Uncategorized

Macijine Shi Page 39-40 Hausa Novel

 

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book  

Page 39/40

________________Wani irin amaine ya tasowa fattu,dan haka da gudu ta mike tana mai riƙe baki,sannan ta nufi toilet.saidai taku ɗaya -biyu tayi kiri ya kwasheta,baya tayi luuuuu!!!zata faɗi.da sauri ta runtse idonta tana mai saki wani ɗan siririn ihu,gaba daya ta gama saddaƙarda cewa ta fadi ,jira kawai take taji ta ina zata fara jin raɗaɗin.saidai maimakon tajita aƙasa,sai taji ta faɗa jikin mutum,wani irin ƙamshine ya ziyarci hancinta mai daɗin gaske,da sauri ta buɗe idanunta dan ganin jikinwa ta faɗa.

ido hudu sukayi da Hammanta, dan shigowarsa kenan dakin ya hangota zata faɗi ,shine yayi saurin tarota, dama yana sauka afadar ko gurin mai martaba baijeba yayi sashin ammi,duk kuwa da cewar maimartaban yana ta kiransa awaya akan ya dawo gida .

Dan kumshe ido fattu tayi cikin azabar  ciwon da mararta keyi ,sannan ta buɗe idonta ,tare da saukesu akan Hammanta,so take ta gasgata shiɗin ne ko gizo idonta keyi.

Aikuwa shine wllh Hammanta ne ya dawo,cikin azama kuwa fattu ta rungume Adeeb tare da sakin kuka,dama kuma kukan take.

” Hamma ina katafi ka barni?inata nemanka amma banganka ba?dan Allah Hamma karka ƙara tafiya ka barni,kaga bani da lafiya cikinsu ciwo yake min sosai” fattu ta faɗa tana mai cusa kanta aƙirjin Adeeb .

Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa tare da rungume fattu shima tsan-tsam ajikinsa,dan kuwa tabbas ba karya yayi kewar fattu sosai ,kullum da ita yake kwana yake tashi,kwana uku da yayi baya ganinta ,jinsa yake kamar mara lafiya.

” Is ok stop crying hulwa,ai gani na dawo ko?”ya faɗa yana mai ɗago kanta .

Buɗe baki tayi da nufin yin magana ,amma gaba daya aman nan ya taho mata ,aiku ba ɓata lokaci  ta wanke Adeeb tass!! Da aman nan ajikinsa.

Shikuwa Adeeb ko ajikinsa ,bai damu da aman da tayi masa ba ,ya riƙe ta sosai ajikinsa yana mai shafa bayanta,tausayinta yake ji har cikin ransa,bata da lafiya sosai dole ya kira likita adubata.

Download>>> Silar Fyaɗe Complete Novel Document

Tsohuwa salima ce ta karaso garesu tare da faɗin”ayya sannu fateema  kinji,maza kawota kaje ka wanke jikinka, wllh tun jiya take fama da ciwon cikin nan,nace yaro kodai girma ne zaizo mata?tsohuwa ta faɗa tana mai kallon Adeeb,

Dan sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana mai sosa kai,dan ya gani abinda tsohuwa ke nufi,ita haka take dama ba ruwanta idan zata faɗi magana,kai tsaye take faɗi.

” Ammm nanny bari na kira likita ya dubata. Ya faɗa yana nufar toilet riƙe da fattu,wanke mata jiki yayi tare da bakinta, shima ya wanke inda ta batashi,sannan ya dawo da ita cikin ɗakin, kwantar da ita yayi akan gado tare da shafa gefen fuskarta yace”sannu yanzu za’a baki magani kinji?”ya faɗa cike da tausayawa,ji yake kamar ya maida ciwon jikinsa.

Lumshe ido fattu tayi tare da kamo hannunsa ta rike gam cikin nata tace”Hamma karka tafi dan Allah” fattu ta faɗa tana mai lumshe idanunta .

Hannun nata ya riƙe da ɗayan hannunsa kafin yace “ba inda zani zan sake kaya in dawo yanzu” ya faɗa yana mai mikewa tare da ficewa daga dakin.

Tare suka dawo shida likita,wadda ta kasance likitar gidan ce , mai duba mata.

Sosai ta duba fattu ,kuma ta gane period ke don zuwa mata ,kuma farkon yine shiyasa take jin ciwo.

Dan haka bayani tayiwa Adeeb tare da bashi magungunan da Fattun zata sha.sannan ta lika always Jikin pant taba nanny akan idan jinin yazo saita bata tasanya.

” Yawwa Ni dama nayi tunanin ko girma ne  zatayi ,dan ciwon yayi yawa,Allah Sarki ashe kuwa shine ,bari na haɗa mata tea mai zafi ta sha”nanny ta faɗa cikin tausayawa tana mai nufar kitchen.

Shidai Adeeb yana zaune bakin gado,tunda yaji abinda ke damun fattu,baice komai ba ,kawai yana kallonta dan ta ɗan sami barci .

Cikin girmamawa likitar tayiwa Adeeb sallama ta fita akan zata dawo anjima .

Kai kawai ya ɗaga mata ba tare da ya kalletaba.

Kusan minti biyar saiga nanny ta dawo riƙe da wani kyakykyawan kofi sai turiri yake ,mikawa Adeeb kofin tayi tana mai cewa” ungo magajin faɗa tashe ta maza ta sha zatayi daɗi,kuma jinin zai sauko da wuri” ta faɗa tana mai nufar ƙofa again tana cewa ” bari i ke in kula da farfesun can dana ɗora mata,kasan shima yana taimakawa mace idan tana jini”ta faɗa tana ficewa.

Download>>> Akan Aikina Novel Document

Kallo Adeeb ya bita dashi,yana mai girgiza kai,yana son tsohuwar nan ,saidai tacika  surutu da sanya mutum jin kunya.

Ahankali ya ɗan shafe fuskar fattu da tayi wani fayau da ita ,sai kyalli take,ahankali ta buɗe idanunta tare da saukewa akan kyakykyawar fuskar hammata.

“Hamma” ta furta ahankali tana kallonsa.

” Tashi Kisha tea maza” ya faɗa yana mai taimaka mata ta zauna bayan ta sanya mata fillo abayanta.

Da kansa yake bata tea ɗin abaki,saida tasha kusan rabi sannan tace ya isheta, ajiye sauran yayi yana mai kallonta kafin yace” ya kike jin jikin naki?”

”  Da sauki Hamma saidai jikina ba kwari ,kuma har yanzu inajin ciwo anan dina”fattu ta faɗa tana mai nuna masa saitin marar ta.

Kawar da kai yayi da sauri yana mai cewa” is ok zai daina “

” Hamma zanyi fitsari” fattu ta faɗa ahankali.

Dan kallonta yayi kafin yace ” zaki iya zuwa toilet ɗin?” 

Kai ta daga masa tana mai yunkurawa ,tashi tayi tsaye tana ɗan yamutse fuska. Sai taji kamar lema ajikinta,juyawa tayi tare da kallon inda ta tashi,zato idanu tayi lokacin data jini agurin,da sauri ta kai hannunta ta shafo bayanta ,tana mai kallon hannun,aikuwa jini ne kuma daga jikinta ya fito,ƙara zato idanu tayi cikin tsoro tana mai faɗin” na shiga ukuna Hamma jini ,jine yana zuba ajikina,wayyo Allah Hamma jini”fattu ta faɗa tana mai nuna masa hannunta ,jikinta na rawa sosai kamar ana kada mata gangi,

Kallonta Adeeb yayi da sauri ,yana mai kallon hannun nata ,lumshe idanu tayi yana mai jin wani iri ajikinsa,tausayi fattu ke bashi,ita bata san komai ba ,yanzu meye abin damuwa akan wannan ga yadda jikinta ke rawa kamar ana yankata.?

Ahankali ya mike tsaye tare da dafa kafadun fattun yace ” ki nutsu mana ,wannan ba wani abun damuwa bane kinji dama hakan na faruwa ga ko wace mace data kai shekaru irin naki” yayi shiru yana ɗan sauke nunfashi ahankali.

Fattu kuwa kuka take tana cikin tashin hankali,sam Bama tajin me Adeeb ke faɗi,sai cewa take ” Hamma jini ajikina, dan Allah kace ya daina zuba ,na shiga uku jinina zai kare wayyo baffana” abinda take fadi kenan jikinta na rawa .

Gaba daya Adeeb yana rasa me zaicewa fattu,dan haka kallonta kawai yake cikin damuwa,suna cikin haka saiga nanny ta shigo, ajiyar zuciya Adeeb yayi tare da kallon nanny amarairaice.

” Aa meke faruwa ne haka magajin faɗa?(da yake haka take kiransa) taci gaba ,naga fateema na kuka ,kaikuma ka tasata gaba  da kallo kaima kamar salati kukan?nanny ta fada tana mai karasowa cikin dakin.

Ahankali Adeeb yace “nanny kiyi mata bayani kuka take, wai bata so” ya faɗa kamar zaiyi kuka.

“Yau naga ikon Allah fateema meye baki so?ko maganin ne baki don sha?kiyi haƙuri ai lafiya ake nema miki kinji ?kuma da kinsha jinin zai….sai kuma tayi shiru tare da bin gadon da fattu ta tashi da kallo,to kace jinin ne yazo ,wato shi tagani take cewa bata so,Allah Sarki ai zaki saba dayake wannan ɗin  na farko ne ,zo muje In gyara miki jiki yi shiru” nanny ta faɗa tana mai kamo hannun fattun suka nufi toilet.

Download>>> Budurwar Mijina Complete Novel Document

Kallonsu Adeeb yayi tare da sauke ajiyar zuciya ,sannan ya fice daga ɗakin,bayan ya janye zanin gadon daga kan gadon,ya ajiye gefe guda,tare da shimfida wani.

Kai tsaye gurin mai martaba ya nufa,yana shiga ya tadda mai martaba tare da amma, zama yayi kusa da mahaifin nashi,bayan ya jefa wa amma wani kallon na tsana .

Kawar da kai amma tayi tare da sakin murmushin gefen baki tace yaro yarone ,cikin zuciyarta.

” Habeebee Barka da dawo ,yanzu nake ƙoƙarin sake kiranka,ai najika shiru,kasan yanzu bana son koda da minti ɗaya ka ƙara nisa dani”abie ya faɗa yana mai shafa kan Adeeb.

Murmushi Adeeb yayi tare da sumbatar hannun mahaifinsa kafin yace ” abie wancan karon ma ,kaddarace ta sameni,har Allah ya ba maƙiya nasara akaina,saidai ahalin yanzu kar nake kallon,kowa sannan ba abinda mutum ya isa yayimin  na cutarwa in Sha Allah” Adeeb ya faɗa yana mai kallon ammi cike da tsana .

Itama ammi kallon Adeeb take ,tana mai suna maganganunsa ,kafin ta sauke ajiyar zuciya tayi sallama da mai martaba tare da ficewa daga ɗakin.

Waya ta dauko tana mai kiran wata number tace ” mu hadu yanzu-yanzun nan” sannan ta kashe wayar.

Adeeb yana fitowa daga ɗakin abie ya nufi bangaren da amminsa ke hutawa,

Wayace akunnenta kuma da alama wayar da take mai muhimmanci ce ,saidai tana hango Adeeb ya tunkarota tayi saurin katse wayar tana mai cewa ” zan kira -zan kira” bata jira amsar dayan vangaren ba ta kashe wayar.

Zama yayi kusa da ita tare da kamo hannunta ya sumbata, kanshi ta shafa taba faɗin Allah yayi maka albarka.

Ya jima suna dan hira ,kuma duk akan kunyar fattun ne ,kafin ya mike yace zaije  ya huta.

Ƙura mata ido naga ammi tayi ta baya ,kuma fuskarta amugun hade ,kafin kuma tayi wani murmushi tana mai jinjina kanta….

Karanta Littafin>>> Gidan Uncle Complete Novel

Masu karatu manage ,

Yau naje gidan suna ne.

Saida na dawo nayi wanna typing ɗin.

Much luv.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

Back to top button