Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 91 Complete Novel

Father of soldiers

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina pls banda phone call just message ta whatsapp,08103884440❤_

 

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

 

*Aunty Babba*

Guntun tsoki taja,yayin da idanunta ke kallon agogon dake manne acikin ɗakin,kusan ƙarfe 6 na marece babu hayaam babu alamarta,har ta fara gajiya da jiranta,tun ɗazu take traying numbar wayarta amma Still Switch off,hakan ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba,tunani tashiga yi ko ina ta shiga?daga zuwa curo kuɗi a banki shiru kake ji wai malam yaci shirwa,
Ruƙe qugu tayi tare da yin ƙwafa,ta koma gefen gadon ta zauna,tana jiran shigowarta,tuntana sa ran dawowarta harta fara fidda rai,lokaci sai gudu yake yi har wurin ƙarfe 7,hayaam bata dawo ba,duk tana azaune har 8 ta buga,
“Allah yasa ba gantalin nata ta tafi ba,daga zuwa curo kuɗi a banki kamar na aiketa wata uwa duniya,tabi duk ta rufe layinta,Mtsww”ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki,

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Yayin da aunty babba ke zaman jiran hayaam,ita kuma tana can rai hannun Allah a ɗakin haroon,Lokacin daya hanata fita daga ɗakin ya zura key a wondonshi yace ta taimaki kanta,tayi tsammanin cewa zata iya kwatar kanta saboda tasa ba gara sofwan saurayinta,hakan yasa cikin salon wayau ta zura hannunta acikin jakarta,batare da ya ankare ba,Ta curo kwalbar turare ta fesa mashi asaman fuskarshi,kai tsaye ya ta6a idanuwanshi,raɗaɗi yasa yayi saurin kai hannu yana murza idanun nashi,ganin ya fita hayyacinshi yasa tayi ƙoƙarin zura hannunta acikin wandonshi,aikuwa batayi wani aune ba yayi mata ƙwaƙƙwarar damƙa,Ya yayyaga kayan jikinta da hannunshi,tundaga tsaye ya fara biyan buƙatarshi da ita,cikin rashin imani haroon yayi mata kaca kaca,Karshe yayi wurgi da ita saman gadonshi,Ya tu6e kayan jikinshi kamar yadda ya cire nata gaba ɗaya,sannan yabi ya danneta kamar wani bakure haka yakai mata Hari,wa’iyazubillah duk yadda taso ta ƙwaci kanta amma hakan ya faskara,Tun tana ihu tana kuka har bakinta ya mutu ƙarshe ta sume…..”

*Boss Bature*

❤🤍❤

*SEHRISH*

Wuraren ƙarfe 10 na dare,tana a kwance saman gadonsu,ta ƙudundune cikin bargo,bacci harya fara ɗaukarta,tajiyo ringing ɗin wayarta,a hankali ta zame bargon tare da miƙa hannu ta dauki wayar dake ajiye saman mattress din,daƙyar ta iya buɗe idanunta masu ɗauke da bacci,ƙurawa screen ɗin ido tayi yayin ta zuciyarta ke bugawa,Sunan My Boss Man ne ya bayyana da manyan haruffa,Gabanta ne yayi wani irin bugu rass!lokaci guda ta miƙe daga zaune tana faman zare ido,hannayenta har kerma sukeyi,Amsa kiran tayi tare da kara wayar a kunnata,Tunkafin tayi sallama Sexy voice ɗinshi ta katse mata hanzarinta da cewa”Am back,”yana faɗin hakan yayi rejecting call ɗin,
Yadda kasan gunki haka sehrish tayi kasaƙai,fuskarnan tamkar ta fashe da kuka,ɗan hutun da ta samu na kwana biyu ya ƙare,
Jiki asanyaye ta sauko daga saman gadon bayan tayi wurgi da wayar saman mattress ɗin,Sleeping dress ne ajikinta white colour masu ɗige ɗigen baƙi ajikinsu,sunyi matuƙar yi mata kyau,Riga da wando ne,

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Kaitsaye ta nufi wurin windown don ta leƙa taga idan dagaske ya dawo din,hannu tasa ta janye labulen tare da zuqe glass ɗinta,
daga inda take ta hango motorshi a parkin space,wannan ya tabbatar mata da cewar ya dawo yana a cikin gidan,hannu tasa tare da dafe goshinta a hankali ta furta”OMG!”
Gyaɗa kawai tayi tare da cewa”Ae shikenan,Za’a koma ƴar gidan jiya kenan,
Juyawa tayi ta nufi shoe rock ɗinsu,flat shoe ta ɗauko ta zura a ƙafafunta,sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar ɗakin tayi bayan ta fita ta datse ɗakin,
Fitowa tayi daga corridor din ta wuce kitchen,gidan tsit babu kowa,duk babu daɗi,tayi kewarsu sosai,musamman ɗan baby junaid ɗinsu,
Batasan ko zai buƙaci abinci ba,tun da yanzu ya dawo,Hakan yasa ta hado mashi Coffee kawai don tasan dole ya bukace shi,a cikin plate ta aza cup ɗin,ta fito daga kitchen ɗin,ta nufi upstairs,tunani tashiga yi ko ina su jahad suke,yanzu haka suna a ɗakin aunty azmee dama kwana biyun nan,duk in dare yayi suna zuwa fira ɗakinta,wani lokacin acan bacci yake ɗaukarsu,sae wurin asuba suke dawowa dakinsu,
A hankali take taka staircase ɗin harta haura sama,wuce wa part ɗinshi tayi,a baƙin kopar shiga falon ta tsaya,kamar yadda tasa ba,sae da fara karanta addu’o’in neman tsari daga sharrinshi sannan ta shiga ciki da sallama abakinta,
Babu kowa acikin falon,bedroom dinshi ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,sallama tayi mashi,daga ciki taji ya amsa mata,tare da bata Iznin shiga,
Shiga cikin ɗakin tayi cike da fargabar ganin fuskarshi,agaban mirror ta same shi tsaye,yana sanye da bathrobe,jikinshi da alamun danshin ruwan da yayi wanka,bata samu damar ganin fuskarshi ba saboda ya juya mata baya,
Ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi coffee ɗin saman table sannan tace”Sannu da dawowa babban yaya ya gajiyar tafiya”?
Tamkar bazai amsa mata ba,har sai da ta fidda rai da zaiyi mata magana sannan yace”Am ok,”ɗaya daga cikin abunda ke ƙona mata rai kenan,Saita saki baki tayi mashi magana mai tsayi ya bata amsa in short,

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

“Ga coffee nan,bansan ko zaka buƙaci wani abu ba,bayan wannan,”
“No,need,”ya ambaci hakan tare da juyowa ya koma daga gefen gadon ya zauna,tsayawa tayi saboda tasan halinshi,in har bashi ya sallameta ba,toh bata isa ta tafi ba,
Ɗagowa tayi ahankali ta saci kallon fuskarshi,yayi haske sosai la66an nan nashi sunyi pink tamkar ya shafa jan baki,ya ɗaure fuskar tamau kamar wanda aka aiko ma saƙon mutuwa,
Mayar da idanuwanta tayi akan fatar ƙirjinshi,ganin yana ƙokarin dagowa yasa tayi saurin kawar da idonta gefe guda,
Hannu yasa tare da daukar Cup of coffee din,sae faman tiririn zafi yake yi,saitin bakinsa yakai cup ɗin a hankali yake kur6arshi,
ɗan dakatawa yayi da shan coffee ɗin batare da ya ɗago ya kalleta ba yace”Ɗaukomin sleeping dress ɗin da zan sanya,”
Amsa mashi tayi da toh,Sannan ta juya,kamar ance ya ɗago idonshi karaf ya sauka akan Wandon jikinta,ɗigon jinin daya gani ne yasa shi yin wurgi da Cup ɗin hannunshi ya faɗi ƙasa ya fashe,wani irin tashin zuciya ne yazo mashi,da gudun gaske ya mike tare da tunkarar toilet ya faɗa ciki,
Hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,batasan meyasa shi jin amai ba,ita dae kawai taga yayi wurgi da cup kuma ya nufi toilet,tuni tasha jinin jikinta,tsananin tsoro ne ya bayyana kan fuskarta,tunkafin ma taji meyasa shi yin amai,
Gaban Basin ya tsaya,sae faman kakarin amai yakeyi,tamakar ƴan hanjin Cikinshi zasu fito waje,Wani irin ƙyanƙyami ne dashi,gaba ɗaya duk yabi ya burkice,almost 8 mins yana acikin toilet ɗin,tanajiyo sautin aman da yake yi,zugudum tayi tana jiran fitowarshi,
Hannu yasa tare da buɗe ƙopar toilet ɗin ya fito,jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin rai,idanuwanshi har sun canza launi,
A zafafe ya tunkareta,ganin haka yasa sehrish tashi ga ƙoƙarin ja da baya,tana ƙoƙarin guduwa daga bedroom ɗin nashi, damƙo wuyan rigar jikinta yayi,tare da janyota yayi wurgi da ita,ta bugi bangon ɗakin,
Raɗaɗin da taji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka,ware hannayensa yayi da nufin ya mare ta,runtse idanuwanta tayi da sauri tana kuka,
Yarfar da hannun yayi gefe guda,tsabar 6acin rai ya hana ya buɗe baki yayi mata magana balle har tasan laifin data aikata mashi,cikin shesshekar kuka tace”Dan Allah kayi haƙuri bansan laifin dana aikata maka ba,”
Tamkar ya rufe ta bugu haka yake ji,daƙyar ya iya buɗe baki yace”karki kuskura ki ƙara shigomin part ɗina da wannan ƙazantar a jikinki!ki tsaya har saikin kammala”
a ruɗe sehrish tashiga tunanin wata ƙazanta ce yake magana akai,da sauri ta shiga bin jikinta da kallo,a ƙoƙarinta nata gano abunda ya kira da ƙazanta,
.  hakan ba ƙaramin fusata shi yayi ba,a fusace ya buga mata tsawa wadda tayi matuƙar girgizata,ta zaburar da ita kuma ta tsoratar da ita,Nan take taji zubar jini acan under ɗinta,tare da matsanancin ciwon mara lokaci guda ya farmata,Sae lokacin ta gane cewa period ɗinta ne yazo mata,jinin ne ya fara zuwa shiyasa batayi noticing ɗinshi ba,sae daga baya raɗaɗin ciwon ya taso mata,
Dogon tsoki yaja,tare da juyawa ya nufi cikin ɗakin,

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

Sehrish kuwa tuni ta soma fita hayyacinta,idanuwanta sunyi jawur da su,kamar daga sama yaji tace”AMMA BAKA DA IMANI”_
gabanshi ne ya faɗi rass,dakatawa yayi da yin tafiyar tamkar antokare shi,
“Tunda nake arayuwata banta6a ganin mutun mara imani mara tausayi ba irinka!Jinin daka gani ajikina lalura ce bani na ɗaurama kaina ba,nikaina bansan dashi ba,da bazan bari ya zuba ajikin kayana ba balle har ka gani,duk irin ƙoƙarin da nakeyi wurin ganin na faranta maka rai baka ta6a gani ba,Nifa ba tsoranka nake ji ba!Allah kaɗae nake tsoro,Idan taƙamarka ƙarfi kazo ka buge ni,kaga in zan mutu,Na rayu da wanda yafi ka rashin Imani da tausayi,Kuma na jure zama dashi,naga tashin hankalin daya fi wanda nagani a wurinka,kuma duk na jure hakan…..”
Tashin hankali,Sanƙamewa sgr yayi atsaye,hankalinshi yayi matuƙar tashi,a arazane ya juyo don ya tabbatarwa kanshi da abunda kunnuwanshi ke juyo mashi,Jikinshi sae faman tsuma yakeyi,abun yayi matuƙar girgizashi,abun Yayi mugu mugun ɗaure mashi rai,Zuba mata ido yayi yana kallonta cike da mamaki,
“Dame ka ke taƙama ne?kaifa mutunne ɗan adam,mai hannu biyu mai ƙafa biyu,hancin ɗaya,da baki ɗaya,idanuwa guda biyu kamar nawa,Wanda idan yayi bacci sai yarda akayi dashi,idan ya mutu kuwa duk  kyanshi duk mun dukiyarshi duk ji dakanshi acikin farin yadi mafi arha za’ayi mashi sutura,ƙarshe ya zama abincin tsutsa,”
Waro ido waje sgr yayi hankali atashe yake kallonta,tunda yake arayuwarshi wata ƴa mace bata ta6a tsayawa agabanshi ba,kamar haka tana gaya mashi magana,Ido cikin ido batare da jin shakkarshi ba,yadda kasan mai iskokai haka sehrish ta rufe shi da faɗa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,har ya fara tunanin kodae Tasha ƙwaya ne?to ae ko wanda yasha ya bugi da giya bai ta6a kallon cikin idonshi ba ya gaya mashi magana,
“Burin ka kawai ka wulaƙanta rayuwata,shiyasa ka aure ni don in cigaba da aiki a ƙarƙashinka,Inayi maka biyayya ne ba don inajin tsoranka ba,kaima ka sani,ni ba baiwarka bace baiwar Allah ce,Kuma idan yau naga dama zan iya barin gidan nan,kuma baka isa ka dawo dani ba,dana so tuntuni wlh dana tafi nabar gidan nan,Ƴanci nane,”
.. Tana magana hawaye na shararowa asaman fuskarta,with confidence takeyin maganar,batare data girgixa ba,
“Zan tafi kuma kada kayi tunanin cewa idan na kammala ƙazantar zan dawo part ɗinka da sunan aiki,Bazan ƙara zuwa ba,kuma kada kayi tunanin cewa zanji tsoranka in gudu daga gidan nan ko inzo in baka haƙuri,Wlh bazan ta6a karaya ba,ka yi duk abunda kaga dama,ƙarshe kace zaka hukuntani ko,Idan ka tashi dan Allah kada kabarni da raina,ka kashe ni,”
Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki,a fusace ta juya tabar cikin bedroom ɗin nashi,
Sai lokacin sgr ya runtse idanunshi,la66ansa sae kerma sukeyi kaf kaf,saboda tsabar 6acin rai,Hannunshi ya cusa acikin sumar kanshi ya shiga cakuɗata,gaba ɗaya ya hargitsar da gashin kan nashi,Cizon la66ansa ya shiga yi,nan take le6en ya fashe jini ya soma ɗiɗɗigowa daga jikinsu,Zuciyarshi har wani boiling take tana burning,wani irin zafi ne ya taso mashi gadan gadan,jiri ya dinga gani acikin idanunshi harya fara tangal tangal zai faɗi ƙasa,
Daƙyar ya iya takawa izuwa gafen gadonshi ya zube ƙasa saman guiwowinshi tare da aza kanshi saman gadon,Tashin hankali Ran manya ya 6aci sosai,ƙoƙari yakeyi ya dakatar da bad temper ɗinshi saboda gudun karya aikata kisan kai,don muddin yakai matakin ƙarshe zaibi bayanta ne kuma sai yayi mata mummunar illa,
A hankali ya shiga furta”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un”!ya ambaci hakan kusan sau talatin,

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Novel

Sehrish kuwa bayan ta fita daga part ɗinshi,daƙyar take ɗaga ƙafafunta saboda matsanancin ciwon marar da takeyi,Gaba ɗaya duk wannan maganganun da ta gaya ma Sgr ba’a cikin hayyacinta tayi su ba,batasan ma ta furta mashi su ba,Zafin raɗaɗin ciwo ne yasa ta zazzaga mashi masifa,dama kuma a ƙule take dashi saboda ya ƙuntata mata sosai,kuma ya kira jinin da takeyi da ƙazanta abun yayi matuƙar ƙona mata rai,hada ƙarin hakan yasa ta balbaleshi da faɗa,
Tun tana tafiya da ƙafafunta har suka gaza ɗaukarta,ƙarshe a bakin shiga corridor ɗin ɗakinsu,ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saman tiles tana birgima,hannunta dafe da mararta,gashi babu wani a kusa balle ya kawo mata agaji,

Kamar yadda sehrish ta kwana waje saman tiles,haka sgr ya kwana zuƙunne saman guiwowinsa,kanshi na asaman gadonshi,Aranar bai runtsa ba,bacci ya ƙauracewa idanuwanshi,

Wuraren sallar asuba,Jahad ta fito daga ɗakin azmee tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsu,idonta suka sauka akan sehrish dake kwance a ƙasa,gashin kanta duk ya rufe fuskarta,da ƙarfi ta ambaci Sunanta SEHRISH,da gudun gaske ta ƙarasa tare da zubewa saman guiwowinta agaban sehrish ɗin,
“Innalallahi’wa’innalairrahiji un,Sehrish!meya faru dake ne!nashiga uku!Aunty Azmee!!!”duk tabi ta ruɗe,musamman data ga jini ya 6ata wandon sehrish ɗin,sai tayi tsammanin kodai taji wani mummunan rauni ne,Jijjiga jikinta tashiga yi tana cigaba da kwalama Azmee kira,
“Aunty azmee!Hosana!dan Allah kuzo ku dubamin!meya faru da sehrish ne!”
A ruɗe ta miƙe tare da tunkarar ɗakin azmee,tura ƙopar tayi ta faɗa ciki a hargitse,Adai dai lokacin Azmee ta kammala sallar asuba,juyowa tayi tana kallon jahad ganin hawaye asaman fuskarta yasa ta miƙe da sauri ta tunkareta tana tambayarta
“Jahad lafiya meya faru ne”
Muryarta har shaƙewa takeyi wurin ambaton sunan sehrish”Aunty azmee sehrish!bansan meya faru da ita ba,gata can kwance a ƙasa bata motsi,ga jini a jikin wandonta…..”tunkan taƙarasa maganar Azmee ta zabura da gudu ta fita daga ɗakin,itama jahad ɗin tabi bayanta da sauri,
Ƙarasawa azmee tayi wurin da sehrish take akwance,ta zuƙunna tana ƙare ma jikinta kallo,tsananin tausayinta ne ya kamata,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin cikin halin ha’ula’e,
Hannu tasa tare da shafa fuskarta,busassun hawayene asaman fuskarta,la66anta duk sun bushe ƙamas dasu,
ɗagowa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tana kuka,
“Ki kwantar da hankalin ki,ina tunanin suma tayi ne sakamakon Ciwon cikin da tayi,Jinin dake ajikinta na al’ada ne,”
Jin haka yasa jahad ta tsagaita da yin kukan,har hankalinta ya ɗan kwanta duk da akwai sauran damuwa atattare da ita,
“Aunty azmee duk laifin mu ne ni da hosana,da ace bamu tafi mun barta a ɗaki ita kaɗai ba,da duk hakan bata faru ba,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin nan,”
“ɗaukomin ruwa,in yayyafa mata,”
Da sauri jahad ta nufi fridge dinsu,hannunta har kerma yakeyi wurin yin saurin ta buɗe,bottle water ta ɗauko,sannan ta dawo wurin azmee ta miƙa mata,kar6a tayi ta 6alle murfin ta ɗan kur6i ruwan abakinta sannan ta fesar dashi asaman fuskar sehrish,
Dogon Numfashi taja,tare da sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,muryarta ƙasa ƙasa tashiga fadin”Cikina zafi,Ciwo yakeyi mun!dan Allah abani magani nasha,kada na mutu,”
“Jahad dauko mata magani,yana nan ajiye saman drawer ɗina,”juya jahad tayi da gudu ta nufi ɗakin azmee,
Hannu azmee tasa tare da ɗago da kan sehrish ta azata asaman laps ɗinta,kafa mata ruwan tayi abakinta,a hankali tashiga kwankwaɗar ruwan,dama makoshinta a bushe yake,
Dawowa jahad tayi hannunta ɗauke da maganin ta miƙa ma Azmee, bayan ta kar6a ta curo mata shi guda biyu ta sanya mata abakinta,tare da ruwan ta haɗiya,

Download>>> The Governor Wife Book 2 Complete Novel 

Bayan ta kammala sha,ta mika ma jahad robar ruwan”ki mayar dashi a fridge,bari na taimakata mu shiga daga ciki,”
Dakyar ta cuccu6i sehrish,don ma ba wani nauyi ne da ita ba,cikin bedroom ɗin nasu ta shiga da ita,Jahad tabi bayansu,
Toilet tashiga da ita,jahad sae faman zirga zirga take yi acikin bedroom ɗin nasu,duk wannan budurin da akeyi hosana nacan ɗakin azmee naɗe cikin bargo tana bacci,
Muryar azmee tajiyo daga cikin toilet ɗin tana yi mata magana”Pad zaki miko mun,tare da pant ɗinta,”_
Jiki na rawa jahad,ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinsu,wurin kayan sehrish ta ɗauko mata pant,sannan ta haɗo mata tare da pads,
Abakin ƙopar toilet din ta tsaya tare da ɗan knocking kopar,zuro hannu azmee tayi ta kar6i kayan,
Komawa jahad tayi saman gadonsu,ta zauna tana jiran fitowarsu daga cikin toilet ɗin,
Within mins,Azmee ta fito daga cikin toilet ɗin,hannunta dafe da sehrish,duk ta rurruketa gudun karta faɗi,Waist dinta na ɗaure da farin towel,sae faman cizon la66anta takeyi,saboda raɗaɗin da take ji har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,
Asaman bed ɗinsu Azmee ta kwantar da ita,jahad ta yafa mata bargo asaman jikinta ta lullu6eta,
“Sannu sehrish,Allah ya baki lafiya,” acewar jahad,
Dama ance ciwon ƴa mace na ƴa mace ne,su da suka son zafin abun gashinan sun taimaka mata,saboda suma sunayi kuma sunsan cewa lalurace,sannan sunsan irin raɗaɗin da takeji ajikinta,dayawa Wasu mazan basu son ya abun yake ba,tunda bayi sukeyi ba,shiyasa har suke ganinshi amatsayin ƙazanta,kuma basu yi ma mata uziri,aduk lokacin da sukayi kuskuren da jini ya bayyana ajikinsu,Wasu mazan nake nufi ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,Haka matan ba,bakowa bace ke taimakon ƴar uwarta ba,acikin irin wannan yanayin na period,
“Sannu Allah ya baki lafiya,”azmee ce tayi maganar,yayin da idanuwanta ke akan sehrish,wadda ta runtse idanunta tana ta faman ciccije la66anta,
Bata bar ɗakin nasu ba,har saida bacci ya ɗauki sehrish sannan tayi masu sallama,
Kwanciya jahad tayi agafenta,suna fuskantar juna,zuba mata ido tayi tana kallonta,cike da so da ƙauna,
A haka har bacci ya dauketa,

A 6angaren Sgr kuwa,ko sallar asuba bai samu ya halarta ba,Acikin bedroom ɗinshi yayi sallar,komawa yayi saman katafaren gadonshi ya kwanta yayin da blue eyes dinshi ke kallon Ceilling,Kalaman sehrish ne suka shiga dawo mashi acikin zuciyarshi,bakomai ne yafi tsaya mashi aranshi ba fa ce kalmomin nan guda biyu da ta kirashi dasu,MARA TAUSAYI MARA IMANI!sannan kuma tayi comparing ɗinshi da wannan fasiƙin mutumin, yaji raɗaɗin abun sosai acikin zuciyarshi,tayi matuƙar ɗaure mashi kai,Ko a ina tasamu ƙwarin guiwar gaya mashi magana?duk irin yadda take jin shakkarshi?yarinyar da ko cikin idonshi tsoran kallo takeyi,balle har ta ɗaga mashi yatsa,
Gyara kwanciyarshi yayi,ya koma yana fuskantar right hand ɗinshi,sannu a hankali bacci ya dauke shi batare da ya shirya yin shi ba,

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Wuraren ƙarfe Takwas na safe,jahad na cikin bacci,taji shessheƙar kuka acikin kunnuwanta,buɗe idanuwanta tayi tare da wurgasu wurin da take jin sautin kukan,Sehrish ta gani zaune ta jingina bayanta a head board ɗin gadon,sae kuka takeyi kamar wadda ta rasa wani mai mahimmanci arayuwarta,
Da sauri jahad ta miƙe zaune,tana kallonta tace”Sehrish!lafiya kike kuka?ko haryanzu ciwon cikin ne”?
Girgiza kanta tayi alamar a’a,
“To ki faɗamun meke damunki ne”?da damuwa a fuskarta tayi maganar,
Cikin shesshekar kuka Sehrish ta soma magana,
“Jahad!na shiga uku!najama kaina bala’e,Jiya nayi ma babban yayanmu rashin kunya,batare da sanina ba,wlh sai yau da safe na tuna duk abunda ya faru,nasan cewa bazai ƙyaleni ba,Dole ya hukunta ni”ta karasa maganar tare da sa hannu tana matsar hancinta,
Hankali atashe jahad tace”Sehrish!kodai mafarki kikayi ne?ae babban yayanmu bai dawo ba,kin manta sun tafi damaturu ne”?tayi maganar tana ƙoƙarin fahimtar da ita,
“Wlh jahad ba mafarki nayi ba,jiya ya dawo acikin gidan nan,yana nan a part dinsa,”
Hannu jahad tasa tare da dafe saitin zuciyarta adan tsorace tace”Munshiga Uku!garin yaya har kikayi mashi rashin kunya?kuma kina acikin hayyacinki babu magagin bacci atare dake”?
“Bana acikin hayyacina jahad,zafin ciwone yasa na balbaleshi da masifa,har ina nuna shi da yatsa…”kaf ta kwashe duk abunda ya faru a tsakaninsu ta sanar ma jahad,
Hannu jahad tashiga tafawa tana faɗin”wlh babu ruwana!sehrish kin shiga uku,mai kwatarki a hannunshi yau sai Allah,hukuncinki yafi ƙarfin ayi maki shi acikin gidan nan sai dai yakai ki can headquater dinsu,”
Jin wannan maganar,ya ƙara ɗaga hankalinta,fashewa ta kuma yi da kuka,
Lallashinta jahad ta shiga yi”Am sorry,zolayarki nakeyi,amma gaskiya sehrish Anya baki sha Codine ba?Yo ni ko giyar wake nasha,ae bazan iya tunkarar babban yayanmu ba,balle har in gaya mashi irin zafafa kalaman da kika yada mashi,”
Cikin shesshekar kuka tace”dan Allah jahad ki bani shawara,kodai in gudu in bar gidanne?kinga su daddy basu nan,zai iya kashe ni,”
Shiru jahad tayi tana saƙa wani abu aranta,sehrish kuwa ta zuba mata ido tana jiran jin shawarar da zata bata,
“Kinsan me!kada ki kuskura kije bashi haƙuri,Dama kin faɗa mashi cewa kada yayi tunanin zaki gudu kibar gidan ne,ko kuma zaki zo bashi hakuri,Sannan kuma kince mashi ba zaki ƙara zuwa part dinshi ba koda ace kin kammala ƙazantar ne,Inaso ya tabbatar da cewar dagaske kike mashi bada wasa ba,hakan zaisa abun ya tsaya mashi acikin ranshi kuma zaiji shakkar ƙara faɗa maki irin waɗannan kalaman saboda gudun kar girmanshi ya faɗi,sannan idan yaga kwana biyu baki je yi mashi aiki ba,ina da tabbacin cewar zai nemeki ne,Amma muddin kika je bashi hakuri,wlh sai kinyi danasani ne,”
“Amma jahad,rashin kunya fa nayi mashi,yakamata na bashi hakuri in ba haka ba Zai gane cewa ina acikin hayyacina na gaya mashi magana,kuma zai dinga yi mun kallon mara kunya ƙarshe ma ya tsane ni gaba daya,”
Murmushi jahad tayi tare da cewa”indai bazai ta6a lafiyar jikinka ba toh da sauki,ƙwara yayi maki kallon mara kunyar,akan dai kije bashi haƙuri,nasan bazaki fahimce ni ba,A yanzu amma nan gaba zaki ga amfanin yin hakan da kikayi,”_

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Zugudum sehrish tayi tana doubting akan abunda jahad ta faɗa mata,Anya kuwa jahad ba hanyar banza takeson ɗaurata ba?in ba haka ba saboda me zata hana ta zuwa bashi haƙuri,bayan itace mai laifi,A matsayin shi na mijinta kuma yayanta,bai kamata tayi mashi hakan ba,sannan kuma taƙi zuwa bashi hakuri,
Shigowar azmee ne ya katse mata zancen zucin nata,atare suka juya suna kallonta,
“An kammala breakfast,yana a dining yana jiranku,”
Ta karasa maganar tare da kai idanunta kan sehrish tace”Ya jikin naki”?
“da sauƙi alhamdullah,nagode ssai da irin kulawar da kuka bani,”
“Kada ki damu ae duk yiwa kaine,Amma naga kamar hawaye akan fuskarki,Ko haryanzu akwai ciwon ne”?
“A’a,naji sauƙi sosai,”
Murmushi azmee ta saki,kafin ta juya ta fuce daga ɗakin,
“Jahad kije kawai kuyi breakfast ɗin,Ni zan zauna a ɗakine,kada mu haɗu da babban yaya,Don nasan bazaiyi mun da kyau ba,”
“kada kisa damuwa aranki mana,duk kin bi kin tashi hankalin ki,Da yunwa zakiyi ta zama ne?bazaki ci komai ba”?
Shiru tayi ba tare da tace komai ba,
“Okey,zan kawo maki breakfast ɗin aɗaki sai kici hakan yayi maki”?
Ɗaga mata kai sehrish tayi”Eh,ki kawomin anan,zan fi samun kwanciyar hankali,akan in fita wajen,”
Saukowa jahad tayi daga saman gadon,ta buɗe kopa ta fuce daga dakin,
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tunani ta shiga yi ko a wani hali babban yaya yake ciki,Yayi bacci jiya ko baiyi ba,Allah yasa dai kalamanta basu ta6a mashi zuciyarshi ba,

shigowa jahad ta kumayi hannunta ɗauke da madaidaicin tray,kayan tea ne sai chips da sauran abunda baza a rasa ba,Asaman drawer ta ajiye mata shi,sannan ta juya ta fuce daga ɗakin,
Matsawa tayi kusa da trayn,sannan takai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin tana ɗan kur6arshi,
Cikin ƙankanin lokaci ta kammala yin breakfast ɗin nata,
Zama tayi cike da fargabar abunda zai biyo baya,
Ranta ne ya bata cewar,ta jaraba kiran aunty azeema ta sanar da ita abunda ya faru atsakaninta da sgr,may be ta samu shawara mai kyau a wurinta,
Da sauri ta ɗauki wayarta dake ajiye saman gadon,contact ta shiga ta lalubo numbarta,ta danna mata kira,tana fara ringing,Azeema ta ɗaga kiran nata,
Tunkafin tafara magana hajiya azeema tace”2 days ba hello ba hi ko?har kin fara mantawa dani ko,”
Murmushi sehrish tayi tare da cewa”ba haka bane,Aunty azeema kusan kullum ne saina nemi layinki,amma baya shiga,”
Azeema tace”Hakane fa,nifa wayata indai bani na kira mutun ba,da wuya ne a same shi,kullum busy nake,”
Shiru sehrish tayi tana tunanin ta ina zata fara kora mata jawabi,
“Ina sauraronki,Har yanzu ba wani cigaba a zamanki dashi”?_
Nan fa sehrish ta samu ƙwarin guiwar sanar da ita duk abunda ya faru atsakaninsu daren jiya,
Tayi tunanin aunty azeema zatayi mata faɗa ne,amma da buɗar bakinta sai cewa tayi”Very Good!hakan da kikayi mashi yayi mun dai dai wlh,”
Sakin baki sehrish tayi tamkar tana agabanta,kusan bakinsu ɗaya da jahad,
“Kada ki kuskura kije bashi haƙuri!nafi so ya gasgata kalamanki”
Cike da mamaki sehrish tace”Aunty azeema dagaske kike?kada na bashi haƙuri”?
“Ƙwarai kuwa,ina goyon bayan hakan ɗari bisa ɗari,kuma kada ki kuskura kije part dinshi da sunan aiki,Ki rabu dashi,dama ae yace kada ki koma mashi har saikin kammala kazantar kibarshi a hakan,kada ki wani ji tsoro,”
Lumshe ido sehrish tayi tare da ware su fuskarta da dan murmushi tace”Shikenan aunty azeema bazanje ba in sha Allah,”
“Namanta ban sanar dake ba,nafa dawo nigeria,tun jiya amma na wuce damaturu,bazan samu zuwa nan ba yanzu saboda abunda ya faru na rasuwar modibbo,amma kada ki damu zan bada saƙo ta wurin junaid,naji yace zai biyo Abusufyan idan ya tashi dawowa,zan bashi ya kawo maki har gida,Sannan zanyi maki bayanin yadda zakiyi amfani dasu,koda ta wayane,”
“Nagode sosai Aunty azeema,Allah yasaka da alkhairi,Amma yaushe zaki dawo nan?don nayi kewarki sosai,”
Dariya hajiya azeema tayi tare da cewa”Very soon zan dawo,”
Sehrish tace”to shikenan,Allah ya kaimu lokacin,”
“Ameen my daughter,”

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Sun jima suna waya kafin daga bisani ta ajiye wayar,har hankalinta ya kwanta,duk da akwai sauran fargaba atare da ita,

saukowa tayi daga saman gadon,Wardrobe ta nufa,hannu tasa ta buɗe,Arab gown ce ta ɗauko pink colour,tare da mayafinta shima pink ne amma bai ciza ba,kamar na rigar,zura kayan tayi ajikinta,sannan ta koma gaban mirror ta zauna,zuba ma mirror din ido tayi tana kallon fuskarta,ta cikin madubin,yayin da zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru adaren jiya,

A 6angaren Sgr kuwa,wata irin matsiyaciyar yunwa ce ta farkar dashi daga bacci,saukowa yayi daga saman gadon,Jallabiya ce ajikinshi,wuce wa yayi wurin closet ɗinshi,withins mins ya shirya kanshi cikin jeans da t shirt Maroon colour,rigar ta fito da surar jikinshi saboda ta ɗanyi tighting ɗinshi,Ƙafarshi na sanye cikin Canvas sneakers,
fitowa yayi daga part ɗinsa,Ya nufi downatairs,a natse yake taka staircase din har ya sauko down,Su jahad na zaune ita da hosana saman Sofa mai mazaunin mutun uku,suka jiyo takun takalmanshi,

ɗagowa sukayi atare suna kallonshi,lokacin da ya ƙaraso wurinsu,da sauri suka haɗa baki wurin gaisar dashi,
Batare daya kallesu ba,Ya amsa masu gaisuwarta su,fuce wa yayi daga cikin main palour ɗin,Kaitsaye Motarshi ya nufa,Amstrong na ganin shi da sauri ya ƙarasa tare da buɗe mashi motar ya shiga daga ciki,sannan shima ya bude driver seat ya zauna,
Kafin ya tashi motar,ya ɗan dago tare da kallonshi ta cikon mirror yace”Sir,Where are we going”?
“Restaurant,”ya bashi amsa atakaice,
Shiru amstrong yayi batare daya tashi motar ba,Hakan yasa shi cewa”what are u waiting for”?
Cikin harshen turanci amstrong yace”Sir,kayi haƙuri da abunda zance,Amma zuwa restaurant ba naka bane,da matsayinka aganka a restaurant ka je cin abinci?kaida ya kamata ace a gida ake girka maka,idan ba damuwa zanje nakawo maka,ka koma ciki pls”
Tunda ya soma magana sgr yayi shiru yana sauraronshi,saboda amstrong yana ɗaya daga cikin waɗanda suke Control dinshi,”
Amsa mashi yayi da okey,sannan ya buɗe motar ya fuce,
Duk wannan abun dake faruwa sehrish na tsaye a wurin window tana leƙen motarshi,taga lokacin daya shiga cikin motar,kuma sai taga ya fito daga ciki,
Aranta tashiga tunanin ko lafiya,
Dawowa cikin gidan yayi,Part ɗinshi ya koma ya zauna saman sofa yana jiran dawowar Amstrong,dan bala’e ga abinci acikin gidan amma yafi ƙarfin yayi ma wani magana ya kawo mashi abincin,tunda ya ƙori mai aikin tashi,
Cikin minti goma sha biyar,Amstrong ya shigo cikin gidan hannunshi dauke da ledojin,Su jahad na ganinshi suka shiga gaisar dashi,fuskarshi ɗauke da murmushi ya amsa mashi,sannan ya wuce upstairs sashen sgr,
Yana barin wurin da gudu jahad ta nufi ɗakinsu,tura kopar tayi ta shiga ciki tana faman ƙwala ma sehrish kira,
tsaye ta same ta hannunta ruke da wayarta,ganin jahad ta faɗo ɗakin babu sallama yasa tace”Lafiya”?
Jahad tace”Yanzu naga wannan sojan wanda yake yin driving ɗin babban yayanmu,Hannunshi dauke da ledojin kuma na restaurant ne don naga sunan ajiki,”
Cike da mamaki sehrish tace”to fa!ko meyasa ya aika akawo mashi abinci bayan ga wanda aka girka agida”?
Jahad tace”Yanzu haka saboda abunda ya faru atsakaninku ne jiya,shiyasa yaƙi cin abincin gidan,”
Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,
“Yanzu haka,saboda yana ƙyamar girkina ne saboda ina yin period,shiyasa bazaici abincin gidan ba,”acewar sehrish,
Jahad tace”Amma ae bake kikayi girkin ba,Aunty azmee ce ta girka,Gaskiya nafi tunanin cewa wani abunne daban yasa bazaici abincin gidan nan ba,”
Murmushi sehrish ta ɗanyi tare da cewa”kinsan Allah babban yaya bazai iya cin abincin nan ba,Ina nan dake ƙarshe sai dai azubar da shi abanza”
Jahad tace”Mu zuba ido mu gani,zaici ko bazaici ba,”

***

Excuse sir!muryar amstrong ce ta dawo dashi daga zurfin tunanin da ya faɗa,
Muryarshi a kasalance yace mashi”Come in,”
Shiga ciki yayi tare da ajiye mashi asaman table dinshi,Sannan ya sara mashi,kafin ya fuce daga ɗakin,

Kusan minti 5 bai motsa ba,kamar ba yunwa yake ji ba,Hannu yasa tare da curo bugger daga ciki,yana ƙokarin kaita a bakinshi ,Ya tuna da jinin daya gani ajikin wandon sehrish,aikuwa nan take Ya sake ta ta faɗi saman table din,Wani irin yunƙurin amai ne ya taso mashi,da sauri ya miƙe ya nufi cikin toilet,ya shiga kwara amai agaban basin,Ba ƙaramin galabaita yayi ba,ƙyanƘyami ya hana yaci abincin ga yunwa na cinshi,har zazza6i ya fara kamashi,
Tap ya kunna ruwa ya shiga kwararowa,tarba hannayenshi yayi ya shiga kuskure bakinsa,kafin ya wanke face ɗinshi,
Fitowa yayi daga cikin toilet,yana faman sauke ajiyar zuciya,komawa yayi saman gadonshi ya kwanta,wasa wasa Zazza6i ya rufe shi,temperature ɗin jikinshi yayi zafi sosai,

Kasa samun natsuwa sehrish tayi,tunda taga an kira sallar magrib da isha’e,sgr bai fito daga part ɗinsa ba,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankalinta yayi ba,jiki na rawa ta fito daga ɗakinsu ta wuce kitchen,Anan ta samu azmee tana ƙarasa gyara kitchen din ita da hosana,
Ganinta yasa azmee tace”Ya jikin naki”?
“Da sauƙi aunty azmee,sai dai….”shiru ta ɗanyi bata ƙarasa maganar ba,
Tunkarota azmee tayi tare da ruƙo hannunta suka ja daga gefe sannan tashiga tambayarta meya faru,
“Aunty azmee,wani abu ya faru jiya tsakanina da babban yaya ban sanar maki ba,”
“Faɗamun meya faru,Allah yasa dae ba wani laifin kika aikata masa ba,”
Nan sehrish ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar mata,
“Ya salaam,’ azmee ta ambaci hakan hankalinta aɗan tashe tayi maganar,
“Wlh aunty azmee ba laifina bane,bana acikin hayyacina ne,shiyasa nayi mashi rashin kunya,”
Muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Cigaba da magana tayi”Ni babban abunda yafi tayar mun da hankali,har aka kammala sallar magrib da isha’e,banga ya fito daga cikin part dinshi ba,kuma inajin tsoran in tunkare shi,saboda nasan dole ya hukunta ni,kuma nayi shawara da aunty azeema tace kada na kuskura naje bashi haƙuri,haka jahad ma tace mun,”
“Sehrish idan kikace zaki ɗauki shawarar Azeema,zata kaiki ta baroki ne,saboda ita wata irin wayayyiyar maca ce,Bazan hana ki ɗauki shawararta ba,amma inaso ki tuna matsayinshi a wurinki,Yayanki ne shi kuma Mijinki,jiya ya kwana da fushinki acikin zuciyarshi haka yauma ya tashi da fushinki,tabbas zaki jefa kanki cikin matsala ne,in har bakiyi hanzarin neman afuwarsa ba,Yakamata kije ki bashi haƙuri,kuma ki sanar dashi cewa ba a hayyacinki kike ba!”
. “yanzu aunty azmee kina nufin inje in bashi haƙuri”?
“Eh,haka nake nufi,”
“Amma fa yace mun kada na kuskura na ƙara zuwa part ɗinshi har saina kammala period ɗina,”
“Kada ki damu da wannan kije kawai,in sha Allah babu abunda zai faru,”
Tashin hankalin da ba’a sama shi date,Shin shawarar wa kuke tunanin zatayi ma sehrish amfani?Shawarar Azeema da Jahad,ko kuwa shawarar Aunty Azmee…

ALSO READ >> SAKONNIN SOYAYYA MASU MATUKAR DADI

Back to top button