Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa Malaman addinin Musulunci gargadi da masu amfani da shafukan sada zumunta da su lura da abin da suke fada domin harshe ka iya kai su ya baro.
Cikin wani hoton bidiyo na minti biyar da kwamishinan addinai na Jihar Kano, Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya yi, ya bayyana matsayar Gwamnatin Jihar Kano kan ce-ce-ku-cen da ya barke bayan yaduwar wani bidiyo da Sheikh Daurawa ke magana a kan al’aurar mata da kuma martanin da Nafisa Ishak wata mai amfani da shafin Tiktok ta yi.
A makon da ya gabata ne, Sheikh Daurawa a wani bidiyo aka ji yana ba da misali da yadda al’aurar mata ke da muni duk da cewa yana cikin kawa duniya.
Hakan ya sa mutane suka yi ta mayar da martani daga bangarori daban-daban, sai dai mafi jan hankali shi ne na wata mai amfani da shafin Tiktok, Nafisa wacce ta yi kakkausan martani ga Malam Daurawan.
Daga baya kuma wani malamin mai suna Asadus Sunnah ya yi nasa bidiyon yana gargadin Nafisan tare da yin barazanar cewa suna da yaran da za su tura su yi maganinta.
Kwamishinan addinan ya bayyana cewa abin da ya sa gwamnati ba ta yi magana tun da farkon lamarin ba, saboda ta tsaya tattara bayanai ne daga bangarorin kafin yanke hukunci.
Baba Impossible ya fara da bayani ne kan cewa Malam Daurawa bai yi daidai ba kan bayanan da ya yi, yayin wani karatu a ranar Litinin wanda yake yi kullum.
“Gwamnatin Jihar Kano ta ji ta kuma saurari abubuwan da ke faruwa duka, ta tambayi malamai da masana, an kuma ji bangarori daban-daban kuma an kalli jawabin kowa.
“Abin da ma’aikata ta tsaya a kansa, kamar yadda muka ji daga bakin malamai, shi mai jawabi na farko ya yi kuskure a jawabinsa, kamata ya yi ya tsaya kan kala Allahu kala Rasulihi.
“Idan akwai wani karin bayani kar a yi shi cikin yadda zai ta da kura ta yadda zai zama kamar akwai batsa, kamar akwai cin mutunci, kamata ya yi a saka ya shi.
“Don haka tun a nan muka fuskanci akwai kuskure a jawabin da ya yi,” in ji Baba Impossible.
Ya ci gaba da cewa malami ba ma’asumi ba ne zai iya yin kuskure, don haka idan malami ya yi kuskure ya iya gyarawa.
Da yake bayani a kan Nafisa Ishak, Kwamishinan ya ce ita ma a jawabanta akwai kuskure masu yawa kuma sun yi nazari kansu.
“Ba ta cikin rukunin wadanda za su iya mayar wa da Malamin martani, idan malami ya yi Magana, malami dan uwansa ya kamata ya mayar masa da martini, idan da kuskure ya fada masa cewa bai yi daidai ba ya gyara. Amma ba ita da take matar wani ko budurwa ko bazawara ba.
“Maganganun da ta yi sun yi tsauri, don haka ba mu yarda da abin da ta fada ba, ba daidai ba ne, ko da yake dai ba zagi ba ne kai tsaye, amma zagi ne idan aka kalli yadda ta furtasu.
“Gwamnati ba za ta yarda da daukar doka a hannu ba, ba wani abu ba ne ya fi tayar wa da Gwamnatin Kano hankali ba, face kalaman malaman addini.
“Jawabai da muka ji daga wasu Malamai a kan mumbarin ko a makaranta, wani Malami an ji shi yana cewa, suna da matasa suna da ‘yan daba wadanda za su iya turawa.
“Idan sun ce a yi wa mutum duka a yi masa in sun ce a kashe mutum, a kashe mutum, wannan babban lamari ne wanda gwamnati ba za ta zuba ido a kansa ba.
“Sannan a cikin jawaban da aka rika zagin wannan yarinya da mayar da martani wadansu suna cewa za su sace ta, wasu na cewa za su yi mata fyade wasu na cewa za su kashe ta, to wannan abin ya tayar da hankalin gwamnati,” in ji kwamishinan.
Ya ce kowa ya sani cewa jami’an tsaro na kallo tare da bibiyar wadannan mutanen da suka rika yi wa wannan yarinya barazana, kuma matsayar gwamnati kan wannan bincike da ta yi shi ne ba za ta yarda da dabanci ba, ba za ta yarda da daukar doka a hannu ba, ba za ta yarda da don an bata wani wani ya fito ya rama ba.
Ya ce abin da yake a doka in ji kwamishinan shi ne, duk wanda aka taba nasa kuma yake ganin ba zai hakura ba sai ya tafi kotu.
Ya kara da cewa ‘yansanda za su bincika su gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu kuma kutu ta yi masa hukunci.
“Muna kira ga su malamai su san abin da suke furtawa kuma su iya bakinsu, su rika furta abin da zai amfani jama’a,” in ji Baba Impossible.