Novel Document

Nihaad Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Description/Story:

Nihaad Complete Hausa Novel Document Written By Khaleesat Haiydar

 

Description

Tun da ta ji furucin wan Abbanta na karshe ta sakar masu kuka me karfin gaske, ta kalli Mahaifiyarta dake goge hawayen dake sauka idonta, babu alamar dai xata ce komai, Ta kalli Abba da fuskarsa ke hade tamkar hadari, shi ma bata samu courage din ce masa komai ba, yayyinta maza biyu dake parlon babu wanda yace komai cikinsu, ta dinga kuka da shesheka ta kalli Umma warce tayi tagumi, kallon Kakarta dake girgiza kafa tayi cikin rawan murya ta kamo hannunta tace “Don girman Allah kice su yi hakuri sharrin shaidan ne, don Allah kice su yafe min, ni ban san wanda yayi min haka ba…” Kakar ta warce hannunta tace “Ja can, Ke har kinsan sharrin shaidan alhalin kece shaidaniyar Nihad, ai kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu kunyata ki, ki ce lalle ke sai kin xama mutuniyar banxa abinda kaf xuri’a babu? Me yake burgeki da rayuwar ‘ya yan iska har wannan abu ya same ki haka?” Kuka kakar ta saki tace “Allah mun gode maka, ka haifi ɗa ne kawai baka haifi halinsa ba, yanxu meye wannan kika mana Nihad” Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta fice daga parlon, direct dakinta ta nufa don tasan ko me xata ce a parlon nan babu wanda xae saurareta, tunda har Umma ma ta ki cewa komai to babu wanda xai ce komai, bayan ta shiga daki ta sa makulli ta fada kan gado tana rusa kuka kamar ranta xai fita, is this actually happening to her? yanda ta ga rana haka ta ga dare, gashi ta kasa sallah ko da raka’a daya ne, gaba daya ta fice hayyacinta, she wish all this is nothing but a dream, she wish xata farka taga mummunan mafarki kawai take, da asuba aka murda kofar dakin ta daga idonta da suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi ta bude, har aka gaji da Knocking aka bar wajen. Sai wajen karfe takwas na safe tana xaune saman darduma ta jawo wayarta da kyar, rabonta da wayar tun shekaranjiya, gaba daya bata son abinda xai hadata da wayar ma balle xuciyarta ya kara rauni, yanxun ma da ta dauko sim card dinta take son cirewa ta karya, missed calls da ta gani ya doshi hamsin, da messages da ya ninka calls din, ko wani message xance daya ne content dinsa, “Is that you on social media Nihad?” “Nihad what came over u?” “Nihad what is happening?” “Nihad something is wrong somewhere, ur Video is all over the internet” Fita tayi daga Inbox din hawaye me xafi na sauka idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da videos… Kashe wayar tayi ta ciro sim card din ta karya kamar yanda tayi niyya sannan ta jefar da wayar saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, wayyo ina ka xata farka taga mafarki kawai take da gaske, tun shekaranjiya take wish din nan, amma taki farkawa wanda hakan ke kara tabbatar mata da gaske ne duk abinda ke faruwa, babu wani xancen mafarki, Knocking din kofa aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Umma ta gani tsaye, nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Umma ta shigo dakin ta kulle kofar, Nihad ta bi ta da kallo har ta xauna gefen gado, Nihad ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace “Umma don girman Allah ku rufa min asiri kar ayi min haka, wllh xan iya mutuwa, talk to Abba plss” Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “It’s too late Nihad, tun da har Alhaji Abubakar ne ya yanke hukuncin nan kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasa, ke dai naki addu’a, mu ma kuma muna nan muna taya ki da shi, it’s okay to make mistakes as long as we learn from them, so ki kwantar da hankalinki everything will be alright, kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya shiryesa” Ta rushe da wani kuka cikin tashin hankali take cewa “Na shiga uku Umma, yanxu baxa ki iya ce ma Abba komai ba? auren dole fa xa su min, Umma ya xan yi da raina idan hakan ya faru, na shiga uku na…” Mikewa Umma tayi ta nufi kofa ta fita ta kulle. Compound Umma ta fita ta tarda Abba dake xaune shi kadai kana ganinsa kasan yayi nisa a tunanin da yake, ta nufesa ta ja daya daga kujerun dake wajen ta xauna tana kallonsa da damuwa karara fuskarta, he looks so disturbed also, ta kwantar da murya tace “Damuwa ba shi ne mafita ba Ranka shi dade, kayi hakuri ka sa ma ranka salama, Allah ne ya tsara haka, sai mu gode masa mu kara gode masa kawai” Abba ya numfasa yace “I think aurar da Nihad yanzu ba shi ne mafita ba Sumayyah, amma Engineer da Hajiya baxa su fahimci hakan ba, she is just 19, ga kuma wannan abu da ya faru, ta ina xata fara xaman aure bata gama mallakan hankalin kanta ba? da xa su sake shawara da ni da na ce masu gwara kawai ta tafi waje ta karasa karatun ta a can, ko da Uk ne….” Umma dake ta kallonsa tace “Wannan gaskiya ne, aurar da Nihad is not a way out, amma ni dai shawarata kar ka tofa naka a issue din nan Yallabai, duk yanda Yaya yayi da Nihad dai dai ne don ‘er sa ce, kuma ran Hajiya xae 6aci idan ka bijiro da wannan batun na taje waje tayi karatu, gani kawai xa su yi kana ma goyon bayanta ne, naka kawai ido sannan kayi mata fatan alkhairi duk yanda suka yi da ita er su ce, kuma baxa su yi abinda xai cuceta ba, tunda suka ce aure mu xuba masu ido duk yanda suka yi dai dai ne, shawara ta biyu kuma kada ka kuskura Yaya yace xai hada Nihad da daya daga ‘ya yansa balle ma bana tunanin xa ayi hakan kawai in case xa a bijiro da wannan gaskiya ka nuna a’a, don in har aka yi hakan zumunci xae tarwatse kasan su waye ‘ya yan nasa da iyayensu, yara ne masu ji da kansu wa enda ba sa rayuwa a kasar, don haka kar ka soma yarda… don walakantattciya xasu mayar mana da er mu, ni yallabai yanda video din nan nata ya tafi viral gwara kawai a samo wani da ba kowa ba, bawan Allah wanda ba ma shi da abun duniya, shi kadai xai iya aurenta ya rufa mata asiri su xauna lafiya ba tare da ya goranta mata wataran ba, bai kuma walakanta mana ita ba, kyau ace ma a karkara yake rayuwarsa yallabai” Abba ya daga kai yana mata wani kallo babu ko kiftawa, tace “Atoh Allah ya baka hakuri, ka samo wani d’an senator ko Attajiri ka hadasu kawai, hakan ma dai dai ne….” Tana kai wa nan ta mike ta ce “Allah ya rufa asiri, ya tsare yan baya” Daga haka ta bar wajen, Abba ya dafe kansa. Umma ta saka Abba tunani iri iri bayan ta bar sa a wajen, ta wani bangaren she is damn right, abinda ta fada gaskiya ne, babu wanda xai yi ma tayin Nihad ya amsa da farin ciki ko dadin rai, Nihad is nothing but a disappointment to him, bai taba xaton hakan daga gareta ba kuma yayi da ya sanin fifitata da yayi cikin duk ‘ya yansa, yayi da ya sanin nuna mata so karara da yayi kan sauran ‘ya yan sa, amma Alhmdlh tunda abinda tayi ya tsaya iya haka, shawaran da Umma ta basa kuma shi xai yi amfani da… Mai gadi ne ya bude gate jin ana horn, Abba ya bi motar da ta shigo compound din da ido har yayi parking, yana xaune aka samesa cikin ladabi ya mika masa ledan dake hannunsa yace “Ga aiken Alhaji” mikewa Abba yayi yace “Mu je can parlor daga nan ka kwashi takalman da xa ayi min polish ka ba mai gadi” Abba na gaba yana biye da shi a baya har suka shiga cikin babban parlon gidan, sannan main parlor din Abba, Abba ya xauna yace “Ka ɗan jira xan yi waya, xan sake aikenka ne” Mai gadi ne xaune a position dinsa tare da driver, mai gadin yayi kasa da murya yace “Ka ko ji abinda ke faruwa kuwa??” Drivern yace “Me ke faruwa?” Mai gadi ya bi compound din da ido kafin cikin rada yace “Daxu Saminu ya xo ya nuna min nima a waya, wllh na gani..” Driver yace “Me ka ga?” Mai gadi ya kai baki kunnensa cikin rada sosai yace “Wllh hoton tsaraicin fitsararriyar yarinyar nan ne duk ya baxu yanar gizo, da idona na gani a wayar Saminu, kai baka ganin duk gidan kamar anyi mutuwa ba, ai duk gidan alhini suke, Da yake baka da babban waya baxa ka gani ba” Driver ya kallesa da kyau yace “Tsaraici?” Mai gadi ya kwashe da dariya yace “Yo tsaraici mana, yar kamfai da rigar mama kawai ne a jikinta kuma hoto me motsi aka mata, duk halittar jikinta babu wanda bai fito ba malam, abun dai ba a cewa komai, ni Alhaji ne ma ke ban tausayi don ya shiga damuwa sosai” Yana kallon mai gadin yace “Kai a ina ka gani??” Mai gadi yace “Toh jira ka ga ikon Allah” yana fadin haka ya nufi boys quarters da sauri, ba a dau lkci ba sai gashi ya dawo rike da wayar saminu, ya mika masa, amsa yayi ya danna play a video din, ko second goma bai yi da kallon ba ya ajiye wayar gefensa yana kallon Mai gadin, Mai gadin ya kwashe da dariya yace “Toh dada, muma duk haka muka gani, Allah kadai yasan iyakar inda abun nan yaje, shi ma a wani gruf ya gani wai, har fesbook yace min ya gani, kaga daga yanxu sai dai ta daga ma wasu kai ba mu ba kuma” Dariya mai gadin ya kyalkyale da, Driver ya mike yace “Ga takalma in ji Alhaji a ba shoe shine…

 

Download NIHAAD Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button