Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 30 Book 2 Complete Novel

  

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

                                  Firgit jahad tayi daga zurfin tunanun da ta shiga tana faman sauke ajiyar zuciya, ɗagowa ta ɗanyi ta kalli hafsat samunta tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace “Tun ɗazu na lura da kallon da kike yi mun Jahad, na menene? 

  ɗan sunnar dakai jahad tayi tace “Babu komai kawai ina mamakin yarda kika canza mana ne ba kamar da ba, kin nuna tausayi agare mu, ba muyi tunanin haka ba,

   Hafsat tace “Nima kaina nayi mamakin yarda na canza wurin nuna muku tausayi, bayan ba hali na bane gaskiya, tun ina yarinya bani da tausayi ko kaɗan kuma bana son mutun mai tausayi, ban sani ba ko kunayin addu’a ne shiyasa Allah ya kawo muku sauƙi ta 6angare na…..’ ta ƙare maganar tana kallonsu,

   Jinjina kai Jahad tayi jin abunda hafsat tace, Lallai ne Allah ne ya amshi addu’arsu ya kawo musu sauƙi ta wurin hafsat,

   Ajiyar zuciya Jahad tasa ki tare da juyawa ta kalli hosana wadda ke zaune wuri da ido, taci ta ƙoshi tayi hani’an,

   Hafsat tace “Ga maganin da dr yace abaki, tun da kin kammala cin abincin bari na baki ki sha, sannan zuwa anjima insha Allah zamu koma gida,”

  jahad tace “Allah ya kaimu lafiya,” 

 “Ameen,” ta amsa mata sannan tasanya hannu ta ɗauki ledar maganin,

 ta shi ga fiddo su tana duba su, kafin tasanya hannu cikin basket ɗin da tazo dashi ta ɗauko robar ruwa, ta buɗe ta bayan ta ciro maganin ta miƙa ma hosana tare da ruwan tana kar6a tana sha, haƙiƙi su Hosana da jahad ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, saboda sun ga tausayinsu ƙarara a fuskar Hafsat kuma da alamun zasu samu sauƙi ta 6angarenta,

   *Shin Ya maganar matar da ta ba Hafsat miliyan shidda don ta zubar mata dasu Jahad? Kuna ganin zata fasa wannan aikin ko kuwa*? 😳

  AUNTY BABBA

Sam ta gaza samun natsuwa hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hafsat ta fara damuwa da twins ɗin da OMAR ya kawo, tabbas dole ta ɗauki mataki akan hakan, kuma haryanzu tana akan bakanta na sai tasa an zubar mata dasu Hosana da Jahad, 

  *Tabbas dole na ɗauki mataki akan hakan*

  tayi maganar tare da dakatawa daga zirga zirgar da takeyi acikin ɗakin nata, fitowarta kenan daga wanka, ta zumbula doguwar rigar Buba ta Material, hannu takai ta ɗauki wayarta dake ajiye saman stool dake agaban mirror,

  cikin hanzari ta shiga contact ta dannawa wata number kira wadda tayi saving ɗinta da *BABA ALAMU*

 Nan da nan kiran yashiga wayar ta soma ringing zuwa wani lokaci mai numbar data kira ya amsa wayar,

  Cikin sauri tace “Assalamu Alaikum,” 

  daga can 6angare wata murya kakkausa ta gawurtattun ƴan iska ta amsa mata da cewa,”Hajiya Laila manyan gari, ashe kuna neman mutane? Ae nayi tunanin daga in da amfanin mutun ya ƙare a wurinki yazama shara……’

  dakatar dashi Aunty Babba tayi da cewa “Baba Alamu ! mu aje wannan gefe, wlh ina cikin tsananin damuwa ne, tunawa dakai yasanya na kira ka domin nasan kai kaɗai ne zaka iya yi mun wannan aikin…..’ ta ɗan dakata tana jiran amsar da zai bata ,

  Baba Alamu yace “Ae dama ke ba’ki ta6a neman mutun sai in buƙatarki ta taso, tun da ansan muna da amfani ae a rinƙa ɗan kiran mu ana bamu hasafi don tafiya tayi kyau ko?, yanzu dai faɗa mun me kike so in aiwatar kawai ! Wa kike so akashe miki har lahira? Ko wa kike so In Naƙasa Miki kasusuwansa ajefar bayan Duniya?😳

 

   Dariya aunty babba tayi cikin jin daɗi tace “Yawwa Mutumina, dama nasan kaine kawai zaka iya share mun hawaye na, abunda ke faruwa wani ƙanin Mijina ne wlh ya tsinto wasu ƴan mata tagwaye ya kawomin a gida na, na tsani yaran nan ko ganin su bana son yi, saboda zasu tarwatsamun target ɗina abunda nakeso kawai so nake kazo ka ɗauke su  Ka fitar mun dasu daga gidan nan ka kai su can bayan gari ka jefar mun dasu Can cikin ƙurmin daji wanda zasu rikice su gaza gane hanyar da zasu fita daga cikin shi,”😳

  tamkar tana agabansa haka take masa bayani tana faman cizon la66a, 😠

 fashe wa da dariya baba Alamu yayi daga bisani ya tsagaita yace “Ƙaramin aiki kenan, ni nama yi tunanin wani za’a kashe maki ne yanzun nan mu kai shege lahira, amma tun da wannan ne kada ki samu damuwa, yanzun dai bana nan kinsan naje lagos ƙarƙashin gada amma maƙo mai zuwa bi iznil lahi, aikin ki zai kammalu, ƴan Canji kawai zaki tanada “

    Aunty Babba tace “in dai wannan ne an gama, zanyi maka biya na musamman  babban kaso mai tsoka,

  Baba Alamu yace “Shikenan sai kin jini, da zarar na dira kaduna zan zo da rugwagwar mota ta na kwashe Maki Sharar azubar abayan gari,’😂

   Jinjina kai aunty babba tayi har wani sauke ajiyar zuciya take yi jin burinta zai cika na kawar da su Jahad, 

   Sun jima suna waya da baba Alamu kafin daga bisa sukayi sallama, ta ajiye wayar saman mirror tana cewa “Yanzu abunda ya rage mun shine, na dakatar da Omar don nasan zai iya zuwa yace zai tafi dasu na lura da hakan I ave to do something ❗‼ ………!😥 wani irin shu’umin murmushi tasa ki, saboda plan ɗin da ta tsara,

*********

Sai wuraren bayan Sallar La’asar sannan dr yayi discharge ɗinsu daga asibitin kamar yadda hafsat ta buƙata don bata son zaman su a asibitin gudun kada Omar yayi musu Dirar Mikiya, duk da dr yaso ya ƙara ma hosana Jini amma ta hana hakan sai dai tayi alƙawarin cewa zata mai do ta asibitin Next time, 

   A hankali take driving ɗinsu acikin motar, hosana na’a a back seat kwance sai faman sharar bacci take yi, yayin da jahad ke agefen  hafsat dake driving,  adai-dai wani Store ta tsaya da motar, sannan ta kalli jahad tace “Ki kula yanzu zan dawo,”

 Jahad ta amsa da cewa “Toh Aunty”

  Shiga cikin wurin tayi bayan wasu mintuna tafito hannunta ruƙe da leda, ta buɗe motar ta shiga miƙa ma jahad ledar tayi tace “Ruƙe wannan a wurin ki,”

Amsa jahad tayi ta ƙanƙame ledar a hannunta, sannan hafsat taja motar suka tafi gida kai tsaye, 

  Bayan tayi parking suka fito daga motar daker jahad tasamu hosana tafarka ta ruƙe hannunta suka nufi ciki hafsat na biye dasu, sai faman jin fargabar haɗuwa da Aunty babba suke yi,

  Aikuwa suna shiga suka same ta zaune a babban falon saman sofa tana faman danna wayarta,

   tana ganinsu ta miƙe tsaye tare da cewa “Sannun ku da dawowa, Allah sarki hosana da jahad kuyi haƙuri ban samu damar zuwa asibiti ba na dubo ku, Ya jikin naku”? ta faɗi cikin nuna tausayin su,

  ai ba su jahad da hosana ba hatta hafsat tayi mamakin jin abunda Momyn nata tace lokaci guda ta canza tamkar ba ita ba, tsayawa sukayi suna kallonta baki asake,

 Ganin hakan yasa aunty babba ƙarasawa ta ruƙo hannun kowannan su , sannan cikin sanyin murya ta wanda yayi nadama tace “Haƙiƙa nasan na cutar daku sosai, Allah ma ba zai yafe mun ba, tabbas jiki na yayi sanyi, nayi danasanin abun da na aikata muku dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun……..’

  Hawaye ne suka soma saukowa daga idon aunty babba fuskarta duk a yamutse tana kallonsu,

   cikin mamaki hafsat tace “Shin mafarki nake ko gaske!? Mom are u serious about what are u sanying? Ko dai kin sha wani abu ne bayan na fita? kece dakan ki kike danasani hada neman gafara a wurinsa? 

   ɗago ido aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace “Shin ni ba mutun bace kamar kowa daba zanyi laifi na nemi gafara ba”? na zauna nayi wani tunani menene riba ta idan na cuci waɗannan bayin Allan? Allah fa dakansa ya haramta ma kansa zalunci kuma ya haramta shi atsakanin mu, kuma yace kada muyi zalunci, amma ni na kansance mai son zuciya……….’

   Sam ta kasa ƙarasa maganar saboda shessheƙar kukan da tafara, juyawa hafsat tayi ta kalli jahad yayin da ita kuma jahad idonta na akan Hosana wadda ke kallonta, gaba ɗayansu mamaki ne ke ɗawainiya dasu, shin taya zasu gasgata tuban da Mommyn hafsat tayi? Anya ba wata ƙullalliya bace?

  “Naji kunyi shiru baza ku yafe mun bane? In har baku yafe mun ba bana ji zan iya bacci adaren nan,” 

  Cikin sauri Jahad da hosana suka haɗa baki wurin cewa “Aunty mun yafe miki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya,” 

   Murmushi Aunty babba ta saki tare da sa hannu ta haɗa su duka ta rungumesu ajikinta, tana faman ci gaba da basu haƙuri akan kuskuren da tayi masu na jibgarsu da tayi,

  Jikinsu duk yayi mugun sanyi, gaba ɗaya kwalwarsu ta rikice sun rasa gane dawa zasu YARDA? SHIN HAFSAT ko MOMMYNSU? Taya hakan zaiyiyu ace lokaci guda sun canza musu izuwa mutanen kirki masu tausayin su? 

  Bayan aunty babba ta janye su daga jikinta ta mayar da idonta kan na hafsat tace “daughter daga yau inaso ki ɗauke su tamkar ƙannen ki, ni kuma insha Allah zan ɗauke su tamkar nice na haife su, zan basu duk wata kula daya dace uwa tabawa ya’yanta, “

  Murmushi hafsat tasaki tare da cewa “Insha Allah mommy as from now hosana da jahad sun zama ƴan gida, zasuyi rayuwar ƴanci acikin gidan nan, babu wanda zai sake cutar dasu acikin mu,” 

   Jinjina kai aunty babba tayi sannan tace “ina so daga yanzu su koma ɗakin Ladi mai aikin mu da kwana,”

 Hafsat tace “a’a Mommy, mattress ce kawai acikin ɗakin, gaskiya ni nafison su dawo bedroom ɗina da kwana yadda zanfi basu kulawa,”

   Aunty babba tace “hakan ma yayi, yanzu yakamata ku shiga ciki ku huta, sannan hafsat ki taimaka ma hosana tayi wanka da ruwa mai ɗumi ko taji daɗin jikinta,

  Hafsat tace “insha Allah mommy,” sannan ta mayar da idonta kansu hosana tace “mu shiga ciki,” hannun su cikin na juna suka bi bayan hafsat har izuwa cikin bedroom ɗinta, 

Da taimakon hafsat hosana tayi wanka  ta canza kayan jikinta izuwa doguwar riga mara nauyi, bayan ta kammala hayewa kawai tayi saman gadon hafsat, tana jiran zuwan jahad wadda ta shiga toilet yin wanka itama, Ajiyar zuciya kawai hosana ke saki amma tana jin fargabar canjin da su ka gani wurin hafsat da Mommynta, sam bata amince dasu ba, kuma taci Alwashin muddin YA OMAR yazo ƙafarta ƙafarshi sai ta bishi, 😠

 **********SEHRISH**************

A gajiye ta shiga cikin bedroom ɗinta bayan sun kammala gyare-gyaren gidan, sai lokacin tasamu damar yin wanka tare da alwala tafito ɗaure da towel, agaban dressing mirror ta zauna saman kujera tana Shafa mai ajikinta, bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare, sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗin kayanta, ta ɗauko dogon skirt brown color ta zura sannan ta sanya t-shirt fara, daga nan ta zura hijab tare da shimfiɗa carpet tayi sallah anatse, tun kafin ta kammala azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo, wuri ta samu gefen gadonta ta xauna,

   bayan sehrish ta kammala sallar ta naɗe dardumar ta mayar da ita cikin wardrobe tare da hijabin, sannan ta juya da fara’a tana gaishe da azmee “Ina yini aunty azmee,”

  Azmee tace “lafiya lou sehrish, zo ki zauna,” 

   Ƙarasawa tayi ta samu wuri kusa da ita ta zauna, azmeee tace “sehrish wai ina wayarki take ne? Na lura tun ranar dana baki ita, ban sake ganinta a hannunki ba, kodai baki so ne?

   zuru sehrish tayi don ita tuni ta manta da zancen wata waya, kuma ba kowa bane yaja mata hakan ba face haroon, shine silar damuwar da tashiga harta manta in da ta jefe wayar

   “Ina sauraron ki ina wayar”? Azmee ta ƙara nanata mata, cikin en ina sehrish tace “Aunty azmee tun….ranar…da…kika…ban…ita..na manta inda na ajiye…ta,’

  ta ƙarasa maganar tana ɗan kallonta azmee tace “Sehrish kenan kin cika shiririta yanzu wayar mai tsada ita kika 6atar? To ina so ki nemo ta yau ɗin nan duk inda take, in ma saman ceilling kika turata ki hau saman ki fiddo ta, Ki kawo min ɗaki na ina jiranki,!” tana faɗin hakan ta tashi ta fuce……..

   tafa hannu sehrish ta shiga yi tana tunanin ta ina zata fara neman wayar, ita kanta abuƙace take da wayar ko don ta rinƙa ɗebe kewar zama ita kaɗai aɗaki, 

   Tashi tayi cikin ƙanƙanin lokaci ta hargitsa ɗakin wurin neman wayarta, duk ta zabure har ƙarƙashin gado ta leƙa, ta bincika cikin laundry basket ɗinta, gaba ɗaya ta zazzago kayan wankinta dake cikinsa babu komai, agajiye ta mayar da kayan, zarya tashiga yi tana tunanin ina ta wurgar da ita, ci gaba da neman wayar tayi, a ƙarshe tayi deciding zuwa ɗakin junaid ta roƙesa ya kira layin wayar ko tayi ringing,

   cikin hanzari ta ɗauki mayafinta dake ajiye saman bed ɗinta, ta yarfa shi a head ɗinsa, sannan ta fita cikin sauri babu kowa a babban falon direct upstairs ta wuce da ƙarfi take tattaka stairs ɗin ko kallon gabanta batayi burinta kawai ta isa bedroom ɗin junaid,. 

    Kamar daga sama taji ta bugi wani abu da ƙarfi nan take wani irin jiri ya kwashe ta, agigice tasaki wata irin ƙara ganin yarda ta tafi gaba ɗaya zata faɗi amma ina tuni yayi mata wani irin kwakkwaran ruƙo da hannu guda ya tallabo waist ɗinta,

     Zazzare ido sehrish tayi cikin Jin tsananin  tsoro yayin da take faman sauke ajiyar zuciya,

  gabanta ne ya soma faɗuwa saboda tuna hannun wa take a ruƙe, sam tagaza ɗago ido ta kalle sa, ae tun daga ƙamshin turaren nan nasa ta shaida kowane ne, 

  ɗago da ita yayi ta tsaya da ƙafafunta sannan ya wuce abunshi, juyawa sehrish tayi cikin sauri tana kallonsa ba ƙaramin wanka ya ɗauka, har sai da ya fice daga babban falon sannan ta kawar da idonta sannan ta ƙarasa haye wa upstair ɗin, har time ɗin jikinta wata irin kerma yake yi hannunta na dafe da ƙirjinta,

   A hankali tayi knocing ƙopar ɗakin junaid tana buga ƙopar a slow saboda zuciyarta dake tariyo mata abunda yafaru yanzun nan,

   kusan 3 times tana knocking sai daga bisa tajiyo muryar junaid yace “Come in,” 

   Ashe door ɗin a buɗe take, tana zura ƙafarta ciki karaf taci ido dashi gaban mirror daga shi sai short towel a waist ɗinsa sam baisan cewa sehrish bace, ta cikin mirror ya hangota, aikuwa cikin sauri yace “dakata !! Kada ki shigo! Ja baya,” dariya sehrish tayi sannan taja da baya ta tsaya jikin ƙopar tana cewa “Junaid yaushe ka fara jin kunyata har haka”?

    daga cikin ɗakin tajiyo muryarsa yana cewa “tun ranar dana gane cewa ke maca ce…..,’

   Murmushi ta saki tana faman sauke ajiyar zuciya har time ɗin temperature ɗin jikinta yayi mugun zafi ba don komai ba sai don abunda yafaru da ita yanzun nan,

   “Come in Sehrish,” junaid ya faɗi,

  Shiga ciki tayi a lokacin harya zura jallabiya ash colour ajikinsa yana gyara hannun rigar, 

   wuri tasamu agefen gadonsa ta zauna tana cewa “Junaid dama wannan wayr tawa nake nema narasa inda na jefar da ita, shine nazo ka taimaka ka kiramin layin dake cikinta, may be in tayi ringing in gano ta,

  Murmushi junaid yasaki kafin yace “shikenan zan kira maki ita, amma under one condition? Ya faɗi ayayin da ya tsaya agabanta ya ruƙe qugu, sehrish tace “Menene sharaɗin?

   Junaid yace “Tun ran nan nake ta fama dake ki nunamin gyaran gashin ki kin ƙiya, to yau indai kina So na kira layin wayarki sai kin cire mun nagani” ya faɗi yana murguɗa mata baki,

    Yamutsa fuska tayi tare da cewa “look junaid yanzu ba lokacin wannan bane, am not in mood  Just ka kiramun wayar,’ ta faɗi tana tsuke baki,

   Bin shi tayi da kallo ganin ya ɗan ɗaure fuskar shi alamar baiji daɗi ba, 

  Cikin lallashi tace “junaid are u angry with me? Am sorry pls ni bazan so naga king of smile ya koma king of Angry ba,’  tayi maganar da ɗan zolaya, 

  Ɗan sakin fuskarshi yayi sannan yace “its ok, go back to ur bedroom i wanna call u righ now,” 

 Murmushi sehrish tasaki tare da cewa “yawwa mutumi na, Allah yabar mun kai,” ta faɗi tare da miƙewa ta wuce bedroom ɗinta cikin sauri,  

   Junaid kuwa acikin ransa yace “Ameen sehrish Allah yabarmun ke till the end of my life,’  sannan yasa hannu ya ɗauki wayarsa dake ajiye saman mirror, contact yashi ga tare da lalubar nombar sehrish da yayi mata Saving da*FUTURE DREAM* sa’an nan ya danna mata kira,

   tunkan sehrish tashiga ɗakinta ta rinƙa jin ringing ɗin wayar da ƙarfin gaske, tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga ciki tana bin inda sautin ke fitowa, ashe tana cikin bedside drawer ɗinta, duk wannan uwar wahalar da tasha, cikin hanzari ta janyo drawer chest ɗin gida na farko, sai ga wayar ajiye sabuwarta kusan 1 month kenan tana ajiye bata mutu ba, saboda ruƙon chargyn ta,  ajiyar zuciya sehrish tasaki tana shasshafa screen ɗin wayar da hannunta, 

 

KARANTA ZAFAFA 2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

. …………………….tuna da azmee dake jiranta yasanya ta fice da wayar cikin sauri ta isa ƙopar ɗakin azmee knocking tayi daga ciki taji azmee tace “in kin son bada wayar kika zo ba ki koma,” wato har ta gane ce sehrish ce ta kwankwasa mata,

    Gyaran murya sehrish tayi tare da cewa “Tare da wayar nazo aunty azmee,”

    Azmee tace “shigo ciki,”  

 Tura kopar sehrish tayi ta shiga, samun ta tayi kishingiɗe saman gadonta, ganin sehrish yasa ta tashi zaune tana cewa “yanzu naji magana,”

   Murmushi sehrish tasaki tare da samun wuri gefen azmeen ta zauna sannan Ta miƙa mata wayar tace “Gata,”

  Azmee ta kalli wayar tare da cewa “dama ba wani abu zanyi da ita ba, ke nake so ki runƙa amfani da ita akai-akai takasance tare dake, saboda daga yanzu duk wani mai buƙatar wani abu ke zai kira kai tsaye a waya yasanar miki,” jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayaninta,

  Sannan azmee taci gaba da cewa “nikam inaso na tambaye ki, shin kin ta6a yin makaranta ne before?

   ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta a wani irin yanayi kamar wani abu yaɗan sosa mata zuciya, shiru tayi na wani lokaci kafin tace “eh nayi primary bayan nan nafara secondry karatun duk ashiriri ce ƙarshe ma muna gab da zamu shiga ss3 nadaina zuwa gaba ɗaya……’ ta ƙarasa maganar asanyaye 

   Azmee tace “yanzu kina da burin ci gaba da karatun ne ko kuwa a’a? Ta tambaya tana kallonta,

   Sehrish tace “ina so mana sosai, ina so nayi Ilmi saboda wata rana nima nazama abun alfahari, kuma wannan burin mahaifiyarmu ne, tun lokacin da ta haife mu takance Sehrish zata zama Achitecture, Hosana kuma Doctor, Jahad kuma Nurse haƙiƙa inaso nacika mata wannan burin nata…………………..’ idonta ne suka cuko tab da kwalla sunnar da kanta tayi ƙasa tana kallon wayar dake hannunta,

  Cikin mamaki azmee ke kallonta ita kanta sehrish batasan me take cewa ba, ci gaba da magana tayi kawai tana cewa “Allah sarki a lokacin ni nafi kwarewa wurin yin zane, hosana ce mai ƙoƙari acikin mu amma yanzu bata da cikakken hankali tun lokacin da ta duro daga saman window mai tsayin gaske ……….ban……ban…….

 Kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata nan take ta fashe da matsanancin kuka, 

   Gaba ɗaya hankalin azmee ya tashi sam tarasa gane ma sambatun da sehrish ke yi, cikin ruɗu tace “sehrish wai meke faruwa ne? Su wanene waɗannan kike magana akansu ne? ƴan uwanki ne?

  ɗaga mata kai tayi alamar “Eh” jinjina kai azmee tayi tare da cewa “share hawayenki daina kuka ya isa haka, duk da bansan Labarin ki ba amma ina da tabbacin cewa wani mummunan abu yafaru acikinsa wanda ke yawan saki cikin damuwa, don haka zanso naji labarinki sehrish amma ba yanzu ba aduk lokacin da muka samu free time sosai zamu zauna ki bani shi tun daga farko har ƙarshensa,’

  “Insha allah aunty azmee na yarda dake sosai baxan 6oye maki komai ba,” ta faɗi ayayin da take share hawayen ta,

  Bayan sun samu natsuwa su duka azmee taci gaba da cewa “Zaki fara zuwa school insha Allah….’

  Cikin mamaki sehrish ta ɗago ta kalle ta tare da cewa “Makaranta? Ni kuma? Aunty azmee taya za’a ɗauke ni a school bayan ko takardun kammala primary ɗin bani dasu na rasa su,’ 

   “Kada ki damu sehrish wannan ba wata damuwa bace, komai za’a iya yi maki shi insha Allah, kuɗi ne kawai ke magana, kuma ni zan tsaya maki harki samu don nasan muddin na tuntu6i koda kanal yusif ne da maganar zai iya sama maki hanya, bama shi ba junaid zai iya yi maki wannan hanyar cikin sauƙi ki fara daga ss1 daga baya kin zana Jsce in time ɗinta yayi,’ 

   Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish har tagaza rufe bakinta, aranta tana cewa nan bada jimawa ba nima zan fara zuwa makaranta kamar kowa ?Alhamdulillah 😇

  Hannu azmee tasanya ta kar6i wayar hannun sehrish tana cewa “ina fata junaid ya nuna miki komai ko? 

   “Eh harma ya tura mun wasu apps ɗin da zanyi amfani dasu,”

 Azmee tace “okey, idan kina so kiyi amfani da data ko wurin yin browsing da sauransu just Wi-fi kawai zaki kunna, ‘

   Jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa, sun ɗan jima suna fira kafin daga bisani ta sallame ta,  komawa bedroom ɗinta tayi cike da murna koba komai in tafara zuwa school zata haɗu da friends irinsu Hafsat Bature Domin ɗebe kewa 😇

  Sehrish first day at school 😮 Can’t wait to see 💃💃💃💃

   

  

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Ga wanda ba suyi payment ba su hanzarta su biya before end of this week👍 Yanzu littafi Zai fara 🔥🔥🔥 (08103884440) ayimun magana direct

Back to top button