Halysaah Page 174 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH II…A hankali Khaleesat ta bude idanuwanta tana bin inda take kwance da kallo, Aunty Farida ta gani zaune gefenta da swollen eyes, ta mike zaune da kyar don kanta yayi mata wani irin nauyi, Aunty Farida sai kallonta take ta kasa cewa komai, tun jiya take kwance bata san inda kanta yake ba, Khaleesat was trying so hard to remember what happened don gani take kamar irin mafarkin da ta taɓa yi kwanaki ne ta kara yi yanxu, Aunty Farida tayi karfin halin mikewa zata tafi ta kira mata likitan dake dubata don likitan na parlor, Khaleesat ta rikota da sauri muryarta ko fitowa bai yi tace “Aunty i had a bad dream? Ya Junaid ya dawo ne?” Aunty Farida ta sauke idonta ta kasa bata amsa sai hawaye, lokaci daya Khaleesat ta gigice ta fara tunanin to ko dai duk mafarkin da tayi suma suka yi ne yau, kokarin sauka ta fara yi daga kan gadon a rikice tana cewa “Aunty wallahi bai mutu ba, don Allah a daina tunanin ya mutu, kwana biyu kawai yace min zai yi fa” Aunty Farida dai taki barinta ta sauka daga kan gadon, Hajiya A’isha ce ta leko dakin jin muryar Khaleesat, tana ganin ta farka ta sanar ma likitoci biyu dake Main parlor, likitocin na shigowa dakin Aunty Farida ta kasa ci gaba da tsayuwa kawai ta fita ta bar su hawaye na zuba idonta ta tafi dakin da su Umma da Nenne suke ta sanar masu Khaleesat ta farka, su Kilishi da Hajiya Sumayya da Mami duk suna zaune parlon cikin sanyin jiki babu me cewa komai, kowa da tunanin da yake a rai, duk da gidan cike yake da jama’a amma su dai a parlon suke zama saboda Khaleesat, Mami na son tashi ta tafi dakin jin yanda Khaleesat ke kuka amma ta kasa, sauran ma dai duk suka kasa shiga dakin, daga karshe Mami tayi karfin halin mikewa ta tafi dakin cikin dakiyar zuciya, tana ido hudu da Khaleesat hawayenta suka yi betraying dinta suka dinga zubo mata duk da yanda ta so daurewa kar tayi hakan, Khaleesat na ganinta ta fara kokarin sauka daga kan gadon duk da rashin karfin jikinta cause she look so weak, likitan taki barin ta sauka, hakan yasa Mami ta daure ta karasa cikin dakin ta zauna kusa da ita ta dafata tana kallonta amma ta kasa cewa komai, Khaleesat ta kwanta jikinta cikin rashin kuzari tace “Mami ce min yayi kwana biyu kawai zai yi, me yasa za su dinga cewa ya mutu, saboda basa sonsa sai su dinga kira masa mutuwa, don Allah ina son inyi magana da Ya Jawwad Mami, nasan shi bazai ce min ya mutu ba” Mami ta kasa ce mata komai hawaye na zuba idonta, a hankali Khaleesat ta rufe idonta ta sauke ajiyar zuciya, Mami tayi saurin riketa ganin ta sake jikinta gaba daya, likitar dake tsaye duk a sanyaye ta ajiye alluran da take kokarin hadawa da sauri ta tafi kusa da su to check on her, nan taga suma ta sake yi, duk dubarun da likitocin suka yi amfani da shi wajen kokarin ganin sun kara reviving dinta bai yiwu ba, don dogon suma ta sake yi, Kuka sosai Mami ke yi tana kallon likitocin cikin tashin hankali tace “Amma Dr cikin jikinta bazai samu matsala ba dai ko? don Allah ku taimaka, we need to protect the pregnancy by all means, Kar cikin nan ya samu matsala don Allah” Likitan ya sauke ajiyar zuciya bayan ya maida Khaleesat ya kwantar da ita yace “In sha Allah babu abinda zai samu cikin ranki shi dade, we are trying our best, shi yasa ake ta mata ƙarin ruwa da allurai” Mami ta dinga goge hawayen da suka ki tsaya mata tana kallon Khaleesat…. Kwanaki biyun da suka wuce a masarauta kwanaki ne da baza su taɓa mance da shi ba a tarihi, kwanaki ne da aka yi su cikin rudani da koke koke da tashin hankali na gaske, waye zai ce abu zai samu Junaid har su damu su shiga tashin hankali me tsanani haka, it was something they never saw coming, shi yasa hakan ya dakesu sosai, ita kanta Aunty kukan gaske take, ta kuma shiga damuwa sosai, bata taɓa tunanin zata ji haka watarana akan Junaid ba, ta dai san tayi attempting kashesa tun yana karami da tasa ayi poisoning dinsa amma daga baya bata sake yunkurin kashesa ba duk asirce asircen da take yi masa babu na kisa a ciki kawai title dinsa na Yarima take yi ma, ko babu komai Junaid a gabanta ya tashi 30 years ago ko da bata kula da shi ba tayi masa rikon tsakani da Allah komai nasa kusan a bangarenta yake sai ko in baya nan yaje gidan Hajja, har zuwa sanda ya girma sannan ya zama independent a nasa part din, bata taɓa tunanin abinda Walid zai aikata ba kenan, abinda ta saka shi daban abinda yaje yayi daban, gashi ko kwarzane basu yi ma Jay din ba, halin da taga Sarki ya shiga ma ya karyar mata da zuciya sosai ba kadan ba, sai a yanxu kowa ya fahimci yana son ɗan sa, so ba kadan ba, kawai yana kauda kai ne akan abubuwa da yawa da ake masa a gidan, rabonta da ganinsa cikin wannan yanayin tun rasuwan mahaifin Jawwad, sai dai a sannan ai har da shi ake karban gaisuwa yana kuma zama cikin mutane sannan bai yi hawaye ba sai dai na zuci sannan yayi composing kansa da ake zaman makoki, but reverse was the case now, don kwata kwata ba a ganinsa, likitansa kawai ya amince ma ya shiga inda yake, masarauta ya dawo so silent…. Kilishi ta mike da hijab dinta har kasa ta fita daga parlor don zuwa sanar ma Hajja Khaleesat ta farka duk da ita ma Hajjan tana can kwance babu lafiya, Ummi na zaune gefen gadon Hajja tayi tagumi tana kallon uwar tata, kana ganinta kasan tana cikin tashin hankali ba kadan ba kuma ta ci kuka har ta gode Allah don idanuwanta har sun kumbura, tun jiya Hajja ke Kwance ko sanin wanda ke kanta bata yi ba, sai daxun nan ta dawo hayyacinta amma kwata kwata jikin ba dadi don ko tashi bata iya yi, tana farkawa daxu duk da halin da take ciki Khaleesat ta fara bude baki ta tambaya tana cewa a kula kar wani abu ya samu cikin jikinta, bayan nan likitoci suka mata alluran bacci shi ne take ta bacci har yanxu, Ummi ta goge hawayen da ya zubo idonta wishing they were all dreaming, Hadiyah ma na zaune dakin ita ma ta ci kuka har ta gode Allah, Kilishi na shigowa dakin da sallama tayi kasa da murya ganin Hajja tana bacci tace “Dama zuwa nayi in sanar mata Halysaah ta farka yanxu ko zata samu nutsuwa idan taji haka” Ummi ta kalleta tace “Ta farka?” Kilishi tace “Yanxun nan ta farfado” Ummi ta mike tana kallon Hadiyah cikin sanyin murya tace “Ki zauna ki dinga duba Hajja kan in dawo” Kai kawai Hadiyah ta gyada mata, Ummi ta bi Kilishi suka fita daga dakin ta jawo kofar ta kulle…. Jay na zaune kan gadon Mami ya tsura ma AC din dakin ido babu ko kiftawa, Mami ta shigo dakin ta karasa har edge din gadon ta zauna tana kallonsa a sanyaye, bata yi tunanin zata shigo ta samesa haka ba bayan alluran baccin da aka yi masa ko minti talatin ba ayi ba, after a while ta kauda kanta saboda hawayen da suka kawo idonta, ya juya ya kalleta, ita dai bata iya ta kara kallonsa ba, tun jiya ake masa alluran bacci amma sai dai ka samesa zaune kan gado ba um, ba um um, sallah ne kawai yake ɗagasa daga kan gadon, Idonsa kawai zaka kalla kasan he is more than traumatized, A hankali ya dora goshinsa kan shoulder dinta, taji hawayensa masu zafi na zuba jikinta, rungumesa tayi tana patting bayansa ita ma hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa na rawa yace “Mami… Junaid can’t go just like that, he was full of life, Mami don Allah a tasheni a mafarkin nan” Mami dai ta kasa ce masa komai hawaye na zuba idonta sosai, tun daga jiya zuwa yau iya maganar da yake ta yi kenan repeatedly tun bayan da yayi gaining consciousness, after a while Mami tayi karfin halin cewa “Kayi istigifari Jawwad, duk wanda kaga ya tafi lokacinsa ne yayi, No one can change that” Ya rungume Mami sosai muryarsa na rawa hawaye masu zafi na zuba idonsa yace “Noo Mami, we had so many unfulfilled missions, he even told me his wife is carrying twins, me yasa zai tafi bai ga yaransa ba….” Mami sai cewa take yayi istigifari, kawai ya kife kansa da pillow wishing he will have a last chance with his brother, the chance he won’t ever misuse, abubuwan da suka faru watannin baya da yanda Junaid ya dinga bin sa yana ignoring dinsa ne suka dinga dawo masa, ji yayi kamar zai zauce, Mami ta mike kawai ta fita daga dakin ta dawo parlonta ta fashe da matsanancin kuka tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” rabonta da shiga halin nan da take ciki tun rasuwan mai gidanta, bata taɓa tunanin akwai wani abu da zai kara girgizata haka ba a rayuwarta bayan mutuwar mijinta, ko Jay ta rasa tasan iya abinda zata ji kenan, sai yanxu tasan ashe tana jin Junaid a ranta…. Duk wani rudani da alhinin da ake ciki a masarauta Walid na can asibiti kwance, babu wanda zai kallesa yace bai yi accident ba da gaske don duk jikinsa rauni ne, dai daikun mutane ne ke zuwa dubasa daga masarauta, da daddare sosai Aunty ta je dubasa, tun da ta shiga ward din take dube duben ko akwai Cctv Camera, ai ko ta hango Camera din, ta kalli Walid tayi kasa da murya tace “Kayi dubara ka shiga bandaki ka jirani Walid” Walid ya nuna mata kwankwason sa da kyar yace “Bazan iya tashi ba ai” Aunty ta kalli Wheel chair dake dakin ta matso da shi kusa da gadon, ya cire drip din hannunsa sannan yayi dubaran komawa kan Wheel chair din ya zauna da kyar, Aunty ta tura Wheel chair din zuwa bandakin dake ward din sannan ta kulle kofar tana kallonsa cikin tashin hankali tace “Walid haka muka yi da kai dama? Walid yace “Babu abinda Jay yayi min da zan kashesa, na dai sa an kashe wanda yayi min” Aunty ta fashe da kuka sosai tace “To gashi ai kana neman kashe uban ka, don tunda nake ban taɓa ganin Mai martaba cikin wannan halin da yake ciki ba wallahi” Walid ya kalleta da sauri yace “Da gaske Mumy?” Tana kuka tace “Ni dai ban ce ka kashe Junaid ba, wallahi ban aike ka ba, abinda muka tsara da kai daban abinda ka aikata daban, me ya maka da zaka saka a kashesa ga wanda Sarki ya nada Yarima ka bar sa yana numfashi a doron kasa?” Walid yace “Kece baki ga abinda yayi min ba, amma ni ai nasan abinda yayi min, sai me don an kashesa, dama menene amfanin rayuwarsa? Gwara ya bi uwarsa inda ta tafi, kina gani yanxu haka ciwon da nake ji a kwankwaso na ya dawo sabo fil, ko motsawan kirki ban iya yi, tun jiya ake ta scan ana saka ni cikin wasu injina” Cikin tashin hankali Aunty tace “Yanxu idan bincike yayi bincike aka gano kai kasa aka yi wannan aika aikan fa Walid?” Walid ya taɓe baki yace “Binkicen me za ayi bayan yan gari sun sheda dai nayi hatsari, yanxu haka ba gashi ko motsa kuguna ban iyawa ba, ai i am too smart to be caught Mom, a yanda komai ya tafi babu me zargina har abada, shi kuma ya mutu banza….” Aunty tace “Wai ta yaya ma ka tsara hatsarin nan har kaji raunuka haka a jikin ka?” Er dariya yayi yace “Motar wani abokina na amsa a Lokoja, shi ne sai da na kutsa ta cikin jama’a na bubbuge teburansu na sana’a sannan na samu wani karfe na daka, a nan motar ta tsaya cak tana hayaki, yanxu haka motar duk tayi damage, da kyar aka ciro ni daga ciki, ina jin na kara fama wannan kwankwason nawa don ko bacci ban yi ba jiya” Aunty ta bude baki tana Kallonsa, tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, da ka kashe kanka garin haka fa Walid?” Yace “Ai accident din da ya faru babu shiri ne ake mutuwa, wannan ai shiryayye ne, dama kafin inyi accident din na ba su Gwaska Passport dina da wayata da zumar sun sace a scene din accident din, na kuma nuna masu number Jawwad da za su kira, dama nasan wawan bazai yarda Jawwad ya taho shi kadai ba sai ya biyosa shi yasa nayi using opportunity din….” Aunty ta kalli kofar bandakin da sauri jin an bude door din ward din, sai kuma ta bude kofar toilet din tayi maza ta tura Walid a Wheel chair suka fita zuwa dakin asibitin, Walid ya ɗan yi murmushi at least he is now the only son of the king, idan ma ba a basa sarauta ba shi ne dai next of kin din Mai martaba daga yanxu….” Hajiya Shafa’atu na zaune ita kadai parlon Mami tayi tagumi, ko zama cikin jama’a bata son yi saboda damuwa, ga hawayen da yaki tsaya mata, tunda ta sauka Masarauta daga Canada take isolating kanta a gefe, sosai abinda ya faru da Ajay ya girgiza ta, ta daga kai jin an bude kofar parlor, Mukhtar ne ya shigo parlon shima duk ya fada saboda zirga zirga da tashin hankali, ganinta ya zauna kasa ya gaisheta, ta amsa cikin sanyin murya tace “Lafiya lau Muktar, ya karin hakuri?” Mukhtar ya sauke ajiyar zuciya yace “Mun gode Allah Mama” Hajiya Shafa’atu tace “And his body is still yet to be found har yanxu kenan Mukhtar?” Mukhtar ya girgiza kai a hankali yace “Har yanxu shiru Mama, nasan wannan ne ma ya tsaya ma Mai martaba ya kara destabilizing dinsa, assuming his lifeless body was seen an san truly ya rasu babu wani sauran magana sai dai kowa ya dau dangana, to amma rashin ganinsa yasa kowa cikin rudani… daga baya aka fara zargin anya ba ruwan suka jefasa ba, tun kwanaki biyu da suka wuce gwamnatin lokoja tayi assigning professional responders su yi organizing search and rescue mission, to har yanzu babu wani feedback” Hajiya Shafa’atu tace “Amma in ruwan suka jefasa zuwa yanxu ai yaci an gansa at the bank of the river Mukhtar” Mukhtar yace “kin san ruwa ne babba connecting different states” Cike da damuwa Hajiya Shafa’atu tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Allah mun gode maka, Alhamdulillah ala kulli halin” Tissue din hannunta ta fara goge hawayen da suka fara zuba idonta da shi tace “Har yanxu bazan iya shiga in ga Mai martaba ba Mukhtar?” Mukhtar ya sauke idonsa yace “Nima rabona da shi tun jiya Mama, He said he wants to be alone, likitansa ne kawai ke shiga dakin nasa” Hajiya Shafa’atu ta girgiza kai tace “Amma na rasa me yasa jikina ke bani Junaid bai rasu ba, wallahi zuciyata taki yarda da cewa he is dead har yanxu…..” Mukhtar ya kalleta yace “A kirji fa suka harbesa Mama” Hajiya Shafa’atu ta girgiza kai tace “To amma dai zuciyata taki amince min ne, ko don ba a ga gawarsa bane ban sani ba, i am still not convinced Junaid is no more” Mukhtar bai sake cewa komai ba, Hajiya Shafa’atu tace “Kuma har yanxu babu labarin wa enda suka aikata wannan abun?” Mukhtar yace “Babu gaskiya ana dai ta bincike, sai dai Walid shi ne suspect number one na hukuma tunda da wayarsa aka kira Jawwad har suka kama hanyar lokoja, although jami’an tsaro basu gaya ma Mai martaba Walid suspect dinsu bane kawai suna aikinsu ne, don da kaina na basu phone number din Walid suna wani bincike duk da yace masu an sace wayar a scene din da yayi accident, but they still requested for his phone number from me, to daxu kuma ake sanar min babu wani call that is suspicious da line din nasa, bai kira baƙon number ba da wayar a ranan, duk kiran da aka duba kuma normal call ne da family members, shi ne suke tambayar ko yana da wani layi daban nace da wannan kawai muka san shi baya amfani da layi biyu” Hajiya Shafa’atu ta ci gaba da goge hawayen da suka ki tsaya mata da tissue din hannunta……
Visit Kundin Hausa Novel For More Novel



