Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 32 By Ayshercool

Bai tanka mata ba, ya ɗauki kofin shayinsa, ya kai bakinsa.”Dan Allah ka yi magana, menene abun yi yanzu? Ko zuwa zamu yi mu ba ta haƙuri” kallon Allah ya kiyaye ya yi mata.Ta gyara zamanta ta ce “Ka san wani abu? Uwa uwa ce, kuma duk lalacewar ɗanta tana son shi, ba zata taɓa mantawa da kai ba, illata mata ɗa da ka yi, babu faɗuwa a ciki idan mun je mun bata haƙuri, idan dan ɗan wani abu mu bata. Ba yanzu ake ji ba gaba ake ji master, duk rintsi duk wuya kar ka bari wani ya ƙullaceka, sai ka manta ka cutar da mutum, amma nauyin hakkinsa yayi ta ɗawainiya da kai”.Ya shanye shayinsa tsaf, kamar a mafarki ta ji ya ce “Alhamdilillah”Ta ce “Masha Allah, Allah ya ƙara mana wadatar zuci da rufin asiri, mu koma waccan maganar master, dan Allah ka yarda mu je mu bata haƙuri”Ƙwanƙwasa gate ɗin gidan aka fara yi, Al’amin ya tashi ya je ya buɗe.Ɗaya daga cikin yaran unguwar ne marasa ji, ya risuna ya ce “Allah ya ja zamaninka””Ya aka yi?””Wallahi guduma ne suka yi faɗa da dattijonsa jiya, ya kore shi daga gidan ya ce ya bar masa gida, ya sallamawa duniya shi, shi ne yau ya je ya sha wani abu, gashi can ya kulle mai unguwa a gida, da makami ya ce sai ya sara shi, an kirawo jami’an tsaro an kasa buɗe gidan”Ya ce “Mu je in gani” Suna zuwa gidan mai unguwa suka tarar da mutane cirko-cirko a ƙofar gidan, ga ‘yan sanda su huɗu, ana ta fama a buɗe ƙofar gidan an kasa, sai kururwar mai unguwa ta cikin gidan, yana a taimake shi, a raba shi da ɗan sa kan ya kashe shi”Al’amin ya zagaya, ya kama katanga ya dira cikin gidan, ya tarar da guduma a tsaye a ƙofar ɗakin mai unguwa, riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa, sai ƙyalli take yana dukan ƙofar ɗakin, yana maye yana sai ya kashe mai unguwa babansa.Sauran matan gidan da yara, duk sun rufe ɗakuna suna neman ɗauki.Al’amin ya tunkare shi, yana zuwa ya riƙe shi, ya karɓi makamin hannunsa ya kwaɗa masa mari, hakan ya sa ya ƙara gigicewa, ya danƙo rigarsa ya buɗe ƙofar ya fito da shi sai tangaɗi yake yi.’yan sandan suka yo kansu, za su kama guduma, Amma Al’amin ya ce “Zamu zo da shi station anjima idan ya dawo hayyacinsa.Mai unguwa da ya tsira da ƙyar ya ce “Ofusa kar ku bari ya tafi da shi, dama shi yake goya musu bayan iskanci a unguwar nan, da ɗa na bai kai haka lalacewa ba, a haɗa a Kama har da shi”.Al’amin bai kalleshi ba ya ce “Ko ya gudu ni a kama ni, ba zai gudu ba, idan ya dawo hayyacinsa zan kawo shi da kaina, mu haɗu a station zuwa ƙarfe biyar na yamma ina son a zauna da babansa””Shikenan, mu na jiranka”Mai unguwa ya ce “Ofusa ya zaka yi mini haka, yaron da ya nemi rayuwata””Mai unguwa ka jira ya dawo hayyacinsa mu gani, Allah ya kaimu ƙarfe biyar ɗin.Jauhar na wanke-wanke, Al’amin ya turo ƙofa, hannunsa riƙe da guduma, ta tashi tana bin sa da kallo.”Sako hijjabinki, ki kawo mini tabarma”Ta jinjina masa kai, ta sako hijjabi, ta kawo masa tabarma, ya kwantar da guduma, ta ƙare masa kallo ta ce “Wannan ai shi ne ya hana wani ya sare ni, lokacin da na je gida da aka tsare ka”Al’amin ya ce “Kawo mini ruwa a bokiti da kofi”Ta kawo masa ruwa, ya ɗiba ya dinga sheƙawa guduma a ka, ya din ga zabura kamar zai zare, ya ɗaukko gawayi a kurfotin Jauhar, ya daddaka ya kaɗa a kofi, ya matse guduma ya dinga ɗura masa a bakinsa, ya sha wani ya zubo da wani, ya gama ya hankaɗa shi ya kwanta.”Master wai meya same shi ne? Ba shi da lafiya ne?””Ƙwayar da ta fi ƙarfin kansa ya sha, ya kusa halaka mahaifinsa”Waro ido ta yi ta ce “Mahaifinsa kuma? Subhanallah lamari ya ɓaci”Bayan mintuna arba’in, guduma ya wartsake, ya din ga kallon gidan,  sai da yayi ido huɗu da Al’amin, sai ya ƙara nutsuwa.”Ka farfaɗo?” Guduma ya sunkuyar da kai.”Ka san me aikata ko?” Yayi shiru bai ce komai ba.Al’amin ya yi ajiyar zuciya ya ce “Me ka sha?””Sigari ce””Da me?””Itakaɗai”A fusace ya ce “Zan saka maka ƙarfe wallahi, uban me ka sha ka ke yinƙurin kashe mahaifinka?””Wiwi ce kawai ban sha komai….. Ba rufe baki ba, Al’amin ya riƙe maƙogwaronsa ya ce “Zaka faɗa ko sai ni na kashe ka?”A rikice jauhar ta ce “Dan Allah Master ka ƙyale shi, kar ka kashe shi”Cikin kakari guduma ya ce “Baƙin capsule ne””Waye ya baka, kuma waye yake dillancin sa a unguwar nan”.”Botorami ne””Botorami, yaran da suka sareni, na ƙyale shi, shi ne ya fara sayar muku da wannan muguwar ƙwayar? To wallahi sai ya bar unguwar nan. Uban me babanka yayi maka ka nemi kashe shi? Bayan sharrin ƙwaya har da iskanci, uban meyasa ba ka yi yinƙurin kashe kowa ba sai shi?”.Cikin damuwa guduma ya ce “Kora ta yayi, ya ce kar na sake zuwar masa gida””Ba dole ya kore ka ba, tun da abun naka babu hankali a ciki, in anjima zamu je police station, ka bashi haƙuri, idan kuma ka bari yayi maka baki, ka shirya lalacewa da taɓewa fiye da wadda ka ke ciki yanzu” ya jinjinawa Al’amin kai.Al’amin ya ce “Ka zauna a nan kar ka fita ko ina”Jauhar mamaki ta din ga yi, dama Al’amin ya san abun da ya dace, amma shi yake wanda bai dace ba.Jauhar ta gama abincin rana, ta zuba ta bawa guduma, ya karɓa ya ce “Ya gode”Al’amin ya zaunar da shi yana yi masa tambayoyi, sai dai bayanin da ya yi wa Al’amin, a kan irin rayuwar da ya tashi a kai, gaba ɗaya jikin jauhar yayi sanyi, wato wasu lokutan mutane na yin gaggawar yankewa wasu hukunci, ba tare da sanin ainihin abun da ke ɓoye ba.”Da la’asar suka tafi police station, tun da suka je mai unguwa yake bala’i, har da cewa ‘yan sanda su kama guduma su yi masa duk abun da za su yi masa shi yafi ƙarfinsa.”Uwarsa ce ta lalata shi, sannan ta dawo mini da shi, baya sana’r komai sai shaye-shaye na tsiya da ya ɗorawa ransa, yau kuma rayuwata yake nema, to wallahi ba a haifi ɗan da zai kashe ni ba, waccan shashashar uwar ta sa ita ce silar komai, bayan ya lalace ta nannaɗo ta kawo mini shi”Al’amin ya ce “Ina mamakin yadda aka bawa mutum irinka jagorancin al’umma alhalin ba ka iya jagorantar gidanka ba. Kai da ka haife shi, baka iya bashi tarbiyya ba hukuma ce za ta tarbiyantar maka da shi? Ka san ba zaka iya kula da shi ba meyasa ka haife shi? Da ka saki majaifiyarsa ka maye masa gurbinta? Sakinta ka yi ka bar mata shi, ba ka san cin sa da shan sa ba, balle iliminsa da lafiyarsa, baka nuna masa sana’a ba, baka bashi jari ba, ita ba cikakken ƙarfi ba itakaɗai tayaya zata iya yi maka rainon ɗa?Ka san jikinka yana buƙatar ka auri mata barkatai, ka yi jima’i ayi ta haifa maka ‘ya’ya amma ba ka tunanin inganta rayuwarsu, ko buƙatar ka kawai ita ce buƙata?””Kaga Al’amin ya isa hak…. Al’amin ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya cigaba da magana.”Babu in da za shi, tun da ka haife shi, dole ka kula da shi, ka yi masa role ɗin uwa tun da ka saki uwarsa a lokacin da ya fi buƙatar ku rayu tare, idan ba haka ba ko ba shi ba, a cikin wannan tulin ‘ya’yan zaka samu mai halaka ka.Ya mayar da idonsa kan Guduma ya ce “Kai kuma ya muka yi da kai?”Guduma ya durƙusa ya ce “Baba dan Allah dan Annabi ka yafe mini, ka yi haƙuri ba zan sake ba in sha Allah, dan Allah ka janye korar da ka yi mini daga gidanka, nayi kuskure ka yi haƙuri “Sai dai mai unguwa yayi tsit, dan kuwa Al’amin ya gama kwaikwaye shi a gaban mutane, yayi mamakin maganganun da suka fito daga bakin Al’amin ɗin.”Officer, zan kawo yaron da yake sayar da wannan capsule ɗin, a riƙe shi a matsa shi, ya faɗi ina yake samota” ya sake kallon guduma ya ce “Ka shelanta, cikin unguwar nan, duk wanda na kama da sayar da irin wannan nau’in kayan, sai na lahira ya fi shi jin daɗi”Ya jinjinawa Al’amin kai.”Yanzu dai ina nema masa afuwa, yayi nadama in sha Allah ba zai sake ba”.”Idan ya sake fa, ni fa gaskiya rayuwata tana cikin hatsari””Ayi rubutu, duk abun da ya yi zan ɗauki laifin”Ba mai unguwa ba, har Guduma Nura sai da ya kalli Al’amin.Aka yi sulhu da rubuce-rubuce, suka fito, guduma ya risuna yana yi wa Al’amin godiya.”Manta, mu je ka rakani asibiti, kan waccan uwar mitar ta sakani a gaba”Guduma ya ce “Antynmu ayi mata godiya, abinci yayi daɗi na gode master” bai ce komai ba, suka tafi asibiti.Ko da suka je emergency, Al’amin har gaban gadon yaron da ya karya ya je, ya tarar da shi a kwance, ana saka masa ruwa.Yana ganin Al’amin ya rikice, ya yinƙura zai ɗago, Viper ya mayar da shi, ya kalle shi ya ce “Na ji babarka na kururuwa na nakasta ka, a ɗaukar mata mataki, kai ba ka gaya mata babu mai iya ɗaukar mata mataki ba? Yanzu ka dawo hayyacinka ka tuna abun da ka yi ko? Ba ka sanni ba ko? Saboda ka sha ta gaya maka ƙarya, ni ka tunkara zaka sara ko? Wai ba kai ne ɗan mama ba, da aka rufe kwanaki madaki ya saka ka kashe wani yaro a dabarku ba? Ya shiga ya fita an sake ka, yanzu kuma da ka nakasa ya kasa taimakon ka ko?”.Ya sunkuyar da kai ya yi shiru.”Za a zo a biya kuɗin maganinka, nan gaba ka sake zuwa ka tari gaban tirela, ta kanka zan bi”Ya kalli guduma ya ce “Tashi mu ware”Ya tashi suka tafi, kamar wa da ƙani, suka bar mai unguwa da kunya.Bayan fitar su Al’amin, jauhar ta kaiwa telar da take yi wa aiki kaya, ta rage mata wani abu a cikin kuɗin, amma ba ta bata duka ba.Ta tarar da yaran matan layin, suna ta bajekolin magungunan mata, ana ta shewa.”Jauhara ba za ki sayi abun arziki ba, ga kaya nan sai wanda ki ke so, kuɗi kuɗi iya kuɗinki iya shagalinki”Kawai tayi murmushi ta basar da su.Wasila ta ce “Wai sai an yi magana sai ki wani din ga mazewa kamar baki san komai ba? Ke an daina irin wannan abun kamar a zamanin da, idan baki zanzare kin fitsare ƙafafuwanki ba,bar ganin mijinki a haka ba ruwansa da kowa, wallahi sai ki ga ya fara ‘yan leƙe-leƙe, ki zo ki ɗauki gyara hajiyata, ita mace sai d gyara, wannan kyan fuskar ta ki ba shi kawai yake so ba”Jauhar ta ce “Hmm Anty wasila kenan””Ba wani anty wasila, malama ki rage maƙo dan Allah, kin iya neman kuɗi sai aukin saka turaren wuta a gida, da goge goge, amma ba zaki sai kayan gyara ba, ina ta tallata miki kayan maman neehal ɗin nan, baki ga kyan su ba, amma sai ki yi burus”.Suwaiba tela ta ce “Wai wasila ki ƙyaleta mana, ki ka sani ko tana abun ta, idan tana yi gaya miki zata yi?””Ba wani, ni fa jauhar ƙanwata ce, ƙanwa na ɗauketa, kunyarta tayi yawa Allah ya sa ba haka ki ke yi masa ba, babu yadda za ayi ki je ki ganta da shirt da wando, sai uban hijjabi da dogwayen riguna kamar zata yi ɗawafi. Ki tsuke ki ci zamaninki tun da ƙuruciyarki, ni ga wani tsumi nan na baki, na maman neehal ne, tested and trusted, ki gwada zaki bani labari.(0706 677 4630 ga lambar da zaku samu maman neehal, domin samun kayanta)Kamar sokuwa haka Jauhar ta karɓa, kasancewar ta san ba wani amfani da zai yi mata.A gurguje ta kammala abun da za ta yi a gidan, ta fito saboda irin manyan karatun da ta ji suna yi, da suka fi ƙarfin kanta.Ta koma gida, ta din ga kallon robar abun da anty wasila ta bata, na wurin Anty lubabatu ma suna nan, ko kallonsu ma ba ta yi.Aka fara kiraye-kirayen  sallar magariba, tana salla, ƙarar wani babur ya cika mata kunne, bayan ta idar tana cikin lazumi, ta ji ana kokowar shigowa da abu, ta tashi ta fito tsakar gida, ta tarar da Al’amin yana shigowa da wani tsohon babur jincheng, hannunsa riƙe da salansar babur ɗin.”Master, wannan kuma fa?””Jaki ne” ya bata amsa.”Wai sai ka yi ta gaya mini baƙar magana, wai ko shi ne ya cika layin nan da ƙara?””Eh””To meyasa ka cire masa salansa? Ka ji ƙarar kuwa ba daɗi, kamar ya shekara ba a kunna ba”.Ya jingine salansar, duk ya ɓata jikinsa da baƙin mai, ya ce “Na fi son sa a haka””To wai a ina ka samo babur?””Sata na fara” yayi maganar zai shigar mata falo.Ta ce “Allah ya baka haƙuri, amma tsaya na kai maka ruwa banɗakin tsakar gida ka yi wanka, idan ba haka ba zaka ɓata carfet ɗin da baƙin mai”..”Naɗe abun ki na wuce, ba zan yi wanka a tsakar gida ba”Ta shagwaɓe ta ce “Ba fa a tsakar gida ba, toilet ɗin tsakar gida”.”Ƙoƙarin shiga falon yake, tayi sauri ta ɗaukko tsumma, ta durƙusa ta ce “Bari na goge maka, kar ka ɓata mini carfet” ta gogge masa, sannan ya shiga.Warin sigarin da yake yi ya sanya ta bin sa da ruwan zafi, ta matsa masa toothpaste a kan brush, ta ajiye masa.Allah ya taimake ta, babu musu yayi wanka yayi brush, ya fito yana goge jikinsa, ya buɗe wardrobe ta shigo da sauri ta ce “Saura ka watso mini kaya ƙasa, na sake gyarawa, nuna mini wanne zaka saka na ɗaukko maka?”Ya nuna mata, ta ciro masa su, kafin ya karɓa ta miƙo masa kwalbar turare ta ce “Ka shafa turaren, sai ka saka”Haɗin da take amfani da shi ne, ta daka alumun, da farin muski na gari, da kanumfari,  ta dafa su suka tsumu ta ta ce, ta zuba madarar turare a ciki.Ya karɓa ya shafa, ya miƙa mata, ta karɓa ta ce “Ai naka ne, na bar maka”Ya karɓa zai ajiye, ta ce “Baka ce ka gode ba” sai ya miƙo mata abun ta, da ya ce ya gode gara ya dawo mata da abun ta.Tayi dariya ta ce “Hukuma sai da rarrashi, na janye ba sai an yi godiyar ba”Ya ajiye, ya fara ƙoƙarin saka kayan, ta fita ta bashi wuri, shi kansa ya ji daɗin jikinsa sosai da sosai, ga ƙamshin yayi masa daɗi sosai da sosai.Ya fita ya kame a falo, ƙamshin turare sai ɗibarsa yake yi.Akwai English wears a cikin kayanta, sai dai ba ta taɓa gwada sakawa ba, dan kunya ma take ji, domin kuwa sai kwanan nan ta daina yawo da hijjabi a cikin gidan.Da ƙyar ta iya fitowa da doguwar rigar atamfa, da ta ɗan kamata cif jikinta, ta zo ta zauna a falon, ta ce “Master ya ku ka yi a police station kuwa?””Labari zan baki ko yaya?”Ta ce “Eh mana””Kunna radiyonki, ki ji labarai idan shi ki ke son ji”.Cikin shagwaɓa ta ce “Ni naka nake so”Ya ce “To ni ban san me zan ce ba”Ta ce “Ai shikenan””Yauwwa, na ce ba ka ga azumi saura ‘yan kwanaki, yakamata ace ko sugar da lemo mu saya mu je mu gaida su Abba””Sai kin dawo” ya faɗa yana shan kunu.”Master meyasa?””Kawai”.”Na san akwai dalili, amma koma menene ka yi haƙuri, ba a fushi da iyaye, kai fa ka gama yi wa wani nasiha ɗazu, meyasa ba zaka yi amfani da ita a kanka ba?”Juya mata baya ya yi, irin idan kin gama kya yi shiru.Zuciyarta cike da fargaba, ta taka ta je kusa da shi ta zauna ta ce “Masu sunanka manyan mutane ne, dattawa, ba sa haka, dan Allah kar ka saka mu shiga fushin Allah, iyaye ba abun watsarwa bane ba, ranar da babu su da kuɗi ba zamu gansu ba, mun rasa iyaye mata, mazan sai mu nemi albarkar su”Ya ɗaga hannunsa ya ɗora a kan kunnensa, ta kalli dogwayen yatsunsa, faratansa sun yi tsayi.”Gobe in Allah ya kaimu friday ce, a yanke farce, sumar nan ma tayi yawa yakamata a rage ta, ayi maka gyaran fuska kafi kyau idan aka aka rageta”Juyowa yayi gaba ɗaya, ya ƙureta da idonsa.Sai jikinta yayi sanyi, tsigar jikinta ta tashi yarrr.”Kin fa dame ni” yayi maganar a hankali, amma muryar da yayi amfani da ita, har cikin zuciyarta.”To me nayi maka na takura?” Shiru yayi bai yi mata magana ba, ya cigaba da ƙare mata kallo.”Baka saka mini lambarka a wayata ba”Ya miƙa mata hannu, ta bashi wayarta, ya saka mata lambarsa, ta ce “Yauwwa na gode, zan din ga yi maka flashing, kamar sau arba’in a rana””Iya arba’in?””Eh, ko yayi kaɗan?” Ya girgiza mata kai alamar a’a.”To ɗan yi mini downloading ɗin game”Ya ce “Sai kin gama jarrabawa tukuna””Ai mun kusa in Sha Allah” ya lumshe idonsa ya ce “Allah ya bada sa’a””Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum master, ‘yar madara na godiya”Ta sake cewa  “Dama wainar fulawa zan yi mana mu sha da tea, bari na ɗora”Ta fita tsakar gida, ta hura kurfoti, ya biyo ta gaban kaskon ya zauna, sai dai kallon da yake yi mata duk ta takura.”Master, kamar fa akwai ɓera a gidan nan, dan Allah ka sayo maganin ɓera”Ya ce “Shi ma tsoron nasa ki ke ji kenan?”Tayi murmushi ta ce “Eh, amma ba sosai ba””Ya haɗa nasa shayin, tana soya waina yana cinyewa””Master ban gane ba, idan ka cinye ni fa?””Sai ki soya wata””Ko kuma ka soya mini ba, ƙullin fa bashi da yawa, ka ƙoshi gaskiya” ta janye plate ɗin.Ta gama ta haɗa nata tea ɗin, ta fara ci.Ya zuba mata ido, cin abincin ma yanga take yi masa.Yana zaune yana kallonta, ta gama ta haɗa wanke-wanke ta yi.Ta gama komai, zata shiga ɗaki ta ce “Na gama taso mu tafi, kar sauro ya saka maka zazzaɓi”.”Dama na ce miki ke nake jira ne?”Jauhar ta ce “Eh dole ka ce haka, tun da na cika maka cikinka, aishikenan sai da safe, dan Allah kar ka sha komai ka ji master”.Yayi mata shiru, ta ce “Master, magana nake fa, na san kana ji na, dan Allah kar ka sha komai ka ji Mai zamani”Ɗagowa yayi ya kalleta, tayi masa murmushi, tasowa ya yi, ya biyo bayanta. Tsayawa tayi ta ga me zai yi mata.Yana zuwa ya riƙe kunnenta ya ce “Me ki ka ce?””Master na ce””In kuma jin kin faɗi wannan sunan, zamu gauraya da ni da ke” sai dai duk wannan abun fuskarsa ba fara’a.Cikin shagwaɓa ta ce “Kunnena zai cire fa” ya tura ƙeyarta, har ƙofar ɗakinta, ta ce “Kar in sake ganinki sai gobe in Allah ya kaimu”.”To na ji, amma dai kar ka sha komai dan Allah” wucewa yayi ɗakinsa, ta ƙarasa gaban gadonta tana murmushi.Ta yi wanka, ta shirya ta shafa turarukan ta, ta nemi wuri ta kwanta. Sai murmushi take yi, tana jin daɗin cigaban da ake samu a kan zaman su.Ta kalli pillown da take rungume da shi, ta shafi pillown a hankali, tana tuna hirarrakin da aka yi ɗazu da su Anty wasila.Tabbas abun da take ji game da aure ya sha banban da abun da ta tarar, to ko ba haka abun yake ba? Sai kuma ta tuna har a littatafan addini ta karanta.Hakan yana nufin Al’amin ba shi da lafiya ne? Ko kuma ita ɗin ce ba ta gabansa, sai dai ya ci, yayi shaye-shayensa ya je yawonsa, ko kallon kirki ba ta ishe shi ba.Tunani take yi ko dai tana da wani naƙasu ne, da ya sanya ba ta gabansa, ko da wasa bai taɓa ko makamancin yi mata wani abu ba.Ta yi juyi ta kalli gadon, yanzu idan Al’amin ba shi da lafiya ne, ko bashi da ra’ayin hakan, haka za su cigaba da rayuwa kenan, ita ba kowa ne da ita balle su tattauna, ko da wasa kuma ta san ba zata tunkare shi da wannan maganar ba, ko ta kai masa kanta, wannan ma ba mai yiwuwa bane ba.Wataƙila wani babin ne na ƙaddarata. Ta faɗa a zuciyarta, a lokacin da bacci yake ƙoƙarin awon gaba da shi.Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, wani matashin saurayi ne, yana ta kai komo a tsakanin wasu gidaje can wajen gari, da alama wani abu yake jira.Wani mutum ne ya zo a keke, ya tsaya ya kalle shi ya ce “Nan ce sabuwar mahaɗarmu?”Mutumin ya amsa da “Eh, kuma ka yi taka tsantsan, kar a gane, kar kuma ka yadda da kowa””To shikenan, yanzu zan je na rarrabawa gayu kayan, ga wannan balance ɗin jiya ne” yayi maganar yana miƙa masa kuɗi, mutumin ya karɓa, shi kuma ya tafi.Sai dai ya nufi in da yake son tafiya, ya ji an danƙi jijiyar wuyans, a take ya sulale sumamme.Suka ɗauke shi suka tafi da shi, Walid ya kira Al’amin ya ce “Maganarka haka take mai dogon zamani, mun kama yaron nan, ka san yaron madaki ne ya rarraba musu ita, idan ban yi kuskure ba madaki yana cikin manyan dilolin capsule ɗin nan.”Ku shigo da shi cikin unguwa, ku ɗaure shi, ɗauri na gasken gaske ku bar shi, zan yi magana da ‘yan sanda””To shikenan, amma ka din ga yi kana ankarewa da hankakin nan ka san ba mutunci suka cika ba””Ina ankare, sai da safe”Har ƙarfe tara na safiya, Al’amin ya je yayi sabgoginsa ya dawo, jauhar bacci take yi.Ya tsaya a ƙofar ɗakinta, yana ƙwanƙwasawa, a hankali ta yi juyi, ya ɗaga labulen ya ce “Ba a san gari ya waye ba ne? Yunwa nake ji””Afuwan gani nan” tayi maganar cikin muryar bacci.Da kayan jikinta ta fito falo, gashinta duk a hargitse ta ce “Yi haƙuri, baccin nawa ne yayi nauyi”.Ta tarar ya sayo gasara, ya sayo awara ɗanya.Mamaki ta din ga yi, a ina ya san ana sayarwa, amma tafi yadda aikawa yayi a sayo masa.Ta shiga ɗakinsa gyarawa, ta buɗe wardrobe ɗin sa, kayan da ya cire jiya ta tattara zata wanke, ya kwasa ya mayar da su cikin wardrobe ɗin, kayan dai da ba ta so, sai da watso su, ya ɗauki abun da zai ɗauka duk ya cukurkuɗa su ya mayar cikin wardrobe ɗin.Yana ganin ta tsaya tana kallon wardrobe ɗin, yayi waje dan ya san mita za ta yi.Ta kuwa biyo shi falon “Master, yanzu duk gugar da nayi ka wargazata, ka haɗa mini wankakkun kaya da marasa wanki, har da jiƙaƙu duk ka gwamutsa mini su a ciki” tayi maganar kamar tayi kuka.”Ke fa ki ka ce, na daina zubar miki da kaya ko ina a cikin ɗakin””Kuma master kaya kala ɗaya da zaka saka, sai ka hargitse ilahirin wardrobe ɗin? Zan samo maka bagco, ka din ga zuba marasa kyau a ciki, dan Allah ka daina hargitsawa” yayi mata shiru, ta gama mitarta ta gama, tana komawa gyarawa ya dafe kai, ta gama mitar kuma ta gyara.Sai da ya tabattar ta fita daga falon, tana aiki a kitchen ya ɗaga wayarsa yayi kira.”Kuna aikin da na saka ku?””Eh muna yi””Kar ku kuskura ku bari wani ya kwance shi, idan ba jami’an tsaro ne suka zo ba”Ya gama karyawa, yana son ya tashi ya fice, ta tistiye shi da zancen yanke farce, haka ya koma ya zauna, ta saka reza ta yanke masa farce tsaf, tana yi tana yi masa surutu.Baya son ta gane ya yi wata tsiyar a waje, kar ta zauna ta yi ta masa kuka.Ta yi masa gugar kayan da zai saka, wai ya tafi masallacin juma’a, shi rabonsa da zuwa sallar juma’a har ya manta, yayi wanka ta bashi goggagun kaya, ta shafa masa turare ta ce “Ka dawo da wuri dan Allah, ina gama abinci ka ci da zafinsa, ka yi mana addu’a idan ka je” Ya gurgura babur ɗin sa da ya cire wa salansa, ya fice ya cika layin da ƙara.Daji ne sosai babu gida a gaba, babu a baya, daga shi sai direbansa suke tafiya sai P.A, har suka ƙaraso wurin wani dutse, suka sauka da shi da P.A, suka tattaka har gaban bukkar.Cikin bukkar tamkar fadar mahaukaci, duk an yi mata ado ƙahunhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, har da wasu sassa na ƙashin ɗan Adam.Gefe ga wani mutum na tsurut, kamar an fato shi, jikinsa ko riga babu, daga shi sai wani ɗan warki ɗaure a ƙugunsa.Suka nemi wuri suka zauna, ya kalli indabo ya ce “Aikin farko yayi, wa’adin da muka ɗiba maka yau ya cika, aljanu sun sha jini a ƙasar da suka buƙata.Saura mahaɗin aiki na biyu, za a samo matashiyar yarinya, matar aure shekara sha biyar zuwa sha takwas, zaka kasance da ita, tsawon kwanaki uku, a ketowar alfijir ɗin kowace rana, zaka fara aikin a larabar tsakiyar wata, shi ne sa’ar aikin! An ɗeba maka wa’adin kwanaki Arba’in ba biyar”

Ayshercool 08081012143

Back to top button