Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 74 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

Cigaban page 74

Murmushi su ka saki gaba ɗayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets ɗinsu suna neman ƙofar nan, Angel tana ruƙe da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haɗa akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman ƙopar ba inda basu ɗaga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet ɗinsu saida batul da Deeja suka haɗa ƙarfi wurin ɗaɗɗagota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka ƙasantama Ashafe Yake babu wata ƙofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko’ina Ciki da bai na sashen toilet ɗinsu saida suka bincika amma babu ƙopa, A ƙarshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waɗanda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garƙame da kwaɗo, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba ɗaya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za’a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda ɗaga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buɗe tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buɗe tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baƙara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A ƙarshe da su ka galabaita, don dole suka haƙura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu.

A saman floor na sashen toilets ɗinsu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka fuskanci juna, Sai haki suke Yi kamar waɗanda suka Sha Gudu, Baccin wahala ne Ya ɗauke su mai nauyi, duk sun ɗaɗɗaura kawu nan su saman kafaɗun Junansu, Baka Jin sautin komai saina minsharin su.

Daga cikin ɗakin su muryar Jamimah ce ke ta ƙwala masu kira, babu mai jinta, farkawarta kenan daga bacci, Hankalinta atashe ya ke ganin babu su asaman gadajen su, saukowa ta yi daga saman gadonta, tare da nufar Sashen toilet ɗin su, shigar ta keda wuya ta yi arba dasu zazzaune suna bacci, Mamaki ne ya kama Jamimah, ganin su anan maimakon saman gadajen su, ƙarasa shiga ciki ta yi a yayin da ta ke leƙa fuskokin su don taga Idan baccin gaske su ke yi ko kuwa tsokanar ta su ke Yi, Kallon ƙurulla jamimah take binsu dashi, adai dai saitin fuskar Angel ta tsayar da eye balls dinta, muryar ta ƙasa ƙasa ta furta”My Genie” shiru bata amsa mata ba, da ta fahimce cewa dagaske baccin su ke yi, Sai ta zauna tare da kwantar da kanta saman laps ɗin Angel ta lumshe idanuwanta kamar maiyin bacci, Tsawon Lokaci babu wanda ya farka, Sun saki baki suna bacci.

A firgice Parveen Ta farka tana ambaton”Nagansu wlh nagansu” Sautin muryarta ne Ya farkar dasu Angel a fujajen su ka wawware Idanuwansu masu ɗauke da bacci suna kallon Parveen, Har suna haɗa baki wurin tambayar Ta”Makullan kika gani? a ina su ke”? Yawu ta haɗiya tana faman Zare ido, tare da ƙare masu kallo, Sam babu natsuwa atattare da Ita, Muryarta Ashaƙe tace”Kamar mafarki na yi nagan su a cikin ƙasar tukunyar fulawar nan, Makullan……..”

Tun kan ta ƙarasa maganar Zumbur suka mimmiƙe har suna bangaje juna wurin shiga toilet ɗin Saboda tsabar sauri, Jamimah batasan Kan me suke magana ba, binsu kawai ta ke Yi kamar bindi.

A Gaban tukunyar fulawar Su ka zuzzuƙunna, Deeja da batul na ƙoƙarin tsoma hannu cikin ƙasar Angel ta dakatar dasu ta hanyar yi masu magana”Bana so acire furennin nan saboda raine dasu, Ina gudun kada silar cire su su mutu……” Bata kai ƙarshen maganar ba, Deeja ta tari numfashinta”A halin da muke cikin yanzu bamu buƙatar furanni, ganinsu ma ƙara tayar mana da hankali ya ke yi, don haka cire su zamuyi” ba tare da 6ata lokaci ba, Mutun Biyar ne su ka tsoma hannayensu Ciki, duk suka tsige furennin tare da jefar dasu ƙasa.

Hankalin Angel sam ba akwance ya ke ba, Saboda ta yi believing da furannin rai Ne dasu, Ko da su Deeja su ka jefar dasu Ƙasa da sauri ta zuƙunna ta sanya hannu ta ɗauki furen daddynta dana Aunty aneelerh hada ƙaramin furennin nan, Har zata miƙe idonta Ya sauka Akan Dogon furen nan da ganyen shi ya koma baƙi, yanzu ya koma asalin colour din shi, Punch pink Ya ciza sosai, hakanan ta dinga jin gabanta Na faɗuwa, Ayayin da ta ke kallon shi, Kasa miƙewa ta yi har saida ta ɗauke shi ta hada da sauran furennin da ke a hannunta, tukunna taji Hankalinta Ya kwanta.

Fasa ƙara Azeeza Tayi tare da faɗin

“Mun samo shi! Gashi nan Makulli ne” jin muryarta Yasa Angel matsowa kusa dasu, Hankalin kowa Akan hannun Azeeza Ta damƙe wani abu dake a nannaɗe Cikin ƙasa, Wani irin farin Cikine Ya bayyana akan fuskokin su, Tun kafin Ta buɗe masu tafin hannun nata su ga menene.

A hankali Azeeza Ta ware tafin hannunta, Ta soma kakka6e ƙasar da ke nannaɗe da abunda ta damƙo, ko da ta kammala Kakka6e ƙasar jikin shi, Murnar da su ke yi ta koma Ciki, Ashe jijiyar fure ce, tsabar takaici Yasa kowaccen su ta dafe goshin ta da hannu, Ƙululun bakin Ciki Ya tokare masu maƙoshin su, Ji su ke kamar su rufe Azeeza da bugu, don ba ƙaramin sanya rai su ka yi ba, Kamar masu zaman makoki Haka suka zazzauna Cikin toilet ɗin Abun duniya ya ishe su, Jamimah ce kaɗai a tsaye ta Ruƙe qugu tana kallon su

“Wai ni kun barni aduhu me ake nema ne? Duk kun cire mana furennin mu, Genie Ki fada mini,” hada ƴar shagwa6arta

Ɗago da ido Angel ta yi tare da kallonta kafin ta miƙa mata hannu”Zo nan” matsawa ta yi kusa da ita, Ta sanya hannu biyu ta janyota zuwa jikinta

“Yaushe kika farka daga bacci bamu sani ba”? Yatsina fuska ta yi”tun ɗazu na farka ina ta kiran sunayen ku babu wanda ya amsa mini, Sai da nazo sashen toilet tukunna nagan ku kuna bacci, ni kun barni a ɗaki”

Harara Azeeza ta watsa ma Jamimah kafin ta soma kwaikwayon maganarta, salon jan faɗa, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba.

“Yanzu fa ba lokacin Yin nishaɗi bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu ɗin dai mune makullan, Ƙofa ce kaɗai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu ɗauka cewa mu ɗin makullan Wata ƙopa ce guda ɗaya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we’re the keys da zamu buɗe ƙofar” Angel ce ta yi jawabin

“Ni kuma aganina akwai makullan, Ma’anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haɗa hannu don mu gano su, Sa’annan waɗannan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin ƙofar tana A cikin su,” Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa ƙwaƙwalwa.

“Ni ma nafi hasashen acikin su ne za’a samu ƙofa, saboda su kaɗai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen ɗakin nan” Acewar Hibba.

“Ku dakata, Kada Mu ɗaura buri akan waɗannan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai ƙarƙashin gadajen mu, Da kuma ɗakin tsohuwa Tamira” Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace”Ai babu ta yadda za’ai mu iya buɗe ɗakin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga ɗakin ba, saboda kullum agarƙame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga”

Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faɗa kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko’ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, Miƙewa tayi tsaye kamar malami agaban ɗaliban sa, A tsanake ta soma magana.

“Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano ƙofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano ƙofar bayan mun ƙi haɗa kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota”? Ta jefa masu tambayar tana ƙare masu kallo, duk sunyi ƙuri da idanuwansu,

“Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buƙatar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faɗa mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, Miƙa ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa”Ruƙe mini su My little sis” Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta.

“Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daɗin Jikin mu brain ɗinmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala Yin wanka Giants sun kawo mana Ganye, Idan mu ka Ci mu ka ƙoshi Sai mu fara wasan Ƴar 6urun 6urun kamar yarda na tsara mana, don kada ayi zargin wani abu tunda suna kallon duk wani moving ɗin mu”

Tun kan ta ƙarasa yin maganar, murmushi ya bayyana akan fuskokin su, gaba ɗaya sun yi amanna da maganarta, without wasting time kowan nan su ya miƙe tsaye, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga cikin toilet ɗin, Ya rage saura Angel da Jamimah, Kallon Juna su ka yi atare suka sakar ma Juna murmushi”My Genie, Ƙofar da zamu gudu ku ke nema mana?

Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, Dariyar Farin Ciki Jamimah ta saki har fararen haƙoranta sai da su ka bayyana, Bin ta da kallo Angel tayi dariyarta ba ƙaramin burgeta ta yi ba, sai da ta tsagaita da yin dariyar ta kuma cewa”Genie Zamu Koma Gidan ku da zama ko? Kuma can babu giants sannan ba zamu ƙara cin ganye ba ko”? Maganar da jamimah ta yi ba ƙaramin ta6a mata zuciya tayi ba, yadda suka ƙwallafa rai akan son zuwa gidan daddynta ba ƙaramin karya mata zuciya ya ke yi ba, duk idan ta tuna cewa ba lallai bane su samu damar tsira dukkan su ba koda ace sun samu ƙopar, wata’ƙil ma babu wata ƙofa tunda hasashene kawai suke yi basu da tabbaci akanta.

“My genie kin yi shiru, pls ki amsa mini, inaso inji a ƙagare na ke,” yadda ta ke yin maganar farin cikine tsantsa akan fuskarta, tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, sam ta kasa buɗe baki ta amsa mata.

“Genie Am talking to u pls ki amsa mini, idan ba haka ba zan cinye furannin da ke a hannuna” Ta yi maganar tare da yin kamar zata cinye su, Nauyayyiyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”Kada mu 6ata lokaci My little sis, Zan yi maki wanka amma kafin nan ki taya ni mu mayar da ƙasar tukunyar nan sai mu mayar da furennin” Amsa mata tayi da toh.

Ba tare da ta ƙara tambayar Angel ba, Atare su ka zuƙunna jamimah ta kwantar da furennin a ƙasa, kafin su ka sanya hannu Suna ɗibar ƙasar da ke a ƙasa suna zubawa cikin tukunyar fulawar bayan sun kammala Angel ta ɗauki furennin ta tsirasu Cikin ƙasar, har ta yunƙura zata miƙa Karaf idanuwanta su ka sauka akan wasu furenni guda biyu da ke yashe ƙasa, ƙura masu ido ta yi tana kallonsu Jamimah sai magana take yi mata amma sam bata Jinta,

Wani irin faɗuwar gaba taji tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, a matuƙar ruɗe ta ke kallon Furennin, Ganyen jikinshi ya bushe ƙasa ya mutu, bakomai ya faɗo mata araiba face Majnoon da Unaiza da suka rasu, Zazzare idanuwanta tayi Hannunta ɗaya dafe da ƙirjinta, Nan take ta fahimci cewa furennin su ne suka mutu, Tun da basa araye that mean sauran furennin dukkan su rayukan ƴan uwansu ne akai, A hanzarce ta ɗaura eye balls ɗinta kan Dogon furen nan Muryarta Na rawa ta furta”DA…NISH!”

Zungurar hannunta jamimah tayi hakan yasa tayi firgit ta dube ta

Fuskarta a ɗaure tace”Kin shanyani Genie, ko ba za ki mini wankan bane? Inje inyi da kaina” Yawu ta haɗiya zuciyarta duk ba dadi, Furen Danish ya tsaya mata aranta, musamman da ta tuna da Lokacin nan da ta tarass Ganyayyakin jikinshi Sunyi baƙi sosai, tana ji aranta cewa wani mummunan abune ya faru dashi wanda silar hakan yasa furen shi canza launi,

“Genie!!” jamimah ce ta ambaci sunanta da karfi ganin ta ƙara shiga zurfin tunani, Numfasawa tayi tare da ruƙo hannun Jamimah, Cikin sanyin murya tace”Am sorry Muje inyi maki wankan” Tayi maganar tare da janta zuwa gaban fanfo, Ta cika bokiti da ruwa ta ɗauko kwandon soso da sabulu, Bayan ta cire mata kayan Jikinta ta ɗaura su saman igiya, wanka ta ke yi mata amma hankalinta gaba ɗaya yana akan dogon Furen nan, A shiririce ta gama Yi mata wankan hada sumar kanta ta wanke mata, bayan ta kammala bata mayar mata da uniform ɗin jikinta ba, saboda sun yi datti, sai tace mata ta koma ɗaki ta Ta lullu6e da bargo kafin kayan da zata wanke mata su bushe saita maida su a jikinta, bayan fitar Jamimah daga Cikin toilet ɗin, komawa Angel tayi gaban tukunyar fulawar ta zuƙunna tana ƙarewa Dogon furen kallo, Yayin da zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, Yatsun hannayenta na kerma ta ɗaurasu kan furen tana shafa leaves ɗinsa, Har cikin zuciyarta ta ke jin kamar sumar kan Danish ta ke shafawa, A hankali ta rufe idanuwanta a yayin da ƙwaƘwalwarta ke tariyo mata Rayuwar su ta baya dashi, baza ta ta6a manta Rana ta farko da ta fara Yin tozali da kyakkyawar fuskar shi duk da bata a cikin kwanciyar hankalinta sai da gabanta ya faɗi ganin irin baiwar kyan da Allah ya yi mashi, Tana matuƙar ƙaunar danish, Jin shi ta ke yi tamkar oxygen ɗin da ta ke shaƙa don ta rayu, taya hankalinta zai kwanta? Bayan ta riga da ta gane furen Masoyinta ne, idanuwanta sun yi maraicin shi, zuciyarta sai azalzalarta ta ke akan ta nemo shi aduk inda ya ke, don taga awani hali ya ke ciki, ya idon shi ya ke? Meya faru dashi da har furen shi Ya canza Launi…………”

💔PRISONERS💔

Hankalin su Yaƙi kwanciya Jin shiru Angel bata fito daga Cikin toilet ɗin da ta shiga ba, Tun suna saran fitowarta har sun fara tunanin Anya kuwa lafiya? Ita kaɗai ya rage ta fito su fara wasan Ƴar 6urun 6urun, don su gano inda ƙofar nan ta ke, tun ɗazu Giats sun kawo masu Ganye kamar kullum tare da ruwan zafi, babu wanda yasan da cewa An kawo masu abinci.

Jamimah kaɗai ta rage a cikin ɗakin nasu, kwance saman gado ta lullu6e jikinta da bargonta, Jin motsin shigowar Giants, ta yi hanzarin yaye bargon data lullu6a dashi ta yi ɗaurin gaba har yana jan ƙasa saboda rashin tsawonta, Ahaka ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko kwandon abincinsu taje ta zuƙunna agaban dining Carpet ɗinsu, ta kwashe ganyan Ta zuba masu Acikin kwandon, bayan ta kammala kwashewa, Giants suka Ɗauki farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, Zama Jamimah tayi saman carpet ɗin, ta soma ɗibar ganyen tana Ci yadda kasan ƴar akuya, Kunnuwanta har motsawa su ke yi saboda daɗin da ya yi mata.

“Angel ke fa mu ke jira! Tun ɗazu kowa ya fito daga wanka, Saura ke kaɗai kin shige toilet kin garƙame ƙofa kin barmu a tsaye” Deeja ce ta yi magnar

Batul tace”Ko dai ta fito daga wankan ne bamu sani ba? ta yi tambayar tare da yin saurin juyawa ta shiga ɗakinsu, Jamimah ta hango zauna tana cusa ganye abakinta, babu alamun Angel acikin ɗakin, dawowa ta yi sashen toilet ɗin tun kafin su tambayeta ko ta ganta, ta riga su cewa Na duba bata a ciki,

Nan fa hankalinsu Ya ɗungunzuma

Sunanta suka dinga kira shiru bata amsa masu ba, Atare suka haɗa ƙarfi wurin bugun ƙofar sai dai ga dukkan alamu An garƙame ta da Jamlock, Tamkar zasu fashe da kuka suka dingayi mata magiya akan tayi masu koda tari ne don su san cewa tana acikin toilet ɗin, saboda su samu hankalinsu ya kwanta amma shiru Angel bata tanka masu ba, kamar zasu 6alle ƙofar saboda Yadda su ke kai mata zazzafan naushi da hannayensu, a ƙarshe da suka Gaji agalabaice suka zuzzuƙunna Haɗi da jingina bayansu Jikin bango, jin motsin shigowar mutun cikin sashen Yasa suka kai idonsu ga mai shigowa,

Jamimah ce ta shigo hannunta ruƙe da kwando ta ajiye masu shi a tsakiyarsu, Bakinta a cunkushe ya ke da kingin ganyen da bata ƙarasa taunewa ba ahaka ta ke yi masu magana,

“Ku ci naku ne na kawo maku” kallonta kawai su ke yi, Ta zumbula bargo ajikinta sai ja da ƙasa Yake yi, jin sunyi shiru basu tanka mata ba, yasa ta haɗe girar ta”Ni ba ruwana Idan ba ku ci ba, Ku yunwa zata kama, Sannan Ina GENIE ɗina ta ke? Ko haryanzu bata fito daga wankan bane?

……………….. WHERE’S ANGEL ????

Ku duba page 75 in kun gama wannan, Da anjima zan daura sauran

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

(Mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button