Description/Story:
Sanadin Bara Hausa Novel Document Written By Maryam Ibrahim
Description
“Yanayin yadda hayakin yake tashi a dakin girkin. Gashi babu wata wadatacciyar iska dazai fita ya haifar da cunkushewa waje daya.
“Baxakayi tunanin akwai mutum a wajan ba saidai tarinsa ne zai sheda maka da wani a wajan.
“Saddika ce tamike tana shartar gumi idanuwanta sun kumbura sosai. Sabida hayakin har muryarta tafara dashewa.
“Kama kugu tayi ahankali tace waiyoni Allah yazanyi wanan hutar da takama.
“Inna batulu ce ta hankado labulan dakin Wanda hujojin jikinsa sin isa akira dakin babu labule.
“Ke wacce irin shashashar yarinya ce kin hadawa mutane hayaki kinkasa magancewa.
“Inna dan allah kabani Leda na hada hutar taki kamawa wallahi. Ican danyene wlh.
“Eyeee ni kike fadawa ice danyene. Kin koyi hali irin na uwarki ko, to idan kikace halin shaffatu zakiyi bazaki ci riba ba..
“Kuma kiyi kidafa abincin nan wallahi ko jikinki yafada miki acewar inns batulu..
“Haka takuma rankwafawa ta cigaba da hada hutar.
“Kafin tagama tayi hujuga, hujuga.
“Ahankali ta furta inns nagama. Ki dauko tukunyar ki kahomin daki. Sanan kuma ga kayan wanki can. Na hada miki.
“Idanuwanta tasauke ahankali akan tulun kayan Wanda tayi kiyasin ta fara wankesu sai dare.
“Amma inns dakin bari wanki nan sai gobe inaso nayiwa su musa nasu.
“Karaf taji a buge mata baki Wanda hakan yasa jini yafara zuba.
“Ke kin isa inna tafada, kifada. Wanki ne saikinyi shi wallahi. In banda inna tana rufa muku asiri ke kin isa kikaho haka.
“Ganin jinin yana zuba a bakinta yasa tace yaya zuwaira. Jini fa kika futarmin. Idan biki shiga hankalinki ba wallahi sainayi maganinki.
“Tana gama fada ta bude labulan ta afka daki.
“Ganin sunshige dakin ta janyo wata Leda dake gefanta. Tafara zuba abincin. Sanan ta lallaba ta tusashi cikin kayanta.
“Ta sabi tukunyar Tashige dakin saidai kafin takai takalmin juwaira ya hardeta tukunyar tayi gefe abincin ya zube .
“Zare ido tayi tare da dafe kirji. Ta dora hannunta akai tana rafsa ihuu tasan ko zata mutu yau sai sun hulakanta ta..
“Bura, ubancan zuwaira tafada abincin namu wallahi yau saikinyi nadama.
“Dan Allah Kuyi hakuri natuba wallahi.
“Wani irin wawan Mari inna batulu ta sakar mata. Da Karfe ta dafe wajan idanuwanta suka kaho ruwa.. Dan Allah kiyi hakuri wallahi be laifi na bane..
“Suna ganin abincin haka ya lalace a kasa.
“Tabbas yau ko ruwan mutuwa tasha sai sun mata illah.
“Dan kwallinta ta fnciko Wanda yataho da gashinta.
“Tayi hurgi da ita jikin bango sanan ta take kafarta. Abbas yau tasha wahala. Koda baa fada ba
“Haka ta huni babu mai rarrashinta.
“Musa busu shigo gidan ba sai Ana kiran sallah magariba. Sabda haka. A rarrabe suka dinga bin bango.
“Ta taga suka hangi saddika Wadda ta tukure waje daya
“D alamu zazzabi ne jikinta.
“Musane ya rike hannunta, yaya saddika menene innace ko, Kitashi munsamu wake da shinkafa. Kici
“Ahankali ta bude bakint sanan tace musa bana hanaku barah ba,
“Wallahi aunty saddika babu inda mukaje illh gidan su faisal. Mamansu tabamu.
“Mikewa tayi tana kallan hanya sanan tace ungo wanan ledar kuje kuhada da ita kada kubari inna tagani
“Amma yaya kefa?.
“Kada kadamu musa nima na rage zan ci.
“Juyi take sosai tama rasa madafar dafawa
“Jan kafata tayi tasaka wani tsinkanken takalmi tayi waje.
“Gidansu salame ta fada
File Name | Sanadin Bara Hausa Novel Doc. |
Title | Sanadin Bara… |
Author | Maryam Ibrahim |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Love Story |
Published Date | 10/02/2024 |
File Size | 445Kb |
Format Size | TXT |
Phone No | 07045465268 |
Download Sanadin Bara Novel Document By Maryam Ibrahim
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.