalzalar da zuciyarta ke yi mata akan taje ta nemo shi taga a wani hali ya ke ciki shi yaja hankalinta, miƙewa tayi a fujajen ta nufi glass window ɗin nan ta sanya Hannu ta sauke glass ɗin ta dire shi ƙasa Jikin bango, duk da irin tsoron da take ji hakan baisa ta fasa ƙudirinta ba, Bayan ta janyo bokiti ta haye sama sai da ta fara Ambaton Bismillahi da kyakkyawar niyya tare da wasu addu’o’in neman tsari masu ƙarfi Kafin ta daddage ta haura tagar ta duro ta bayanta, tsananin tsoro ne ya kamata da firgici Amma a haka ta daure ta cije saboda idanuwan ta a makance suke bata ji bata gani burinta Kawai ta gano inda Danish ɗinta Ya ke, Cike da ƙwarin gwiwa ta miƙi doguwar hanyar nan wadda zata sada ta da ground floor ɗin Gidan kurkukun, Tana tafiya tana ambaton sunan Allah, Duk addu’ar da tazo mata a cikin bakin ta karanta ta take yi, hada ɗan gudu gudun ta wurin yin tafiyar, lokacin da ta kawo ƙarshen hanyar ta faɗo ta cikin babban Filin dake a kewaye da waɗannan Dogayen benayen, Ras taji gabanta ya faɗi tunawa da abunda ya faru da ita a rana ta farko da ta fara zuwa wurin, ba zata ta6a manta irin baƙar wahalar da tasha ba, A tsananin tsoroce take ƙare ma benayen kallo don ta ga ko zasu motsa kamar yarda su ka yi mata aranar farko, ganin sunƙi Motsawa yasa ta soma tafiya Cikin sanɗa tana tunkarar su, shiru baka jin hayaniyar komai, ita kaɗai kwallin ƙwal kamar ba mutane A gidan Kurkukun.

Har ta kai bakin benan ta soma Jin sautin Wata shaƙaƙƙiyar murya tana ambaton sunanta, A gigice ta juya tana kallon bayanta don taga wanene Sai dai bata ga komai ba, Sautin dariya mai kama da haniniyar Doki ta dinga Ji a cikin kunnuwan ta, Tuni zufa ta wanke fuskarta sharkaf, Can kuma ta dinga jin kukan jarirai Enyaaa enyeeh, Da sauri ta toshe kunnuwan ta da tafin hannuwan ta, bugun zuciyar ta na ci gaba da hauhawa, Jikin ta ya hau rawa, Saboda taurin kai irin nata a haka ta soma hawa benen la66anta na kerma wurin ambaton sunan Allah, ba zato ba tsammani taji Matattakalar Benan ta soma Motsawa, hakan ya sa ta daddage ta watsa da gudu tana haura matattakalar Yayin da benan ke mayar da ita baya har tuntu6e take yi ta kife Ƙasa, Staircases ɗin suka dinga janyeta suna mayar da ita baya kamar zasu saukar da ita daga saman gadon, Cikin zafin nama ta ɗago da kanta tare da miƙewa ta dinga gudu zufa na bin jikinta har sai da Allah ya bata nasarar kaiwa ga Second Floor, Ta ƙarfi ta buga tsalle ta haye sama tana faman Haki, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, Ƴan hanjin Cikinta sai kaɗawa su ke Yi, A hankali ta yunƙura ta miƙe tsaye tare da juyawa tana kallon benan, Wani abun mamaki Gaba ɗaya ya daina motsawa sauke ajiyar zuciya ta yi, Angel da kasada taci gaba da tafiya Saman hawa na biyu, Sai faman baza ido ta ke yi tana ƙarewa ginin kallo, tsarin shi yadda kasan Ƴan hanjin Cikin mutun saboda kwana kwanar da ke gare shi, A dai dai Bakin wani corridor taci burki tana leƙa Ciki, Ɗakuna ta hango A jere Kusan guda Huɗu biyu suna fuskantar biyu, Ƙofofin su a rufe su ke sai dai bata da tabbacin Ko an sanya masu Kuba.

“Ya Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abun cutarwa, Ya Allah ka haɗa ni da abunda nazo nemo Cikin sauƙi ba tare da nasha wahala ba,” acikin zuciyar ta take ambaton hakan, ɗaga kafarta tayi tare da nufar Ƙofofin, Hannu ta kai ta ɗan ta6a Jikin ƙofar farko ba zato ba tsammani taji ƙofar tana lilo alamar a buɗe ta ke, Sai da ta fara karanta addu’ar neman tsari ba tare da Jin tsoro ba, ta faɗa Ɗaya daga Cikin ƙofofin, wurga ƙafar ta ke da wuya wani uban wari ya daki hancin ta, Idanuwan ta a zazzare ta ke ƙare ma Ɗakin Kallo, tamkar Igiyar Shanya ce kewaye A cikin shi ta kowane 6angare, babban abunda yayi mugun ɗaga mata hankali Gangar Jikin Matasan Ƴan mata ta gani da maza Wanda basu haura shekarun su Batul ba, zindir babu kaya a jikin su, An ɗaure wuyan su sagale Jikin Igiyoyin nan kamar kayan wanki da alama Sun gama amfani dasu, wasu An cire nonuwan su,wasu kuma an cire gaban su,Wasu Idanuwan su aka kwalkwale Yayin da wasu kayan Cikin su aka wawake, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!

Wata irin narkakkiyar zufa ce ta wanke ko’ina na jikinta da ke ta yin kerma kamar wadda ake kada ma mazari, duk ta bi ta furgice ganin komai ta ke yi tamkar a mafarki, Hannayen ta daddafe da kanta cikin fitar hayyaci ta fito daga Cikin ɗakin, Maimakon tayi reverse ta koma Inda ta fito sai ta ƙara gaba saboda gushewar da hankalin ta yayi, A gigice Ta fito daga ɗakin Wani irin jiri take gani a cikin idanuwan ta, Hannunta dafe da ƙirjinta Zuciyar ta sai tashi take yi ga wani irin zazza6i da ya lullu6eta.

A bakin Ƙofar ɗaki na biyu ta faɗa tana faman haki, Karaf idanuwan ta suka sauka Akan Giants da ke gudanar da aikin su na Theatre, gadaje ne sunfi talatin Cikin Ɗakin mai faɗin gaske, kowani gado Yana ɗauke da mutun kwance saman shi, Sun fafe cikin su suna ɗibar kayan cikin nasu tare da ɗaura su saman table ɗin da ke a gefen su, A matuƙar razane ta juya tana neman hanyar da zata bi ta Fitar da ita daga Cikin Corridor ɗin, Allah Yaso basu lura da ita ba babu wanda Ya ganta don gaba daya hankulan su na akan aikin da suke kuma basu zaton wata matsala , Watsawa ta yi da gudu Ita kanta batasan inda take tunkara ba Sunan Allah kaɗai ta ke iya ambato a cikin bakinta, adaidai saitin wata ƙopa ta soma jin Wata kakkausar murya tana magana da wani irin gur6ataccen yare mara daɗin ji, A hautsine takai idonta Ƙofar Dogon labule ne launin Ja ya rufe ta, Yatsun hannunta na kerma ta ɗan yaye labulan.

Babban ɗaki ne mai girman gaske kamar palour, komai Na cikin shi Red & black Colour ne, bangon ɗakin Zanunnukan kan ƙwarangwal ne dana kunama, da na wasu halittu masu dogon harshe Da zaƙo zaƙon akaifu irin na shaiɗanu, Zanen su ne ta ko’ina gwanin ban tsoro, Mutane ta gani a jere sunkai su Talatin Kowannan su na sanye Cikin Jajayen dogayen riguna masu huluna, hannuwan su ruƙe da ƙoƙuna masu ɗauke da jini, daga tsakiyar su wasu tiƙa tiƙan mutane ne kusan su Shidda, Yadda kasan Irin malaman Majami’u na ƙasar India, Tumbur babu Kaya ajikin su, Sae dai wani ƙaramin Jan ƙyalle da su ka ɗaure ƙugunan su dashi, ga wani uban tumbi da suka tara, Jikin su bulbul ansha Jini An ƙoshi, Jan fentin da ke saman fuskokin su Ya rufe ainihin Suffar su sun koma kamar dodonni, Sun kewaye wani Dodon tsafi dake a zaune saman armchair, Wata irin halitta mai matuk’ar muni miyau sai zalalowa yake yi daga bakin shi, Zir Jikin shi babu kaya sai uwar yanar da ta nannaɗe gangar Jikin shi tayi mashi tamkar sutura.

A kowace kusurwa ta cikin ɗakin jajayen ƙwaryoyi ne a jere an rufe su da faifai, Ga wasu ƙananun Yara da basu haura 7 years ba mata zuƙunne saman gwiwowin su babu kaya a jikin su, gabansu ca6a ca6a da jini, daga gani amfani aka yi dasu.

Wani ikon Allah duk tashin hankalin da idanuwanta su ka yi tozali dashi baisa ta kurma ihu ba saida taga waɗannan yaran ƙananu tukunna sautin muryar ta ya dawo har ta ƙware Baki zata Kurma Ihu ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun saman bakinta, sosai Ya toshe mata baki! Batasan wanene ba hakan yasa ta zazzare idanuwan ta waɗanda su ka kaɗa su ka yi jawur dasu, tsoro da firgici ne.

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

 

Back to top button