Hausa novels

Gargadar So Chapter 57 By M Shakur

Washegari Khaleel yafarka adakinsa da kyar ya lallaba yaje yayi salla wuraren 9, ko wanka baiyiba yafito yasauko kasa Mommy na falo tace “good morning Son” ko kallonta baiyiba Noor ta taho wajenshi da gudu tace “Daddy” kanta yashafa kadan yace “go to grandma I’m coming Noor” yafice idanunshi sunyi ja duk sun nuna alamun bacci, yayi waje yana kallon Salman daya taho da sauri Khaleel yace “ya?” Salman yace “we tracked the numbers duka numbers din beggars ne dake hanyar banex, da kyar bayan nabasu kudi suka iya sanar dani wata mace ce tazo tabasu 5k tayi amfani da wayansu” dasauri Khaleel yace “did you ask them description nata?” Salman yace “yeah wai batada tsawo sosai she’s very fair and da Toyota tazo” shiru Khaleel yayi kaman mai tunani, kawai yawuce wajen motar sa Salman yabiyosa ya shiga driver ma yashiga sukabar gidan, ahankali cikin muryan gajiya da bacin rai yace “my wife’s house” jan motan sukayi har zuwa unguwan su Hawwa.Baba na kofar gida azaune da aswaki a bakinsa ya hango mota yasan Khaleel ne kawai sai yafara murmushi kafin ma abudemai Khaleel yabude da kanshi yafito Baba ya tsareshi da idanu ganin idanunshi adan kumbure hakama fuskanshi dasauri Baba yataso shima Khaleel yawuce wajen Baba kafin yayi magana har Baba yakai hannunsa kan fuskanshi cikeda so yace “bakada lafiya ne Ibrahima”?Baba Khaleel ya kalla dan ranshi abace yake yayi shiru yakasa magana sai dan huci da yasauke Baba sai kawai hankalinsa yatashi yace “meya sameka? Tell me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Salman da hannu yamai alamu yakawomai wayanshi wayan aka kawomai muryan Khaleel ba dadi yanunama Baba wayanshi yace “Baba wasu sakonni aka turamin marasa dadi bazan iya karanta maka ba kaima, nasa ammin tracking number” yadanyi shiru Baba da gabanshi ke faduwa yace “ina jinka gayamin menene ke faruwa”? Cikeda jin zafi Khaleel yace “Baba matana ta batamin rai sosai, ina kyautata zaton har yanzu tana tareda mahaukaciyan nan, so nazo na ganta ne”Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni’ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu yabaci tsabagen bacin rai yace “muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan kiramaka itaba, ai gidana nakane ban maka iyaka da ko’ina acikin gidannan ba, muje” Baba yayi gaba Khaleel yabishi abaya suka shiga cikin gidan ko’ina a gyare ta buga sallama gaban dakin Hawwa, Ammi ta amsa yace “da mijin Hawwa nazo Zainabu” Hawwa dake zaune daga ita sai dan rigan bacci tana danna wayanta dasauri tadauki hijabi tasaka dark blue har kasa, ita dama Ammi da hijabi ajikinta Ramla kuma na kitchen tana aiki dasauri Ammi ta tashi da fara’a tace “bismillah bismillah kushigo” shigowa Baba yayi Khaleel biyeda shi abaya, kan Khaleel na kasa yace “ina kwana Mom” “muntashi lpy Khaleel” ahankali Baba yace “biyoni Ammi” binshi Ammi tayi suka fice daga dakin tareda maido musu da kofan suka rufe, Khaleel yazuba hannu a pocket nashi yana kallon Hawwa dako dagokai batayi ta kalli inda yakeba, kaman ma batasan da mutum awajen ba, Babu wasa kan fuskanshi rai abace yace “wacece ke tareda ke jiya a office?” Batare da Hawwa ta kalleshi ba tace “da wanda nake tare, ko wanda nai magana, ko wanda nagani a office is none of your damn business” ran Khaleel abace ya daka mata tsawa da saida dakin ya amsa. “Nace dawa kike tare jiya an office!”? Dagokai Hawwa tayi adan tsorace sabida yanda yayi mata tsawa ta tabbata anji a tsakar gidan, tashi tayi daga gadon ta taho inda yake dasauri dan bataso su Ammi suji tanamai ihu suhau mata fada akanshi, hakan yasa tace “who do you think you are kanamin ihu aka?” Ran Khaleel abace yanunata da hannu yace “dawa kike tare an office jiya?” “My friend!” Hawwa ta amsa kai tsaye ganin yadameta da tambayan, cikeda jin haushi tace “I was with Ni’ima me akayi? Sabida an auramin kai saina tambayeka kafin naga kawata konai magana da kawata”? Wani irin fizgota Khaleel yayi yakai hannunshi zuwa wuyanta ranshi abace yace “what is so special about that witch of a woman da kin kasa hakura da ita? Are you a lesbian!? Are you really into girls?”Ja idanun Hawwa suka soma yi tafara dukan hannunshi hakan yasa yasaki wuyanta tadanyi tari kadan sannan ta kalleshi tace “da aurenka gwara zama da Ni’ima! At least ita bata living wayward life irin naka!”Radadi zuciyan Khaleel yafara sai kawai yakara fizgo Hawwa yakama kafadunta ya matse yana kallon cikin idanunta zuciya yakaimai wuya da kishi kai da komi ma ganin yanda Hawwa ke son Ni’ima yace “idan nakara ganin ki da yarinyar nan i will killl her! I will ruin her life! I will make her life a living hell you know me so well to know duk abinda nakeso nayi sainayi, stay away from that witch evil vile woman inba hakaba saina kasheta!”

Back to top button