Halysaah Page 34 By Khaleesat Haydar
Wajen karfe goma na dare Khaleesat na zaune dakin Aunty Farida da fruits a gabanta ta kasa sha, ita dai Aunty Farida na zaune opposite dinta ta zuba mata ido don har ta gaji da ce mata ta sha fruit din, ga abinci ma taki ci, tun tuni makociyar Aunty Farida ta shigo ta cire mata drip din bayan ya kare, ta daga kai ta kalli Aunty Farida a hankali tace “Aunty su Housemate dina sun tafi ne?” Aunty Farida tace “Waye kuma Housemate din ki?” Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, Aunty Farida tace “Junaid din ne Housemate din ki?” Khaleesat ta girgiza mata kai tace “Wanda suka zo tare” Aunty Farida tace “Ohk, tun daxu ai suka tafi kina bacci, ta yaya ya zama Housemate din ki?” Khaleesat na juya fruits din gabanta a hankali da fork tace “Gida daya muke da shi a America” Aunty Farida ta ɗan buda ido da confusion tace “Gida daya kuma? Kamar yaya? Amma ba kin ce makociyarki mace bace?” Khaleesat tace “Eh daga baya ta tashi daga apartment din, shi ne shi ya dawo gidan” Aunty Farida tace “Ikon Allah, shi kuma Junaid din a ina kika san shi?” Khaleesat tace “Cousin brothers ne ai, dalilin Housemate dina na san shi” Aunty Farida ta kafe ta da ido, Khaleesat ta sauke kanta bata boye ma Aunty Farida duk abun da ya faru tun daga dawowar Housemate apartment dinta, yanda ya biya mata kudin jirgi to and fro ta dawo Nigeria ta duba Umma, irin zaman da suka yi da shi da kirkin da yayi ta mata, har zuwa lkcn da Abdul ya zo kasar a karo na biyu da kuma abinda ya faru tsakaninsa da Ajay, da yanda suka maidata gidansu har ta gama Exams, babu abinda ta boye ma Aunty Farida hawaye na zuba idonta, Aunty Farida ta kasa cewa komai sai kallonta kawai take jiki a sanyaye, after almost a minute Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tayi tagumi don she is just speechless bata san ma me zata ce ba, amma ta fahimci wani abu a labarin da Khaleesat ta bata….. Washegari wajen karfe goma na safe Jay ya bude kofar dakin Ajay ya samesa tsaye yana buttoning din shirt dinsa ya gama shiryawa, Jay ya jingina da jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonsa calmly yace “You know what Ajay?” Ajay ya dau face cap dinsa ya saka, yana kokarin daura agogonsa a hannu yace “All ears” Jay yace “I think we shouldn’t say anything to Abba akan kudin da muka yi magana jiya” Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace “Why?” Jay yace “Kasan zai yi querying dinmu about what we are using that huge amount of money for, i think gwara in amshi kudi wajen Mamina kawai, cause you know i can’t lie to Abba idan yayi insisting akan abinda za mu yi da kudi haka, zan iya gaya masa me za muyi da kudin if he insist” Ajay ya masa wani kallo daga sama har kasa yace “Sannu saint, ita Mamin ce bazata yi querying dinka akan me zaka yi da huge sum of money din ba?” Jay yace “Yeah, but i know how to convince her” Ajay yayi wani murmushi yace “Mamin ce zaka yi convincing, i see” Bai jira amsar da Jay zai basa ba ya dau makullin mota da wayar sa ya bi gefensa ya fice daga dakin ya sauka downstairs, Jay ya bi sa da kallo, after a while ya jawo kofar dakin ya kulle sannan ya bi bayansa, Ummi dake zaune parlor ta bi su da kallo ganin alamar fita za su yi tace “Ina kuma za ku da safen nan?” Without looking at her a takaice Ajay yace “Bar beach” Ummi tace “Dama ana zuwa Bar beach da safe?” Ajay yace “Eh” daga haka ya fice daga parlon, Ummi ta kalli Jay tace “Wai Beach za ku?” Jay ya ɗan sosa kansa yace “A’a sai da yamma, yanxu dai kawai yawo za mu yi a gari” Ummi ta tabe baki tace “Ai shikenan, traffic ma kadai ya isheku, Mami ma suna hanya yau in sha Allah, sun ma kusa sauka” Jay ya sauke kansa yace “Eh haka tace min” Ummi tace “To sai kun dawo” Jay yace “Allah ya sa” Daga haka ya fita daga parlon, ya tarar da Ajay a mota yana jiransa, yana shiga motar Ajay yace “Ko ina ruwanta da inda za mu, ni bana son sa ido a rayuwata, shi yasa bana sauka gidanta a garin nan, i hate what i don’t like” Jay yace “Ikon Allah, what’s wrong with her asking us where we are going?” Ajay yace “That’s very wrong, we are not kids da zata dinga tambayar mu inda za mu idan za mu fita, ko Abba baya controlling din mu yanda matar nan take yi, i don’t think i am going back to that house zan je in kama hotel kawai” Jay ya girgiza kai yace “Kai fa matsala ne da kai kamar gidan haya, ni ban ga wani abu ba don ta tambayemu inda za mu da safe, it’s normal ai” Ajay ya kallesa yace “To ni ba kai bane da ake controlling yanda aka ga dama a family, kai da kaga za ka iya sai ayi ta controlling dinka Jawwad” Jay bai sake ce masa komai ba, Ajay ya ja motar suka fice daga gidan. Da sallama Safiyyah ta daga buhun dake makale kofar shiga compound din gidansu Khaleesat, Mama Shatu da Mama Zubaida ne tsakar gida ko wacce na zaune bakin murhunta ana girka abincin talla hayakin icce duk ya cika ko ina na gidan, Mama Zubaida sai mita take an siyo masu jikakken icce, gaishesu Safiyyah tayi suka amsa ana mata wani kallo kasa kasa, Safiyyah ta tsaya suka gaisa da Labiba dake wanke robobin da za a zuba abincin siyarwa, sannan ta nufi dakinsu Khaleesat ta daga labulen ta shiga da sallama, zaune ta tarar da Umma ta jingina da bango hannunta rike da carbi ga kawarta Mama salame da wata Zaliha makociyarsu sai Sha’awa ita ma makociyarsu zaune dakin ko wanne yayi jigum, zaunawa Safiyyah tayi tana kallon Umma ko gaisheta bata yi ba ganin yanayinta tace “Umma baki da lafiya ne?” Umma tayi karfin halin cewa “Sannu da zuwa Safiyyah” Safiyyah ta gaisheta sannan ta gaida sauran mutanen dake dakin, ta sake maida dubanta kan Umma kan tace komai Mama Salame da ta san kawar Khaleesat ce ita tayi kasa da murya tace “Tsakaninki da Allah Sapiya baki san inda kawarki Khaleesah take ba?” Safiyyah ta zaro ido tace “Kamar yaya Mama?” Sha’awa ta gyara zama tace “Ae tun ranan asabar rabon da a saka Khaleesat a ido, daga ta dawo kasar waje ta tarar an daura mata aure da audallah washegari Asabar aka nemeta aka rasa, babu inda ba a shiga neman Khaleesah ba amma babu ita babu labarinta, jiya jiya yan sanda suka zo suka tafi da Malam Ali” Safiyyah da ta shiga wani shock jin wai an daura ma Khaleesat aure da Abdul ta ajiye jakarta a gefe ta dafe kirji tace “Wani Abdul din aka daura mata aure da?” Sha’awa na gyara barkakken zaninta tace “Audullah saurayinta dai da kika sani, ranan juma’an nan da ta wuce aka daura masu aure, tana dirowa kasar aka sanar mata shine ta gudu har yau babu ita babu labarinta, gashi an tafi da Malam Ali an kullesa” Safiyyah tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Mikewa tayi tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba tsabar shock din da ta shiga maganganun Sha’awa na yawo a kanta, hawaye ne ya cika idonta tana girgiza kai ta kasa cewa komai, ina jin bayan Khaleesat da tayi bakin cikin auren da aka daura mata da Abdul idan aka cire su Jay babu wanda yayi bakin ciki kuma irin Safiyyah, don ji tayi kamar an aza mata katon dutse a kirji tsabar bakin cikin wannan labarin, kawai ta fashe da kuka cike da tausayin kawarta, Abdul fa?? Housemate din Khaleesat ne ya fado mata a rai, nan Safiyyah ta dinga rera masu kuka kamar ita ce Khaleesat din, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana kunduma ma su Mama Shatu da Mama Zubaida zagi tana cewa “Wato har sararin kunna rubabbun murhun ku kuka samu a gidan nan baku dubi bala’in da ake ciki ba, ai in dai ɗa ne kowa ma ya haifa wallahi, yanda ku ke nuna halin ko in kula da abinda ya samu ɗa na ku ma dai kun haifi ‘ya yan nan naga, shegu masu fararen kafafuwa tunda ɗa na ya auro ku yake shiga bala’i sinka sinka a duniya amma saboda baku da imani da tausayi ko wacce ta zauna bakin shegen murhun ta” Mama Zubaida ta kauda kai tana tabe baki tayi kasa da murya tace “Sai kuma yunwa ta kashe mu saboda yan sanda sun zo sun dauki Malam” Ita dai Mama Shatu sai juya miyarta take kar ya kone taki ko kallon inda Nenne take, Nenne na huci ta nufi dakin Umma ta dage labulen tana kallon cikin dakin tace “Saka dogon hijabi da rike carbi ba shine mafitarki ba Zahra’u, duk inda kika tura yarinyar nan waya kawai zaki buga masu ki ce ta dawo tun lamari bai lalace mana gaba daya ba, in ko ba haka ba wallahi sai a wanke daya daga kanninta a ba ma Awdul din tunda abinda yayi ta shi yayi su, in jar fata da gashi irin ta buzaye ne su ma duk suna da shi, babu abinda zata gwada masu sai shekaru tunda ta basu shekaru bakwai, don bazan zuba ido a karo na biyu ɗa na ya koma fursin ya tagayyara ba, Allah kadai yasan nawa na kashe wajen shige shige har Allah ya bamu mafita a wancan lokacin da aka kullesa, tun asali bata san bata son Awdul din ba sai bayan da ya kashe mata uban dukiya da bazai lissafu ba? Wace masifa ku ke son ja ma ɗa na ke da er ki a garin kano? Shi kadai fa ya rage min namiji sai mata, wallahi ki fito da ita Zahra’u in ya so su riketa a sake min ɗa na, nasan har da hadin bakin makirar tsohuwar can Gaje, yanxu kuma zan kama hanya in tafi Hotoron duk inda ku ka boye Khaleesah sai kun fito da ita baza ku kara ja min salalan tsiya ba, sha’awa taso ki rakani gidan tsohuwar banzan can Gaje” Da sauri Sha’awa ta mike ta figi baƙin gyalenta ta fita daga dakin ta bi bayan Nenne dake huci suka fita daga compound din gidan, Mama Zubaida da Mama Shatu suka saki guda a tare bayan Nenne ta fita, Mama Shatu ta kyalkyale da dariya tace “Ana yi muna hura murhu, ma ga dai karshen wannan dirama me dadin kallo a gidan nan, su buzuwa sai a koma dajin da aka shiga aka nemo maganin farin jini ayi ma Malam bayanin lamari ya kwabe, ba dai ‘ya yanmu bane munana masu baƙin jini, maji ma gani dai” Umma dake jin duk abinda suke cewa ta jinginar da kanta da bango hawaye na sauka idonta Mama Salame na bata hakuri, Safiyyah dai jingina tayi daga bango a inda take tsaye hawaye na zuba idonta ita ma, ganin abun take kamar a mafarki wai an daura auren Khaleesat da Abdul, to amma ina Khaleesat zata tafi tun ranan Saturday ita da tasan Khaleesat ko kawaye bata da su a kano, Housemate ne ya fado mata, ta dau jakarta da sauri tana share hawayenta ta fita daga dakin Umma, Umma ta bi ta da kallo hawaye masu zafi na bin idonta daga ranan asabar zuwa yau har ta rame, ko abinci bata iya ci ta kira Aunty Farida yafi a kirga akan ta zo gareta ko zata ji saukin radadin da take ji a zuciyarta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi Safiyyah da wani kallo suna tabe baki har ta fita daga compound din, Mama Zubaida ta matsa kusa da Mama Shatu da yake murhunsu kusa da kusa yake, tayi kasa da murya tace “Kin ga ki hakura da dafa waken nan da kika ce don gaskiya zai bata mana lokaci ga waje da nisa, gwara mu je a kara kada hankalinta taji ta tsanesa da auren kuma taki dawowa, in ya kama a kadata ta shiga duniya duk sai mu ce ayi, kudi ne dai zai yi kuka ba wani abu ba, kinga daga karshe in ma Labiba ko Lamisah duk wanda yace a basa duk daya ne a wajen mu babu banbanci, babu abinda zata gwada masu sai farin fata da uban gashi kamar na doki, in idanuwa ne su ma suna da shi, sannan suna da hancinsu dai dai gwargwado, tun asali kece kika yi ta makon fiddo kudi da ba a kai ga haka ba ma wallahi” Mama Zubaida ma tayi kasa da murya tace “Wallahi ban taba zaton aikin mutumin na ci haka ba Shatu, kinsan Malaman Jabu sun yi yawa yanzu sai dai ka kai masu kudinka su yi cefanen gidansu, shi sa kika ga ina ta ja da baya naki sakin kudi dama jarina ba jarin arziki ba, kinsan tun bayan rasuwar Malamin nan da yayi mana aiki kan Parida naki sakewa da Malamai don asaran kudi kawai mutum yake shi din dai ne malami gangariya amma mutuwa ta dauke mana shi kwatsam, gashi har yau duk uban kyan parida babu mashinshini tana can tana tuwo tuwo a Legas tana aiko ma yayar kudi kuma in sha Allahu a haka zata kare ga dai kyan da diri da komai amma babu mashinshini, to in anyi duniya don manzon Allah haka Khaleesar ma zata kare, amma yanxu tunda muka samu sabon Malamin nan naga aiki da cikawa kema kin san fiddo kudi bazai kara min wahala ba, ba gashi har na sa an amso min adashina ba daxu, in sha Allah sai mun karkato da hankalin Abdul kan ‘ya yan mu, ko Labisah ko Labibah, ba dai kyau suke takama da shi ba wai su buzaye, to wallahi sai dai su ga ana aure…..” Shiru Mama Zubaida tayi ganin Salame ta fito daga dakin Umma ta ci gaba da juya miyarta with serious face, Safiyyah na fita kofar gida ta ciro wayarta a jaka don tana da number Housemate, tayi dialing numbersa gabanta na faduwa tana hoping yasan whereabout din Khaleesat, jin Khaleesat take a ranta kamar er uwarta ta jini, she can’t imagine halin da take ciki yanxu, yana fara ring Jay dake mota tare da Ajay ya daga wayar ganin Safiyyah ke kiransa yayi picking ya kai kunne calmly yace “How are you Safiyyah?” Da kyar Safiyyah tace “I am fine, ina kwana?” Yace “Lafiya lau, kin dawo Nigeria kenan?” Ta gyada kai da kyar tace “Pls tambaya nake son in maka Ya Jawwad” Jay yace “Ina jin ki Safiyyah” Safiyyah tace “Don Allah kasan whereabout din Khaleesat, wai tun Saturday ta bar gida har yanxu ba a san inda take ba, yanxun nan na zo gidansu nake samun labarin” Hawaye na zuba idonta ta kare maganar, a hankali Jay yace “Halysaah?” Lkci daya Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma ya fixge wayar ya katse ya ajiye, Jay dai kallonsa kawai yake, can yace “Kawarta ce fa” Ajay yace “And so? Assignment din announcing whereabout dinta aka baka ne? Me yasa baka da sirri ne kai?” Jay yace “But it’s nothing, kawarta ce kuma tana sonta sosai, nasan bazata gaya ma kowa komai ba” Ajay ya dau wayar jin ya fara ringing, yayi rejecting call din Safiyyah sannan ya saka wayar a silent ya zura a aljihunsa yace “Dama ka saba tona ma mutane asiri kayi ruining plan dinsu ai” Jay yace “Bani wayata malam” Calmly Ajay yace “Bazan bayar ba” Dai dai sanda Ajay yayi parking a kofar gidan Aunty Farida ya kashe motar ya sauka ya bar Jay a ciki. Nenne na isa kofar gidan Gaje tare da Sha’awa er rakiyarta suka ga yan sanda biyu kofar gidan Gaje da motarsu, ga yan unguwa sun tsaya cirko cirko ana salallami, Nenne ta ja burki inda take tsaye tana gwaggwale ido sai ga wata er sanda ta kado keyar Gaje sun fito daga cikin gidan, Gaje na rusa kuka cikin rudewa take cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wallahi ban san inda take ba tsakanina da Allahn da ya halicce ni, in nasan inda take Allah ya tsine min albarka, Al-qur’anin Allah babu abinda na hada da ita ba dangin iya ba na Baba haduwar gidan duniya ne kawai, don manzon rahama ku min rai ban hada komai da ita ba” Er sandar tace “Amma ai an ganta ta shigo gidan ki ranan asabar da daddare, iya gaskiyar ki kadai ne zai cece ki a wannan case din aki kai ki furson, in kuma kika ce zaki ci gaba da karya zaki ga illar karya kuwa” Cikin tashin hankali zufa na keto ma Gaje ta ko ina tace “Wallahi zan fada gaskiya ku tsaya ku saurareni, tsakanina da Allah ta zo gidana da daddare wajen karfe goma tace in rufa mata asiri amma bata gaya min abinda ke faruwa ba, ni kuma da na tashi sai na kai ta gidan wata er dakina Sadiyah Chamo, Sadiyah ce ta bata mafaka a gidanta ta kwana, kashegari kuwa ta kira wani gingimemen mutumi a wayarta ya zo da katuwar motarsa ya dauketa suka tafi inda ban sani ba, idan na maku karya a wannan zance kada Allah yayi min rahama” Er sandar tace “Ina gidan Sadiyar yake?” Jiki na rawa Baba Gaje ta nuna hanyar gidan Maman Fu’ad, er sandar tace “Shiga mota mu je ki nuna mana gidan” Gaje ta rushe da kuka tana cewa “Na shiga uku na lalace ni Al-haqqatu na ja ma kaina masifa a garin kano” Bayan mota aka bude ma Gaje tana kuka ta shiga er sandar ta dago mata yakunannen gyalenta dake jan kasa ta dora kan cinyarta sannan ta shiga bayan motar ita ma, tuni Nenne ta juya sum sum tun ba a lura da ita ba ta shige wani layi, sai juyawa sha’awa tayi taga gefenta wayam babu Nenne…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:Gyaran gashi da kitson zamaniKwalliyar Sallah mai ɗaukar idoWanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya raiKayan gyaran fata na gaskeLalle mai kyau da salo na zamaniTura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗiShirin amare da na musammanBa kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.Tambaya/Booking:WhatsApp: 08062991549Kira: 09016108092 / 08064532391Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
