Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 20 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na ashirin_

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

         _1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

           _2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

              _3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

        _4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

AKWAI BONANZA TA MUSAMMAN TA 24HRS
DAN SAMUN RANGWAMEN BIYAN 1K GA DUKA HUDUN💃💃💃💃💃💃💃
Daga yau 25 December zuwa gobe 26 December🔥🔥🔥🔥🔥

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

_Kuyi maza kada bonanza ta ƙare babu ku_🙈
_________________

………Cikin rawar hannu ta ɓalle murfin motar ta fita, hakan yay dai-dai da juyowar ƙanin nata da abokinsa ke nunama motar. Kallonta yake daga sama har ƙasa tamkar mai son tuna inda ya santa ko son gaskata ita ɗince ko gizo ne. Tana ɗaga ƙafa domin nufarsa kamar wanda aka zabura ya shige cikin gida da gudu yana ƙwala kiran “Mama! Mama!!…..” sai dai ya gagara cewa komai sai nuna ƙofa kawai yake yi yana hakki.
Kusan a tare Mama da ƙannen Khadijah biyu Zuhrah da Jamilah suka fito a ɗaki a rikice. Jamilah ce ta daka masa tsawa da faɗin, “Kai Kamal wane iya shegene haka shigoma mutane cikin gida da gudu babu ko sallama sai ihun kira, waye ya biyoka ne?”.
“Aunty Kha..di..jah a mota ƙofar gi.. gida. Wlhy da gaske nake, kuma kuzo ku gani”.
Kasa cewa komai sukai su duka, sai kallan kallo kawai, kai kace suma sukai a tsayen. Sai mamace tai ƙarfin halin faɗin, “Shashancinka yayi yawa Kamal.” ta ƙare maganar muryarta na rawa da ƙoƙarin juyawa zata koma. Dai-dai nan Khadijah ta shigo gidan. Cak mama ta sake komawa ta tsaya, su duka suka zubama Khadijah idanu jikinsu na ɗan rawa kamar yanda nata keyi itama. Da ƙyar ta iya jan ƙafarta zuwa inda suke, ƙasa ta zube gaban Mama ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tare da kama kunnuwanta duka biyu. Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, face zuba mata idanu da sukai kawai suna kallonta. Baka jin motsin komai a gidan face sautin kukan nata….

       Tunda ta shige gidan suma suka fito a motar. Sai dai Awwal ne kawai a waje shikam yana daga cikin mota ya dai buɗe murfin ne kafafunsa duk a waje. Magana Awwal ya jiyo da nufin masa sai ga Baba an sauke a napep tare da Ni’ima, da ga asibiti suke, ta raka baba amsar magani. Ni’ima na kama da Khadijah sosai, dan haka a kallo ɗaya suka gane ƴar uwarta ce. Baba da tun fitowarsa a napep ɗin ke kallon motar ta su da Awwal ya ƙara so garesu yana mai dogara sandarsa, dan yanzu baya iya tafiya sai da ita. Sallamar Baba ta saka su juyowa su duka garesa. Bayan sun gaishesa yake tambayarsu ko suna neman wani ne?.
Awwal ne ya amsa masa da faɗin “Eh Baba, muna neman mai gidan nan ne”.
Murmushi Baba yay da jin jina kansa. Cike da dattako ya ce, “Ni ne mai gidan yaro. ALLAH yasa dai lafiya ba laifi nayi ba”.
Murmushi shima Awwal yayi, sai dai kafin yace wani abu Yayansa da tun bayan gaisuwa bai sake magana ba ya ƙarɓama Baba da cewa, “A’a Baba bakayi laifin komai ba. Alkairi ne tafe damu.”
“To masha ALLAH. Bissmilla. K Ni’ima shiga ciki ki amso tabarma ko”.
Da to Ni’ima ta amsa masa bayan ta gaishesu. Sai dai tana nufar shiga gidan Yaya ya ce, “Baba bama sai ta amso tabarmar ba. Dan muna saurine”.
Idanu baba ya ɗan zuba masa, dan haka kawai yaron ya birgeshi saboda nutsuwarsa da cikar kamala. Kansa ya jinjina tare da dakatar da Ni’ima, sannan ya sake juyowa garesu yana nuna musu dakalin dake ƙofar gidan. Shi da Baba ne suka nufi dakalin, Awwal na daga tsaye jikin motar. Sai da ya sake gaida baba sannan ya ɗaura da faɗin, “Baba dama muna nemanka ne adalilin wata yarinya datai mana kwatancen gidan nan muka kawota. Mun taho da itane tun daga Adamawa……” tsaff ya kwashe komai ya sanarma Baba, tare da miƙa masa takarda ya ɗora da faɗin, “Wannan a jikinta ta faɗo da alama itama bata san da ita ba”.
A hankali Baba da jikinsa ke tsuma ya ɗago hannunsa ya amshi takardar. Sai kuma yay ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido da sakin murmushin ƙarfin hali ya ce, “Nagode yaro, ALLAH yay maka albarka. ALLAH ya kareka da sharrin duk wani abun ƙi. Ban san yanda zan misalta maka jin daɗina ba akan wannan taimako da kukai mata. Amma na maka alkawarin addu’a a gareku a kowace sallata. Zan so kuma ace kumu shiga ciki kusha koda ruwa ne”.
“Kayi haƙuri Baba mun gode sosai. Hakan ma ALLAH ya saka da alkairi. Zamubi jirgin ƙarfe bakwai ne zuwa Abuja shiyyasa. Amma in sha ALLAH na maka alƙawarin watarana zan shigo domin gaisheka.”
Godiya sosai Baba ya ƙara musu da sanya albarka. Sai da zasu shiga mota Awwal ya sauke wasu manyan ledoji yace a bama Khadijah…

     Bayan wucewar su Baba ya shigo gidan yara biye da shi da ledojin nan. Har yanzu Khadijah na zube a tsakar gidan tana kuka Jamilah da Kamal na taya ta. Yayinda Ni’ima da Zuhrah da suka kasance kamar sakonta suke tsaitsaye kawai ransu a ɓace. Dan sukam dai sunada wayonsu sosai a lokacin da Khadijah tabar gidan, sannan komai daya faru kafin ta gudun basu manta ba. Mama ko na zaune a yanzu kanta a ƙasa, dan tunda hajijiya ta nema zubar da ita Zuhrah ta taimaka mata ta zauna. Sallamar Baba ta saka Khadijah ɗagowa da sauri, idanu ta zuba masa. A take zuciyarta tai wata irin girgiza tamkar zata fito ta baki ganin yanda gaba ɗaya kamannin Baba suka sauya fiye da mama. Ya rame sosai yayi duhu ga shi yana jan ƙafarsa ga kuma sanda a hannu alamar itace ke taimaka masa a tafiyar. Shima dai kallon nata yake daga sama har ƙasa. Kusan mintuna biyu y kauda kansa batare da yace uffan ba ya nufi tabarmar da Ni’ima tai saurin shimfiɗa masa ya zauna.
Rarrafowa Khadijah tayi har zuwa inda yake tana kuka. “Baba ku yafemin, dan ALLAH na roƙeku ku yafe min. Nasan nayi kuskure babba na bijire muku nabi wanda kansa kawai ya sani. Baba nayi nadama, nayi dana sani, wlhy bazan ƙara ba baba….” kuka mai nauyi ya sake sarƙeta. Maimakon cewa wani abu daga baba sai kawai ya dubi Ni’ima ya ce, “Kubata abinci”. Da ga haka yaja buta da Jamilah ta kawo masa ya fara alwala dan an fara kiraye-kirayen sallar magrib…

      __________★

METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da’ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1….12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za’abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al’umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah

Phone number 07038708382/09069163665

____________★

    Kwana biyu cur Dafeeq na hotel abinsa hankali kwance a dalilin yarda da zuciyarsa kan Khadijah na gidan baba hakimi. Dama ya zare layinsa da yasan za’a iya samunsa da shi. Tsaf ya gama shirya yanda zai fara tafi da Kainaat tare da fara aiwatar da shirinsa kamar yanda yasan itama tana can ta gama shirya masa da batun jiran saki.
Tunda ya baro hotel ɗin murmushi ya gagara barin ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Bai wuce gida kai tsaye ba, sai da ya biya wani waje ya amshi saƙo kafin yay sayayyar kayan ƙwaɗayi. Ana sallar isha’i ya shigo anguwar mara yawan hayaniya, tsayawa yay shima yayi sallar sannan ya ƙarasa gida. Ganin motocinta uku a harabar gidan ya tabbatar masa tana gida, amma duk da haka sai da ya tambayi maigadi. Maigadi ya tabbatar masa da ai tumma daya bar gidan bata fita ko ina ba tana gida, sister ɗinta dai tazo ta kwana jiya ta wuce gida. Kai tsaye ya fahimci Nadwa ce, dan ta sanar masa sister ɗinta ce batare da tasan yasan alaƙarsu ba.
Cikin gidan ya nufa hannunsa ɗauke da ledojin tsarabar daya kwaso mata. Yana tura ƙofar ya shigo wani ƙamshi mai daɗi ya daki hancinsa ga sanyin ac. Shaƙa yay ya lumshe idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya sannan yay sallama. Da sauri Kainaat da ke zaune cikin kwalliya ta ɗaukar hankali kamar tasan da dawowar tasa ta ɗago. Kallon ido cikin ido sukaima juna, a mamakinsa sai yaga ta wani sakar masa lalataccen murmushi, sai kuma ta taso a hankali cikin takun isa da yauƙi na ƴan ƙwalisar mata a bazata ta rungumesa tana kai masa kisses a kumatunsa da saman lips ɗinsa. Sosai Dafeeq ya shiga ruɗani a wannan gaɓar, amma da yake shima shegen kansa ne sai ya dake abinsa domin ganin iyakar gudun ruwanta da son gane manufarta. Hannu biyu yakai bayanta shima ya rungumeta da ƙyau. A cikin kunnenta ya raɗa mata, “Ki yafe min amaryata. Gwuyawuna bisa ƙasa Hajjaju na”.
Makirin murmushi ta saki tana mai ɗagowa ta kashe masa ido ɗaya. Cike da kissa ta ce, “Ni ya kamata na baka haƙuri ai mijina, domin na fusataka da yawa har ka kai gamin yaji na kwanaki biyun amarcina. Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake ba Baby”.
“Ai ke baƙya laifi Gimbiya. Ni ne mai laifi dana tafi na barki, nayi hakanne kuma domin nesanta kaina da ke har sai kin huce. Ki yafe min abinda na aikata sharrin shaiɗanne, amma in sha ALLAH bazai sake faruwa ba, dan yanzu ke kaɗai ce mai Dafeeq babu wani shamaki a tsakaninmu na har abada”
(Zakaci ubanka ne) ta faɗa a zuciyarta. A zahiri kam saita sakar masa murmushi da kai yatsarta saman lips dinsa ta ce, “Shiiii!!! Karka sake cewa komai. Abinda ya faru ya riga ya wuce har abada, na kuma yafe maka mijina muje kai wanka kazo ga abinci na shirya maka…”
“Abinci fa? Sai kace wadda tasan da dawowa ta?” ya faɗa cikin tarar numfashinta. Sai da gabanta ya faɗi, amma sai tai azamar gyara yanayinta da faɗin, “Akoda yaushe cikin tsammanin dawowarka nake gareni ai, shiyyasa nake shirya abinci safe, rana, dare batare da jin gajiyawa ba Baby. Ba gashi an dace ba yau kuma ka dawo ka sameni a yanda nake fata”.
“Hakane! Ina godiya Gimbiyar mata”. Ya faɗa yana shafa fuskarta da sakin murmushi. Sai dai a zuciyarsa yana jin lallai akwai wata a ƙasa. Fakar idonta yay ya watsa mata harara, a ransa ya ce, (Tsuntsu mai wayo, ta baki ake kamashi hajjaju). Shima kuma yana juya baya ta zabga masa hararar a zuciyarta tace, (Yaro yaro ne, yaro bai san wuta ba sai ya taka. Ƙiris ya rage na shafe tarihinka a nawa)

     😂😂Cuta ta ɗau cuta kenan🚴🚴🚴🚴🚴.

     _________★

         Kwanaki biyu kenan da dawowar Khadijah gida. Har yanzu daga Baba har mama babu wanda yace da ita komai. Hakama ƙannenta idan ka cire Kamal dake ƙarami babu mai shiga sabgarta. Garama Jamilah takan ɗan mata magana. Amma Ni’ima da Zuhrah ko kallo bata ishesu ba. Akan bata abinci wadatacce da zataci ta ƙoshi, idan ta gaida Baba kuma yakan amsa sau ɗaya ya tsuke bakinsa. Hakama Mama idan ta amsa sau ɗayan nan bata sake kulata. Idan su Zuhrah na aiki kuma ta taso ta ce zata tayasu suce ta barshi. Tayi kuka tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Dan da wannan shirun da suke mata gara ace dukan da yafi wanda Dafeeq ya mata Baba ya kamata yay mata zaifi mata sauƙi. Kuma data fara magiyar roƙonsu su yafe mata sai baba ya ɗaga mata hannu kawai alamar baya son ji. Mama kam ma tashi take tabar wajen batare data tanka mata ba. Gaba ɗaya duniyar ta mata zafi, ta rasa ina zata kama taji daɗi. A wajen Kamal take ji Baba baida lafiya yana fama da paralysis ne. Amma yanzu yaji sauƙi tunda har yana iya ɗan fita ƙofar gida. A wajensa taji an sakama Ni’ima da Zuhrah biki nanda wata bakwai ma za’ayi, sannan a gabanta suke fita makaranta tsaff da su. Tasan ta cuci kanta bana wasa ba, dan duk wanda ya kalla ƙannen nata a yanzu yasan ilimi ya ratsasu addini da boko.
Shigowar wata makwafciyarsu a randa take cika kwanaki biyu yasa aka san da dawowarta. Tana fita kuwa ta fara bazama ƴan anguwa cewar ai Khadijah na nan ta dawo a mawuyacin hali. Da alama ma cikin farkunan nata na bariki wani yay mata duka dan jikinta duk bandage ne. Abu kamar wasa sai ga zance ya cigaba da zagayawa, har takai wasu sun kasa danne gulmarsu suna shigowa ganin Khadijah afakaice. Bata fahimci zaryar da mutane keyi gidan dominta bane sai da Kamal yazo yana bada labari wai yaji a majalissar ƙofar shagon Kalu Nigge ana gulmar Khadijahn. Ranar taci kuka sosai, sai dai abinda bata sani ba har su Ni’ima ma sunsha kuka a ɓoye. Dan duk da ta kasance mai laifi a garesu basa jin daɗin yanda ake aibantata a anguwa tunda suma komai na dawo musu a cikin kunne. Kawai dai maganarce basayi su.
A randa take cika sati guda a gida sai ga mahaifiyar Dafeeq tamkar an jehota……✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 21 By Billyn Abdull Complete Novel

METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da’ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained.
METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba.
Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah
Yana da matakai 1….12
Level 1 anafarawa da 5$
Level 2 anadarawa da 10$
Level 3 anafarawa da 20$
Hakadai har zuwa level 12
Alkhairan metaforce
Kingama register za’abaki TR coins na adadin level din da kika bude
Samun reffaral bonus
Ga garabasar spillover
Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake
Babu faduwa Babu asara aciki
Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al’umma.
Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah

Phone number 07038708382/09069163665

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button