Novel Document

Inda Rai Book 2 Complete Hausa Novel Document

Inda Rai Book 2 By Aisha Aliyu Garkuwa

Description/Story:

Inda Rai Book 2 Complete Hausa Novel Document Written By Aisha Aliyu Garkuwa

 

Description

Yar uwa kinsan illar dake tareda infection kuwa,to bari kiji kadan daga cikin illar da infection yake da ita,kinsan cewa infection yana hana haihuwa,yana hana ma’aurata jindadin mu amala,yanasa warin gaba kowane irin tirare kika sa bazai hana wannan warin fita daga jikin kiba fitar farun ruwa kaikayin gaba tusar gaba duk suna daga cikin illar da infection yakewa lfyr ki.
Ina masu fama da ulcer, Asthma,sickle, ina matar dake fama da fibriod, matsalar rashin haihuwa ko bushewar jiki da fata haddake mai son hibs da breas ina uwar gida maison faranta ran oga a othe room kema ba abarkiba jawarawa da yanmata ku garzayo kuma ku kwada ku gani da ikon Allah da izinin Allah munada VIP chair akwai blood circulatory machine kedai kira number nan domin karin bayani 07035275119 ko kiyi joining group dinmu dan gani da ido👀 sai kunzo ngd https://chat.whatsapp.com/LqcXIrhogcQC1iLdGGNJcZ

Spjg
“Ban fahimci me ɗaya kake son bayyana mana ba Tajudden kana neman mu baka izinin fara neman Mamana ne ko,ko kana gabatar da soyayyar kane? Ko neman Aurenta kakeyi gaba ɗaya!?”.
Ya kai karshen maganar yana kallon Taj kallon cikin ƙwayar Idanu saboda tuna cewa shin meyesa Tajuddeen bai zo da iyayensa ba saboda duk cikin falon baiga ɗaya daga cikin wanda zai iya kasancewa mahaifansa tunda dai yasan shi ɗan ƙasar Ethiopia ne waɗanan kuma duk yasan mutanen ƙasarmu be kuma sanannun ma, sai kuma ya juya idanunsa ya kalli Tajj jin yana cewa.
“Duk abu uku nake haɗewa awaje ɗaya Uncle Bello idan zan samu duk abinda kuka min akai ku mallaka min Ishmah shine burina da Fatana shine kaɗai abinda zai samar min nutsuwa ita kaɗai ce zata zame min tsagi da zai cike gurbin da na rasa, itace kuma zata zeme min inuwa da zan samu in fake”.
Cikin rashin walwala da jin wani irin kallo mai nuni da bincika yace.
“Kuma sai gashi banga waliyyanka ba ko kuma ince magabatan kaba”.
Cikin sauri Sheikh Tijjani Taju Usman Bauchi yai gyaran murya wanda shine Babban ɗa ga Sheikh Tajuh Usman yace.
“Gamu nan mune matsayin waliyyansa kuma magabatansa kuma shaƙiƙansa”.
Anutse Abba ya gyara zamansa tare da sakin wani lallausan murmushi.

Atare suka juya suka kalli Sheikh Tajuh Usman Bauchi jin yana cewa
“Ni da kaina zan wakilci Aurensa sannan in daura auren zan kuma yi farin ciki idan kuka bashi Auren Ishmah zan kuma shugabanci al’amarin in shige masa gaba akan komai saboda matsayinsa mai girma ne awajena nima kuma matsayina halattaccene a wojensa”.
Cikin sanyi suka sauƙe numfashi sai kuma suka kalli juna tare da yin ƙasa da kansu jin Dottijon nayi musu kalamai masu kama zuciya.

Cikin sanyi suka fara yunkurin miƙewa tsaye jin Sheikh Taju Usman Bauchi na cewa.
“Ku tashi mu tafi saboda lokacin sallah ya ƙara to”.
Daga nan suka fita suka bar gidan…

Acan cikin gida kuwa Ishmah ce zaune a falo yayin da akwatina set biyu ke gabanta set ɗaya Maroon color set ɗaya Milk color suna zaune ta juya ta kalli Aunty Nana tare da jan gajeren tsaki saboda wani irin iska mai sanyi da take ji yana ratsa jikinta haka nan kawai take jin zuciyarta yana mata sanyi haka gangar jikinta yayin da jikinta ke amsar baƙon yanayi wanda yafi kama da samar da nutsuwa da kwanciyar hankali wanda batasan sanadinsa ba cikin sanyi tace.
“Aunty Nana ki gani fa har yanzu babu wanda yazo kuma fa sun san munyi dasu ƙarfe uku zamu tafi mu kai kayan saboda mu samu kafin huɗu mu dawo muyi sallar la’asar agida kuma har yanzu basu zoba”.
Juyawa aunty Nana tayi ta kalleta tare da cewa.
“Wallahi fa nima abinda nace kenan?,Shiyasa ma kika ga nayi abinci da yawa saboda ina tunanin za’a zo muci abincin rana ne anan kafin mu tafi”.
Maryam dake shigowa ne ta karbi maganar da cewa.
“Ai dama sai da nace miki Kada kiyi wani abinci ki wahalar da kanki saboda Nasan da wuya azo da wuri kasancewar yau juma’a kuma in munje can ma Nasan abubuwan da zasu bamu in mun dawo shi za’a cicci abinci anan shiyasa ni ban shiga kitchen Bama”.
Ta ƙare maganar tana zama gefen Ishmah.
Dariya Rahama dake fitowa daga bedroom tayi tare da cewa.
“Ke dai Aunty Maryam kina nan wani lokaci idan mutum yace Miki marowaciya bai kyauta ba kina nan kamar Gajimare saboda kyauta, wani lokaci kuma in kinyi magana kamar ta marowata”.
Murmushi Maryam tayi kana tace.
“In kinga dama ma kice ni marowaciya ce”.
Dariya Rahama ta sanya tare da faɗin.
“Kuma kona faɗa babu yanda zakiyi dani tunda nice Autah shiyasa nake fadan abinda naga dama kuma in kwana lafiya”.
Murmushi sukayi dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamar Garkuwa.

Cikin jin daɗi da farin ciki Ishmah ta miƙe tare da amsa mata sallamar kana ta nufi Kofar Falon ta rungumeta fuskarta ɗauke da Murmushi tace.
“Sannu da zuwa kece kika riga kowa fara zuwa”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Aikuwa dai na riga kowa zuwa dama cewa nayi sai an saƙƙo Daga sallar Juma’a in zo”.

 

File Name   Inda Rai 2… Hausa Novel Doc.
Title    Inda Rai 2
Author    Aisha Garkuwa
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    05/05/2024
File Size     263Kb
Format Size    TXT
Phone No   09097853276
Download Inda Rai… Book 2 Complete Novel Document By A’isha Aliyu Garkuwa

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button