Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 7 Hausa Novel

Wasu gungun matasa ne ɗauke da makamai suna ƙoƙarin Hankaɗa hamdiyya su rufta mata ai da wani irin hanzari ta mayar da kofar ta rufe jikinta na wani irin ɗaukar tsuma, hankalinta sai ta ji yayi wani irin tashi tsoro da fargaba suka rufe ta, ko kafafunta ta kasa motsa su daga inda take tsaye… Ƙuuuuu haka cikinta yayi wani irin ƙara a sadda ta ji kukan uncle haɗi da maganarshi daga bakin kofan “Ki buɗe ki ba ni yarana…! Kin riga kin cuce ni kin raba ni da uwarsu rabuwa ta har Abada a yanzu ba zan iya sake ɗaukar raba ni da su ba, in kuma su ma kin cinye kurwarsu ne kaman uwarsu nima duk ki haɗa da ni ki cinye Afeefah…”Sossai yake gunji daga jin muryarshi zaka san baya cikin hayyacinshi ne.Tsurewa ta yi tana jin kaman ta zauce ko kunnuwanta ba sa ji da kyau. Tamkar sauƙar aradu ta ji wani da kaman yanzu ya iso a gigice yana furta “Da gaske ne Usman Zainabu ta rasu?”‘Zainabu ta rasu!’Ko kan kalaman su gama shiga kwakwalwanta sai ji tayi uncle na amsawa “Zainabu ta tafi ta bar ni. Sai da aka gargaɗe ni amma na ƙi saurara saboda ta ba ni yaƙini a kan yarinyar, ashe ba haka ba ne kai duniya…! Ashe wanda ya maka rana za ka iya masa dare? Afeefah ta yi mana shigo shigo ba zurfi, lafiya ƙalau muka kwanta da zainabu daga ciwon ciki farar ɗaya muna zuwa asibiti sai ga kiran hamdiyya take sanar min ta yi mummunar mafarki a kan zainabu, sai na sanar mata muna asibiti bata da lafiya ta tsorata tace gata nan zuwa Dukda dare ne haka ta bi gidan wani malami ta taho da shi akan mafarkinta mai muni ne Afeefah ta gama cinye kayan cikin zainabu ashe da gaske ne! Duk irin taimakon da malamin nan ya so bata ya gaza haka likitoci suna gani ta ce ga garin ku…”Hamdiyya ta chafe cikin kuka”in ba aikin maita ba menene wannan? an riga an cinye mata kurwa, sai da na faɗa wlh sai da na gargadi Aunty akan mayyar yarinyar nan..”Gayyar mutane bayan waenda hamdiyyar ta zo da su suka sake cigaba da taruwa suna hayaniya akan tabbas ita ce mayyar ai dama daga Dutsen-wai ma gudu wa ta yi saboda yunkurin kashe ta da Ƴan uwan wadda ta kashe last suke kawai a kasheta.Ƙafafunta sai suka gaza ɗaukarta, ta zube yaraf a ƙasa, hawayen da suke zuba tuntuni sai suka ƙafe kamar rijiyar da aka yi wa yaso. Zuciyarta na raya mata cewa da gaske ita ɗin annoba ce, da gaske ita ɗin mayya ce. Tana ji jama’a na maimaita lafiya ƙalau ta kwanta ciwon ciki ya turniƙe ta cikin dare daga isa asibitin su sai mutuwa. Hujjar da suka kafa kenan suna ƙara tunzura shi wasu na ta faɗan abubuwan da ita karan kanta da ake yi wa ƙagen bata san yaushe aka yi ba, ina ma da bata biyo Aunty zee ba? Ina ma da bata zo ba! Ina ma da bata biyo ta ba! Da gudu ta miƙe tana komawa cikin ɗaki gunjin wahalallen kukan da ta fashe da shi haɗe da ƙara na bala’i na cika ilahirin gidan ba wai don gudun rayuwarta da mijin antinta ke ta iƙirarin ita ma sai an kasheta ta bi matarsa ba sai don rungumar mutuwar a karan kanta, tana so a yau ta kawo karshen komai tana so tayi mai gabaɗaya da rayuwarta wai haihuwa da hanji… bayi ta shige kai tsaye babu wani tunani ko shawara ta zaro piya-piya da su ke ajiyewa saboda sauro ta buɗe tare da kafa bakinta a kai tana kuka me tsanani da dugunzuma zuciya, ƙwatt! ƙwatt!! ƙwatt!!! haka maƙogoronta ke ba da sauti a sadda ta ke haɗiyewa tana jin ta yi sallama da rayuwa kaman yadda mamanta, babanta, kakar ta, innarta da ma Aunty zee suka yi. Lallai an yi mata mummunan zato da ba za ta taɓa wankuwa ba a duniya, ta gaza! Ta kasa rayuwa kaman kowa, a yanzu wa zai dauke ta kuma? Wa zai yarda wani nasa ya aure ta ko ya raɓe ta? Mutuwa ita ce abu mafi sauƙi a gare ta kaman yadda ta yankewa kanta.Kururuwa da take ji a nesa bai sa ta sauƙe kwalbar fiya-fiyan ba sai da ta ji an yi wani irin wurgi da kwalbar ya tafi ƙasa yana tarwatsewa kwatankwacin yadda rayuwarta ta tarwatse. Dishi Dishi take gani jiri ya diɓeta sai taji an tare ta sun tafi a tare suuuuu ƙasa.***A kafa su ke takawa sanye cikin uniform kasancewar assignment da aka ba su a cikin Anchau sun gama shi kuma a lokacin ne suke shirin barin garin zuwa cikin Kaduna, Zaratan matasa ne biyu sanye da khakin Sojoji daga yanayin tafiya da tsarin zubin halittarsu zai tabbatar maka da waennan ɗin ko a cikin Sojoji zaƙaƙuran ne, da wani irin ginshira suke tafiyan kowannensu na da kalar nashi kyaun, haiba da tarin kwarjini abin da ya bambamta uniform ɗin nasu abu ɗaya ne, shi wadda ya fi cin maganin fuskan nan tamau daga damtsen hannunshi akwai wani farin bandage da aka zagaye ƙarshen uniform ɗin dashi a jiki akwai zanen plus ➕ Da jan tawada wadda zai tabbatar maka da wannan ɗin Medical soldier ne.”Ko wanchan taron na me?”Na gefen da bai kai haske da wani irin ƙasaitar wanchan ɗin ba ya faɗa cikin natsuwa.A sace ya ɗan kalli wurin ya watsar kaman ba zai yi magana ba cikin halinshi na i don’t care ya furta “How would I know Saleem after all tare mu ke da kai?”Wadda aka ƙira da Saleem ya sake kallon taron a lokacin da suka tunkaro su sossai “Ko ma menene Rayyan ba na tunanin lafiya…”Ko ya tanka sai ma kanshi da ya mayar ƙasa yana ci gaba da takunshi cikin ƙasaita da isa kaman yadda yake a halittarsa.Ihu da ƙarar da ya ratsa kunnuwansu haɗe da furta kalaman”sai mun kasheta yau za mu ga karshen maita”Da jama’ar wurin suke ta furta wa wasu ma ɗauke da makamai ya sa Saleem taka birki yana riƙo hannun Rayyan da yayi kaman bai ji ba.”Guy akwai matsala, we cannot neglet our duty ba za mu ga ana shirin ɓarna mu kama hanya mu wuce ba”Ko ya tanka sai birkitattun idanunsa da ya kai wurin yana nazarin situation ɗin fuskar nan babu walwala ko na miskala zarratin.Bai yi magana ba har Saleem ya isa ga mutanen, yana tsaye daga gefe da farko jama’ar sun so yin gardama amma jin ya kira akan a turo squad kuma ya zaro bindiga ya sa aka fara watsewa uncle da hamdiyya dai sai kuka da Allah ya isa suke yi, a mayar da maganan da ake ne ya ji abin da ke faruwa.”Wait here!”Ya faɗawa Saleem kan ya haye katangar gidan da ba shi da wani tsawo chan chan, bai buɗe kofan ba sai yayi cikin gidan yana dube dube, motsi da Sheshekar da ya ji ne ya saka shi kai kyawawan idanunshi wurin sai suka sauƙa kan kwalbar fiya-fiya a take warin ya shige cikin hancin shi da wani kalar hanzari ya fusgo madarar ruwa da ya gani nan cikin ɗakin Auntyn kasancewar ta mai jego ya fasa guda biyu ya isa gabanta ya sanya hannu yayi wani irin wurgi da kwalbar ya haɗe da gini ya tarwatse… Sulalewa take ƙoƙarin yi a lokacin da ya ɗago madarar yana shirin bata, bashi da zaɓin da ya wuce ya sanya hannunshi ɗaya ya tareta suka kai ƙasa ita tana ƙoƙarin sumewa shi kuwa ya sauƙa a kan gwiwowinshi, kanta ya ɗago da take ta kokawar numfashi ya kafa madarar tare da matse hancinta sai da ta kwankwadi mai yawan gaske kan ta sake yunkurowa tayi gaba wani kalar amai na kwace mata, tana gamawa ya sake dura mata ɗayar ta sake kwarara wani aman ko idanunta bata iya buɗewa alamu sun nuna ta jima da ficewa hayyacinta haka ya sanya hannu ya ɗauko ta zuwa waje, Fitowar shi da isowar motar Sojoji lokaci guda sai ciki aka sanya ta ya shiga tare da barin Saleem wurin suka fice a guje kaman yadda suka saba.Da gudu Uncle da hamdiyya suka shiga suka ɗauko yaran da ke ta kuka suna rurrungumesu a lokaci ɗaya suna ta tsinewa Afeefah, Saleem dake tsaye ya iso gangar uncle ɗin “A komai ya kamata ku dinga adalci da tunani, ƙage ko sharri ba abu bane mai kyau shin kun taɓa jin maita ko a addini? Ko kun taɓa ganinta ta yi maitar?””Wallahi billahi na rantse da Allah idona idon Afeefah sai na sa an kasheta gwara ku gaya mata tun daga inda ta tafi ta san inda dare ya mata, sam Shigowar ta rayuwarmu bai mana rana ba”Hamdiyya ta karɓi zancen “ba kai kaɗai ba ai gwara mata mutuwar ta da dawowa unguwar nan tsinanniya”Juyawa kawai Saleem yayi ya bar gidan suna ta zaginta da kwashe mata albarka wasu mata na shigowa ana ta kokarin mayar da magana ai dama an gargadesu.BAYAN WASU AWANNIA hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da suka matuƙar yi mata nauyi tana jin yadda kanta yake wani sarawa, a tunanin ta za ta tsinci kanta cikin ƙabari ne kaman yadda ta jima da sallamar da rayuwarta wa mutuwa sai kuma ta ga akasin hakan. Idan ma tunanin ta ya bata daidai kaman nan ɗin ɗakin asibiti ne take ciki duba da yanayin tsarin ɗakin da kuma ƙarin ruwan da ke shiga jikinta ta canular dake ɗaure a hannunta. Tunanin dalilin mutuwar tata ne ya bijiro mata kaman ana haska mata majigin rayuwarta…”Aunty zee ta rasu” Daram! Haka zuciyarta ya buga zuruf ta miƙe zaune kaman ba jiri ne ke walagigi da rayuwarta ba, hannayenta ta sa duk biyu ta toshe dukka kunnuwanta don ji take kaman ana maimaita mata kalaman na rasuwar Aunty zee da speakern da ya fi komai ƙara a duniya. Tamkar zautacciya haka ta saki wani irin ƙara da ya shigo da nurses har uku ɗakin da gudu da ma an ba su aikin kula da ita kar ta farka ta sake yunkurin cutar da rayuwarta.Shigowar su da fara fusge-fusgenta kusan lokaci guda rirriƙeta suke kokarin yi amma kaman mai tashin aljannu sai wani irin ihu take mai tafe da gunjin kuka mai taɓa zuciyar mai saurare don kowa ya ji kukan ya san ba na wasa bane”Ku barni na mutu! Don Allah ku bar ni na mutu ba zan iya rayuwa ba! Ku sakeni….! Ku sake ni na ce!”Duk ta haukace kuma yawan su bai sa sun iya natsar da ita ba..”Will you shut up and stay still?? Giyar wake kika sha ne?? Hauka kike yi ne??”Kalaman suka fito cikin wani irin amo da ya amsa duka ɗakin…

Back to top button