Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 67 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-SEVEN📍

Shafa kyakkyawar fuskarta me kama da tata sak umm tayi tana murmushi tace;
“Be dade da fita ba dear”…
Kamo hannun umm tayi cikin muryar marasa lafiya tace;
“Dan Allah ki kiramin shi”…..
Shafa kumatunta tayi tace;
“Okay sweetie, zan kira shi but I want to know how you’re feeling first?”….
Yatsina fuska tayi kamar batasan magana ta kamo hannun umm ta dora a gefen cikinta tace;
“Nan yana min ciwo”….
Gyada kai umm tayi cikin tausayawa tace;
“Sorry love, dole ze miki ciwo because of the stitches but you will be fine very soon”….
“Okay”…..
“Babu inda yake miki ciwo bayan nan?”….
“Babu”…..
Doubtfully umm tace;
“Baby are you sure?”…..
“Yes mom”…..
“Okay bari na kira miki shi”…..
Umm ta fada tana barin dakin….
Wani sanyi baby tee taji a ranta, ta lumshe ido tana jiran shigowarsa….
Umm na fita sukayi clashing da deen daya zo kawo mata wayarta dake hannunsa saboda kiran da ake mata…
“Yauwa kai nake nema saif”…..
“Gani umm, nima wayarki na kawo anata kira, how can I help you?”…..
“Kanwarka ke nemanka, tinda ta tashi take tambayarka, let me have my phone”…..
Ta fada tana karban wayar, bata jira cewarsa ba ta bar wajan….
Kamar dazu haka ya sake shiga da sallama ciki ciki a bakinsa, kamar dazu ita ta fara hangosa saboda yanda hankalinta yake kacokam akan kofar, saurin rintse ido tayi saboda wani irin kwarjini da taga ya mata……
Karasawo har bakin gadon yayi ya shiga binta da kallo, musamman gashin idonta dogaye daya dan nannade saboda yanda ta garkame idon…..
Sai da yayi kusan 2mins yana kallonta sannan cikin dan daga murya yace;
“Kehhh!”…..
Shiru tayi gabanta na faduwa, sai a lokacin tayi dana sanin kiransa da tace ayi, data sani da cewa umm tayi su dawo tare, yanzu da yazo yana mata ihu me zata ce masa?…..
“Open your eyes nace!”…..
Da sauri ta bude idon kanta na wani mugun sarawa saboda tsawan daya daka mata…..
“Meyasa kika ce a kirani?”…..
Murya na rawa tace;
“Ba..komai”…..
“I’m not taking that as a reason! Ki fadamin abinda yasa kika ce a kirani before I lose it for you”……
“I want to say thank you”…..
Ta fada a sanyaye cike da tsoro….
Sai da yaji wani abu me sanyin ya taba zuciyarsa saboda laushin muryarta amma ya dake yace;

https://aihausanovels.com.ng/sirrin-rike-miji/yadda-zaki-kula-da-nononki-lokacin-shayarwa/

“What did I ttell you the other time?” …..
“Kayi hakuri”…
Ta fada tana dauke dan guntun hawayen daya zubo mata, bata sani ba haka kawai takejin duk abinda ya mata har cikin zuciyarta….
Sosai yaji ba dadi a ransa amma ya tabbata idan ya biyewa zuciyarsa zatayi leading dinsa zuwa ga halaka shiyasa ya dage sosai gurin ganin ya tsaya akan abinda ya dora kansa, dauke idonsa daga kanta yayi ya koma ya samu guri ya zauna daga chan gefe.
Umm na karban wayan ta tafi dan nesa da mutane tabi call din datayi missing, gama call dinta keda wuya ta hango abby na tawowa, sauke wayar tayi daidai abby ya karaso gurin…
“Boddi”….
Ya fada a hankali…
Shiru tayi ita bata amsa ba ita bata bar gurin ba….
“We need to talk”….
Ya sake fada yana kallonta…
“About what?”…
Sai a lokacin ta dago ta bashi amsa….
“Saifuddeen”…..
“What about him?”…..
“He has tried a lot, don’t you think son fatima yake?”.
Wani irin kallo ta masa tace;
“In ma sonta yake ba ka riga ka bada ita ma wanda kake so ba?”.
Girgiza kai yayi yace;
“Ba haka bane boddi, kema kinsan if I knew there’s something going on between fatima and saifuddeen babu yanda za’ayi inso bare akansa”…..
“Toh yanzu kuma da bappa ya shiga maganar you thought abu me sauki ne ayi wannan zancen? I will advise you karka sake tada maganarnan”…….
“Insha Allah boddi na”….
Haderai tayi tana shirin barin gurin yayi saurin fadin;
“Dan Allah ki tsaya, there’s something I want to ask you”….
Juyowa tayi fuska a daure tace;
“Menene?”……
Sai da yayi gathering duka courage dinsa sannan yace;
“Meya hanaki yin aure tun bayan rabuwarmu?”….
“Ra’ayi!”….
Ta bashi amsa a takaice….
“Nasani choice dinki ne boddi because you’re a very beautiful woman and getting married again will be the easiest thing for you but you refuse to, could it be that son da kike min ne ya hanaki wani auren?”…..

Hanyoyin Magance Matsalolin Ma’aurata

Wayam yaga babu mutum a gurin abinda be sani ba tinda ya fara zancen ta bar gurin saboda bazata iya sauraran kayan takaici ba, Allah ya taimakesa bataji karshen zancen ba…….
Chan ya hangota har ta kusa shigewa ciki, bin bayanta yayi da sauri, ko kafin ya karasa ya nemeta ya rasa…..

“Toh yanzu me kikeso ince?”…..
Cewar mami tana dariya bayan ta bata labarin tambayar da abby ya mata….
“Warning nakeso ki masa babu ruwansa da personal life dina, he should respect himself and never intrude!”….
Dariya mami ta cigaba dayi tana sauraran warnings din da umm take bata kamar itace abby, sai da taga tayi shiru sannan tace su tafi su tawo dasu bappa su duba baby tee, ba musu umm tabi bayanta suka nufi inda su bappa suke, suna zuwa ba bata lokaci suka fito tare dasu.
Da sallama suka shiga dakin gabadayansu banda khaleel daya tsaya jiran abby, basu jima da shiga ba sai ga Abby da khaleel sun shigo suma, sannu suka hau yi mata a tare suna mata addu’a, tana jinsu amma ta lafe kamar me bacci dama idonta a rufe yake, karasowa gaban gadon khaleel yayi a tausashe yace;
“Sannu wifey, Allah ya baki lafiya”…
Dagowa deen yayi ya kalleta daga zaunen da yake ya tabe baki yana girgiza kai, sarai yasan idonta biyu amma besan abinda yasa taki kulasu ba….

“Yaya saif”….
Suka jiyo muryarta a hankali tana kirasa…
Babu wanda beyi mamaki ba dan duk a tinaninsu bacci takeyi, sai duka hankalinsu ya koma kan deen.
Ganin yanda kowa ya juyo yana kallonsa yasa sa mikewa ya karasa gaban gadon tare da fadin;
“Gani, menene?”…
A sanyaye cikin muryar marasa lafiya tace;
“Ka dagani, inaso in…”.
“Bazan dagaki ba”.
Ya dakatar da ita tin kafin ta kai karshen zancen.
Khaleel na ganin haka ya matsa da niyar dagata, har ya mika hannunsa zai tabata deen yayi saurin ture hannun, sannan cikin bacin rai ya juyo yace;
“Bakada hankali ne? Kai shahon ina ne? Waya gayamaka ana zama daga suggery? Haka kawai zan ki dagata ne ni?”…
Sai kuma ya juya kan baby tee yace;
“Ke kuma kar in karaji kince wa wani ya dagaki, idan kin kwantar da hankalinki ma nan da awa uku zaki bar kasar gabadaya, suma banso sun zo ba, so nayi muzo mu biyu a miki abinda za’ayi mu koma amma tinda sun zo sai mu rankaya mu koma gabadaya”….

https://aih
Shiru dakin ya dauka ba wanda ya iya tanka ma deen duk da basu ji dadin yanda yayiwa khaleel masifa ba, saidai duba da kuma akan gaskiyarsa yake shiyasa suka kasa cewa komai.
Tsaki yaja ya koma inda ya tashi ya zauna, da fita zeyi ma wata zuciyar tace gwara ya zauna kar ayi wani shirmen baya nan.
Kiran da Dr. Max yayiwa umm a waya ne yayi breaking silence din da dakin ya dauka, picking call din tayi yace mata ze turo a tawo da ita office dinsa yanaso suyi magana akan health din baby tee, okay kawai tace sannan ta juyo ta kalli deen tace;
“Muje ka rakani”.
Tashi yayi yabi bayanta batareda ya tambayi ina zasu ba.
Suna fita sukaci karo da wanda Dr. Max ya turo, sai a lokacin umm take gayawa deen kiran da Dr. Max ya mata, deen na jin haka yace yayi tafiyarsa shi yasan office din.

Zaune suke a gaban Dr. Max bayan sun gama tattauna yanda zasu shawo kan lamarin baby tee da yanda zasu kula da lafiyarta har Allah yasa stitches din ya warke ta dena experiencing duk wani pain da sauransu.
“Saif isn’t it too early? Dadai mun bari ko gobe ne?”…
Cewar umm da bataso maganar discharge da deen ya dauko bayan sun gama zance ba…
“A’a umm kina ganin yanda zahrah duk ta kagu ta tashi ai gwara mu koma gida zatafi jindadi, besides zamu fi kula da ita a gida, idan tana cikin asibitin nan kuma bazasu yarda ta motsa ba sai gobe”..
“Since you insisted saif bari kawai suyi discharging din namu”…
Nan da nan suka fadawa Dr.Max abinda suka yanke, ba bata lokaci ya basu discharge letter saboda ya yarda da kwarewarsu yasan kuma tinda sukace zasu kula da ita zasuyi… Godiya suka masa sosai sannan sukayi sallama suka tafi already deen yayi clearing bills din tin kafin a basu appointment, dama ka’ida kenan..
Sun dauko hanyar komawa ward din da baby tee take deen yayiwa umm tambayar da ta dade tana damunsa..
“Umm baki taba magana akan education din zahrah ba why?”….
“Nifa ban dauki degree din da akace tanayi a matsayin karatu ba because banga alamar tasan abinda takeyi ba saif, she’s still very young, I just want her to start afresh”….
Umm ta fada da iya gaskiyarta..
“No umm tinda ta fara gwara ta karbi certificate din, she can go for a second degree but this certificate will make it easier for her in building her future career”…
“Eh kace wani abu kuma saif, that’s so considerate of you, yanzu a wani level take toh?”….
Dariyar da be shirya ba yayi yace;
“Wai fa a final year take, jiya suka gama first semester exam”….
Zaro ido umm tayi tace;
“What?? What’s she even studying? You mean batayi exam ba?”…
“MLS, kamar paper daya tayi”…
Ya fada yana cigaba da dariyarsa….
“And you’re telling me ta karbi certificate ta ina din?”..
Saita kansa yayi yace;
“Kwantar da hankalinki umm, nayi accessing transcript dinta naga performance dinta is very good, infact bata da carry over ko daya, na riga nayi filing undertaken na rashin lafiyanta, Insha Allah zatayi resiting idan ta samu sauki”…..
“Project fa? I don’t think ko proposal tayi”….
“She has gone through a lot, ga rashin lafiya and the rest, kinga dole mu mata uzuri umm”….
“Hakane saif”…
Ta fada a sanyaye tana jin wani daci a zuciyarta, Allah ya sani kota yafe bazata taba dena jin takaicin abun a ranta ba, ita kadai tasan yanda abun yake damunta idan ta tina what her daughter has gone through.
Murmushi yayi cikin karfafa mata gwiwa yace;
“It’s not too late for her umm, just like you said she’s still very young so zamu iya re shaping rayuwarta and I promise you she’ll bag this degree this year Insha Allah”….
Shafa kyakkyawar fuskarsa tayi tace;
“Jazakhallahu bi jannah habeebee”.

Kamar yanda deen ya fada after three hours suka bar asibitin, a gadon marasa lafiya aka fita da baby tee aka sata a emergency vehicle din da ze kaisu airport lokacin tana bacci batasan ma anayi ba, sai bude ido kawai tayi ta ganta a Nigeria….

One month later
A cikin wata dayan nan abubuwa dayawa sun faru, masu da dadi da marasa dadi saidai masu dadin sunfi yawa, na farko akwai samun lafiyar baby tee bisa ga kulawar saif da umm, sosai suka tsaya a kanta suka tabbatar tana kiyaye duk wani abinda suka san zeja mata matsala ko kawo side effect, da kuma shan magani bisa ka’ida a kuma kan lokaci, sosai saif ya taka rawar gani akan lafiyar baby tee dan a ka’ida sai tayi wata biyu kafin ta warware cikin ikon Allah ko tun ba’ayi sati biyu ba suka ga chanji sosai saboda yanda suke kula da ita, haka ma mami ba’a barta a baya ba dan itama tana nata kokarin a matsayinta na wacce ba likita ba, haka su abby da dad kullum suna hanyar zuwa dubata, dangin abby ma babu wanda bezo ya dubata ba na nesa da kusa, mahaifiyar abby haka ta dinga kuma tana rokan yafiyar umm da baby tee, ta kuma roki umm ta bari a kawo musu ita idan ta warke…..
A cikin wannan wata dayan zuwan umm UK sau uku tana dawowa shiyasa jinyar baby tee ta koma kochokam a hannun deen har Allah yasa ta warware sai dan abinda ba’a rasa ba, ya bata kulawa iya kulawa saidai kash tarayyarsu ta tabarbare kamar yanda ya kudirta, dayazo ya bata magani ya mata allura shikenan baze kara kulata ba, ko kallonta bayayi bare ya amsa gaisuwarta, sosai yasa mata mugun shakkarsa dan indai yana guri shikenan sai ta nemi nitsuwarta ta rasa, saidai kuma tarayyarsu da khaleel ta kara karfi, sosai suke zuba soyayya me sanyi me tsafta tana kuma gudin bacin ransa saboda ciwonsa, kusan kullum sai yazo zance ya kuma tawo mata da kayan ciye ciye kala kala, shima kuma yaya sama yaya kasa yake yiwa deen dan gaisuwar mutunci ce a tsakaninsu yanzu, ita kanta yanzu ta yarda tana son khaleel tsakani da Allah saidai ta rasa meyasa tana ganin deen take rikicewa taji hankalinta ya koma kansa gabadaya, a haka ma tana dannewa gudin kar mutane su gane halin data shiga amma ita kadai tasan yanda take ji aranta, haka zataita satan kallonsa a boye, duk randa tayi rashin sa’a ya kamata yata masifa kenan yana zaginta, a gabansu umm ne kawai yake raga mata, abinda batasani ba kuma indai tana guri baya iya dauke idonsa akanta saidai in magana yake da wani, shiyasa bayaso ta kallesa karsu hada ido ta gano kallonta yake…..
Kamar yanda deen yaci alwashin focusing akan career dinsa haka ya kasance dan ya rage zaman gidan, wataran ma sai suyi kwana biyu basu gansa ba saida umm ta taka masa burki tace ko be kwana a gidan ba yana zuwa yana gaishesu kullum, sosai yayi concentrating akan asibitinsa da companies dinsa kamar ba unserious deen ba, sannan kamar yanda yace ze bude ido ya samo matar aure be zauna ba tinda suka shigo Nigeria, da farko ta social media account dinsa yaso ya fara ko allah zesa yaga wacce ta dace dashi ta online amma yana zuwa yaga baby tee ta masa operation a kowanne account dinsa, yayi niyar mata tass ya tina patient ce kawai ya hakura ya kyaleta, amma yaci alwashin sai ya mata magana koda gaba ne, na biyu wa’yenda suke kawo masa hari a office ya fara bawa chance, mutum uku ya kula kuma kowacce kwanansu uku da fara soyayyar ya gwadata, sai ya kirasu yace suzo su samesa a hotel, abun mamaki sai yaga sun zo ba musu, kuma ko wacce tana zuwa sai ta nuna masa tasa abinda yasa ya kirata basai yace komai ba ita a shirye take ta bada hadin kai, sosai abun ya basa mamaki ya fatattakesu babu shiri, shine daya gwada har mutum uku yaga duk babu na Allah yaci alwashin baze kara kula masu kawo kansu ba, da kansa ze cire girman kai yayiwa wata magana, ana haka rannan yana driving ze tafi office yaga wata black beauty tayi whining down tana bada sadaka, hakan kawai sai ya burgesa, juyowar da zatayi suka hada ido, murmushi me kyau ya mata tayi saurin sunkuyar da kai, ana gab da basu hannu ya fita da sauri ya zira mata card dinsa ta window ya shiga mota yaja ya tafi….
Yana kwance da daddare yaga call da sabuwar number, sharewa yayi saboda gabadaya ya manta da ya bama wata numbersa, saida yaga kiran yayi yawa sannan ya dauka, bayani ta masa wacce ya bawa card dinsa dazu a traffic ce, sai sannan ya tuna ta, satinsu daya suna waya da ita yace tazo guest house dinsa ta samesa, tana zuwa ya fada mata kudirinsa ta amince ba mata lokaci ta kuma fada masa ita yar hannu ce duk sanda yake bukatarta a shirye take, mamaki ne ya kamasa saboda yanda yake mata kallan me hankali ashe itama duk sune, mutum biyu ya sake kulawa yaga suma duk sammakar, ba karamin sarewa da lamarin mata yayi ba ya zubawa sarauta Allah ido yana tinanin next step daya kamata yayi taking, sai abubuwan suka taru suka masa yawa ya koma deen dinsa na da, kullum cikin kunci da rashin walwala…..
Wani sabon abu daya faru shine dinkewar baby tee da eesha, sun zama tamkar best friends, kawancen ya samo asali ne tindaga ranar da baby tee suka dawo daga india, shikenan eesha kullum sai tazo gidan dake hutu suke, tun baby tee bata kulata har tazo tana kulata saboda yanda ta nace mata, komin wulakancin da zata mata bata nuna damuwarta ko a ido, sai tazo ta fara kulata har suka zama kawaye sosai, a halin yanzu ma eesha bata da kawar da tafi baby tee dan bikin yayanta da ake shirin yi ma komai iri daya suka dinka da baby tee har style iri daya sukayi, wani abun nasara daya samu eesha kuma shine amsa gaisuwarta da deen yakeyi yanzu, sannan tana kiransa a waya ya dauka su gaisa amma daga gaisuwa babu kari, ita iya wannan ma ji take kamar ta cimma wani abu a rayuwarta sannan gani take duk saboda baby tee ta samu yake kulata, abinda eesha bata sani ba kuma deen yana da dalilinsa na yin hakan..
Wani abun farin ciki daya sake faru shine samun cigaba me yawa a lafiyar su daddy da alhaji habibu, sosai bappa ya tsaya akan lamarinsu likitoci nayi malamai nayi , bisa ga amincewar Allah an samu chanji sosai a lamarinsu dan sun fara gane mutane sama sama, a halin yanzu ma bappa ya dade da barin garin yace kuma bazai dawo ba sai bikin baby tee da khaleel sannan kowa ya koma har su uncle A, twins kawai aka bari wai su tayi baby tee jinya kafin suyi resuming school dake hutun karshen session sukeyi, kuma hutu ne me tsaho…

Taku yake cikin isa da izza kamar yanda hakan ya kasance yanayin tafiyarsa, sanye yake cikin black suit sai rigar ciki dark blue, sosai kayan ya zauna masa, hakan sai ya kara fito da cikar halittarsa da zatinsa, sosai yayi balakin kyau amma fuskarnan a hade kamar be taba dariya ba, da sallama ciki ciki ya murda kofar parlourn mami, sa kai yayi ya shiga yana kara daure fuska dan yau da wani mugun bacin rai ya tashi, yana shiga yaci karo da baby tee da hussy a zaune suna kallo, kana kallonsu kasan basu dade da tashi daga bacci ba saboda suturar dake jikinsu, gwara hussy rigar bacci ce a jikinta wacce ta sauka har kasa, ita kuwa baby tee wata yar fingilar mini gown ce a jikinta da karyane ta duka ba’a ga bayanta ba, ranshi ne yayi mugun baci yana ayyana idan bashi kadai ya shigo ba fa.. A kausashe cikin sabon bacin ran daya taso masa bayan wanda yake ciki yace;
“Mahaukatan ina ne ku da zaku zaunawa mutane a parlor ba kaya, dalla ku bace min daga gani yan iska marasa hankali kawai”….
Rige rigen tashi sukayi saboda tsoro suka rasa hanyar da zasu bi, dauke kansa daga kan baby tee da iskar standing fan data tsaya a gurin ke kokarin daga mata rigar yayi yana forcing kansa ya goge image din daga brain dinsa, guri ya samu ya zauna bayan sun bar parlourn yana saita kansa .. Sai da yayi minti biyar yana saita kansa kafin ya mike ya haura sama, direct bedroom din umm ya nufa saboda yasan mami ta fita office, sai da ta bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama, amsa masa tayi ya duka ya gaisheta cike da ladabi…
Tashi tayi daga kan desk din da take zaune tana operating system ta dawo inda yake zaune a gefen gado, zama tayi a gefensa ta kamo hannunsa a bazata yaji tace;
“I don’t like the person you’re becoming saif!”…..
Da mamaki yace;
“What am I becoming umm?”….
“You’re becoming a sadist!”…
Girgiza kai yayi da sauri yace;
“No, not at all umm, I’m fine”….
“You’re not fine, this is why I really want to see you settle down, bana jindadin yanda nake ganinka kwana biyun nan”…
Kasa shiru yayi saboda ta sosa masa inda ke masa kaikayi, cikin wani irin yanayi yace;
“Toh ni ya zanyi umm, matan ne sun zama sai a hankali, the moment I started getting along with one sai inga bata da tarbiyya, besides na kasa samun wacce nake so”…..
Sake kamo hannunsa tayi cikin tausayawa tace;
“Insha Allah you will get to find a perfect love, you just have to open your heart sannan ka dage da addu’a sosai sai kaga Allah ya kawo tagari, muma muna maka habeebee”…..
“Insha Allah, thank you so much umm dina”….
“You’re welcome darling”…
Ta fada sannan tayi pecking dinsa a kumatu…..

Tinda suka shige cike suke bawa hassy labarin abinda ya faru, baby tee sai tsinewa deen take wai yace musu yan iska, tana cikin masifa wayarta ta fara ringing, ko duba wanda yake kira batayi ba tayi picking hade da sawa a kunne….
“This is your supervisor speaking, I want to see you in my office in the next five minutes!”…
Taji wata dakakkiyar murya ta fadi haka, ko kafin tace wani abu taji kit an kashe wayar, bata gama dawowa hayyacinta ba taji karar shigowar message, tana dubawa taga location din office ne kuma da number da aka kirata aka turo, sosai tasha jinin jikinta saboda daga jin meshi kasan bashida kirki, su hassy na tambayarta meya faru kawai suka ga ta fada wanka, gudu gudu suka ga ta fito ko bra bata sa ba ta zira wata abaya, ta figi mayafi ta dau mukullin motar da abby ya siya mata ta fita, sai magana suke mata taki kulasu, ko umm bata yiwa sallama ba ta shiga mota taja a guje sai school, tana zuwa bata tsaya a ko ina ba sai address din da aka turo mata, bata sha wahalar gane office dinsa ba saboda yanda yayi detailing komai…
Tsaye take a bakin office din gabanta na wani dukan uku uku, bata taba jin shakkar wani da bata sani ba irin ranar, sosai take jin kwarjinin meshi tun kafin ta gansa, hannunta ta dora akan handle din kofar bugun zuciyarta na tsananta, tsabar rudewa ko knocking batayi ba kawai ta danna kai ta shiga….

Back to top button