Novel Document

Matar Taj Book 2 Complete Romantic Hausa Novel Document

Matar Taj Book 2 By Queenmarh

Description/Story:

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Document Written By QueenMarh

 

Description

For the second time ta sake dagowa ta kalli wadda ta shugo ganin ta tsaya bakin kofar kuma tayi shuru tana kallonta ‘’babu salam?’’

Rufo kofar wadda ta shigo tayi, itama kyakyawa ce ajin farko saidai ita tafi wanda ke kwance kan gadon haske sosai kuma suna kama sosai, hannunta na rike da hand dryer da alamu gyaran gashinta tayi daya sauko har wajen mazaunen ta yana sheki, gaba dayansu kana kallonsu kasan larabawa ne kuma jinin larabawan asali, ga hancin ga idanu kamar sun qera kansu.

Wadda ta shugo sai kamshin bakoor take,ita kuma tana sanye da riga da wando wanda suka dan kamata sai yar jellabiya data daura akai baqa kuma transparent, fuskanta adan hade ta karaso inda yar uwar tata take zaune kafin ta zauna gefen gado ta soma Magana cikin harshen larabci da turanci ‘’kedai wallahi idan kika maqale a daki bakyasa futowa kamar wadda ke boye boyen wani abu, marasa gaskia ne ke kulle kansu waje daya, ni bama wannan ba kinsan waye yazo kuwa fadwa?Guess who?’’

Wadda ta kira da fadwa bata dago ba hankalinta nakan wayar dake hannunta tace ‘’who?’’
‘’khaal’’( meaning uncle) yar uwar ta bata amsa
Cikin hanzari ta ajiye wayar tata ta zauna tana mai kallon ta tace ‘’khaal kuma afiya? meyazo yi kuma na dauka ay ya daina zuwa gidan nan tun bayan abunda ya faru last zuwan nashi?’’ fadwa ta tambayi yar uwar tata tana mai sauraronta don tasan ba haka kawai zaizo ba don it’s been a while rabonshi da yazo don kwata kwata zuwanshi rikici yake kawowa.
Kallonta wadda ta kira da afiya tayi kafin tace ‘’its obvious mana yazo duba wannan mara hankalin ne gashi ukty bata nan, hmm I don’t even know what’s going to happen today’’
Fadwa ce tayi saurin cewa ‘’uktyn bata dawo daga office din bane? Naga yanxu it’s almost 5?’’
‘’nop not yet but I’m sure zaman jiranta zaiyi,saita dawo tukunna ni karma ya fara min maganar aure cause….’’ Dan jinkirtawa tayi da Magana kafin ta tabe baki ta cigaba da cewa ‘’anyways muje dai kasan mu gaisa dashi muji dame yazo yau kuma, I don’t understand why he’s wasting his energy akan wanda baima san ina kanshi yake ba’’ tana kai aya ta mike tsaye ta nufi wajen dresser ta ajiye handryer din.
Afiya ce ta fara fita kafin fadwa tabiyo bayanta.

*
Atare suka sauko daga stairs din mai shegen tsayi dayasha floor carpet, saida suka fito ne na masu kallo tass, gaskia suna da kyau, masha allah ga gashi tabarakallah,bazasu wuce shekaru from 31, 33 ba, kamannin su daya kana ganinsu kasan siblings ne, hannayensu dasuke rike da manya manyan wayoyi sanye da zobunan gold haka zalika kana ganinsu kasan kudi ya zauna a jikinsu saboda yanda skin dinsu ke sheqi, saidai kuma jikin ne dan kiff dan sirara ne basuda girman jiki.
Kwata kwata babu alamun girma na shekaru a tattare dasu saboda arziki ya danne tsufan sai ya zamana kamar yan 20s.

Yanda suke saukowa cikin aji kamar bazasu sauko ba, sama sama suke hira suna dariya, Wato gidan ma ya gama gajiya da haduwa, daga waje ma ba komai bane ba don saika shugo daga ciki zaka tabbatar da haka don yasha kayan alatu na zamani, duk inda suka gifta ma’aikata ne suna ta hidima kowannen su sanye da uniform daban daban, gidan dai kamar gidan sarauta don yana da girma sosai ga kofofi da yawa alamun parts parts ne.
Ko’wanne lungu da sako shaqe yake da kayan zamani, ga luxurious interiors ta ko’ina.
Hanyar second sitting dake cikin gidan suka fara wucewa kafin su karasa first sitting room wanda shine face of the house.

Da sallama suka shiga parlorn afiya na gaba fadwa na biye da ita abaya saboda tana receiving call din daya shugo mata saida suka zauna tayi sallama da wanda take wayan dashi inda tace ‘’bye qalb’’ kafin ta sauke wayan daga kunnenta.

Azaune suka taddashi idanunshi nakan news saidai kwata kwata hankalin shi ba’akan news din yake ba,babu abunda yake mashi yawo akai sai tunanin last zuwanshi da yayi cikin gidan, ba da karamin bacin rai yabar gidan ba saboda y’ay’an dan uwan nashi musamman hidaya, kwata kwata bata ganin girmashi, tafi karfinshi ma, don sai abunda tace za ayi, darajar alqawari da kuma mahaifinsu ne kawai ke sashi zuwa gidan badan haka ba da bazai sake saka kafafunshi cikin gidan ba, bayan wannan akoda yaushe idan ya zauna babu abunda yake dana sani akai sai tilasta dawowar taj da yayi, dukda ya yarda komai muqaddari ne daga allah saidai deep down yana regretting dawowarshi don shine ya tsaya tsayin daka akan dole saiya dawo, sai yake jin kamar ta dalilin nan ne abunda ya faru wata uku da suka wuce ya faru.’……

Muryoyin su da ya soma jiyowa ne ya sashi fargawa daga tunanin daya fada, duban tafkeken wall clock din da akayi ado dashi a parlon yayi, karfe 5 da rabi Kenan na yamma,
sallamarsu ya sanya shi dagowa ya kallesu daya bayan daya, zaman half an hour yayi a wajen sai aynxu suke saukowa, shidai yana mamaki hali irin nasu koda yake baa abun mamaki bane don yanxu kam ya saba da halayensu, .

kauda kanshi gefe yayi daga garesu ya maida kan tv, kowannen su sanye take da kayan zaman gida gashin nan a bude don ko rufewa basuyi ba,bayan wannan yasan su da practicing rayuwar turawa so su hakan ba komai ne a wajen su ba dukda shi dai hakan a wajenshi ba wayewa bace da girmansu kuma da shekarunsu, shigar fadwa ne ma yafi tsaya mashi arai don ita tana da aure ba kamar afiya ba amma idan ka gansu zaka dauka gaba dayan su basu da auren
.
Karasowa sukayi inda yake zaune dan nesa dashi, kan kujerun single chairs dake facing nashikafin su zauna, fadwa ne tayi saurin cewa ‘’marhaban khaal’’
Ba tare da ya kalleta ba fuskanshi adan hade yace ‘’shukran fadwa,’’
Afiya ce ta dan tabe baki don daman itace tafi rashin kunya kuma yawanci yafi sa ido akan ta musamman rashin auren da bata dashi.
‘’Marhaban khaal’’
‘’shukran’’ ya amsata kai tsaye ba tare da ya sake kallon inda suke ba.

Takun sahun kafafun da sukaji ne yasa duk suka dago, wani dan yaro ne ya shugo kyakyawan gaske bul bul dashi, bazai wuce 12years ba, yana sanye da kayan paw patrol sai wata yar cute jaka a bayanshi, hannunshi rike da pack of doritos chips da nintendo switch gaming pad, sai faman cin doritos din yake.
Cikin sitting room din ya karaso aguje yana washe hakora ‘’Jadd’’ (meaning grandpa)
Inda dattijon yake zaune yaron ya nufa cikin farin ciki da jin dadi, farin ciki ya gama lullubeshi,

Hannu dattijon ya bude mashi ya taho a guje ya shige jikinsa kafin ya rungumeshi shima dadi duk ya gama lullube shi sosai, ‘’Barad’’
Dattijon ya kira sunan yaron bayan ya fiddoshi daga kirjinshi, murmushi yaron ya soma mashi kafin ya soma gaishesa, kumatun shi dattijon ya kama irin yanda ya saba yi mashi koda yaushe‘’I missed this cute baby face’’
Turo baki yaron yayi kamar zaiyi kuka yace ‘’jadd I’m not a baby anymore, I’m turning 13 next month’’
Shafa kanshi dattijon yayi kafin ya sumbaci kumatunsa yace ‘’kaje school yau?’’
‘’yes jadd’’ yaron ya amsa dattijon.

Wani irin kamshi ne ya danno cikin parlorn mai tsada don lokaci guda ya bade parlor kamar anyi ruwan turare, takun tafiyar ta ne ya biyo baya ‘’qwas qwas qwas’’wanda yasa duk suka juyo suna kallonta banda dattijon da yayi mata kallo daya ya dauke fuska sai yanayin fuskanshi ya chanza gaba daya kamar bashine ya gama yima yaron nan dariya ba.

Nima dai kallota na soma yi, kasa dauke idanuna nayi akanta, wato wata irin classy matace a tsaye, daganin fuskanta kasan ta soma manyanta saidai tsufan ya boye sosai don kwata kwata bazaka iya tantance shekarunta ba dukda tana early 40s, farace tass kamar a bula fatarta jini ya futo,ya allahu, tana da kyau sosai don doguwace, sanye take da wata azababbiyar abaya baqa wadda ta haskata sosai tayi mata kyau don ta haska fuskanta data dan hade girar sama da kasa, gaba daya zubinta irin na matan nan ne da basa daukan nonsense, ga jii da kai da kudi da aji, waya ce kawai a hannunta kirar iphone 15 pro max latest, gefenta kuwa wata maid ce rike da Jakarta da wasu document tana biye da ita a baya don kusan taku uku ne tsakaninsu saboda ita ba a jerawa da ita.
Idanun matar sunsha kohl baki wuluk tayi lining idanun nata sai bakinta dayasha jan matte lips stain.
Kamaninta sun fito sosai da su fadwa saidai kamannin nata yafi zama visible da afiya don tama fi yanayi da afiya akan fadwa dukda kamanninsu ta jini itama ta fito.

Saida ta gitto parlorn ta hango dattijon sai kuma maganganunsa da barad data jiyo.
Chak ta tsaya tana kallonshi kafin ta tako cikin kasaita ta karaso parlorn, fadwa ce tayi saurin miqewa tana mata sannu da zuwa kafin ta bata inda ta zauna ta koma gefe.

Kamar an mata dole haka ta dago ta kalli maid din kafin ta bata umarnin wucewa da Jakarta zuwa sama, kallon barad tayi kafin ta mashi nuni da hanyar stairs ba tare da tace uppan ba, miqewa yayi yana ma dattijon murmushi kafin ya fuce daga parlor.

Gyaran murya tayi kafin tayi relaxing bayanta akan kujerar ta daura kafa daya kan daya duk akan idanun dattijon yana kallon ikon allah, saida ta dan dauka yan few seconds kafin ta soma Magana anatse with class
‘’marhaban khaal’’
‘’shukran Hidaya fatan na sameku lafiya’’
A gatsale ta yatsine fuska tace ‘’alhamdulillah’’
Shuru ne ya biyo baya, su fadwa dai kallonsu suke daga shi har ita, yanda kasan maqiya sun hadu.
A duniyar nan hidaya bata kaunar ganin mutumin nan agidannan,a yanu tana mashi kallon kamar maqiyinta dukda yana matsayin qanin mahaifinta marigayi Taheel, duk yanda taso akan ganin ya raba hanya da gidan abun yaci tura don ita gani take yana son ya shiga tsakaninta da big baby dinta ne to wama ya isa? Babu shi a doran kasa.
Bata qaunar kowa ya rabe shi kwata kwata,wannan yasa duk yanda zatayi saitayi don ganin tayi pushing uncle away.

Ganin shurun yayi yawa ne yasa hidaya cewa ‘’ko zan iya sanin dame kake tafe?’’
Mamakin jin tambayarta yayi da yanda tayi mashi tambayar saidai saninta da halinta yasashi dannewa kawai ya gyara zama don idan har zai bi abunda zuciyarshi ke raya mashi akan yayan dan uwan nashi marigayi Taheel to fah bazai kara waiwayar su ba, gyara zama kawai yayi ya danyi relaxing bayanshi kafin ya soma magana.

‘’ba komai ne ke tafe dani ba sai maganar Tajudeen,’’
Saurin rintse idanu tayi kafin ta budesu ta sauke akanshi,
Ganin haka yasa shi cigaba da cewa ‘’yanxu wata uku Kenan babu wani progress akan condition dinshi, shine nace ko zamuyi trying wasu expert health organization da suka kware sosai ta wannan fannin na wasu kasashen daban ko za a samu dacewa’’
Tsagaitawa yayi kafin ya nunfasa ya cigaba da Magana cikin kamala ‘’ ni ina ganin idan muka dage sosai akanshi za a samu cigaba akan matsalar tashi’’

Wani irin kallo take mashi mai wuyar fassara wanda yana hango tsantsar bacin rai a cikin idanunta saidai fuskanta bai nuna hakan ba shima hakan bai sashi ya tsagaita ba don hakan bazaisa yayi shuru ba.

Cikin muryarta mai tafe da wani irin salo mai jan hankali ta soma Magana ‘’so yanxu kana ganin babu abunda nakeyi akai ne?well likitocin nan kasar ma top notch doctors ne kuma there are one of the best in the whole world and I trust them, khaal I know what is best for him, babu wanda zai nunamin damuwa akan matsalar big baby, so please idan kazoo ne akan wannan maganar ka ajiyeta don I know what is best for him baka fini sanin abunda zai taimakeshi ba don nice komai nashi, so please..’’ta karashe tana mai kallon cikin idanunshi babu ta kunya balle ganin girmansa

Fadin irin bacin ran da dattijon da suke kira da khal yake ciki ma bata lokaci ne, yau yaga karshe rashin mutunci wajen yar dan uwansa, yarda aka haifa a gaban idanunsa.

Wani irin heavy abu yaji a kirjinsa kamar an buga mashi dutse, haka yayi saurin runtse idanu yana danne abunda yake ji.

Mikewa yayi tsaye ba tareda ya kalleta ba yace ‘’shikenan na barku kuyi abunda kuka ga yayi dace, saidai ina tunasar dake, ba’a wasa da amana duk qanqantarta zan samu ganinshi yanxu?’’
Cikin sauri ta dago ta maida dubanta gareshi da jajayen idanunta kafin ta maida dubanta ga agogon rolex dake maqale a hannunta ‘’I’m sure he’s asleep by now, don…’’
Kasa daukan wulaqancin yayi don haka yayi saurin katseta ta hanyar cewa
‘’ ba damuwa na barku lafiya’’

Yana kaiwa nan ya masu sallama ya nufi hanyar futa, harya fuce hidaya bata bar kallon hanyar dayabi ya fuce ba, tafarfasar da zuciyarta keyi kamar an zuba tafashen ruwan zafi, su fadwa kuwa kasa cewa uppan sukayi sai zuba mata idanu da sukayi suna kokarin karantar reaction dinta,
‘’tirkashi ana wata ga wata,interesting’’ fadwa ta fada a zuciyarta tana mai tunanin wani abu.
Ganin ta mike tsaye yasa suka bita da idanu harta wuce hanyar stairs anatse kamar wata dawisu.

Kallon juna sukayi atare kowannen su da irin tunanin dake yawo a zuciyarshi…

 

 

File Name   Matar Taj 2… Hausa Novel Doc.
Title    Matar Taj Book 2
Author    QueenMarh
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    29/04/2024
File Size    433Kb
Format Size    TXT
Phone No   08032542629
Download Matar Taj Book 2 Complete Novel Document By QueenMarh

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button