*💃LAIFIN DAƊI ƘAREWA💃*
Join this link to follow my tiktok acct👇
@boss_bature
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags
Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃
Tun bayan sallar Asuba sehrish ta koma bacci,ringing ɗin wayarta ya tayar da ita,lalubo wayar tayi ta duba me kiran nata,Murmushi tasaki ganin Sunan Oummansu Ya bayyana,Picking tayi ta kara wayar a kunnanta”Oumma ina kwana,kun tashi Lafiya,”ta yunƙura ta miƙe daga zaune,
On the other hand Oumma tace”Lafiyalou rishina,ina fata kuna cikin ƙoshin Lafiya,”
“Alhamdulillah yanzu ma na tashi daga bacci,”_
“An samu hutu ko?Ae naga hotonanku,kunyi kyau sosai hutu ya zauna maku,”
Murmushi sehrish tasaki”Ina Daddy Oumma,nayi missing ɗinku sosai”
“Ya shiga toilet,nima nayi kewarku sosai,”
“Yaushe zaku zo?
“Kinji ki da wata magana,daliline kawai zai kawo munan kinsan me nake nufi,”
Murmushi sehrish tasaki”Allah ya kawo dalilin nan Oumma,i will keep praying har sai dalilin nan yazo,”
tana jiyo dariyar Oummansu”ina Jahad ina Hosana,duk nayi trying Layinsu ba’a ɗaga ba,”
“Ae yanzu basu isa su farka daga bacci ba,nima ringing ɗin wayarki ne ya tashe ni,kuma naji daɗi sosai,”
“Ina surukin nawa yake”?
“Baidawo ba,tunda suka tafi sallar Asuba,Amma nasan suna akan hanya,”
“Ki gashe mun dashi”
“Zaiji insha Allah,”
Shiru suka ɗan yi kafin Oumma ta kuma cewa”Bansani ba,kowani ya faɗa maki,”
A ƙagare tace”Mekenan Oumma?Banyi waya da kowa ba,babu wanda ya faɗamun”
“To Albishirinki”.
“Goro,”ta faɗi tana murmushi,
“Surukarki ta musulunta”waro ido waje Sehrish tayi,tsabar farin ciki yasa ta duro daga saman gadon ta daka tsalle bakinta yaƙi rufuwa”wayyo Allah Oumma,Mommy ta musulunta”?
Dariya abu tayi”Bayan tafiyarku,ta kar6i addinin musulunci,Nima a wurin Daddynku naji,Yanzu tace batason kowa ya dinga kiranta da Alexandra,Sunanta FATIMA,”wani irin farin cikine Ya lullu6e sehrish,
“Amma na tayata Murna,baki ji irin farin cikin da nake ciki ba,”
“Albishir ɗin bai ƙare ba,Akwai saura,”
A ƙagare sehrish tace”Ina sauraranki Oumma,”
“Ina wannan yayan naku”?aɗan ruɗe sehrish tace”Wanne daga ciki”?
“Ɗan wurin Azmee”A ruɗe Sehrish tace”Ya haroon?Ya dawo?an ganshi?bari na maida Video Call,nan take ta canza kiran zuwa Video,A gaban window ta tsaya ta ɗaga wayar suna kallon juna,kwance Oummansu take asaman gadon dakinta na Gidan Abusufyan wanda su Jahad suka ta6a yin rayuwa aciki,jikinta sanye da kayan bacci,Hutu ya zauna mata yadda kasan baturiya dama jawur take,ta saki gashin kanta gefe da gefe,
Sai faman murmushi suke sakarwa Juna,
“Oumma faɗamun Ya Haroon Ya dawo”?
Jinjina mata kai Oumma tayi”Ya dawo tare da wannan yayan naku,Brigadier general Abuhaisam,Ashe Lokacin da Azmee taba shi kuɗi akan ya gudu yabar ƙasar saboda gudun kada a Yanke mashi hukunci,sun shirya mashi komai na tafiya,Shi kuma yaji bazai iya tafiya ba,Saboda Yana son Ya nemi yafiyarsu Abba,maimakon ya tafi sai ya wuce Jos gidan wani abokinshi ya fara sauka yayi jinya,kafin Bayan wani lokaci yaje gidan shi Abuhaisam din cikin mawuyacin hali,bai 6oye mashi komai ba game da abunda ya faru ya nuna masa yayi nadama,Haisam ya taimakeshi sosai don abunda haroon din bai sani ba shine, lokacin an riga anga Junaid kuma alokacin duk sun san cewa abunda haroon din yake yi ba yin kanshi bane,Shiya kaishi Asibiti yayi jinya sosai,Kafin aka sallamesu,a gidanshi yake kwana,Ko Lokacin da Irfan Ya rasu daya zo gida Baisanar da kowa game da haroon ba,har yazo Shagalin bikinsu Yousouf,duk Haroon Na’a wurinshi,Sai da yaji Labarin Abba na nemanshi,Tukunna Ya nuna yana son dawowa gida,Cikin satin nan suka yi mana zuwan bazata,baki ga yadda ya canza ba,Babu ruwanshi bawan Allah,
Tuni idanuwan Sehrish sun cicciko tab da ƙwalla,
“Allah sarki Ya haroon,Na tausaya mashi sosai,Aunty azmee zata ji daɗi sosai,idan taji labarin dawowarshi,”
“Daddynku ya sanar dani cewa Zasu rakashi can prison ɗin don ya gana da ita,”
“Naji daɗi sosai,Oumma ki gaishe mun dashi,”
“Aikuwa dai yana ta tambayarku,musamman ke,”
“Allah sarki,idan Allah ya kawo dalilin da zaku zo nan,Dan Allah atattaro kowa da kowa yazo,”
Fashewa abu tayi da dariya,daga ita har sehrish ɗin kunya suke ji,Dalilin da suke nufi bakomai bane face Ciki,In sun haihu lokacin suna zasu zo America,”
“Kunyi waya Da mommy azeema ne”?girgiza kai sehrish tayi”a’a,tun jiya dai Da rana munyi waya da ita,
Oumma tace”Yau da safe ta Koma Lagos,Mijinta ya dawo,”
Waro ido Sehrish tayi irin mamakin nan”Dama Mommy Azeema tana da aure?”
Dariya abu tayi”Tana da aure mana,Mijinta business man ne,A dubai yake da zama,atare suke kasuwanci dashi,koda muka Je Yi maku siyayyan kayan lefenku,A gidanshi dake acan muka sauka,Mutumin kirkine Kamar ita haka yake,”
Murmushi sehrish tasaki”Allah Sarki,gaskiya zanso na ganshi mu haɗu,”
Sun jima Suna waya har Daddynsu ya fito daga toilet ya kar6i wayar suka gaisa da Sehrish,kafin tayi masu sallama,tana kokarin ajiye wayar gaban mirror,Taji shigowarshi ɗakin,juyawa tayi tana kallonshi,
“Ya rafayet”ƙarasawa yayi tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta,bayan ya manna mata kiss a gefen fuskarta holding hands dinta yayi”inaso kije ki duba jikin Hosana,”aruɗe tace”me ya sameta”?
“Ba wani abu bane,she’s not feeling well,inaso ki ɗan lallasheta,”Jinjina mashi kai tayi,a hanzarce ta fuce daga ɗakin,Side bed ya zauna,tare da curo wayarshi ya kira layin Abbansu don su gaisa kamar yadda yasaba,duk safiyar Allah sai ya kira Iyayenshi da Surukanshi a waya ya gaishe dasu,
Sehrish na shiga part ɗinsu,suka ci karo da doctor jonet tana ƙoƙarin fita,nan fa hankalinta ya ƙara tashi,Daƙyar ta tsaya suka gaisa kafin ta nufi bedroom ɗin,
Faɗawa ɗakin tayi da sallama abakinta,A kwance ta samu hosana jikinta lullu6e da bedsheet,saman drawer sirinjin allura ne,hada magunguna,
Omar na zaune gefen gadon,fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,baisan da wani ido zai kalli hosana ba,Yadda ta ƙullaceshi aranta zaiyi wuya ya fahimtar da ita,don daƙyar aka dubata tana ihu tana ɗura mashi ashar,dole saida akayi mata allurar bacci tukunna ta lafa,
“Ina kwana Ya omar”juyowa yayi tare da kallonta cikin sanyin murya Ya amsa mata”Lafiya lou Sehrish,”
“Ya mai jiki”?
“da sauƙi,Anyi mata allurar bacci ne,”miƙewa yayi tare da nuna mata gefen gadon”Ki zauna kusa da ita,”ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi a gefen gadon ta zauna,Shi kuma ya koma palour,
Bin fuskar hosana tayi da kallo,lokaci guda ta gane meya faru,murmushi ta ɗan saki”Su Hosana an girma,”
Lokacin da Junaid ya koma bedroom ɗinsu,Still Jahad tana ƙudundune cikin bargo tana bacci,hawa saman gadon yayi Ya zame bargon ya shiga ciki, janyota yayi jikinshi ya rungumeta sosai,Zafin da ya ji ajikinta ne ya tashi hankalinshi,da ƙarfi ya ambaci sunanta”My Juliet”
Ƙasa ƙasa ta amsa mashi”My Romeo”
“Are u okey?Naji jikinki da zafi,Bari naje na faɗa ma Babban yaya,”yana kokarin zame jikinshi daga nata tayi saurin ruƙo hannunshi”My romeo,Banason kowa yasan abunda Ya shiga tsakanina dakai….”ashagwa6e yace”But you’re not feeling well,jikinki yayi zafi,”
“Kada ka damu zanji sauƙi,Kaima naji jikinka da zafi,”
“Amma nafi jin naki”
Murmushi ta ɗan saki,tare da buɗe idanuwanta waɗanda ke a lumshe,Shafa gefen fuskarta yayi”I love u so much My juliet,kin faranta mun raina daren jiya,kamar zan zauce,Ashe dama haka abunnan yake?Sai mutun yaji shi A wata duniya yabi ya rikice,Allah Jahad ƙiris Ya rage numfashina ya ɗauke saboda daɗi…..”bai kai ƙarshen maganarba,tayi hanzarin rufe mashi bakinshi”Its okey,abar maganar,”
Cire hannunta yayi”Zan yi shiru,amma pls ki faɗamun kinji daɗi lokacin da nakeyi….”katse shi tayi”banaso Junaid,banace kayi shiru ba,”
“Am sorry My juliet,but i need a second round,”
Wurga mashi harara tayi”Ka kashe ni ka huta,”gudun kada ya sake yi mata magana yasa tayi saurin cewa”Yunwa nake ji,Bana buƙatar abu mai nauyi,Tea nakeso me ɗan zafi,ka haɗo mun da indomie,”
“Dakaina ma zan girka maki a kitchen,”ya sauko daga saman gadon Ya fuce daga ɗakin,Sae zumuɗi yake yi,Murmushi tasaki cikin sanyin murya ta furta”Inasonka Mijina,”
A ƙa’ida ƙarfe 9 na safe masu aikin Gidan suke shirya Breakfast ɗin gidan A dining,komai nasu a tsare Yake,”
Cikin ƴan mintuna Junaid ya shigo da indomie ɗin da romo sosai ya dafa mata ita,Ya haɗo mata da kakkauran Tea,da taimakonshi Jahad taci abincin,Taji daɗinta sosai,kuma dagaske shi ya dafa mata ita,bayan ta kammala,kwanciya suka yi a rungume da juna,duk da haka bai ƙyaleta ba,sai faman luguiguita ta yake yi,ba yadda ta iya dashi,
Sehrish tashiga zurfin tunani Hosana ta farka A hargitse take faɗin”Allah Ya Isa ban yafema ba,Mugu macuci Azzalumi wlh bana sonka Ya Omar….”hankali atashe Sehrish ta rufe mata bakinta da hannunta”Ya isa haka hosana!Ya Omar kike zagi”atsiwace Ta buge hannun Sehrish”Anje an zaga,Kuma wlh saina faɗama Daddy abunda yayi mun,Ya Omar ɗan iskane,Ni bana sonshi”
Gigitacciyar tsawa Sehrish ta daka mata,Lokaci guda Hosana ta fashe da matsanancin kuka,Sassauta murya Sehrish tayi”Dan Allah hosana kiyi haƙuri,Ki yafe mashi komai ya wuce,Banji daɗin zagin da kike yima Ya Omar ba,Ina son da kike mashi ne?wannan abun fa da yayi maki Sunna ce ta Manzon Allah SAW,kidaina ce mashi ɗan iska Mijinki ne shi,Halak malak,kuma haƙƙinshi ne Ya Amsa a wurinki,Ni kin bani mamaki,Keda zaki taimakeshi yayi komai Cikin natsuwa Amma duk kin bi kin hargitsa komai,Shi kanshi dana yi tozali dashi lokacin dana shigo hawaye fa nagani Akan fuskarshi,duk ya shiga damuwa saboda ke ɗinnan,wannan abunfa ba kanki farau ba,Nima anyi mun,Kuma in mace nason haihuwa dole sai anyi hakan sannan zata samu ciki,kowa da kike gani ta hanyar hakan aka same shi,ko kin manta da abunda Mommy azeema ta koyar damu?”
Tun Hosana na yin shessheƙar kuka har ta dakata da yin kukan tana sauraron Nasihar da sehrish ke yi mata,da alama jikinta ya fara sanyi,
Sai da Sehrish takai ƙarshen maganarta,tukunna Hosana ta soma magana cikin shessheƙar kuka”Shikenan na haƙura,bazan ƙara ba,Amma yanzu zan samu cikin”?
Ba sehrish ba,hatta Omar dake la6e a ƙopar ɗakin sai da ya fashe da dariya,
ɗaure fuska tayi”na tambayeki kinyi shiru,”
Jinjina kai Sehrish tayi”Zaki samu in sha Allah nan bada jimawa ba,Zaki haifama Ya Omar Baby boy or Baby girl”
Fashewa tayi da dariya kamar bamai jinya ba,murmushi Marshal ya saki A yayin da yake ƙarasa shiga bedroom din,Koda suka haɗa ido da hosana ɗaure fuska tayi,tare da kawar da kanta gefe,Miƙewa Sehrish tayi”bari na baku wuri,”
“thank u so much My Sister”acewar Omar,don ba ƙaramin ƙoƙari tayi mashi ba,
Bayan fitar Sehrish ya koma gefen gadon ya zauna,rankwafa yayi saitin fuskarta”Babyn Omar,”A ƙule tace”Niba babynka bace,Babyn Oumma da Daddy ce,”Hannu yasa yaja kumatun ta”Am Sorry My Hosana,Yanzu ba gashi Anyi an wuce wurin ba,Saura jiran tsammani ko bakyason Baby ne,”
“Inaso”ta bashi amsa a shagwa6e
“Yawwa,ki cigaba da bani haɗin kai,Nan da ɗan wani lokaci buƙatarmu zata biya na samun baby”Da wayau da wayau ya shiga lallashinta,sai gashi ta sauko sosai,hankalinsa ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
Lokacin da Sgr yayi ma Sehrish Pt,result ɗin ya nuna positive,Farin ciki kamar wanda akayima albishir Da gidan Aljanna,Yini suka yi Manne da juna,ko ƙwaƙƙwaran motsi baiso tayi saboda cikin jikinta,tasha tarairaya,saboda cikin ga kuma laulayi da ta fara yi,Sgr Ya bata haƙuri game da zuwansu Honeymoon,Ya lallasheta akan tabari cikin nata yayi ƙwari sai su tafi,batayi mashi musu ba duk da ba haka taso ba,ba ƙaramin kulawa take samu a wurinshi ba,ya sanya mata ido sosai,Har masu aikin gidan Ya ba Umarnin su sanya mata ido,Da zarar sunga tayi gudu su sanar dashi,don ya hanata,gata gwanar yin tsalle tsalle,amma in har yana gida Har swimming pool suke shiga tare suyi nishaɗi aciki,suna jin daɗin hakan sosai,babu yadda batayi da Sgr ba akan karya sanarma kowa cewa tana da ciki,Ae tun a ranar da ya gane cewa tana ɗauke da ciki Ya kirasu Abba ya sanar dasu,Kowa saida yaji,Aka dinga kiranta daga gida Nigeria anayi mata Congratulation,tasha tsokana wurin Oummansu lokacin da ta kirata a waya,duk kunya ta cikata,Omar ma yayi farin ciki sosai,har shagali sukayi acikin gidan,batare da sunyi inviting ɗin kowa ba,A ranar Ya bata Special gift ɗinta Na key ɗin Mota,danƙareriya sabuwa fitigil Cikin Ledarta,ƙirar Bugatti chiron Kamar zatayi hauka ranar saboda tsabar Farin Ciki,Bata iya tuƙi ba,Yace da kanshi zai koya mata,Tun ranar suka fara ɗanɗana motar da zasu fita Tour (yawan buɗe ido),Zafafan hotuna suka ɗauka a beach(ga6ar teku)sunje cinema,Wurare daban daban suka je,lokacin da cikin Sehrish yakai 3 month,Suka shirya tafiya honeymoon ganin lafiyarta lou,ko kwaikwan ciki bata yi,A private jet ɗin Sgr suka yi tafiyar,Uk suka fara zuwa kamar yadda Mommy ta basu shawarar suje saboda akwai ƴan uwanta dake acan,Da kuma Sydney Australia,daga cikin ƙasashen da suka je Hada Turkey,Dubai,India,korea,ƙasashe daban daban,daga ƙarshe suka je Saudi Arabia sukayi Umrah,sun yawata sosai,Kafin su dawo Jahad da hosana Allah Ya albarkacesu da samun Ciki tun basu daɗe da yin tafiyar ba,A lokacin Cikin Sehrish ya tsufa,sati uku kenan da dawowarsu Los angeles,Ta fara naƙuda kamar bazata rayu ba,Hankalin kowa ya tashi,A katafaren Asibitinshi dake anan L.A aka kwantar da Sehrish,dole sai anyi mata C.s,ba ƙaramin tashin hankali Sgr ya shiga ba,tsoranshi kada Ya rasata,a ƙarshe da yaji bai iya jurewa,shiga ɗakin da za’ayi mata aiki yayi domin ayi atare dashi,Dama kullum saita roƙeshi akan Ya tsaya akanta a lokacin da zata haihu bataso kowa ya kar6i haihuwarta in bashi ba,cikin sa’a Akayi mata aiki,aka ciro mata triplet ɗinta,Kyawawan gaske,Sgr kamar zai zauce saboda tsabar farin Ciki,Zaratan samari ta haifa mashi guda biyu mace ɗaya,Farare tass dasu,kamannin Mazan sak irin na Sgr,hatta ƙwayar idonsu blue ce irin tashi,Macen kuma Sak kamannin fuskar Sehrish ne Amma Ƙwayar idonta blue ce irinta Ubanta,Kuma Hasken fatarta irin nashi ne,baturiya sak,Amma kana kallonta kaga sehrish,Tubarkalla ma sha Allah,Hada ƴan jarida suka zo ɗaukar rahotan haihuwar matarshi,Jariran Sunyi farin jini sosai,Kamar za’a lashesu,kowa sonsu yake yi,sai ɗaukarsu hoto akeyi,Omar yadda kasan Shi akayima haihuwar,Saboda farin ciki hada ƙwallarshi,
Haihuwar tazo mata da sauƙi,bayan da suka dawo gida,Anan Sgr yaci gaba da jinyarta tare da likitarsu ta gida,triplet ɗin data haifa Suna da ƙoshin Lafiya,Har tsokanarta Sgr yake yi,yana cewa yafita ƙoƙari shiyasa Suka ɗauko kamanninshi,next time ta bada himma sosai a samo masu kama da ita,a duk lokacin da yayi mata wannan Zolayar dariya yake bata sosai,
A can gida Nigeria,Lokacin da Labarin haihuwar Sehrish yazo masu,Tuni sun fara shirye shiryen Zuwa Suna America,Mommy tayi farin ciki sosai,ba ita kaɗai ba, mutanan gidan gaba ɗaya,kowa murnar haihuwar sehrish yake yi,Har video Call Sgr ya kirasu ta hanyar laptop din fawan da ya Ajiyeta a Palour,Ya kira kowa na gidan Suka taru suna kallon Ƴan ukunshi dayake nuna masu,kwance saman gado,an sanya masu kayan sanyi,Sunyi murna sunyi farin ciki sosai,
Saboda Shagalin Sunan da za’ayi a U.S,Matasan gidan suka ɗauki hutun aikinsu,dama an basu hutu tuntuni,tun lokacin da suka Farmaki Tawagar miyagun da suka addabi ƙasar,Aka Yankar masu hutu maitsayi basu yi ba,Gaba ɗayansu suka shirya halattar sunan,hada Amaren da akayi bikinsu Bayan tafiyarsu Sehrish,Waɗanda aka sanya bikin auransu,Hafsat da Ya Mu’allim da kuma Najeeb,khaleed da talal,Hada Na jos Abuhaisam shima ba’a jima da yin Auranshi ba,
Babu wanda yayi tsammanin zuwansu U.s,Sai dai kwatsam Aka gansu,gaba ɗaya Hadasu Abba da Mommy,Oummansu da Uncle abusufyan,Hajiya azeema da gwaggon katsina,Kanal yusif da amrish,Fawan Da matarshi,Kowa da kowa hada Haroon akayi tafiyar,Sunyi farin cikin ganin ƴan uwansu,A gidan kowa ya samu masaukinshi,Gagarumin bikin Suna aka shirya,A ranar sunan kowa Ya ɗauki wanka,Mai jegoma akayi mata ado na musamman Aranar ta sanya sarƙar gold ɗin da Sgr ya bata ta sadakinta,haɗaɗɗiyar gaske,Mai matuƙar ɗaukar ido,Kayan hausawa suka sanya,A masallaci aka raɗa sunan Jariran,Mazan Sunci sunan Abba dana Omar,Ita kuma macen taci sunan Oummansu Sehrish wato Zainab,Ba ƙaramin dadi iyayen suka ji ba,Musamman abu,Taji daɗi da Sgr yayi mata kara yasanya ma Ƴarshi sunanta,Haka Abba ma Yaji daɗi sosai,Omar yafi kowa farin ciki,Tun a lokacin yayi alƙawarin in har Hosana ta haifi ɗa Namji,Zai sanya mashi sunan Rafayet,
Bayan anyi suna da sati guda,Su kanal Yusuf suka shirya tafiya Honeymoon ɗinsu da basu samu sunje ba,gaba ɗaya matasan gidan suka shirya tafiya,Kowa da kowa,tun daga kan Yusif,Ayan da jahan,Fawan,khaleed,najeeb,Talal,harda su Ya mu’allim,Duka tare da matayensu,Sgr ya ɗauki nauyin tafiyarsu,Yanzu gidan ya rage Saura su Oummansu,Mommy,Hajiya Azeema,gwaggon katsina,dasu Ishaq da hajjaju,domin kuwa hadasu akazo U.s ɗin,sai Haroon,Duk yaƙi sakin Jikinshi,Har yafiya ya nema awurin Sehrish,Ta nuna mashi cewa komai ya wuce a wurinta,Shima ya manta kawai,Yaji daɗi sosai,musamman da ta bashi shawara akan Ya samu mata yayi auranshi,Bakowa tazo mashi aranshi ba,face Hayaam duk cikin matan da yayi mu’amala dasu ita kaɗaice Yayi mata ba’atare da son ranta ba,Ya haiƙe mata,shi kanshi yasan bai kyauta mata ba,Yanzu itace a tunaninshi,Ya gama yanke shawara da zarar sun koma Nigeria zaiyi magana da Abba,A nema mashi auranta,dama Abuhaisam yayi mashi alƙawarin da zarar Ya samu wadda zai aura,Zai ɗauki nauyin komai na bikinshi, bayan tafiyarsu Yousouf Honey moon da Sati ɗaya,Aka ɗaura auran Eva tare da Amstrong A church,bakowa bane Ya haɗasu ba face Sgr,gaba ɗaya saida suka halacci ɗaurin Auran,Abun burgewa Sgr ne yayi mashi babban aboki,kuma aranar Amstrong Ya kar6i addinin musulunci,Saboda kyautatawar da Sgr yayi mashi,Ya nuna yana ra’ayin komai nasu ya zo ɗaya,dama addinine Ya bambantasu,Yanzu Ya musulunta Ya ci sunanshi Muhammad,Bayanshi Uncle Donald ma Ya kar6i addinin musulunci saboda Ƙanwarshi da ta musulunta,Wato Mommyn su Junaid,Ganin Haka yasa ya’yanshi duk suka Musulunta suma,ba ƙaramin farin ciki suka yi ba,
Tsawon Watanni da tafiyarsu Kanal Yusif honeymoon,Aranar da suka dawo,Jahad da Hosana suka sauka a lokaci ɗaya,Allah ya albarkaci Junaid da samun Tagwaye Mace Da Namiji,Hosana kuma ta haifi Namiji ɗaya,duk zumuɗinta da haihuwa sai da tayi ƙorafi hada kukanta,Don me zata haifi ɗan ɗaya,Sehrish ta haifi uku,Jahad ta haifi Biyu ita kuma sai aka bata ɗan ɗaya,6alli ta tada masu aranar,Ta hana kowa sakat da koke kokenta,Har sai da Oummansu tayi mata nasiha sosae ta nuna mata in ta gode da wannan Allah sai ya bata fin dayan in zata kara haihuwa,amman in tana yin hakan tamkar bata gode mashi bane kuma hakan yana iya sawa taki ma kara haihuwar,jin hakan yasa ta haƙura,Ga Jinjirinta kyakkyawan gaske,Kamanninshi sak irin nata,Komai na Hosana yaron ya ɗauko Omar ba ƙaramin farin ciki yayi ba,Allah ya kar6i addu’arshi ya samu ɗa Namiji,A 6angaren Junaid kuwa,Lokacin da aka nuna mashi twins ɗinshi saboda tsabar farin ciki har sume masu yayi,da aka yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo kuka ya dinga yi hawaye jaga jaga akan fuskarshi,Abbansu Ya bashi shawarar ya ɗauro alwala yayi salla,Ya nuna godiyarshi ga Allah,
Aranar Sunansu Jahad,Tagwayen Junaid,An raɗa masu sunayensu Macen Aka sanya mata Sunan Auntynsu AZEEMA,namijin kuma Aka sanya mashi sunan Uncle,Wato abusufyan,murna a wurin Mommy azeema da Uncle abusufyan kamar waɗanda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,tagwayen junaid kamar yayi kakinsu Saboda kamanninshi da suka ɗauko,
Ɗan wurin Hosana kuwa Yaci Sunan babban yayansu,Wato Rafayet,Sgr Yayi murna sosai,ranar suna anyi shagali sosai,sun samu kyaututtuka a wurin ƴan uwansu da abokanansu Omar,Har kyautar Motoci Suka samu,Bayan wasu kwanaki da haihuwarsu,Gaba ɗaya suka ɗunguma zuwa Nigeria hada masu jego,A can zasu ƙarasa wankan jegonsu,Daga nan zasu zaga dangi,A sada zumunci kafin su dawo America,Sam Sgr da Omar basu so tafiyarsu ba,Junaid ma anan aka barshi saboda University ɗin da ya fara zuwa,Yana karantar Medicine & Surgery,duk cikinsu shi kaɗaine bai gaji Abbansu ba, yana ji yana gani aka tafi da Jahad da twins ɗinsa har da ƙwallarsa
Bayan sun kammala wankan Jego,suka shirya zuwa kai ziyara,Wurin danginsu,damaturu suka fara zuwa,Sukayi sati biyu acan kafin Suka wuce zariya wurin dangin Abbansu,duk inda sukaje hannu bibbiyu ake tarbarsu,Kowa sonsu yake yi,daga zariya suka wuce Kano,Ziyarar bazata sukayi ma su Maman Sadeeq,Sunyi farin cikin ganinsu sosai,kusan sati ɗaya sukayi a kano,Harsu Hayaam saida suka zo Gidansu Maman sadeeq wurinsu Jahad don su gansu,Hafsat ce ta sanar masu da zuwansu kano ta basu Numbar wayar Sehrish,Ita tayi masu kwatancen gidan sukazo,Hayaam tayi kuka sosai lokacin da taga Ƴan ukun Sehrish,Tabi ta ruɗe ta susuce,Kyawawan gaske,kamar Sgr yayi kakinsu saboda tsabar kamanceceniyar dake tsakaninsu,kafin Su sehrish su koma America,wasu daga cikin amaren Gidan suka haihu,matar Yusuf Amrish,da matayensu Twins da fawan,Amrish ta haifi tsaleliyar budurwa,Yuhana matar Ayaan ta haifi Namiji,Amal Ta Haifi twins maza,ɗaya yaci sunan Irfan,Ɗayan kuma Yaci sunan kakansu Salahudeen,sauran amaren wasu suna ɗauke da tsohon ciki,Sai bayan da akayi shagalin sunansu Amrish,Kafin Su Sehrish suka koma U.s,wurin mazajansu,Sunsha soyayya ranar da suka koma,kusan First night ɗinsu Sgr ya maimaita,Dama sunsha gyara wurin Mommy azeema,musamman saboda zuwansu Nigeria,tazo gidan don ta Gyarasu kafin ta koma ɗakin Mijinta,tamkar amare haka suka koma,
Sgr ya bada shawarar Ayi masu Family planning saboda su samu damar yin karatu,Omar yayi na’am da maganarshi,atare aka sanyasu Makaranta,private school ɗin Mommy matar Uncle Donald,gaba ɗaya S.s.one aka kaisu,duk da su Jahad basu kaiba hanyace kawai akayi masu ga kuma girman da su kai,da taimakon mommy aka yi masu komai.
Tabbas Family ɗin Salahuddeen sunyi babban rashi,wanda Yayi matuƙar girgiza su,na Kakarsu AMMI,Bayan Tayi jinya ta ɗan lokaci,ta koma Ga mahaliccinta,mutuwar Ammi ta girgiza su sosai,Sunji mutuwarta,A ranar Alhamis Ta rasu,A washe garin ranar da ta rasu,Su Sgr suka zo Nigeria,a Damaturu suka sauka don duk suna can zaman gaisuwa,satinsu ɗaya suka Koma America,
Kullu nafsin za’ikatul maut,
Ammi bata dade da rasuwa ba akayi bikin Haroon da Hayaam da farko taki amincewa dashi sai da suka yi waya da hafsat take sanar da ita komae game da haroon ta kuma sanar da ita cewa shi din jinin Abba ne,daga baya ta amince mashi aka daura masu aure,at last dae hayaam ta zama surukar Abba,ba’a dade da yin aurensu ba Allah ya Albarkaci Amani da haihuwar da Namiji sunyi matukar farinciki sun gode ma Allah,abunda suka dade suna nema,da farko amani har ta fidda ran haihuwa taba Abbas shawarar ya kara aure don ta san yana son yara,yace zai yi tunani cikin hukuncin Allah kafin ya yi tunanin sai ga ciki,indeed,Mahakurci mawadaci ne.
Bayan wasu shekaru,Alokacin sauran Amaren duk sun haihu, Kowa da ƴa’ƴanshi,Hada Hajjaju ta haifama Ishaq santalelan ɗa Namiji,Hafsat kuma ta haifi Ƴa mace taci sunan Mahaifiyarta wato Laila,Oummansu Sehrish itama Allah ya albarkaceta da samun Twins Maza sunci sunan Mahaifinta marigayi Baba buzu,Ibrahim da sunan mijin gwaggon katsina wato Nuraddeen,ba karamin farin ciki gwaggo tayi ba harda Dr harris ma yaji dadi sosae,shima suna katsina Saude ta haifa mashi budurwa har yarinyar ta d’an girma sunan gwaggo taci wato Ameenatu,ƙannansu Sehrish Masu kama da Oummansu sak,Jama’a gida ya cika maƙil da jikoki,Dama burin Abba kenan,duk inda ya waiga ƴan jikokinshi ne,Ƴan dugui dugui dasu,tun da yayi retired,Kullum Yana zaune cikin Jikokinshi,Yana wasa dasu,Ya Manyata sosai,kanshi Duk hurhura,Idan yana wasa Da Yaran Abun saiya baka sha’awa ya saka dariya,Har wasan Ƴar 6urun 6urun suke yi dashi,Sun saba da kakansu Fiye da iyayensu,Ya sangartasu sosai,daga zarar wani ya 6ata masu rai,Zasu zo wurinshi kawo ƙorafi saboda Yana goya masu baya,Mafi yawancin lokutta a garden Yake yin wasa dasu,ba ƙaramin nishaɗi yake samu atare dasu ba,sam bai da wata damuwa irin yadda wasu in suka yi ritaya sukan shiga damuwa saboda rashin zuwa aiki kullum sai zaman gida,
*Boss Bature*
*Ga duk Mai buƙatar Karanta Littafin Abban Sojoji Daga Complt a jere Daga Book One zuwa 3 Suyi mun magana ta whatsapp 08103884440*