Novel Document

Inda Rai Book 3 Hausa Novel

Inda Rai Hausa Novel By Garkuwa

Description/Story:

Inda Rai Book 3 Hausa Novel

Written By Aisha Aliyu Garkuwa

 

Description

Yar uwa kinsan illar dake tareda infection kuwa,to bari kiji kadan daga cikin illar da infection yake da ita,kinsan cewa infection yana hana haihuwa,yana hana ma’aurata jindadin mu amala,yanasa warin gaba kowane irin tirare kika sa bazai hana wannan warin fita daga jikin kiba fitar farun ruwa kaikayin gaba tusar gaba duk suna daga cikin illar da infection yakewa lfyr ki.
Ina masu fama da ulcer, Asthma,sickle, ina matar dake fama da fibriod, matsalar rashin haihuwa ko bushewar jiki da fata haddake mai son hibs da breas ina uwar gida maison faranta ran oga a othe room kema ba abarkiba jawarawa da yanmata ku garzayo kuma ku kwada ku gani da ikon Allah da izinin Allah munada VIP chair akwai blood circulatory machine kedai kira number nan domin karin bayani 07035275119 ko kiyi joining group dinmu dan gani da ido👀 sai kunzo ngd https://chat.whatsapp.com/LqcXIrhogcQC1iLdGGNJcZ

Spjg
“Ban fahimci me ɗaya kake son bayyana mana ba Tajudden kana neman mu baka izinin fara neman Mamana ne ko,ko kana gabatar da soyayyar kane? Ko neman Aurenta kakeyi gaba ɗaya!?”.
Ya kai karshen maganar yana kallon Taj kallon cikin ƙwayar Idanu saboda tuna cewa shin meyesa Tajuddeen bai zo da iyayensa ba saboda duk cikin falon baiga ɗaya daga cikin wanda zai iya kasancewa mahaifansa tunda dai yasan shi ɗan ƙasar Ethiopia ne waɗanan kuma duk yasan mutanen ƙasarmu be kuma sanannun ma, sai kuma ya juya idanunsa ya kalli Tajj jin yana cewa.
“Duk abu uku nake haɗewa awaje ɗaya Uncle Bello idan zan samu duk abinda kuka min akai ku mallaka min Ishmah shine burina da Fatana shine kaɗai abinda zai samar min nutsuwa ita kaɗai ce zata zame min tsagi da zai cike gurbin da na rasa, itace kuma zata zeme min inuwa da zan samu in fake”.
Cikin rashin walwala da jin wani irin kallo mai nuni da bincika yace.
“Kuma sai gashi banga waliyyanka ba ko kuma ince magabatan kaba”.
Cikin sauri Sheikh Tijjani Taju Usman Bauchi yai gyaran murya wanda shine Babban ɗa ga Sheikh Tajuh Usman yace.
“Gamu nan mune matsayin waliyyansa kuma magabatansa kuma shaƙiƙansa”.
Anutse Abba ya gyara zamansa tare da sakin wani lallausan murmushi.

Atare suka juya suka kalli Sheikh Tajuh Usman Bauchi jin yana cewa
“Ni da kaina zan wakilci Aurensa sannan in daura auren zan kuma yi farin ciki idan kuka bashi Auren Ishmah zan kuma shugabanci al’amarin in shige masa gaba akan komai saboda matsayinsa mai girma ne awajena nima kuma matsayina halattaccene a wojensa”.
Cikin sanyi suka sauƙe numfashi sai kuma suka kalli juna tare da yin ƙasa da kansu jin Dottijon nayi musu kalamai masu kama zuciya.

Cikin sanyi suka fara yunkurin miƙewa tsaye jin Sheikh Taju Usman Bauchi na cewa.
“Ku tashi mu tafi saboda lokacin sallah ya ƙara to”.
Daga nan suka fita suka bar gidan…

Acan cikin gida kuwa Ishmah ce zaune a falo yayin da akwatina set biyu ke gabanta set ɗaya Maroon color set ɗaya Milk color suna zaune ta juya ta kalli Aunty Nana tare da jan gajeren tsaki saboda wani irin iska mai sanyi da take ji yana ratsa jikinta haka nan kawai take jin zuciyarta yana mata sanyi haka gangar jikinta yayin da jikinta ke amsar baƙon yanayi wanda yafi kama da samar da nutsuwa da kwanciyar hankali wanda batasan sanadinsa ba cikin sanyi tace.
“Aunty Nana ki gani fa har yanzu babu wanda yazo kuma fa sun san munyi dasu ƙarfe uku zamu tafi mu kai kayan saboda mu samu kafin huɗu mu dawo muyi sallar la’asar agida kuma har yanzu basu zoba”.
Juyawa aunty Nana tayi ta kalleta tare da cewa.
“Wallahi fa nima abinda nace kenan?,Shiyasa ma kika ga nayi abinci da yawa saboda ina tunanin za’a zo muci abincin rana ne anan kafin mu tafi”.
Maryam dake shigowa ne ta karbi maganar da cewa.
“Ai dama sai da nace miki Kada kiyi wani abinci ki wahalar da kanki saboda Nasan da wuya azo da wuri kasancewar yau juma’a kuma in munje can ma Nasan abubuwan da zasu bamu in mun dawo shi za’a cicci abinci anan shiyasa ni ban shiga kitchen Bama”.
Ta ƙare maganar tana zama gefen Ishmah.
Dariya Rahama dake fitowa daga bedroom tayi tare da cewa.
“Ke dai Aunty Maryam kina nan wani lokaci idan mutum yace Miki marowaciya bai kyauta ba kina nan kamar Gajimare saboda kyauta, wani lokaci kuma in kinyi magana kamar ta marowata”.
Murmushi Maryam tayi kana tace.
“In kinga dama ma kice ni marowaciya ce”.
Dariya Rahama ta sanya tare da faɗin.
“Kuma kona faɗa babu yanda zakiyi dani tunda nice Autah shiyasa nake fadan abinda naga dama kuma in kwana lafiya”.
Murmushi sukayi dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamar Garkuwa.

Cikin jin daɗi da farin ciki Ishmah ta miƙe tare da amsa mata sallamar kana ta nufi Kofar Falon ta rungumeta fuskarta ɗauke da Murmushi tace.
“Sannu da zuwa kece kika riga kowa fara zuwa”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Aikuwa dai na riga kowa zuwa dama cewa nayi sai an saƙƙo Daga sallar Juma’a in zo”.

Gyara zamansa yayi tare da fesar da sassayan numfashi murya cike kamala da daraja ya fara motsa lips inshi cikin nusar wa yake maganar.
“Ita ƙaddara haka take juya fari ya koma baƙi, ko ta juya baƙi ya koma fari, haka Allah ke tsara abubuwa bi bayan bi, komai na faruwa tamkar yadda yake a ru babuce a lauhul Mahfouz, babu abin da ke sauya baƙar ƙaddara ta koma fara kamar kusantar Allah da addu’a mai cike da yaƙini da kuma tsananta wa wajan kiyaye dokokin Allah, haka babu rayuwa mai daɗi sama da bin Allah da manzon sa, kiyaye dukkan dokar Allah na saka hasken zuciya da kwarjini da arziƙi da ɗaukaka, ka bi Allah ka huta da masifar duniya, domin shi Allah ne ya ce kiyaye sallah na hana mutum aikata alfasha.
Ubangiji Allah ya ba mu ikon bin Allah sau da ƙafa.”
Tajj ya ƙara sa yana rufe alƙur’anin da ya biya wa Laylah.
Cikin nutsuwa Laylah ta ta ce.
“Amin Amin.”
Ta ƙare tana rufe nata Alkur’anin tana turawa Afisha abin wasanta.

Ishmah ce ta shigo da tirtsetsan cikinta tana wata iriyar tafiya kamar mai shirin faɗuwa ƙasa.

A hankali ta zauna muryarta na ɗan rawa ta ce.

“Ina zaton naƙuda ce…..”

Da sauri ya miƙe ya tunkarota ya taimaka mata ta miƙe suka koma ɗaki.
Yana dubawa ya ga tabbas haihuwar ce, yana ƙoƙarin taimaka mata wajan saka kaya Addawa ta shigo a ƙagauce.

“Laylah ta ce min ta ji Ishmah na faɗin naƙuda ce…”

Cikin tashin hankali ya ce.

“Ita ce, asibitin za mu tafi yanzun nan.”

Da sauri Addawa ta yo wajan Ishmah cikin kulawa.

“Sannu Ishmah, sannu kin ji daure, Ubangiji Allah ya raba lafiya, in Sha Allah cikin sauƙi za ki haihu kamar yadda kika haifi Afisha.”

Da Addawa da Tajj ne suka taimaka mata dan ilahirin jikinta rawa yake haka ciwon murɗa mata yake sosai cikin jin azaba bayan sun shiga mota ta kasa daure ta na nishi ta ce.

“Wayyo Allah na Yah Afif wannan ciwo! Ya yi min yawa ya ilahil alamina ka sassauta min, dan Allah Sheykh ka yi min addu’a.”
Sai kuma ta sauke Ajiyan zuciya tana fitar da wani irin nunfashi.

Idan ciwon ya lafa kuma sai gumi, da ya dawo sai ta ƙanƙame hannunta akan mararta tana nishin azaba jikinta na karkarwa ta ce.

“Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahlan wa anta taj’alul hazna iza shi’ita sahlan.”

Sai ta fara nishin azabtar jin zafi.

Da wannan ciwon suka isa asibitin, Dr Farida da Sister Nuraini, ce suka amshe ta.

Shi kuwa Tajj yana can neman zam-zam ɗin sa daya tanada dan ya yi mata addu’a.

Sai da ya gama ya kawo mata har a lokacin tana nuƙurƙusar azaba dan har ƙwalla sai da ta yi, duk jikinsa ya mutu murus hak hankalinsa ya tashi dan bai taɓa ganinta cikin wahala irin yau ba.

Sai kusan bayan minti goma kana ta fara nishin da ke tabbatar da fitowar ɗa.

Da sauri ya sha mur ya ce Dr Farida da Nuraini su fita ya yi supporting ɗin matarsa.

Ala dole suka fice dan dama sun san a rina sun saba,

Cikin hukuncin Allah ta haihu ɗan yaron na fitowa wani ya ƙara fitowa mahaifarsu kuma ta zama ɗaya, sun tabbata Identical twins kenan.

Tuni kukansu ya karaɗe asibitin, nan da nan Tajj ya yanke musu cibi ya shinfiɗe su kan ƙirjin Ishmah yana murna da farin cikin baiwar Allah a kansa na ba shi duk abin da ya nema, da fari ya nemi Afisha Allah ya ba shi yanzu ya nemi ƴan biyu ga shi ya samu duk maza.

Ita kuwa Ishmah duk da a gajiye take sai da ta ji tsananin farin cikin godiya ga Allah.

A lokacin da Tajj ya kuma yin sujudush shukur, a lokacin Dr Farida ta shigo tana cewa wallahi sai ta taimakawa Dr Ishmah ko me za a yi ayi, tana zuwa ya ɗebo yace ta gayawa dukkan ma’aikatan cikin asibitin tun daga kan Doctors har Nurses cewa zai ninka musu albashinsu na wannan watar. patients ɗin dake cikin Hospital ɗin kuma yau duk kyauta za’ayi musu komai.

Kowa cikin asibitin cike yake da murnan abin alherin da ya samu, kana bakunansu ɗauke da addu’ar Allah ya raya ya ƙara lafiya.

Ko da Laylah da Hamisu da Zulaihat da suka zo, dukkansu sun yi murna matuƙa.

Cikin jin daɗi Laylah ta ce.

“Ni ƴar gata, lokaci ɗaya na samu ƙanne maza har biyu ga Afisha ta kuma, alhamdulillah.”

Hamisu kam matsowa yayi kusa da yayarta yana cewa.
“Ku dai rayuwa na yi muku kyau, Allah ya ƙara kyawun rayuwa a gaba, duk sanda kika tashi haihuwa anty Ishmah sai ki haifa mana kyawawan yaran da za su zama abun kallo da ta’ujibi a wajan kowa, gaskiya ƴan biyu suna da kyau, ga kama nan sak da Afisha.” Murmushi tana tana kallonshi cikin son ɗan uwan nata da takeji duk Qatar bata da kamarsa.

Sai dare ta koma gida domin ƙalau take daga ita har yaran, Afisha da ta fara iya magana duk da ba sosai ake ganewa ba saboda tsamin baki irin na yara ganin kowa na murna itama ta fara murna tana ta nuna yaran tana magana.

“Amty lelah ce ta she kannena ne ko?”

Haka take ta faɗa tana nuna yaran tana murna.

Ko ta sunkuyar da kanta ta rinkayi karatun Qur’ani tana tofa musu.

Tun a daren Tajj ya raɗa musu sunan da tun kafin a samu cikinsu suka yanke shawarar sa. Ayeed da Ayaan. Rahma da Dr Amdaz ma a cikin daren ya kawo ta dan ta yi tsalle ta dire akan ita fa dole ta zo ta yi wa anty Ishmah zaman wanka, daƙyar ya lallasheta akan kwana ɗaya za ta yi ta dawo dan ya ce sai dai shi da ita su je gidan su tare dan ƙafarsa ƙafar matarsa.

Ethiopia kuwa sosai yan uwa suka rinƙa farin ciki da samun yan tagwayen Tajj More especially team Arfah da Imran.

Hakama su Abba a Nigeria.

Ranar suna kam sun sha shagali duk lecture aka yi kamar wancan sai dai wannan an yi sa ne akan falalar aure da tara zuri’a.

Ma sha Allah walima ta yi walima an raba kyautuka yara sun sha addu’a da fatan tsawon rai da Kyakkyawar rayuwa.

Tun da akayi suna Hamisu ya ɗauki hoton Ayeed da Ayaan ya tura wa Arfah da Imran suke tsananin murna dan sai da Arfah ya tura group ɗin su na dangi ya ce Uncle ɗin su na can Allah na azurta shi da zuri’a masu albarka, haka kuma ya turawa Ya Abana yana faɗa masa idan ya kore shi, to Allah ya raya shi da zuri’a cikin ƙanƙanin lokaci haka dai rayuwa taci gaba da tafiya….

BAYAN SHEKARA BAKWAI.

Hall ne faffaɗan gaske, da ya haɗa manyan malaman musabaƙa na duniya.
Ko wacce ƙasa da wakilanta da kuma ɗalibanta wajan…

Inda Rai Book 3 Hausa Novel txt

File Name   Inda Rai 3… Hausa Novel Doc.
Title    Inda Rai Book 3 Hausa Novel 
Author    Aisha Garkuwa
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    05/09/2024
File Size     263Kb
Format Size    TXT
Phone No   09097853276
Download Inda Rai Book 3 Complete Novel Document By A’isha Aliyu Garkuwa

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button