Novel Document

Rainon Soja Book 1 Complete Document By Maman Teddyt

Description/Story:

Rainon Soja Complete Hausa Novel Document Written By Maman Teddyt

 

Description

Wata moto ce ke guda a tsakiyar ƙwalta inda babu gida gaba babu baya sai Falfalan dajin ALLAH.

Mota ce irin ta haya wanda yake dauke da mutane sun kai Goma zuwa goma sha biyu , kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci matafiya ne wanda suka fito daga cikin garin Zaria zasu iso Garin Abuja . Kowa hankalin sa yana akan hanya banda Mace Ɗaya wacce tun da suka shigo moton idanun ta ke tsiyayar da Ƙwallah, daga saman jikin ta kuma yarinya ce Wacce a shekaru ba zata Haura Ɗaya ba zuwa ɗaya da Rabi a Duniya . Tausayin yarinyar nata take jin yana ratsa ta haka zuciyar ta na kuka mata . Juyawa tayi tana kallon mai gidan nata wanda shima jimami ne da kuma tsoro fal a zuciyar sa. Hajara kina ganin idan muka je Muka koma a halin yanzu Ƴan uwan ki zasu amshe mu? Zasu amince da Auren namu a yanzu kuwa? Hajara ko zamu koma ne…..Ɗaga masa hannu tayi tana saurin riƙo hannun shi kamin cike da Raunanniyar murya ta fara cewa ” A’a Salihu ” kar ka ƙara furta hakan , yanda muka ƙudurci kawo Zahra dangina Don taga iyayen ta da kakanni a yau babu abun da zai fasu daga yin hakan sai kuma idan ƙaddara ta Gifta .

Ka janye Tsoro ka manta da komai nasan su ma a yanzu sun manta kuma kowa zai yafe mun inshallah. Fatan mu a yanzu shine Allah yasa mu sauka lafiya .

“Hummm” .

Sauke Ajiyar zuciya Salihu yayi kana yakai hannun shi yana ɗaukar ƙaramar yarinyar tasu yana daura ta bisa jikin sa . Ƙurrrr yayi mata da ido kamin yace ” Wai Haihuwar ki ce aka ce mun ba alheri a rayuwa ta Zahra , Ni nasan Allah shine mai yin komai shine wanda yasan ƙaddara ba ɗan Adam ba. Ko ina raye ko ina a mace ina rokon ALLAH ya kare mun ke da kariyar sa. Shiru Hajara tayi tana kallon uba da ƴar wanda yake ji tamkar ya haɗa ta da jikin sa ya zamana babu wani abun cutarwar da zai iso gareta . Murmushi take bin su dashi kamin ta juya tana kallon dajikan da suke wucewa.

Kaman wanda aka ɗaga moton suka ji tayi sama tayar gaban ta yana fita fittttttt ji kake kwaltan da tayar suna fidda wani irin ƙugi ƙuuuuuuiiiiiiii nan take moton ta ɗaga tare da kifowa kif kaman wanda aka dirkake su . A dai dai kuma wannan sa’ilin da babu gida gaba babu gida baya ,sai falfalan dajin ALLAH . Yanda moton tayi ƙwatsa ƙwatsa jini na malala a tsakiyar titin ga hayaƙi dake tashi tamkar an kunna Masu fetur da ashana wurin yayi baƙiƙirin kai daga Ni kasan babu mutum ɗaya daga cikin moton nan da ya shura sai dai muce Allah yajiƙan wanda suka rigamu gidan Gaskiya 😢 .

**
Nigerian defence academy ( NDA)
#Nd 1 .
Yaran sojoji ne birjik a ƙame rana na dukan tsakiyar kan su , amma yanda wurin yayi shiru da yanda sukya a ƙame tamkar wanda ruwa yaci yacinye su . Mutumin dake daga nesa ba zai taɓa kawowa da akwai mutum ko ɗaya a wurin ba,bare kuma sojoji da sun haura 100 ɗari duka a layi . Kasancewar su Nd 1 yasa duka yawancin su yara ne matasa wanda daga secondary ne suka shigo , duk girman yaron dake wannan wuri babu guda ɗaya da ya haura 18 . Duka ƙasa da haka ne sai kuma 18 din , ciki har da masu 15 years yayan manyan kenan masu faɗa aji a ƙasa . Sune suke kawo yaran su tun da yarinta .

Cike da Wani irin ƙaraji tamkar zai tashi wurin da yaƙi Muryar Major ɗin su ya katse su yana furta ” Hand salute! Daram dam dam….kaji takon su duka ya sauya suna juyawa ga Major ɗin a lokaci guda suna ɗaga yatsunsu tare da ƙamewa da ƙafafun su . Bin su da kallo yayi dukan su Sanye suke cikin t.shirt na sojoji sai wandon su mai ratsin tambarin su na soja.

Idanun Major Jibril ne ya sauka akan Wani kyaƙyƙyawan yaron dake daga can tsakiyar layi , su duka a ƙame suke amma shi a wannan lokacin Wayar hannun sa yake latsawa cike da kula murya ƙasa-ƙasa yake furta ” Mami…Hello .

Wani irin Tsawa Major Jibril ya daka masa Wanda sai da Hantar cikin Duka yaran ya kaɗa yana bada amon ƙulululu… Mamaki ne ya kama su Ganin Yanda Aliyou Haidar bai Girgiza ko ya saki wayar tasa tayi ƙasa ba ,sai ma ƙara mannata da yayi da kunnen sa yana furta ” Mami I’m in trouble Major Jibril ya na mun magana bye bye .kamin ya jira jin mene Zata furta ya datse kiran da Sauri yana maida Wayar cikin Aljihun sa .

Cike da shouting da ɗaga murya irin na Sojoji Major ya furta ” Who are you ? ….kamin ya rufe baki cike da Ƙwarin gwiwa tare da gigiwa irin na Aliyu ya furta” ALI HAIDAR “. yana furta zancen tare da ƙamewa kaman yanda suka saba yi don respect. Kallon shi Major Jibril yayi kana ya bashi umarnin ya fito wajen layin . Cike da kuzari da Sauri ya fito yana gyara tsayuwar sa , kallo Ɗaya Major yayi masa yaga tsayayyen namiji ne a gaban sa tun kan ya girma a yanzu ma zaka fahimci hakan , ƙwayar idanun sa ya kalla ganin rashin tsoron sa yasa shi Furta ” Waye Soja a tare da kai ? .

Sorry sir
Fa furta yana kame ma Major ɗin , Tambayar ya kara nanata masa karo na biyu wato a dangin sa Waye soja? Wanda a wannan karon kai tsaye Ali haidar ya basa amsa da my Dad…! Ya furta da ƙarfi yana Ƙara ƙame ma Major Jibril . Meye sunan Mahaifin ka ? General Saleh Yelwa . Girgiza kai Major Jibril yayi tamkar General ne a gaban sa , don yasan Waye General Yelwa babban sune shine ya basu horo a lokacin tasowar su .

Kallon Aliyou Haidar yayi kana ya cigaba da cewa ” Ya ake yin Hand salute?

Ok sir . Ya furta yana Sara masa tare da hade ƙafafun sa .

Kallon Sauran sojojin abokanan sa yayi shigowan yanzu Nd 1 kana cike da Arrogant voice ɗin sa ya fara cewa Hand salute!

“You raise the right hand smartly in the most direct manner a kuma lokaci guda extending and joining the fingers …keep the falm plat and facing the body.

“Yana maganan tare da nuna masu yanda ya kamata suyi don haka Majorn ya sanar dasu a jiya . ”

Komai dai dai ya faɗa , Wannan yasa Major kallon sa yana basa horo da ya fita can Rana ya fara tsallen kwaɗo shine punishment ɗin sa na yau , Gobe ba zai ƙara kuskuren da yayi irin na yau ba.

Ficewa Ali haidar yayi yana nufar inda Major yace yayi tsallan kwaɗon , Ɗan waigawa naga yayi yana kallon wani direction yana murmushi .

Gani nayi wani Matashin yaro wanda ba zai haura 17 ba yana kallon Aliyu idanun shi sunyi ja na damuwa ga gumin dake karyo masa , damuwa duka sun bayyana ƙarara a fuskar shi . Haɗa ido suka yi da ƙanin nasa yana jifan sa da harara tare da cewa a zuciyar sa ” Yaushe Haidar zai daina rashin ji ne? Yau sai ya sani bari ya gama mu koma . Murmushi Aliyu haidar yayi yana furta to menene na dumuwa Yaya Khaleel bafa wuya ne dashi ba . Yanzun xanyi na gama .

 

Tsallan ƙwadon ya fara yi su kuma sauran sojojin suna fara fareti . Fiye da Awa ɗaya yake aikin tsallan ƙwaɗon amma babu alamar gajiya a tare da shi , don shi jin sa yake tamkar training din da suka saba yi ne a gida yake yin sa a yanzu. Ni Ko nace yo ba dole ba , Mahaifin su soja mahaifiyar su babban Ƴar sanda ce , Wanda a yanzu take da matsayin mataimakiyar Commissioner of police. Hajiya Nafisat Yelwa kenan . Ƙaramar ƙanwar su kuma jidderh itace take makarantar yara na karatun architecture . Sauran labari zamuji shi a gaba inshallah ku dai ku cigaba da biyo wannan Golden pen din don wannan tafiyar ta musammance .

Ali Are You not tired ? Baka gaji ba Haidar? Muryar Areef ya katse shi wanda yake fareti dai dai inda Aliyou Haidar yake . Cike da hade gira tamkar wani bad boss yace ” Na riga da na saba da ko wani horo na soja tun kamin nazo nan. Ɗan wannan tsallen kwaɗon ba zai gajiyar Dani ba .

Da kyau!

Muryar Major Jibril ya katse su wanda basu san yana tsaye da a bayan su ba. Tabbas wannan yaron yana da jan rai da zuciya kangararriya , haka ake son soja ya kasance , Major yayi maganan a zuciyar sa yana juyawa tare da kallon Manyan sojojin dake bayan sa. Ina so ku bi mun bayan Ali haidar Yelwa yayi gudu tun daga nan Kaduna jaji har zuwa Zaria ya dawo a ƙasa ba tsayawa ko Hutawa yanzu . Ok sir ……! Suka yi maganan cike da amsa kuwa . Juyawa Ali haidar yayi yana kai hannun sa tare da miƙa yana miƙewa tsaye . Da sauri ya furta ” Major idan ba damuwa zan iya ɗaukar Helmet da Armor idan ba damuwa da ruwa ma . Wani irin kallo duka suka bi shi dashi , yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace ” Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment now , shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi me zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo …………………..!

Download  Rainon Soja Complete Novel Document By Maman Teddyt

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button