Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 83 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

 


Saman Gadon ta haye ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e,zuciyarta cike da wani irin farin ciki,sai faman sakin kayataccen murmushi take,daƙyar bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,❤

Wuraren sallar asuba,jahad ta farka tare da tashin su hosana,atare bayan sunyi alwala su kayi salla,bayan sun kammala suka koma saman gadon suka dasa wani sabon baccin don bai ishe su ba,

Ƙarasowa hafsat tayi ƙopar bedroom ɗin nasu,jikinta sanye da dogon hijabi,hannu tasa ta ɗan bubbuga ƙopar ɗakin,shiru ba’a buɗe ba,ƙara bugawa tayi,bugun ya isa cikin kunnan sehrish,cikin bacci tace”Wanene”?
Hafsat tace”Ni ce,”
“Kece wa”? Sehrish ta tambaya a yayin da ta miƙe tare da tunkarar ƙopar ta buɗe,Tun daga ƙasa har sama sehrish ke bin ta da kallo don batasan wacece ita ba,amma tabbas ta ta6a ganin fuskarta,kuma jiya taga gifcinta acikin gidan,ga kuma kamannin fuskar Yaya ishaq a fuskarta,
ƴan kame kame hafsat ta shiga yi,muryarta na inda inda tace”am…um..jahad..” katse ta sehrish tayi da cewa”ba ita bace,Ni sunana sehrish,jahad tana ciki tana bacci,”
“In ba damuwa inason ganinta,”
Matsa mata hanya sehrish tayi,ta shiga cikin ɗakin nasu,rufe ƙopar sehrish tayi sannan ta koma ciki itama,sae faman kallon kallo suke ita da hafsat,duk tabi ta kama kanta,kana ganin fuskarta zaka fahimci cewar bata da gaskiya,
Wuri ta samu gefen gadonsu ta zauna,idanunta na akan su jahad da hosana dake ta sharar bacci,
Muryarta a sanyaye tace”in ba damuwa,dan Allah ki tashe su daga baccin inason yin wata magana dasu mai mahimmanci,”
Batare da musu ba,Sehrish tace toh,sannan ta haye saman gadon tana ambatan sunayensu,gami da bubbuga ƙafafuwansu”jahad!hosana!ku tashi ana son ganinku,”
cikin bacci hosana ta buga tsoki tana fadin”dan Allah a ƙyale ni,kar a takuramin,”
Jahad kuwa tuni ta farka,tana faman mutsustsuka idanuwanta,wurga idanunta tayi kan sehrish tace”Wai lafiya”?

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Wannan ce ke son magana daku,”tayi maganar tana nuna hafsat dake zaune,
Juyawa jahad tayi tana kallonta,cike da mamaki ta ambaci sunanta”Aunty hafsat!” sunnar dakai ƙasa hafsat tayi,fuskarta dauke da matsananciyar damuwa,daƙyar ta iya amsa mata”Na’am jahad,”tashi zaune jahad tayi,suna fuskantar juna ta sake ambatar sunanta”Aunty hafsat,”
“Kinsanta ne”? Sehrish ce tayi tambayar,jahad tace”Niko na santa,itace ɗiyar wannan matar da nake faɗa maki wadda ta azabtar da rayuwarmu,kuma wannan itace ta ɗauke mu acikin motarta,ni da Hosana ta kai mu hannun wannan mugun mutumin wanda ya kai mu daji har yayi ƙoƙarin cutar da Hosana,”
Jin wannan maganar yasa ran sehrish ya 6aci,harara ta wurga ma hafsat tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace”Dan Allah malama tashi ki fita ki bamu wuri!bamu son ganinki!mugaye kawai Azzalumai,kun cutar da rayuwar ƴan uwana,saboda son zuciya irin naku,basuyi maku laifin komai ba,Amma kuka tsangwamesu,saboda kunga basu da gata,Insha Allah sai kunga sakayyar da Allah zaiyi masu,kuma sai kun ɗanɗana irin uƙubar da kukayi masu,”
Hawaye ne suka shiga zarya a fuskar hafsat,dama saida ranta ya bata cewar dakyar ne su yafe mata,
Janye idanunta tayi daga kan sehrish ta mayar dasu kan Jahad,cikin shessheƙar kuka tace”dan Allah ku yafe mun Jahad,nasan mun cutar daku,amma inaso ku sani bada son raina ba,na kaiku wurin wannan mutumin,Mommy ce ta sanar dani cewa Gidan marayu za’a kaiku,shiyasa har na ɗauke ku,kuma nayi hakan ne saboda tsoran karta halakar daku acikin gidan nan don ba yadda banyi ba akan ta kyale ku amman ta kiya,shiyasa ma na amince da akaiku gidan marayun ashe zubar daku tasa ayi,’
“Ba zamu ta6a yarda da kalamanki ba,saboda tun farko baki nuna kina son mu zauna acikin gidan ba,ke da mommynki,shiyasa kuka haɗa baki ke da ita,kika fara yaudararmu kina nuna kamar kina son mu ashe,so kuke ku fitar damu daga cikin gidan,saboda rashin Imani Aunty hafsat kika damƙa mu a hannun wannan mutumin,to bari kiji Ya Omar ya kashe shi har lahira!!
Gabanta ne ya faɗi rassss!hankalinta yayi mugun tashi,a kiɗime tace”Ya kashe shi!”
Jahad tace”kwarai kuwa Ya Omar shi ne ya kama shi da hannun shi acikin gidan gonarsa,lokacin da yake ƙoƙarin keta haddin hosana,aikuwa ya fasa mashi kai,anan wurin ya zama gawa,’
Tana kai ƙarshen maganarta sehrish ta ɗaura da cewar”tun yanzu kwara kusan inda dare yayi maku!don wlh Ya Omar bazai sassauta maku ba!muddin yaji cewar kune kukayi silar da har wannan mutumin ya ɗauki su jahad ya kaisu daji,sannan ku fara tunanin irin hukuncin da kuma zaku fuskanta a wurinshi!”
Wani irin wahalallan yawu hafsat ta haɗiya,tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,ba don komai ba sai don jin cewa An kashe mutumin nan!tun da har Omar zai iya kashe rai akan su hosana,tabbas ba ƙaramin so yake masu ba,kuma akansu zai iya hukunta kowa,yanzu su menene sakamakonsu?
“Baku da wata mafita,shawara nake baku tun kafin hosana tayi maku tonan asiri,kwara kusan abunyi,don tace saita sanar ma Daddy da Ya Omar abunda kukayi mana!” jahad ce tayi maganar,
Gaba ɗaya duk sun bi sun tsoratar da ita,la66anta har kerma suke wurin rokonsu tana cewa”Dan Allah ku yafe mun,wlh nayi dana sanin duk wani abu da mu kayi maku,har ga Allah ni bada sanina ba,mommy ce ta shirya duk wannan,Allah shine shaidata,bazan yi maku ƙarya ba,”sosai hafsat ke kuka,
Ruko hannun jahad tayi acikin nata tana fadin”jahad nasan kina da sauƙin kai,dan Allah ki yafe mun,wlh nayi nadamar abunda mu kayi maku ni da mommyna,nasan naƙi ku da farko amma daga baya naso ku sosai,kuma nayi kukan rashinku atare dani,lokacin da nagane cewa Mommy ba gidan marayu tasa akaiku ba,har faɗa sai da mu kayi da ita,ko isasshen bacci bana samu a lokacin saboda tunanin wani hali kuke ciki……”ƙarasa maganar tayi tare da sanya hannu tana share hawayen dake zuba a kan fuskarta,
Shiru su kayi da alama jikinsu ya ɗanyi sanyi,Sehrish tace”Jahad,idan kinyi niyya ki yafe mata,’jinjina kai jahad tayi tare da cewa”Ni dama ban ruƙe ki araina ba Aunty hafsat,na yafe maki Allah ya yafe mana gaba ɗaya,”

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Amsawa tayi da “Amin,sannan tace”Hosana fa?dan Allah ku tashe ta inaso in nemi yafiyarta,”
Hannu Sehrish takai tare da bubbuga ƙafarta,farkawa hosana tayi,idanunta sunyi suntum saboda bacci,
“Hosana ki tashi,ga Aunty hafsat nan tana son magana dake,”jin an ambaci sunan Aunty hafsat yasa ta wartsakewa ta miƙe daga zaune,koda idanunta su kayi arba da fuskar hafsat,nan take ta murtuke fuska rai a6ace tace”Ni bana son ganinta,na tsaneta kamar yadda suka tsane mu ita da Mommynta,Aunty hafsat muguwace bata tsoron Allah,itace takai mu wurin wannan mummunan mutumin wanda yakusa kashe …..”katse ta jahad tayi da cewa”pls hosana just forget about the past,forgive her pls,Aunty hafsat tayi nadama,kuma bada son ranta ba ta kaimu wurin mutumin nan ba,Mommynta ce ta shirya wannan,”
Maƙe kafaɗa hosana tayi alamar bata yarda ba,harara ta wurga ma hafsat ɗin tana murguɗa mata baki tace”Allah saina faɗama Ya Omar da daddy,ko kukan jini zatayi sai dai tayi,amma saina faɗa,saboda rashin Imani kamar wasu dabbobi haka kuka rufe mu acikin store babu abinci ga ƙishin ruwa,ko iska babu,amma ko ajikin ku mu rayu ko mu mutu wannan ba matsalarku bace,zafi kamar zai kashe mu,adaren ranar da muka kwana a store,ba don jahad tayi mun fifita ba da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya don rashin imani ku kuna can kuna shan A.c,wlh saina faɗama daddy…..”fashewa hosana tayi da kuka,hada bubbuga ƙafarta,daga gani abun ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba,ya tsaya mata arai,
Gaba ɗaya jikinsu yayi wani irin sanyi,musamman hafsat,duk yadda taso ta shawo kanta amma abun yaci tura,hosana ta rantse ta maya akan cewar saita faɗa ma Ya Omar,hatta jahad sai da taso ta lallasheta,amma ina ƙarshe sai ta dinga ƙoƙarin bugun jahad din,
Ganin haka yasa sehrish kallon hafsat tare da cewa”dan Allah kiyi haƙuri ki tafi kawai,hosana batasan ganinki,idan tana kallonki haukanta zai iya tashi,”
Jiki asanyaye Hafsat ta mike,tana tafiya tana waiwayonsu yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,a haka har ta isa ƙopar ɗakin ta buɗe ta fuce da gudu tana kuka,
Hannu Sehrish tasa tare da janyo hosana ta rungumeta sosai ajikinta tana lallashinta,da ƙyar ta samu hosana tayi shiru,sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,komawa su kayi suka kwanta kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

*Aunty Babba*

Suna kwance ita da hayaam sai faman sharar bacci sukeyi suna jan minshari yadda kasan bijimayen sa,sun cika gadon su biyu kawai,babu wanda ya farka acikinsu balle suyi tunanin yin sallar asuba,can cikin bacci Hayaam ta dinga jin ana bugun ƙopar ɗakin nasu tamkar za’a balle ta,dogon tsoki taja tana faman yatsina fuska alamar an takurata,a ƙule tace”Wai dallah wanene ke buga ƙopar ɗakin nan”!?
Muryar hafsat tajiyo daga waje cikin shessheƙar kuka tace”Ni ce,ki zo ki buɗe mun ƙopa,”
Jiki na rawa hayaam ta saukko daga saman gadon ta ƙarasa tare da buɗe ƙopar,gabanta ba ƙaramin faduwa yayi ba ganin fuskar hafsat sharkaf da hawaye,hankali atashe tace”Meya faru ne kike kuka”?
A tsiwace hafsat tace”Ba dole inyi kuka ba!kun jefani cikin masifa!ki bani hanya na wuce,Da Mommy nake so inyi magana,”tana faɗin hakan ta bangaje hayaam tare da wuce wa ciki,duk tabi ta ruɗe,wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ma hafsat maƙoshinta,lokacin da tayi arba da Aunty babba,baje saman gadon tana sharar bacci,wato hankalinta kwance ita,batasan wainar da ake toyawa ba,

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Da karfi ta ambaci sunanta”Mommy!Mommyyyyyyyy!
A firgice Aunty babba ta farka,agigice ta tashi zaune tana faɗin”Lafiya hafsat kike mun irin wannan kiran”?
“Ina fa lafiya mommy!ashe ke kina nan kina sharar bacci,ni kin barni cikin tashin hankali,jiya ko isasshen bacci ban samu ba,saboda tunanin hukuncin da Ya Omar da daddy zasu yanke mana…”
Jin wannan maganar yasa Aunty babba fashewa da dariya tana tafa hannu,
Hakan ba ƙaramin fusata hafsat yayi ba,muryarta na rawa tace”Mom…my dariya ma kike yi”?
Aunty babba tace”to me kikeso inyi in banda dariya,ke bakisan meya faru ba jiya”?
Zuba mata ido hafsat tayi tana kallonta,
“Hayaam zo ki faɗa mata da alama batasan meya faru ba,ae mu yanzu bamu da sauran damuwa,hankalinmu a  kwance yake kamar muna cikin jirgi gobara ta kama,” tana magana tana faman washe baki,
Ƙarasowa inda hafsat take a tsaye,hayaam tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli hafsat tare da cewa”ke bakisan cewa jiya Ammi ta kori su Jahad daga gidan nan ba?korar ma korar wulaƙanci,ae shiyasa kika ga mun saki baki muna bacci hankalinmu kwance,saboda bamu da sauran damuwa yanzu,”
Wani irin kallo hafsat ta wurga mata tare da cewa”Amma dae a mafarki hakan ya faru ko”?
Aunty babba tace”Wani mafarki,jiya agabanmu Ammi ta korasu,da gudu suka fita daga gidan nan suna kuka,”
Tsabar takaici ya hana hafsat cewa komai,
Hayaam tace”Ae kawai ki kwantar da hankalin ki kema,babu mai tuhumarki akansu,Yaran da yanzu ba’asan ma inda suke ba,”
“Mommy!dama tunanin da kuke kenan?shiyasa baku damu ba,ko kaɗan”
“”Kwarai kuwa akan me zamu damu”?
Hannu hafsat tasa tare da dafe kanta,tana faɗin”Ya salam!Wlh Mommy idan mafarki kike toh ki farka!domin kuwa jahad da hosana suna acikin Gidan nan!babu inda suka je!!
Wani irin bugu zuciyar Aunty babba tayi ji kake daraam,a ruɗe tace”Kamar ya kenan”?
“Mommy Jahad da hosana suna nan!Yanzu haka daga bedroom ɗinsu nake,naje ne domin in nemi yafiyarsu akan laifin da muka aikata masu,”
Saboda tsabar tashin hankali har suna haɗa baki Ita da hayaam wurin cewa”Jahad da hosana suna acikin gidan nan!!!”
Jinjina kai Hafsat tayi kafin ta ɗaura da cewar”mun shiga uku mommy,mun ja ma kanmu bala’e da masifa!Ashe Ya Omar shine ya taimake su hosana acikin gidan Gonar mutumin nan,kuma a dai dai lokacin da yake ƙoƙarin yin raping ɗin hosana!
Hannu Aunty babba ta aza aka tana fadin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!”
Hayaam kuwa sai faman zazzare ido take,
“Mommy,bugu da ƙari,a nan wurin Ya Omar ya tarwatsa kan mutumin nan ya mutu har Lahira,”tunkan hafsat ta ƙarasa maganar Aunty babba ta saukko daga saman gadon,hannayenta asaman kanta take fadin”Nashiga ukuna,Na bani na lalace,na ru6e!hafsat dan Allah ki faɗamun gaskiya,!dagaske baba alamu ya mutu!kuma Omar ne ya kashe shi saboda su Hosana!ashe shiyasa kenan naita neman number wayansa daga baya ban samu,wannan wata irin masifa ce!,
Zarya tashiga yi acikin ɗakin tana faman cizon yatsa,Hayaam tace”Aunty laila don Allah ki kwantar da hanlinki….”
Hankali tashe Aunty babba tace”taya zaki ce in kwantar da hankalina?bayan ga kashi cike a wandona,ni bansan wani irin hukunci Omar zai yanke mun ba” tana magana zufa na gangarowa a fuskarta,
Ita kanta hayaam,duk a tsorace take duk da ba ita ta aikata laifin ba,amma ta razana da jin cewar Omar ya kashe mutumin da Aunty babba tasa ya zubar mata da yaran,
“Yanzu hafsat menene mafita”!tayi maganar muryarta tamkar zata fashe da kuka,
Kafin hafsat tace wani abu hayaam ta rigata cewa”Ni ina ganin kawai Aunty laila,ku tattara kawai kubar gidan nan ke da hafsat,”

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Wani irin kallon rainin wayau hafsat tayi mata tare da cewa”Mu tattara mubar gidan nan fa kika ce?ke kuma fa?ko kina tunanin cewa In asirin mu ya tonu,ke bazai shafe ki bane?tun wuri kusan inda dare yayi maku ke da Mommy!saboda kune baku da alaƙa da gidan nan!Ni kuwa ba inda zanje saboda nasan cewa duk hukuncin da daddy zai yanke mun bazai ta6a korata ba a gidan nan,saboda Ni ƴarsa ce,nan kuma gidan kakana ne,”
Zuru zuru hayaam tayi jin abunda Hafsat tace,Aunty babba kuwa batasan ma me suke magana akai ba,saboda kanta ya ɗau chargy,sae faman zagaye ɗakin takeyi,ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,
“Wlh da nasan yaran nan suna acikin gidan nan,da tun jiya da daddare zanbi dare,in taushe masu hanci da pillow har sai sun bar duniya don ubansu,yara sun zame man bala’e!”
Girgiza kai hafsat tayi tana kallonta,har yanzu dae babu alamun dana sani atattare da ita,
“Tunda nake ban ta6a shiga tashin hankali ba arayuwata sai akan waɗannan yaran!komai nasa agaba sai naci nasara akanshi,amma waɗannan tsinannun yaran sun tarwatsa mun duk wani plan ɗina,Ba kowa nafi jin haushi ba,face Ubansu,duk shine silar daya auri uwarsu a 6oye harta haifo mana mugun abu,Allah danasan da zaman yaran tun suna cikin ciki zansa a markaɗe munsu,don karsu duniya,’
“Mommy dan Allah kidaina wannan soki burutsin!kin ishemu da surutu kamar wata zautacciya,duk waye ya jefa mu cikin halin nan in ba ke ba?maimakon ma kiyi tunanin sama mana mafita,Sai wasu sambatu kike marasa kan gado,ni bazan iya jurar jin waɗannan munanen kalaman da kike jifar su jahad dashi ba,inaso ki sani su ɗin ƴan uwana ne,”
Juyowa Aunty babba tayi tamkar zata rufe hafsat da bugu,”Don Ubanki Har ni zaki faɗama cewar ƴan uwanki ne!sun fini kusanci dake ne?Ko ciki ɗaya kuka fito tare dasu ne?
“Wlh mommy da ace ciki ɗaya na fito dasu dana fi kowa farin ciki,tun daga kan halayansu da ɗabi’unsu zai tabbatar maka da cewar mahaifiyarsu ta basu tarbiyyar daya dace,kuma ita mai kyakkyawar zuciyace shiyasa ƴa’ƴanta ma suka kasance masu kamar yadda take,Ni ce dai nayi babbar asara,dana fito daga jikin ki!gashi nan yanzu sai danasani nake…..”kasa ƙarasa maganar tayi,a hanzarce ta watsa da gudu tabar ɗakin,saboda yadda taga Aunty babba ta tunkarota azafafe,yadda ranta ya 6aci ɗinnan komai zata iya aikatawa,
ƙafafunta ne suka fara yi mata raɗaɗi ba arziƙi ta koma daga gefen gadon ta zauna,idanunta sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,zuciyarta sae faman tafarfasa takeyi mata,tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito waje,zama hayaam tayi daga gefenta,kowannansu yayi zuru zuru,
“Aunty laila!ni ina ganin kawai ki gudu batare da sanin kowa ba,in ba haka ba,inajiye maki tsoron abunda zai biyo baya,”
Cike da takaici Aunty babba tace”Hayaam naso ace hada Amani muka aikata wannan laifin,saboda banaso taci galaba akaina,yanzu in ishaq ya sake ni,ni kaɗae zanyi zawarci na,bakowa nafi jin haushi ba face hosana!mahaukaciyar banza,ina zaman zamana lafiya na,ta nemi tozarta ni agaban kannen mijina,wlh in har ta tona mun asiri,ni kuma sai nayi silar mutuwarta!!!!!!!!!!!!!!

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Dan Allah Aunty laila kidaina kira mana mutuwa,muji da abunda ke damun mu,duk yadda za’ae yanzu kada ki bari kuyi arba da hosana ɗin, yunwa nata cinsu,amma saboda gudun haɗuwarta da Omar ko Ishaq,yasa ta gaza ko ɗan leƙawa waje,

Bayan fitar Hafsat tashi suka yi suka zura Hijabs ajikinsu,sannan suka fito atare suka nufi ɗakin daddynsu,kamar yadda Sehrish ta basu shawarar su je su gaishe da daddynsu da Ammi da su hajiya Azeema,

Abusufyan na kwance saman gadonshi yaji ana knocking door ɗin ɗakinsa,miƙewa yayi tare da ajiye wayar hannunshi saman side drawer,ƙarasawa yayi yasa hannu ya buɗe ƙopar,zuba masu ido yayi yana kallonsu,sam baiyi tsammanin zai gansu ba,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba sunsha hijabai ajikinsu,sae faman murmushi suke sakar mashi,
“My triplets”ya ambaci hakan tare da basu hanya don su shiga ciki,rufe ƙopar yayi bayan sun shiga daga ciki,
Saman gadonshi hosana ta haye,jahad da sehrish kuwa a ƙasa suka lankwashe ƙafafunsu suka zauna,
Wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana kallonsu,
“Ina kwana daddy,an tashi lafiya,”
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace”Lafiya lou my daughters,Nayi mamakin ganinku,waye acikinku ya bada shawarar azo agaishe ni ne”?yayi maganar yana kallon fuskokinsu,
Jahad ce ta nuna sehrish da hannu,
“Kinyi tunani mai kyau,dama yanzu nake shirin zuwa in taso ku,don muje ku gaishe da Modibbo,da Ammi da sauransu,abunda ya dace ne,kullum da safe ku dinga zuwa kuna gaishe dasu,”
Atare suka haɗa baki wurin cewa”In shaa Allah zamuyi hakan daddy,”
Juyawa yayi tare da kallon hosana dake kwance,hada rufe ido tana minsharin ƙarya,don yayi tunanin cewa bacci ne ya ɗauke ta,
Hannu yasa tare da jan kumatunta,nan take ta fashe da dariya,shima dariyar yayi kafin daga bisani,yace”ku tashi mu tafi ɗakin Ammin atare don ku gaisar da ita,
Saukowa hosana tayi daga saman gadon,ya ruqo hannunta dana jahad,suka jera tare suka fuce,

Suna tsaye a ƙopar ɗakin Ammi,sae ga Junaid,yana hangosu ya shiga sakin murmushin nan nashi,jiki na rawa ya nufi wurinsu,Gaisar da Abusufyan ya fara yi”Gm Uncle,”cike da zolaya Abusufyan yace”a haka zan baka auren ƴa ta?kana gaisar dani daga tsaye sai kace wani tsaranka ba wani respect”?jin haka yasa junaid saurin duƙawa ƙasa,sannan yace”Ina kwana Uncle”?
Dariya su kayi gaba ɗayansu,ganin yadda ya zuƙunna,
“Lafiya lou in law ɗina,ko kaifa,miƙe tsaye toh tunda ka ƙaraso sae mu shiga ciki atare,”mikewa yayi fuskarshi a washe,duk a tunanin Abusufyan junaid wasa yake yi masa yawan zancen zai bashi auren ɗaya daga cikinsu,baisan dagaske shi kamu yake yi ba
da sallama a bakunansu suka shiga cikin ɗakin,koda ammi taji muryoyinsu,da sauri ta kashe tabar da take zuƙa,ta sanya ta acikin Ashtray dake ajiye ƙasa,da ƙafarta ta tura shi ƙarƙashin gado,duk akan idon Abusufyan abun yaso ya bashi dariya,lallai Ammi ta kimtsu tunda har ta fara jin kunyar jikokinta su ganta tana zuqar sigari,
A saman carpet,kowannansu ya zauna tare da lankwashe ƙafa,Abusufyan ne ya fara gaisar da ita”Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya”?
“Lafiya lou Alhamdulillah,”ta amsa mashi,Sannan su Jahad suka haɗa baki wurin miƙa gaisuwarsu,da murmushi a fuskarta ta shiga amsa masu ɗaya bayan ɗaya,a ƙarshe ta tsayar da idanunta kan Hosana tace”Kin tashi lafiya”?
Murmushi hosana ta saki tana faman noƙe kai tace”lafiya lou,”
Janye idonta tayi daga kan hosana ta mayar dashi kan junaid tace”Sarkin Murmushi,Angona nakaina naga kayi kyau sosai ka kuma ƙara haske,faɗamun menene sirrin”?
“Kishiya zanyi maki ne”yayi maganar yana murmura mata ido,ɗan waro ido waje tayi tare da cewa”Wacece ita”?
ɗagowa yayi yana kallonsu,Sehrish har sai da ya gano jahad sannan ya nuna ta da hannu yace”Gatanan,”
Ammi tace”Kin shirya yin kishi dani ko”?
Girgiza kai jahad ta shiga yi alamar a’a,
“To kaji bazata iya kishi dani ba,sai ka haƙura da auren gaba ɗaya,don ni bazan zauna da kishiya ba,”
“A’a wlh Ammi sai dai ki haƙura dani in aurota,”

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya basu ba,don har saida suka dara,
Ammi tace”wato Ni zaka juya ma baya ko?saboda ka samu zankaɗeɗiyar budurwa sabuwa gal cikin leda,Ni kuma nayi maka tsufa,”gyaɗa kai tayi tare da cewa”bakomai na haƙura,”
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,mayar da idonta tayi kan Abusufyan”Yanzu ya ake ciki game da zancen Mahaifiyar yaran nan”?
Jin an sako zancen abu yasa shi gyara zama,sannan yace”Muna nan muna shirya waɗanda zasu je kano domin binciko gidan da suka zauna acikinsa,saboda muna sa ran zamu samu wasu muhimman bayanai a wurin makwabtansu,”
Jinjina kai Ammi tayi”hakan yayi kyau,banason a tsaya 6ata lokaci nafi son ayi komai tun da wuri don ba’a san halin da take ciki ba,”
“In sha Allah zamuyi hakan,daga nan suka miƙe tare da yi mata sallama suka wuce ɗakin Modibbo,ba ƙaramin daɗi yaji ba daya gansu,sun jima a wurinshi,kafin daga bisani suka wuce ɗakin gwaggon katsina,sun sha barkwanci a wurinta,daƙyar suka samu tabarsu suka fito,ɗakin hajiya azeema suka wuce,sun jima a wurinta suna shan fira,ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ɗakunansu kafin daga bisani,Lokacin yin breakfast yayi suka hallara gaba ɗayansu a dining,kowa saida yazo banda Sgr,saboda yasa ma ranshi cewar za’a kawo mashi ne har part ɗinsa,Azmee ce takai mashi,saboda Sehrish ta sanar da ita cewar,bazata samu damar kai mashi ba,tana so tabi Umarnin mahaifinta ne,

Lokacin da Azmee ta shiga part ɗinsa,yana daga kishingiɗe saman Sofa mai mazaunin mutun ukku,jikinshi na sanye da jallabiya,shigowa ciki tayi gabanta na faɗuwa don tasan cewa dole ya tuhumeta akan me ya hana sehrish zuwa,lalla6awa tayi ta ajiye masa tray ɗin a asaman table,gudun karya tuhumeta yasa tayi saurin ja da baya zata gudu tabar ɗakin,har takai baƙin ƙopar ɗakin tajiyo muryarshi yana fadin”ke zo nan,”dakatawa tayi da tafiyar hannunta dafe da saitin zuciyarta,jiki asanyaye ta dawo ta tsaya agabanshi,kwata kwata idanunshi na a lumshe,wayarshi na ajiye asaman wide chest ɗinsa,
dakyar ta iya cewa gani yalla6ai,
“Bana ce kar na sake ganinki a part ɗina ba da sunan aiki?ko bata faɗa maki bane”?
Shiru azmee tayi,tana faman zazzare ido,ranta ne ya bata cewar kawai ta sanar dashi gaskiyar zance,
Don haka tace”Sehrish ta sanar dani cewar bazata ƙara aiki a part ɗin ka ba….”tunkan ta ƙarasa maganar ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu,nan take azmee tasha jinin jikinta,
“Ita da bakin ta,ta faɗi hakan”?
Muryarta na kerma tace”Eh,
Ya kuma cewa”ta faɗa maki dalilin yin hakan”?
“Eh,tace tana son bin Umarnin mahaifinta ne,”
ɗan ciza gefen la66ansa yayi tare da cewa”its Okey,just leave……..” da sauri azmee ta juya tare da kama hanya ta fuce daga part ɗin nasa,

Wuraren ƙarfe goma sha biyu modibbo ya shirya tafiya,Kanal yousouf ne tare dasu Irfan suka kai shi har Airpot ya hau jirgi,

Yinin Ranar Aunty babba na ƙumshe a cikin ɗakin Hayaam,tsoro ya hanata fitowa waje,da yunwa ta addabe ta Hayaam ce ta ɗebo mata abinci ta kawo mata a ɗakin,hosana kuwa kar take dasu,don taci alwashin sai ta tona masu asiri wurin daddynsu,da kuma Ya omar,

Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,jin Cewa sgr bai nemeta ba,duk da ta damu akan son ganinshi,jurewa kawai takeyi,

A ranar Talal Da captain najeeb suka ƙaraso,murna a wurin ƴan uwansu kamar zasu haɗiye su don farin ciki,musamman junaid daya kasance rival ɗinsa ne ya dawo wato Talal,da yake shima autane a ɗakinsu Omar,

After 1 day

*Boss Bature*

Around 2:00 pm,

Zaune take a hakimce saman 2 seater,jikinta na sanye da turkish dress Riga da wando,a launin fata fara ce amma hasken nata hada na bleaching tayi 6au sosai,babbar mace ce a ƙalla zata kai shekara 35,gaba ɗaya idanunta na akan plasma tv din da take kallo aciki,yayin da hannunta ke ɗauke da cup na coffee,lokaci bayan lokaci take kur6asa,ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,wuyan kafarta na sanye da ziririyar sarƙa,sai faman karkaɗa kafar takeyi,Tana da manyan idanu dara dara,ga dogon hanci wanda ke manne da nose ring,kai kana ganinta zaka san cewar cikakkiyar ƴar bariki ce,
Jin ringing din wayarta dake ajiye asaman hannun kujerar da take ne yasa ta Ajiye cup din hannunta asaman madaidaicin table din dake a kusa da ita,sannan tasa hannu ta dauki wayar,hidden number ce aka kirata da ita,picking call ɗin tayi ta kanga wayar a kunnanta,cikin harshen fulatanci take magana,

Tana cikin yin wayar taga inuwar mutun tsaye akanta,ɗagowa tayi a hankali don taga wanene,sauke ajiyar zuciya tayi ganin Amrish ce,jikinta na sanye da uniform,ta goya school bag dinta a abayanta,dawowarta kenan daga school,fuskarta a ɗaure kwata kwata babu annuri acikinta,

Rejecting call ɗin tayi tare da ajiye wayar asaman sofa din,sannan ta mayar da hankalinta sosai akan Amrish,
“Welcome back my daughter,Am really glad to see u,”
Tayi maganar tana buɗe mata hannunwanta don tazo ta rungume ta,rai a6ace tace”Mommy na tsani ganinki wlh,banason ki,saboda baki da halin kirki,so kike ki kashe mun rayuwata da hannunki,”tana maganar hawaye na gangarowa akan fuskarta,
Maimakon ta nuna damuwarta akan hakan sai ma ɗan ta6e la66anta tare da cewa”Kamar yadda baki so na,Nima haka bana son ki,donni a tsarin rayuwata ban shirya haihuwa ba saboda bana son ƴa’ƴa don su takura ne,na samu cikinki batare dana shirya ba,babu yadda banyi ba don na zubar da cikin,amma ya liƙe ya nace sai ya zauna a mahaifata,a ƙarshe nayi deciding zuwa ƙasar waje a markaɗe mun shi,mahaifinki ya hana hakan,nayi takaici a wannan lokacin kamar nayi suicide,”
Hankalin Amrish ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda mahaifiyarta ke faɗi da bakinta,tuni wasu zafafan hawaye suka shiga wankowa a saman fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace”ki faɗamun!Su wanene iyaye na!don ina da tabbacin cewar bake kika haife ni ba,”
Fashewa da dariya matar tayi yayin da take karkaɗa kafafunta,
Jin tayi banza da ita yasa ta daka mata tsawa tare da cewa”Mommy ki faɗamun su wanene iyaye na?In ba haka ba zan je na kashe kaina!”
Yunkurawa mommyn tayi tare da mikewa tsaye ta daddage ta kifa ma Amrish mari tare da cewa”Sai me idan kin kashe kanki!?wa kikayi ma asara!shashasha kawai,”
Fashewa da kuka Amrish tayi yayin da zuciyarta ke tafarfasa tace”Mommy yau ke da kanki kika mare ni”?
Dogon tsoki taja tare da cewa”Har kashe ki ma zan iyayi,Saboda kinyi mun tsawa,ko iyayena da suka haife ni basu ta6a gigin daka mun tsawa ba,balle ke ƴar dana haifa,idiot”
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta ɗauki wayarta,sannan tabar falon tana fadin”kafin gobe in samu gawarki dan Allah,”tayi maganar cikin halin ko in kula,
Da gudu Amrish ta watsa,izuwa bedroom dinta dake a upstairs,datse ƙopar ɗakin tayi,bayan tayi wurgi da school bag dinta,ta shiga neman igiyar da zata shaƙe kanta don ta mutu,ganin bata samu ba yasa ta buɗe kopar ɗakin,ta fita,bada jimawa ba sai gata ta dawo cikin ɗakin hannunta dauke da insect powder,buɗe murfin tayi da sauri sauri ta daga robar tare da zazzagawa acikin bakinta,

Mommyn na acikin bedroom ɗinta,ta jiyo wata irin razananniyar ƙara mai rikitarwa,sakin wayar dake hannunta tayi,da gudun gaske ta fito daga bedroom ɗinta dake a downstairs,tamkar za tayi tuntu6e ta fadi kasa haka take gudun,lokacin da ta ƙarasa bedroom din Amrish,hannu tasa ta dinga bubbuga ƙopar tana faɗin”AMRISH!AMRISH!!baki da hankali ne,bakisan wasa ba,me kika aikatawa kanki!ba zaki zo ki buɗe mun ƙopa ba!!Amrish gaba daya duk tabi ta rikice,
Shiru amrish bata buɗe mata ƙopar ba,hakan yasa ta dawowa wurin window ɗin ɗakin ta buɗe ta don ta gane ma idonta,
A gigice ta fasa uwar ƙara tare da aza hannyenta asaman kanta tana fadin”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!na shiga uku!!!!zubewa tayi ƙasa saman guiwowinta tana faman zabga kuka,hawaye jaga jaga a fuskarta,tana cikin wannan yanayin,taji shigowarsu Zeenat da sofia ƙawayen Amrish cikin falon gidan,mikewa tayi da sauri har tana tuntu6e ta saukko downstairs,tunkararsu tayi tana fadin”Nashiga uku!!Amrish ta kashe kanta!!bansan ya zanyi da rayuwata ba!!
Kallon juna sukayi hankalinsu a matukar tashe suka haɗa baki wurin cewa”Am…Amrish!!meya faru da ita!taya akai ta kashe kanta!!!
Kasa bude baki tayi don tayi masu magana,da hannu ta dinga nuna masu bedroom ɗinta,nan suka gane cewar tana acikin ɗakinta,da gudu suka nufi upstairs ɗin,itama tabi bayansu,nan fa suka shiga ƙoƙarin 6alle ƙopar ɗakin nata.

Back to top button