Hausa novels

Gargadar So Chapter 61 By M Shakur

Suna kaiwa gaban gidan Baba yabude mota yafice haka Ammi cikinsu babu wanda yakalli Hawwa sabida yanda tacikasu da bakin cikin kukan datake a mota, yunkurawa itama Hawwa tayi zata fice Khaleel yarike mata hannu baice komiba hakan yasa driver Umar yabude kofa yafita, Khaleel yakalli yanda har lokacin takasa daina kuka kaman zai kama da wuta yace “are you seriously still crying sabida matar chan? That woman dabata da intention mai kyau akanki, the woman that was trying to ruin marraige namu” cikin kunci sosai Hawwa tace “I wish tayi ruining marraige dinma!” Dasauri Khaleel yace “mene?” Dauke kanta Hawwa tayi takai bayan hannunta ta goge fuskanta tace “I will not expect you to understand my situation sabida bakasan menene so ba, you’ve never loved anybody da duka zuciyanka wholeheartedly kasaken mini hannu” ta yunkura zata fita Khaleel ya fizgota tadaw ba karfi ajikinta takalleshi da rinannun idanunta, cikin bakin cikin fushi da tsiwa kaman ba itane tagama rungumeshi a office yanzunan ba tace “ka saken mini hannu Khaleel I wanna go home” yana kallonta right in the eye yace “naki nasake ki, ni kika cema dama tabata auren namu”? Azuciye Hawwa tace “yes! Sabida bana sonka! How many times kakeson namaka repeating you don’t deserve me kafin ka haddace akanka? Danasan kaine zanyi ending up with danayi abinda ma Ni’iman tai accusing dina of doin……” yanda Khaleel yake huci yasa takasa karasa maganan kawai ta dafe kanta tace “let me go you will never understand abinda nakeji araina right now, kasakeni nace” Khaleel dakejin ciwo aranshi yace “you are this hurt sabida wata dake neman halakaki”ihu Hawwa tamai hawaye na bulbulowa daga idanunta tace “I’m angry sabida ka aika Ni’ima prison! Kome Ni’ima tamin bazan taba iya mance she has been there for me ba during difficult times na rayuwana, she comforted me idan Baba yabatamin rai, idan ina bukatan taimakon gaggawa tana zuwa ta daukeni nakirata, Ni’ima give me a shoulder to cry, she listens to me, muntaso tun muna yara, I know tamin abubuwa da dama this days, kome Ni’ima tamin bazai taba kore tamin alkhairi da ba, inma da zuciya daya tayi ko bada zuciya daya tayiba I don’t care but I know she was there for me then emotionally and morally” Hawwa tai shiru tana kuka sosai tana kallon Khaleel tana shesheka tace “atleast for the sake of old times, old days, kuruciyan mu daka barta Khaleel tunda ai nace narabu da ita har abada eh? Have you ever been to prison”? Putttssss tayi da bakinta cikin kuka tace “why will I even ask you that nasan maybe that day dakazo prison was the first time kataba zuwa bama kasan menene condition na cikin prison ba, Ni’ima does not deserve to be there Khaleel why did you send her there kaitama laifi koni? I begged you ka barta ka barta maisa zaka turata wajen must you punish her? Bazaka iya barinta da halinta ba? Metayi kisankai tayi why why why ka turata prison”? Hannunta Khaleel yasaki ranshi yabaci iya baci, it took him courage ya daure baikaima Hawwa duka ba, cikin kakkausan murya yace “get out!” Cikeda fushi ta harareshi tace “kaima get out of my life, kuma auren banyi banyi banyiiii!”Tabude motan azuciye tafita abinta ta bugomai kofan motan da saida motan ya girgiza Khaleel yabita da kallo.Tana shiga gidan dakinta tawuce tabude kofa ahankali Ammi na tsakar dakin tahade giran sama da kasa bawasa kawai tace “kicire kayan jikinki ki nemi kaya kala daya dazaki dinga amfani dasu kiwuce chan dakin mai gyaran jikinki Munnawar ta iso daga Maiduguri” Ammi na maganan tawuce tafita daga dakin Hawwa tabita da kallo ganin Ammi fushi take da ita sosai tawuce ahankali ta zauna tacire Hijabi batajin dadin komi, zuciyanta ba dadi, bawai bataji zafin abinda Ni’ima tamata bane taji kuma taji ciwo, sannan ta tsani Ni’ima but again bata manta da alkhairan da Ni’ima tamata abaya ba, koda ba dan Allah tayiba, koda bahar zuciya tayiba itadai tamata, Ni’ima ke lallashinta idan Baba yagaya mata maganganu, batada saurayi mai kiranta Ni’ima call her every day sannan duk daren duniya sai sunyi waya sunyi chatting kafin suyi bacci that company kadai da Ni’ima tai keeping nata is something to her, Ni’ima tazo graduation nata, Ni’ima always check up on her, like ita mutun ne da tasan alkhairi sannan bata mancewa, kodan darajan alkhairan da Ni’ima tamata abaya bai kamata su aikata gidan yari ba, sabida Khaleel yaga yanada kudi yasa yake oppressing talakawa? Yasa an kwace licence nata an koreta a aiki yanzu yakaita gidan yari idan ta kashe kanta fa? Idan depression yakamata fa?.Azafafe Ammi daga waje tace “kinsan tun yaushe tazo tana jiranmu bama nan kuwa kikai zamanki adaki Oganniya sarauniya Hawwa”? Dasauri Hawwa ta tashi kayan jikinta tacire tadauki waji simple light gown tasaka tafito ta taho dakin, wata mai gyaran jiki ne da zatakai 50 yes daga maiduguri Ammi tabiyata 1M kudin aikinta na 3weeks, ga hakoran maka sunkai 6 a bakinta tabi Hawwa da kallo tace “Masha Allah tubarkallah amaryan namu akwai kyau Zainab, ga tsayi kaman hawainiya” dan murmushi Ammi tayi for the first time tunda ta shigo gidan tace “shareta Minawwara, namiki bayanin komi awaya gameda ita ai” ahankali Hawwa tace “ina yini Anty” murmushi tamata tace “lafiya lau Hawwa karki damu zan hadaki da Billahillazi sai mijinki yayi kuka ya susuce akanki, hadi zan miki da bazai karajin dadin wata aduniya banda ke ba, Alhamdulillah Mamanki tace bakida kishiya dan banwa mai kishiya package dazan miki” Hawwa aranta tace “niko keda kishiyoyi” Munawwarah tai murmushi tace “sai yaji kinfi yar shekara sha uku dadi” sauke kanta kasa Hawwa tayi akunyace, Ammi tawuce tafita daga dakin da har yanzu akwai yar kunyan nan tsakaninta da Hawwa, ganin haka yasa Hawwa ta dago kanta dasauri ahankali tana rage murya tace “Anty dan Allah karkimini komi, banson nasha wani magani ko wani gyaran fata, bana son shi, ni banso amin komi sabida shi, idanma akwai abinda zai kashemin natural Ni’ima abani sabida yaji bakin cikin aurena duk randa ya karba ta karpi danni bazan taba bashi kaina da kaina ba Anty” hawaye yafito daga idanunta, kallon Hawwa Munawwarah tayi sai kawai tayi murmushi tace “kika kara magana haka saina kira Mamanki bakisan aure haka kinaji bakison miji yafi dadi ba bayan anzo an fara shiri? Baki alfahari da kin sami gidan hutu ba kalli gidan ubanki, bazakije ki dangwalo arziki nan da bayan wata biyu ki chanzama mahaifinki gida? Kinsan nawa Mamanki tabiyani alamun yaron yasaki kudi, ke kiyi shiru kawai hadi zan miki gangariya Hawwa wlh sai ya susuce yarude sabida ke!” Hawwa ta dauke kai kawai bakin ciki nataso mata.

Back to top button