Description/Story:
Juyin Kwado! Complete Hausa Novel Document
Written By Salma Ahmad Isah
Description
MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.
ARMAN IƘBAL.
Babu abin da yake tashi a ko ina sai hayaniya da iface-iface, sai kuma sautin sara da sukan takkuba. Kuma ko ina jini ne ke zuba… A tsakiyar wannan hatsaniyar yaƙin yake tsaye, can ya hango wani mayaƙi ya taho da gudu ya iyo kansa, hannunsa riƙe da wani takobi me tsananin kaifi, ya kawo masa sara da ita…
Tahowar sukan takobin cikin tunaninsa ya yi dai-dai da tahowar sukan takobin abokin karawarsa a tsakiyar filin hall ɗin koyon wasan takobi na MK fencing academy. Cikin zafin nama ya buɗe idonsa, sannan ya yi azamar kaucewa sukar takobin wasan. Cike da ƙwarewa kuma ya yi amfani da nasa takobin ya kaiwa abokin nasa farmaki, farmakin da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan yasa ya zamo zakaran wasan, domin shi ne ya lashe!.
Malamai da ɗaliban wasan na takobi suka shiga tafa masa, hakan yasa ya juya kansa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a hankali yake fitar da numfashi, domin wannan mafarkin da ya saba yi ido biyu yau ma ya raɓe shi, ya rasa mece ce alaƙarsa da wannan yaƙin da yake yawan yin mafarkinsa ido biyu ko cikin bacci. Ba ya jin ya taɓa tsallake sati ɗaya ba tare da ya yi mafarkin wannan yaƙin me firgitar da ɗan adam ba.
Shi dai ya san ba a haifeshi a ƙarnin da aka yi yaƙin ba, amma kuma ya rasa dalilin da yasa a ko da yaushe yaƙin yake raɓar rayuwarsa. Hannu ya kai ya taɓa farin glasses ɗin da ba ya taɓa rabuwa da su duk rintsi, kasancewar yana fama da lalurar rashin gani, wadda aka haife shi da ita. Da ace kuɗi yana samar da lafiya ya tabbatar da mahaifinsa Sayid Iƙbal Alhadi zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka domin sama masa lafiyar ido.
Amma tun yana ƙarami ake fafutukar naima masa maganin da zai warkar da idon har zuwa yanzu da yake da shekaru talatin da ɗaya a duniya ba’a dace ba. Hakan tasa aka haƙura aka ƙyale maganin, ya ci gaba da amfani da glasses ɗin da da taimakonsu kaɗai yake iya ganin abin da Allah ya yassare masa ya gani.
“Muna tayaka murnar lashe wannan gasa Arman! Fatan nasara!”
Faɗin ɗaya daga cikin malaman dake koyar da su wasan takobi cikin harshen larabci. Yayin da yake miƙa masa award ɗin da aka tanada domin zakaran da ya lashe wannan gasa da aka saka a tsakanin ɗaliban makarantar. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi award, sannan ya yi murmushi me kyau, tare da furta.
“Na gode”
Ya juya ya kalli abokansa da yake koyar wasan tare da su, ya ɗaga musu award ɗin, suka saka tafi har da masu ihu, shi dai murmushi kawai yake, har ya sauƙa daga kan stage ɗin wasan. Ya nufi ɗakin sauya kaya dake cikin hall ɗin, a nan ɗakin da ya shiga ya sauya kayan fencing ɗin da suke jikinsa, ya mayar da kayan da ya zo da su. Wato black plain hoodie, wadda ya ɗorawa red bomber jacket a sama, da blue jeans sai baƙaƙen canvas ɗinsa.
Sannan ya nufi backpack ɗinsa ya buɗeta ya saka award ɗin da aka ba shi, kafin ya ɗauki wayarsa dake ciki, ya buɗe da fatan ganin missed call ɗin abokinsa ADAM, amma babu alamar ma ya kira, dan haka ya ja tsaki, ya buɗe wayar ya nemo lambarsa ya sake aika masa kira, a karo na barkatai a ranar, dan tun kafin ya shiga fencing class ɗin yake ta kiran wayarsa.
*House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.*
ADAM ALI ABBAS.
“Adam! Adam! Adamm! Wai ba za ka buɗe ƙofar nan ba!?”
Wata bahaushiyar mata ke faɗi, cikin harshen hausa, yayin da take tsaye a jikin ƙofar ɗakin da take a kulle, yanayin shigar dake jikinta kaɗai zai sanar maka da ƙabila da kuma ƙasar da take. Duk da su mazauna ƙasar ta Dubai ne bai sa ta daina saka kayan al’adarta ba, a matsayinta na ainahin ‘yar ƙasar Nigeria, kuma bahaushiyar arewacin ƙasar.
Daga cikin ɗakin da take buga ƙofarsa kuwa, wani matashi ne tsugunne a ƙasan desk, ya lulluɓa da blanket har kansa, yanayin tsoro shi ne kwance a kan fuskarsa, ban da rawar ɗari ba abin da yake, kamar wanda ya kwana a cikin fridge.
Ɗakin bai cika girma ba, amma yana ɗauke da kaya masu kyau da sauƙin kuɗi, kallo ɗaya za ka yi wa ɗakin ka san cewa na mai ɗaukan hoto ne. Dan ko wace kusurwa ta ɗakin na ɗauke da hotunan mabanbanta abubuwa, da kuma hotunan cameras da ma cameras ɗin na zahiri, tarkacen da ɗakin ya cika zai sa ka san cewa ɗakin matashi ne. Daga wajen ɗakin, matar nan ta ɗazu da take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta girgiza kanta cike da takaicin halin ɗan nata.
“Allah ya raba bawa da wahala!”
Ta faɗa kawai, sannan ta juya ta dawo ɗan ƙaramin falonsu dake ƙasan gidan, wanda ke ɗauke da kyawawan furnitures masu kyau. Tana shirin wucewa kitchen ɗin dake haɗe da falon wayar Adam ɗin dake a falon ta yi ringing kamar ɗazu. Dan yawan kiran wayar da ake run ɗazu ne yasa ta gane cewa Adam ɗin bai fita ba, shi ne ta je domin duba shi, amma sai ya ƙi buɗe ƙofar ɗakin.
Wata shawara ce ta faɗo mata a rai, hakan yasa ta nufi wayar tasa ta ɗauka ‘Bin Iƙbal’ shi ne abin da aka rubuta a matsayin sunan wanda yake kiran, kuma ta gane cewa abokinsa Arman ne, dan haka ta ɗaga wayar, ta sanarwa Arman ɗin halin da Adam ɗin ke ciki.
Daga ɗayan ɓangaren, Arman ya sauƙe wayarsa ƙirar iPhone ‘yar yayi yana dariya a nutse, ba sai Maaman Adam ta yi dogon bayanin abin da yasa ya shiga ɗakinsa ya kulle kansa ba. Dan ya san dalilin ba zai wuce ya kalli wani horror ko Zombie movie ba, ya san abokinsa da tsoro kamar farar kura. Kuma ga shi da naci, dan duk yadda ya kai ga tsoron horror film ɗin sai ya kalla daga zarar sabo ya fito, Allah yasa yanzu haka bai kwanta zazzaɓi ba.
Kansa ya sake girgizawa yana ɗaukan backpack ɗinsa, ya goyata a bayansa yana kama hanyar barin Business Bay, sai da ya fita daga building ɗin sannan ya fara dialing numbern ɗaya ƙawar tasu wato IVANA!.
*Repton school Dubai, Nad Al Sheba 3, Abu Dabhi, United Arab Emirates.*
IVANA SAGAR.
Zaune take a kan maroon bowl chair, sanye take cikin farar hoodie da baƙin distressed jeans, ƙafafunta cikin farin canvas, baƙin dogon gashin kanta kwance a gadon bayanta, yayin da hannayenta ke kaɗa guitar ɗin dake kan cinyarta. Farar balarabiya ce, kyakkyawar gaske, me manyan idanuwa da dogon hanci da madaidaicin baki me ɗauke da farar fata me haske.
Murmushi ne kwance a kan fuskarta, yayin da take kallon ɗalibanta da take koyawa kiɗan guitar zaune a gabanta. Dukansu sun nutsu suna sauraron daddaɗan kiɗan guitar ɗin da take… Wayarta dake aje a gefenta ce ta kaste musu darasin, ta hanyar ringing ɗin da ta fara.
Hakan yasa ta dakata da kaɗa guita ɗin, ta kalli wayarta dake ruri, alamun shigowar kira ‘Rafiƙi’ (Abokina) shi ne rubuce tare da heart emoji a gaban sunan, kuma kaf duniya mutum ɗaya ne ta yi saving numbernsa da hakan.
“A’aziruni lahza! (Excuse me please)”
Ta faɗi cikin harshen larabci tana duban yaran ɗabilan nata. Sannan ta juya ta ɗauki wayarta, ta ɗaga kiran Arman dake shigowa.
“Shu wainak halla? (Yanzu kana ina?)”
Ta tambaya ba tare da ta bari ya yi magana ba, dan ta san sun yi da shi a kan yau yana da gasa tsakaninsa da abokan koyon wasan fencing ɗinsa.
“Ai dai kya bari mu gaisa ko?”
Arman ya faɗa daga ɗayan ɓangaren, sai ta yi murmushi, tana cire handle ɗin guitar ɗin daga wuyanta, sai da suka gaisa, sannan ya sanar mata da dalilin kiranta.
“Na kira Adam Maama ta ɗaga, ta sanar min da tun jiya ya kulle kansa a ɗaki, ya ƙi fitowa. Da alama ya kalli wani horror film ɗin ne”
Ivana ta kwashe da dariya tana rufe bakinta, dan ita ma ta sa halin abokin nasu.
“Yanzu kana ina?”
“Na baro business bay a motata”
“Mashi (Okay) ka biyo ta nan sai ka ɗaukeni”
“Ɗayib (Okay)”
Ya amsa, sannan ya aje wayar.
*
Arman ya kwashe da dariya yana kallon Adam da yay tsuru-tsuru da shi, saboda yanda yake a tsorace. Ivana ta ɗan yi guntun tsaki tana dafa kafaɗun Adam dake basu labarin film ɗin ban tsoron da ya kalla daren jiya, wanda ya hana shi sukuni har zuwa yau ɗin nan.
“Shifti? Huwa am yadhak alaiyyi” (Kin ga ba? Dariya mayake min)
Adam ya faɗi yanayinsa na nuna damuwar da yake ciki, dan har yanzu a firguce yake.
“Armaan la ad tadhak!” (Armaan kada ka sake dariya)
Ivana ta gargaɗe shi, sai ya ɗora hannunsa a kan bakinsa, yana son toshe dariyar dake cinsa, amma ya kasa. Ivana ta girgiza kanta, sanan ta tura Adam suka fara tafiya tana kwantar masa da hankali. Arman ya biyosu yana ci gaba da ƙyaƙyatawa Adam dariyar mugunta. Da haka har suka shiga Cavo Espresso Bar dake kusa da inda suke, har suka zauna Arman bai daina dariya ba, ko ya so ya danne daga sun haɗa ido da Adam zai ji dariyar da taso masa.
“Ivana kalli yaskut! Wa illa rah irja’a ala bait” (Ivana ki saka shi ya yi shiru, idan ba haka ba zan koma gida).
Ya faɗa yana kallon Ivana. Ivana ta ɗakawa Armaan duka a baya tana faɗin.
“Da ƙyar muka saka shi ya fito daga gida, yanzu kuma idan ka ci gaba da masa dariya ko zai koma gida ba zan yi ƙoƙarin hana shi ba”
“Asif (Ku yi haƙuri)”
Faɗin Arman yana toshe bakinsa. Ivana ta sake dafa kafaɗar Adam da har yanzu yake a dame.
“Laik Adam! Shabah mu haƙiƙi! Killu mazah! Wa ma bi kaffu!”
(Ka ga Adam, fatalwa ba gaskiya ba ce, duka shiri ne, kuma ba su da ban tsoro).
“Me ya sa za ki faɗi haka? Bayan ni na ganta da idona, wata doguwa, me dogayen farata, idonta ja… Wayyo Maama”
Ya ƙarashe yana rufe fuskarsa, saboda fuskar fatalwar da ya hango. Ivana ta sake dafa shi.
“Ihda! Halla rah jiblak shai. Biddak shai mu?” (Ka nutsu, yanzu zan kawo maka shayi, kana son shayi ko?)
Ya jinjina mata kai yana kallon Arman dake ta ƙoƙarin danne dariyar da ke ciyo shi. Ivana ta gyaɗa kai, sannan ta miƙe ta zagaya ta nufi wurin da zata yi order. Cup uku na shayin ta karɓa, sai dai a yayin da take shirin juyawa ta yi karo da wani mutum da shi ma yake ƙoƙarin zuwa wurin.
Farko kofunan shayin dake jere a kan tray ta fara kalla, da ta ga ba su zube ba sai ta kalli mutumin da ta yi karo da shi. Wani kyakkyawan matashin balarabe ne, wanda ke sanye da baƙar suit, kalar farar fatar jikinsa me ɗaukar hankali ce, haka ma kammaninsa, dogo ne, kuma me matsakaicin jiki, yana da faffaɗan ƙirji, sannan sumar kansa na cikin asken high pade. Yana da buɗaɗɗen ido, wanda yake ɗauke da shuɗiyar ƙwaya, sannan hancinsa dogo ne sosai, ga bakinsa dai-dai wa dai-dai, yana da saje da kuma gemu, wanda suka ƙara masa kyau.
“Ana ba’atazir! Ma intabahat!” (Ki yi haƙuri ban lura da ke ba ne).
Ta ji muryasa me daɗi ta furta, sai kawai ta jinjina kanta, alamun ba komai, sannan ta raɓa shi ta wuce, har ta koma table ɗin da su Armaan suke bai daina kallonta ba.
“Rifaƙ (Guys) ko kun san cewa yau Chris Brown zai yi live performance a Coca-cola Arena?”
Faɗin Arman yana nuna musu takardar sanarwa a cikin wayarsa. Adam da Ivana suka dubi juna.
“Wai yau?”
Adam ya tambaya yana aje cup ɗin dake hannunsa.
“Eh yau, duba ka gani”
Ya miƙa masa wayar , Adam da Ivana suka haɗa kai suna karantawa.
“Za mu je ne?”
Cewar Ivana.
“Akid! (Of course)”
Arman ya bata amsa. Domin duk inda za su je ko za su fita shi ne ke biyan duk kuɗin da za’a kashe, ko cinema za su je shi zai sai musu ticket. Saboda kaf cikin su ukun babu wanda ya kai mahaifinsa kuɗi. Dan mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, wanda yake da kamfanunuwa masa masu zaman kansu.
Shi Adam photographer ne, yana aiki tare da wani kanfanin magazine, ita kuma Ivana musician ce, tana koyar da kiɗan guitar a Repton school Dubai. Sannan tana aikin kiɗa a waƙoƙi idan har an buƙata, duk cikinsu shi Arman ɗin ne ba shi da aikin yi, ba wai dan ba’a naima masa a gidansu ba. Sai dan shi a rayuwarsa ya tsani duk wata harka da ta shafi kasuwanci.
Duk da ya taso a gidan da ake kasuwanci, kuma hakan ya samu asali ne daga nakasar gani da yake fama da ita tun lokacin yarinta. Tun a tasowarsa kawunsa, yayan mahaifinsa ya saka masa ƙin harkar kasuwanci, dan a ko da yaushe abin da yake faɗa masashi ne.
“Harkar jagorancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ba na makafi ba ne”
Ya sha faɗa masa hakan tun ba shi da wayo har ya taso ya yi wayo, tun ba ya gane abin da kalaman ke nufi har ya zo ya gane abin da kalaman ke nufi. Sannan tsangwamar da ake yi wa mahaifiyarsa a halinsu ya ƙara cusa masa ƙiyayyar kasancewa ɗaya daga cikin ahalin Alhadi a ransa.
Kuma suna nunawa mahaifiyarsu wariyar launin fata saboda ita ‘yar Pakistan ce, su kuma ahalin mahaifinsa larabawan Qatar ne. Shi da ƙanwarsa Gulzar kaɗai iyayensu suka haifa, kuma bayan shi babu wani wanda zai iya gadon kasuwancin mahaifinsa sai Faisal!. Ɗan yayan mahaifinsa da shi ma ya bada tasa gudummawar wurin cusa ƙiyayyar son karɓar jagorancin Majmu’at Shirkat Alhadi (Alhadi Group of Companies).
Zama shugaban Alhadi Group of Companies shi ne babban burin Iƙbal, wato mahaifin Arman. Kuma saboda yana yawan takura masa a kan batun kasuwancin yasa suka fara raba gari. Dan a yanzu Arman ba ya jin yana da maƙiyi sama da kujerar jagorancin gammayar kamfanunuwan Alhadi.
Alaƙarsu da su Adam ta samo asali ne tun daga makaranta, abin da ya sa tafiyarsa da su ta yi nisa shi ne su ba su tsangwamarsa dan yana da ƙarancin lafiyar ido. Kuma sam ba sa ɗaukan cewa bai kai ba, dan yana saka glasses ɗin da za su taimaka masa wajen gani, saɓanin yanda ya taso ana nuna masa cewar tun da ba ya gani shi makaho ne.
“Na ga kamar sauran awa ɗaya a fara wansa fa!”
Adam da ya ci gaba da karanta takardar sanarwar ya faɗa, sai duk su ukun suka dabi juna, kamar wanda suka haɗa baki, haka kowa ya finciki jakarsa suka ruga da gudu zuwa waje, Ivana na faɗin.
“Gara mu yi sauri kafin tikitin ya ƙare!”
Ai a ɗari suka shige motar Armaan ƙirar Ferrari venon, Adam ya figi motar zuwa Coca-cola Arena, kamar yanda suka yi zato ticket ɗin ya kusa ƙarewa. Dan duk da haka sai da suka bi layin siyan tikitin. Yayin da suke bin layin siyan tikitin, Adam ya shiga bawa Adam labarin film ɗib da ya kala jiya. Shi kuma Arman sai kwasar dariya yake, kamar daga sama ya ji an kira shi da sunan da ya fi masa na mutuwa ɗaci a kunne.
“Marhaba makaho! (Hello makaho)”
Idonsa ya rintse, dan ko ba’a faɗa ba ya san wa ya mallaki muryar, dan haka ya buɗe idonsa yana gyara glasses ɗinsa, wanna ita ce ɗabi’ar da ya fi yawan yi, ba ya haura minti goma ba tare da ya gyara zamansa glasses ɗinsa ba, ko da ko bai zame ba. Ya juyo yana kallon Faisal tare da wata budurwa tsaye, dariyar da ya ga Faisal ɗin na yi ita ta fi baƙanta masa rai.
“Ashe kuma makafi ana ganinku a wurare irin wannan?… Na ɗauka makafi ba sa zuwa kallon live performance!”
Ya ƙarashe yana sheƙewa da dariya, budurwa dake tare da shi tana taya shi.
“Ka ga malam! Babu wada ya buƙaci jin ra’ayinka a nan, dan haka bama son tada zaune tsaye.”
Ivana ta dakatar da shi, dan ko kaɗan Arman ba ya iya tanka masa ko ƙanwarsa Sakina idan suna aibanta shi, idan suka taɓa Gulzar ko mahaifiyarsu ne dai ba ya shiru.
“Yi haƙuri malama, ba da ke muke ba, da wannan makahon muke…”
Ya yi fasali yana yin taku uku zuwa gaban Arman, sannan ya yi kamar zai rungume shi, ya kai bakinsa saitin kunnensa yana murmushi, sannan ya furta.
“Jin daɗi da sharholiya irin wannan ba ta kamaceka ba, ka fi dacewa da yin bara a gefen hanya!”
Ya ja baya yana dariya, Ivana ta riƙi kwalar rigarsa a fusace za ta mayar masa da martani, Armaan ya jata baya yana girgiza mata kai. Haka Faisal da budurwasa suka wuce suka barsu a wurin suna dariya.
“Da ka bari na mayar masa da martanin da zai hana shi ba ci daren yau. Amma ka hana”
Arman ya girgiza mata kai.
“Maganganu irin wannan na saba jinsu tun tasowata, ba shi ne mutum na farko da ya fara faɗin hakan ba, dan haka ki share kawai”
Ya ƙarshe yana ɗauke kai, cike da damuwa Ivana ta kalli Adam da bai ce komai ba, dan ba zai ce ɗin ba, tsoro ba zai bari yace komai ba, ko shi ya je ya takalo faɗa Ivana da Arman ne ke tare masa, amma ba ya iya taɓuka komai.
*House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai.*
Motar Armaan ta faka a gaban ƙaramin gidan da bai cika girma ba, amma duk da haka ko daga waje ma yana da kyau. Ivana dake gidan baya na motar ta buɗe ta fita, sannan ta goya jakar guitar ɗinta a baya, ta rufe motar tana kalon Adam da Arman dake gidan gaba.
“Me kuka shirya mana zuwa gobe?”
Arman da Adam suka dubi juna, sannan Adam ya sake subanta yana girgiza kai.
“Babu wani abu, sai dai idan mun haɗu zuwa goben”
Ta ɗaga hannunta suka yi fits bump, sannan ta ɗaga musu hannu ta nufi gidansu. Ƙofar shiga gidan ta buɗe, ta shiga, sannan ta rufe ƙofar tana cire takalman dake ƙafarta, ta saka wasu dake aje a bakin ƙofar, sannan ta nufi falon gidan dake a farkon gidan.
“Assalamu alaiki ya Yumma!”
Ta yi wa mahaifiyarta dake zaune a falo tanq cin fruit sallama, fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma tsohuwar matar na ganinta ta fara murmushi, Ivana ta risina ta sumbaci kan mahaifiyarta, sannan ta zauna kusa da ita tana cire jakar guitar ɗin dake bayanta, tare da ajeta a gefe, ta gyara gashin kanta tana faɗin.
“Shu yalli ɗabaktil yaum ya Yumma”
(Yumma yau me kika dafa?)
Mahaifiyar Ivana me suna Khadija, wadda Ivana da yayarta Hala ke kiranta da Yumma tace.
“Shish taouk”
“Ba na jin yunwa sosai, dan mun tsaya a Al Fayrooz lounge mun ci abinci tare da su Arman, dan haka ki zuba min kaɗan”
“To”
Cewar Yumma, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗinsu dake haɗe da falon, dan wata gajerar katanga ce kawai ta raba kitchen ɗin da falon, komai dake cikin falon ba shi da tsada, kuma kayane irin na da, dan a cikin gidan aka haifi Ivana da yayarta Hala, wadda a halin yazu ta yi aure, har da yaronta guda ɗaya.
Mahaifinsu ya rasu tun da ƙarancin shekarunsu, hakan ya sa suka taso ba su san shi ba sai Yumma, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma ba su ɗauki rayuwa da zafi ba.
Ivana ta miƙa hannu ta ɗauki apple ɗin dake cikin wani bowl a kan center table, tana shirin fara cin apple ɗin idonta ya kai kan wata magazine dake aje a kan center table ɗin. Sai ta aje apple ɗin ta ɗauki magazine ɗin da hannunta na dama, yayin da take saƙala gashinta a bayan kunnenta da hanunta na hagu.
Ba komai ya ja hankalinta zuwa kan magazine ɗin ba face hoton dake jikin bangon magazine ɗin. Gani take kamar ta san mutumin cikin hoton, shiru ta ɗan yi tana son tuno inda ta taɓa ganin mutumin. Fuskarsa a yammacin yau ta da ta ganshi ta haska a cikin kanta. Ƙwarai kuwa, shi ne mutumin da ta haɗu da shi a Cavo Espresso Bar, sai ta shiga karanta bangon magazine ɗin. ‘Business week’ shi ne babban maudu’in abin da magazine ɗin ta ƙunsa.
Sai ta zarce zuwa kan sunansa dake gefe guda, Sayyid UWAIS FAZIL… Ta sake kallon fuskarsa tana furta sunan a kan leɓenta.
“UWAIS!”
Ta furta sunan ba tare da ta ji komai a ranta ba, saboda ɗan adam ba shi da ikon hango abin da ke tunkararsa a gaba, ba shi da masaniyar abubuwan da za su faru da shi, sai na wanda suka riga suka faru da shi.
“Ki ci Shish taouk ɗinki”
Yumma ta faɗa tana aje mata Shish taouk da ta zuba a cikin plate, Ivana ta aje magazine ɗin tana murmushi, sannan ta kalli Yumma tana ɗaukan plate ɗin, ta soma cin abincin tana bata labarin yadda live performance ɗin da suka je suka kalla yau ya kasance.
Bayan ta gama cin abinci ta nufi upstairs, dan gaba ɗaya ta gaji bacci take ji, ƙofar ƙaramin ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki tana kallonsa kamar baƙonta. Ɗakin sam ba shi da girma, amma ya ɗauki duka kayanta da take ajewa a ɗakin, akwai gadonta ɗan siriri na kwanciyar mutum ɗaya.
Wanda ke ɗauke da baby pink duvet, sannan akwai pillows manya da ƙanana, sannan akwai wardrobe da ba ta cika faɗi ba, akwai kuma desk ɗinta, sannan dressing mirror. Mafiya yawan abubuwan dake ɗakin pink cokor ne, hatta da stikern dake jikin bango pink ne.
Miƙa ta yi tana rataya jakar guitar ɗinta a sama, inda ta saba ajeta, sannan ta nufi bathroom, ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, wardrobe ɗinta ta buɗe, ta ɗauki mayafi a ciki, ta yafa a kanta, sannan ta tada sallah a kan center carpet. Sai da ta gabatar da sallahr isha, sannan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa night wear.
Tana hamma ta bi lafiyar gado ta kwanta, tana rayawa ranta cewa me ake da rayuwar da babu gadon bacci, ita a duniyarta babu abin da ya fi birgeta sama da lallausan gado, dan ko a kan sofa ba ta iya bacci.
_________________
_Ehem! Ehem! Ehem!_
File Name | Juyin Kwado… Hausa Novel Doc. |
Title | Juyin Kwado Complete Novel |
Author | Salma Ahmad Isah |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 01/01/2025 |
File Size | 200KB |
Format Size | TXT |
Book Price | ₦800 |
Phone No | 08130172702 |
Download Juyin Kwado Complete Hausa Novel Document By Salma Ahmad Isah
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.