Hausa novels

Fentin Zina Page 2 Hausa Novel

Kuna tafe ashe?Eh inna, ta fada tana ajiye basket din abincin ta sauko jakar bayanta na kayan shureim data shiryo masa.Kallon jakar inna tayi ta dubeta don neman karin bayani.Hum inna kibar wannan maganar mu shiga ciki kafin muyi ta.Toh muje inji bazan iya jira ba.Suka shiga inna tana rike da shureim ita kuma rungume da jaka da dayan hannun dayan kuma dauke da basket din abincin!Bayan sun zauna inna ta dubi ‘yar tata cikin natsuwa tace fada mun meya faru naganki da jaka, ina fatan lafiya dai ko?Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa don tana kunyar hada ido da mahaifiyarta tun bayan da wannan jarabawa ta fada mata.Inna kamar dai yadda aka saba kinsan zaman shureim a tare damu bawai da son Abdul bane nadai nace ne zan rike dana a gurina toh matsaltsalu suna ta faruwa sam baya son shureim baya kaunar bude ido ya ganshi sannan duk sa’adda zai ganshi ya gilma cikin falon nan bakar magana ce zata dinga biyowa bayan hakan, jiya yaya yusuf yazo gidana kinsan ya jima baya nan.Inna ta gyada kai tace hakane!Ameena ta numfasa ta ci gaba.Bayan mun gaisa bai wani zauna ba yace zai tafi na rakashi iya kofar falo daidai zai fita gate Abdul ya dawo shine fa ya hauni da fada yana hargowa har harbin shureim da kafa yayi saida ya fadi kasa yana zargina da yaya yusuf inji shi, ta karashe tana fashewa da kuka tana fisgar numfashinta da yake barazanar daukewa.Kiyi hakuri kinji! Ko wani bawa da tashi jarabawar kiyi shiru ki share hawayenki,Share hawayen tayi tana sauke ajiyar zuciya.Yanzu ke wane shawara kika yanke ina dai fatan ba yaji kike kokarin yi ba?A’a, ta girgiza kai, ko kadan bazanyi yaji ba inna nadai yanke shawarar dawo da shureim hannunku ne zuciyata bazata iya sabawa da yanayin ba kofa dakina Abdul ya hanashi zuwa sai kace bani na haife shi ba inna? Yanzu na dawo da rikonshi gareki da baba malam ina fatan inna baza kuki rike mun shi ba.Inna tana murmushi tace, yaro kenan toh ai ko dacan idan baki manta ba kece kika ki zaman shi anan ke lallai ga wacce ta iya haihuwa ko kada mu cutar miki dashi.A’a inna ba haka bane kiyi hakuri.Toh shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.Ameen inna ina fateema ne kam nadai san ba makaranta yau.Na aiketa yanzu ma zaki ga ta dawo don ba nisa.Sallamar fateema ya katse su.Ameena tace inna kinji ‘yar halak taki ambato.Murmushi inna tayi fateema ta shigo da sallama tana ganin Ameena tayi tsalle ta fada jikinta tana murna Ameena tace tana ture ta, ni kam dagani kada ki balla mun kafa.Ayya adda nayi kewar kine fah, ta fada da shagwaba.Fateema ai nima nayi kewar naki amma wannan tsallen sai kiji mun ciwo ai.Shureim…..Fateema ta fada tana jawoshi jikin ta tace, nayi kewarka shureim dina kyakkyawa na.Mummy ina kwana! Cewar shureim yana dariya da kokarin boye fuska wai shi a dole yaji Kunya.Iye ni daka raina ai baka gaisheni ba zaka ga mai baka tuwo da dare.Ai Mummy am Zata bani, Ko mummy? Ya fada yana kallonta.Ta gyada mai kai haka ne yaron mummynshi.Sun taba hira sosai kafin akayi kiran sallahr azahar duk suka mike sukayi alwala sukayi sallah.Ameena tace ni inna zan wuce inada aiki a gida kuma bana so harya dawo ban gama ba.Gaskiya ne kam gara ki hanzarta Allah ya muku albarka.Ameen inna idan baba malam ya dawo ki gaishe mun dashi na kira wayarshi jiya da yau bata shiga ba.Ina jin matsalar service ne don garin daya je ba’a cika samun shi ba sai in shine ya kira amma nasan kila sun taso domin yau dama yace zasu dawo.Allah ya dawo dashi lafiya, ga abinci nan ba sai kunyi girki ba da yamma sai kuci wannan din tunda zai ishe ku.Toh an gode Allah ya saka da alkhairi amma da kinje kin gaida goggonku kafin ki wuce.Toh inna idan na fita gaba daya sai fateema ta raka ni muje amma ni kinsan bana son zuwane saboda maganganunta daga mun hankali kawai sukeyi inna.Toh ya zakiyi Ameena jarabawace dai babu yadda zamuyi abunda ya faru ya riga ya faru sai dai mu tari gaba.Toh shikenan barin kimtsa sai inyi haramar tafiya.Wannan yaron dai bazaiyi kuka bako?Bazaiyi ba domin yama fi son zaman nan din dacan gidana.Inna ta kalle shi tana mai tausayin halin da yake ciki.Kamar yadda ta fada din sunyi sallama a gidan suka tarar da goggo tana tsakar gida tana gabatar da alwala sai yanzu zata yi sallahr azahar.Watsawa Ameena wani mugun kallo tayi ta tabe baki. Meya kawo wannan dattin gidana ta fada tana nuna Ameena da shureim da hannu.Fateema tayi karfin halin fadin dama goggo zuwa tayi ta gaishe ki yanzuma tafiya zatayi.Bana so ta rike gaisuwarta kurum zata kwaso kazanta ta kawo mun gida indai gaisuwace na yafe aje umma ta gaida assha, gata wata sum-sum kamar ta kwarai amma munafuka ballagaza.Ameena data kasa rike kukanta tayi waje da gudu bata ko tsaya jiran fateema ba tana fita ta dauki hanyar da zata kaita ainahin bakin titi tana tafiya maganganun goggo suna mata dirar mikiya a kwakwalwarta tana sharar hawaye da haka har ta isa bakin titin ta tari napep ta fada ko ciniki bata tsaya yi ba ta mai kwatancen inda zai kaita.Fateema wani kallo tayiwa goggo taja hannun shureim suka fita, goggo ta tabe baki tace a dake dai bazan daku ba ko ni nasa ta je tayi abun kunyar data yi din.Fateema gida ta wuce ta sanarwa inna abunda ya faru, batayi mamaki ba daman tasan za’a rina sai taji dama bata tura Ameenar taje ba.Kuma wallahi inna adda bazata kara zuwa gidan goggo ba wulakancin ya isa haka taji da abunda ke damunta koda matsalar mutane.Nidai bance ba kima bar wannan maganar.Fateema tayi shiru tana kumbure-kumburen fuska.Ameena Koda ta isa gida a falo ta yada zango tana sakin ajiyar zuciya da tunanuka fal a ranta.Ganin tunani bazai fishsheta ba sai ta mike ta Shiga daki ta sauya kaya ta fito ta nufi kitchen duk jikinta a sanyaye tana jin babu dadi na rashin Adam a tare da ita.Cikin sanyin jiki ta kammala duka ayyukanta tayi wanka ta shirya cikin wani purple lace da aka yiwa dinkin bubu gown, sosai kayan suka zauna a jikinta suka mata kyau ta fesa turaruka ta jefa chuwing-gum centre fresh a bakinta ta ciro takalmanta masu kamar na sarauta ta zura kafafunta a ciki ta komo falo ta zauna tana danna wayarta duk da t.v na aiki bata damu data kalla ba sai aikin chart dinta kawai take lokacin magriba ta kusa don haka ta duba ko yana online ai kuwa tayi sa’a yana nan online murmushi tayi na jin dadi don dai tana matukar son mijinta, sallama ta mishi tare da hoton zuciya tana fadin yadda tayi kewar shi.Ya maido mata da ansa ya kusa shigowa ta tsammace shi.Ajiyar zuciya ta sauke kana tace ya Allah ka daidaita mun mijina bisa tafarkin addinin musulumci ka kare imaninsa ka tsarkake zuciyar sa ka hana shi saba maka.Lumshe ido tayi daidai lokacin da ake kiraye kirayen sallah already da alwalarta don haka anan falon tayi sallah koda ta idar bata tashi ba tayi azkar dinta na maraice tana a haka ne taji karar motar shi a tsakar gida don haka ta nade sallayar da hijab dinta ta adana su ta fita zuwa kofar falon tana kallon shi, kashe mata ido daya yayi ta taka a hankali saitin kofar shi ta bude ta rankwafo ta sumbace shi a kumatu tace, barka da zuwa mai mulkin zuciyata hasken idaniyata abokin rayuwata ina fatan baka wahala mun kanka da yawa ba?Ya jawota jikinshi yana sunsuna wuyarta ya dago ya dubeta yace, irin wannan salo ai zaki sa na rasa hanyar falon ma baki daya meenalita ina son ki ni kaina bansan iya adadin soyayyar da nike miki ba dan Allah ki tayani son kanki kinji, ki kuma rika mun uzuri akan kishina sam bana jurar inga wani ya rabe ki sai inji zuciyata tana zafi sai inji na kasa sarrafa kaina kiyi hakuri akan komai ni dai ina sonki wannan shine!Wannan karatun ka dade kana biya mun shi ruhul jasad nima na yadda da irin soyayyar da wannan basaraken mijin yakewa matarsa sai dai nima ina so ka rika bincikar abu kafin ka mun fada ka sani bana son fada ban saba da fada ba kuma bana jin zan iya sabawa ta fada tana tura baki.Wannan bakin ya iya shagwaba, ya fada yana jan lebbanta.Ture hannun shi tayi ta mike taja dayan hannun nashi tace ni ka taso mu shiga ciki sanyi yana kadawa sosai.Ai wannan yanayin yafi dadi da lamarin soyayya.Naki din nidai muje dan Allah, ta fada tana langwabe kai.Fitowa yayi daga cikin motar ta karbi jakar sa ta rataya ta ciro hularsa tasa a kanta tace ya ka ganni? Ta rike kugu.Cancarascas ya fada yana murmushi lokacin da yake fitowa daga motar gaba daya ya kama hannunta bayan ya rude motar suka shiga cikin falon.Dakin shi direct suka nufa ta fada toilet ta hada masa ruwan wanka ta fito yana zaune saman gado ta isa gare shi ta kama hannunshi yako mike ta jashi zuwa toilet din.Ita ta taya shi yayi wanka dukda yaso ya dan latsata a bayin amma taki bashi dama karshe ma guduwa tayi daga bayin ta barshi a zuciyarta tana cewa haka kawai bazaka jaza mun ba.Ko kafin ya fito ta fitar masa da kayan da zai saka tayi waje ta dan kara duba dining din ko da bukatar karin wani abu.Shiryawa yayi cikin kayan data fito masa dasu lokacin ana kokarin tada sallah a masallaci da yake akwai a kusa da gidansu.Anan falon tayi sallahr ta bayan ta idar taje ta same shi yana kwance yana danna waya ta karaso kusa dashi.A bazata yajita kusa dashi yayi saurin fita a WhatsApp din daya shiga yana murmushi.Kayi sallah ne? Ta tambaye shi.Banyi ba amma yanzu zanyi, ya bata amsa.Amma kana ji ana kiran sallah fa ruhul jasad gaka ga masallaci amma ace kayi sallah a gida? Sam hakan baya mun dadi.Shiru yayi bai tanka ta ba hakan yasa ta mike tace muje dining food is ready.Ok! Yace yayinda ya mike still rikeda wayar shi babbar.Kujera masu fuskantar juna suka zauna tayi serving dinsu a plate guda daya ta zubawa kowa lipton a cup domin kusan dabi’ar suce shan lipton kamar jikokin buzaye.Har suka gama baiji duriyar shureim ba ya lura da hakan tun dawowar shi saidai yakiyin magana ne ya bari sai anjima sunzo kwanciya ya tambayeta.Haka ko akayi saida sukayi shirin kwanciya tukun ya dubeta.Ameena tunda na dawo na lura da rashin motsin yaron nan a gidan nan ko lafiya.Ta dago da mamaki ta dubeshi batayi tsammanin zai tambaya ba kuma daman batayi niyyar fada masa ba sai dai tunda ya tambaya zata fada masa din.Na baroshi a gidan inna dazu dana je.A wani dalilin? Ya kara tambaya a gimtse.Bata damu da yanayinsa ba tace, babu wani dalili nadai kaishi can dinne kawai inaga kamar zaifi samun natsuwa sannan da kanshi ya rokeni in mayar dashi can.What!!?Ya mike a fusace, wato yaro ya yanke hukunci ke kuma kin biye masa ba tare da neman shawara ko izinina ba saboda baki daukeni da daraja ba ko.Ta dube shi da mamakin meya shafe shi kuma? Mutumin daya nuna ya tsani yaron to meye ma damuwar shi da duk inda ka zata kai shi, ta cije tace kayi hakuri ba haka bane.Toh yaya ne? Nace yaya ne? Domin ki nuna gazawata a gareki da danki don ki gwadawa iyayenki kasawata kika dauke shi kika maida musu shi can kisa a zageni a gari, ke kenan ba’a isa a miki fada ba inkinyi laifi sai kin nuna ke kinfi kowa?Tanaso tayi kuka, hawaye suna neman zubowa amma ta danne ta hana su zubowa wannan dalilin nema ya hanata magana.Dole kiyi shiru ai tunda harya tsallake iya kanki kin koyawa danki tsanata bai daukeni a bakin komai ba, ko baki gode mun ba ai bazaki tsine mun ba nida bansan ma waye uban dan naki da kike tutiya dashi ba amma duk da haka nayi hakuri na rufa muku asiri daga ke har shi sai kuma na zama ba komai ba?A fusace itama ta tashi kanta na juyawa tana ganin dishi dishi ta daka mai tsawar data gigita shi…..YAYA KUKA JI WANNAN SALON?SHAR£…..LIKE…….COMMENT…..matar majeedadi✍️

Back to top button