Zamantakewar Aure

Maganin Rage Yawan Sha’awa Don Matasa Marasa Aure

Hanyoyin Yadda Ake Maganin Rage Yawan Sha’awa

Matasa da yawa musamman wadanda ba su yi aure ba na korafin sha’awa na damun su. Kuma suna neman hanyoyin yadda za su magance yawan sha’awa.

A binciken da mukai mun gano akwai magungunan da ake yin amfani dasu don rage yawan sha’awa, amma sai dai binciken namu ya gano wadannan magunguna suna da illa sosai ga lafiyar jikin dan adam.

 

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Daya

 

Mu dai a addini babu wani magani da ake amfani dashi don rage is yawan sha’awa, amma duk da haka musulunci ya samar da hanyoyi, wanda mafita kawai kabi shawarar fiyayen halitta Annabi (S.A.W) kamar haka:

Maganin Rage Yawan Sha’awa 

Aure, yin aure da wuri, rashin aure na daga cikin abinda ke haifar da yawaitar sha’awa, domin idan kana da aure bakada matsalar yawan sha’awa. Yi kokarin yin aure domin rage karfin sha’awa.

 

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Ga Budurwa Da Matar Aure Kashi Na Uku

 

Azumi, yawaita azumin nafila yana taimakawa Kawar da tunanin sha’awa, idan kana da yawan sha’awa yi kokarin ku dinga yin azumi, domin azumi yana taimakawa wajen rage tunanin sha’awa.

Sallah, yawaita sallolin nafila bayan cika na farilla, shima yana daga cikin abinda ke tsare mutum daga yawan jin sha’awa.

 

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

 

Ibada, yawaita ayyuka masu shagaltarwa ga tunane tunane, kamar karatun Alqurani Maigirma, ko yin tasbihi da sauransu. Suna taimakawa shagaltar da mutum daga tunanin sha’awa.

Abinci, rage cin abunci masu motsa sha’awa na taimakawa wajen Kauracewa jin sha’awa. Domin akwai wasu nau’in Abinci da na sha dake jawo yawan sha’awa.

 

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

 

kiyaye ido daga kalle kallen haram, ku kiyaye kallon fina-finan batsa, domin kuwa suna daga cikin abinda ke haifar da yawan sha’awa da son yin Jima’i.

Amma haduwar kan malamai da duk wasu ma abota hankali da sanin yakamata babu hanyar da tafi dacewa wajen rage sha’awa da magance ta irin aure, sannan a yawaita azumi.

 

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

 

Don haka a matsayin ka na uba ko uwa ku ji tsoron Allah (SWT) ku tuna ya’yan ku amana ne a kan ku. Ku tuna lokacin da kuke matasa yaya kuke ji sanda kake saurayi ko budurwa yaya kuke ji idan sha’awa ta motsa muku. Don haka dole iyaye ku kula kuma ku aurar da yaran ku tun wuri.

kada yayanku sun isa aure amma dan son duniya ku hanasu aure, hakan laifine babba, kada don karatun boko ki hana yarki ko dan ki aure da wuri. Domin bpzincike YANUNA 95% na yanmata masu karatun boko suna matuqar son aure.

 

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

 

Kuma wallahi mafiya akasarin yan mata da samari da ba suyi aure da wuri ba suna biyawa kansu bukata kodai ta hanyar zina ko soyayyar jiki da jiki ita da saurayinta

ba tare da zinar farji ba, ko kuma ita karankanta ta biyawa kanta bukata.

Abin takaici kuma sunki karatu nakirki ba wanda za su taimaki yan uwansu mata kamar karatun lafiya mai zurfi, sai dai kawai su yi dan su samu abun duniya a karshe ya hana su zaman aure, alhali karatu bai hana aure.

Karanta>>> Abubuwan Da Ma’aurata Za Su Sha Don Samun Dauwamammiyar Ni’ima

Back to top button