Ruwan Zuma Page 32 Hausa Novel
(32) Bayan Laila ta 6oye fuskarta Haydar yayi shiru bai ce komai ba amma fara’ar dake fuskarsa ba za’a iya misaltawa ba. Cizon fatar cikinshi da tayi yasa ya dawo daga kogin tunanin daya fad’a yana kai hannu gurin, amma kafin nan yaji ta hura iskan bakinta a daidai gurin data ciza. “Bera ne yake haka Laila, idan ya ciji mutum sai ya hura iska saboda kar mutumin ya farka daga bacci.�? “So, you are saying nima Bera ce?�? Ta d’ago idanunta tana hararanshi cikin wasa. “Na isa? Ke sabuwar Amarya ce ai yau.�? Ya shafa fuskarta yana jin wani mugun sonta na k’ara hauhawa a zuciyarsa. “Better.�? Ta maida kanta ta kwanta. “Laila.�? Ya kira sunanta. “Na’am.�? “In fad’a miki wani burina?�? “Yes.�? Ta d’ago idanunta tana kallon kyakkyawar innocent fuskarshi da tun farkon had’uwarsu ya tafi da ita. Shima idanunsa na cikin nata yana aika mata da tsadadden murmushi mai sanyata shiga wani hali da take maraba dashi a yanzu. “Ina son idan nayi aure aka kawo mini matata in ga tayi k’unshi, tayi kitso, tayi kwalliya sannan ta lullu6e kanta akan gado tana jirana. Ina son kiyi haka.�? Ai da sauri ta mik’e zaune tana girgiza kanta, “Don Allah Haydar karka mini haka, zan yi lalle da kitson amma banda lullu6in Amarya. Wallahi kunya hakan zai bani, nifa ba budurwa bace.�? “Idan naji zan fad’a miki.�? “Ban gane ba.�? “Kiyi tunani.�? “Haydar.�? “Laila.�? “You are so stubborn wallahi. Ya Allah, mena aura?�? “Someone that will take you to cloud nine.�? Ya bata amsa yana kashe ido. “Baka da kunya.�? “Baki ga komai ba Laila, trust me.�?“An rufe gari Haydar, ya za’a yi in samu mai kunshi da kitso?�?“One of your staff gidansu a unguwar nan yake. Sai kije gidansu ta miki ko kuma ita tazo.�? “Amma kasan an hana fita ko k’ofar gida ko? Sojoji na yawo a kowanne lungu da sak’o, kuma ina tsoron Corona.�? “Ba abunda zai faru ki tashi muje in rakaki gidan.�? Ya mik’e tsaye ya shige d’aki ya d’auko jallabiyarsa da hijabinta ya fito yana sakawa. “Wallahi Haydar ina tsoron fita. Na iya k’unshi zan yi da kaina, kitso kuma kayi hak’uri idan aka cire lockdown zan je a mini.�? Fad’in Laila tana tashi tsaye. “Kin cika tsoro. Nikam ki tashi mu tafi kar lokaci ya kure.�? Ba yanda bata yi dashi ya hak’ura ba amma yayi k’ememe yace dole sai sun fita. Hand sanitizer ta d’auka tare da face masks, ta tilasta masa ya saka sannan suka fita maigadi yana musu sallama amma sai daya k’ara da cewa, “Amma Hajiya an hana fita fa. Nima sallamar iyalina nayi na dawo nan gidan zan zauna.�? “Kash! Kasan banyi tunanin hakan ba? Gaskiya ya kamata ka koma gurin iyalinka saboda bamu san ranar da za’a d’age wannan abun ba. Zamu yi magana da maigidana, duk yanda aka yi zaka jini.�? “Shikenan Hajiya.�? Ya bisu da kallo har suka fita, har gobe bai daina mamakin wai yaron daya taimakawa shine ya zama mijin uward’akinsa ba. Suna fita Laila ta fara zare ido tana kalle-kalle, Haydar ya rik’o hannunta ya jawota gefenshi suka fara tafiya. “Wai ya akayi kasan ina da staff a nan unguwar?�? “Mas’ud ne ya fad’a mini.�? “Wani irin magana kuke yi a kaina da har kasan hakan? Me Mas’ud yake fad’a maka?�? “Kin cika surutu.�? Shiru tayi bayan ta harareshi suka cigaba da tafiya tana leading d’insu. Har suka isa gidan basu had’u da sojoji ba kamar yanda take tsammani, hasalima sun had’u da wasu mutane suma suna yawo kamar su. “Ki shiga ki kiranin wacce zata miki lallen.�? “Ka mata me?�? Ta tambayeshi cikin mamaki. “Zan kwatanta mata yanda nake son ta miki kitson ne.�? Ya bata amsa yana mai jingina da katangar gidan. Ajiyar zuciya Laila tayi ta shiga gidan da sallamarta. Minti biyu da haka ta fito tare da yarinyar, har k’asa ta tsugunna ta gaishe da Haydar ya amsa da fara’arsa wanda Laila bata so hakan ba. “Kin gane irin kitson nan da akeyi sai ya zubo ta gaban goshi?�? Ya kwatanta mata da hannunshi zuwa fuskarsa. Yarinyar bata d’ago ta kalleshi ba ta kad’a kanta tace, “Na gane.�? “Yauwa to irinshi zaki mata. Sannan k’unshin kar ayi bak’i, ja za’ayi wanda ake shafawa sai a rufe da leda d’in nan. Sannan ayi a hannu da k’afa duka.�? Laila dake gefe tana kallon k’arfin halin Haydar tace, “Ya Allah!�? Da haka ya ciro kud’i har dubu hud’u a aljihunsa ya mik’awa yarinyar ta d’ago ido tace, “A’a Yalla6ai ka barshi. Hajiya tafi k’arfin haka a gurina.�? “I insist ki kar6a.�? Da Laila ta lura yariyar zata k’ara musu sai tayi saurin katseta, domin bata son suci gaba da magana duk da cewa babu mai irin tunaninta sai ita, wato na kishi. “Na’ima ki k’ar6a tunda shi ya baki.�? Bata k’ara musu ba ta k’arba da hannu biyu tana sunkuyawa, hakan yasa Haydar ya k’ata fad’ad’a fara’arsa, ta masa godiya ta shige cikin gidansu. Laila na ganin haka ta tsuke fuska tace, “Shikenan sai na dawo.�? “No, idan an gama ki kirani in zo in d’aukeki.�? “Haydar…�? “Laila zan zo in d’aukeki domin nasan kafin a gama miki dare yayi.�? Yana fad’in hakan ya tako zuwa gurinta ya d’aura goshinshi kan nata yace, “I can’t wait dare yayi.�? Idanunta ta sauk’e k’asa tana murmusawa, sannan ta janye jikinta ta shige gidan tana masa sallama tare da tuna mishi amfani da hand sanitizer in ya koma gida. Sai daya tabbatar ta shiga gidan sannan ya ciro wayarsa ya kira Mas’ud, bayan an d’auka yace, “Ya kana ina ne?�? “Ina gidana.�? “Gani nan zuwa.�? “Ohh, baka san anyi lockdown ba ko?�? “Duk karya ce, gani nan yanzu haka a waje na kai Laila wani gida nan cikin unguwarmu.�? “Kai Baaba. Ance sojoji duka suke yi fa.�? “Bari in zo.�? Minti biyu da haka ya isa gidan Mas’ud ya sameshi a waje yana jiranshi. Musabaha suka yi sannan ya masa jagora suka shiga gidan zuwa falonsa. “Nayi mamakin yanda akayi Laila ta yarda kuka fito bayan duk tsorontan nan.�? Mas’ud ya fad’a yana dariya domin ya lura muguntarsa bata yi tasiri ba. Haydar ya cire face mask d’insa ya ajiye a gefe yace, “Bani hand sanitizer domin na mata alk’awarin zan shafa.�? Mas’ud yana dariya ya kwalawa matarsa Naana kira ta fito yace ta mik’o masa, bayan ta gaishe da Haydar ta koma ta d’auko ta kawo masa tare da ruwan sha. “Ina Aunty Laila?�? Ta tambayeshi tana zama a gefen mijinta. “Tana gidan kitso.�? Mas’ud ya d’ago ido ya dubi Haydar yace, “Yaushe Kalti ta fara kitso? Rabon da naga kitso a kanta shekara ashirin kenan.�? “Well, yanzu ta fara.�? Ya bashi amsa yana masa ido kan yayi dropping zancen. Hira kad’an suka yi Naana ta tashi ta basu guri ta shiga kitchen d’aura girkin dare. “Amm nace akwai sauran abun nan ne?�? Mas’ud ya kece da dariya yace, “Na zama k’ani kuma babban banza. Yau kace kai Ango ne?�? Haydar ya mik’e tsaye yana cewa, “Zan koma gida in d’aura girki idan babu ne in tafi.�? Wata dariyar Mas’ud ya k’ara yi sannan ya tsagaita yace, “Wallahi karka yarda ka zama boyi-boyinta. Menene na wani komawa gida ka mata abinci? Mu zauna a nan idan ta gama sai in rakaka ka d’aukota.�? Haka Mas’ud ya shagaltar dashi suka zauna suna hira, “An ce ku masu shagon magani za’a bari ku bud’e tunda mutane ba fasa rashin lafiya zasu yi ba.�? “Sai gobe ko jibi muke tunanin zasu yarje mana, kafin nan suna son killacewa kowa garin ya zama yanda suke so.�? Haydar yana nan har bayan magriba a gidan Mas’ud sannan Laila ta kirashi wai ta gama, Mas’ud ya shige d’akinsa can kuma ya fito ya mik’a masa Haydar ya saka a aljihu. Sallama ya yiwa Naana wacce ta mik’a masa food flask a cikin kwandon abinci tana cewa, “Ga abinci munyi daku.�? “To ai kin kyauta ba kad’an ba, da yanzu idan na koma ni zan yi.�? Suka kwashe da dariya dukkansu tana fad’a masa ai Mas’ud ma yana girki. Mas’ud na fitowa waje yaga gari shiru babu alamun mutane na yawo, yace, “Kai Mallam na fasa rakaka. Kaje kawai Allah ya kiyaye hanya.�? “Dama bani na rok’eka ba.�? Da haka suka yi sallama ya kama hanyar gidan da zai d’auko Laila. Yayi mamakin har ya isa gidan bai had’u da kowa ba, yana tsayawa ta fito tana kalle-kalle tace, “Baka had’u da sojoji ba?�? “Laila sarkin tsoro. Ni akwai wanda ya isa ya tareni ne?�? Tana jin hakan tayi ajiyar zuciya ta d’iga masa Hand sanitizer ya shafawa hannunsa suka fara tafiya, “Wannan food flask d’in fa?�? “Daga gidan Mas’ud ne, a can nake tun d’azu.�? “Baka ce zaka ga k’unshin ba.�? “Sai mun je gida in gani da kyau domin bana son kowa ya gani sai ni kad’ai. Sai dai kafin ma in gani nasan yayi kyau.�? Murmusawa tayi suka cigaba da tafiya suna hiransu gwanin ban sha’awa, sai dai suna shiga layin gidansu suka ga motar sojoji guda biyu, Laila tayi saurin kamo hannun Haydar ta 6uya a bayanshi tana cewa, “Innalillahi, Haydar kaga abunda nake gudun ko?�? “Babu abunda zai faru. Ke dai kiyi shiru kar kiyi magana.�? Hasken motar aka dallosu dashi wanda yasa hanjin cikin Laila kad’awa ta ruk’unk’ume Haydar tana addu’a. “Kai daga ina kuke?�? Wani daga cikin sojojin ya tambayesu yana sauk’owa daga motar. K’ato ne na gaske kuma babba wanda Haydar yasan mutumin ya girmeshi a shakeru nesa ba kusa ba. “Daga gidan wani relative d’inmu muke.�? Haydar ya bashi amsa cikin dakewa. “Baku da labarin an sanya dokar hana fita ne?�? “Muna dashi. Emergency ne yasa muka fito.�? Ya k’ara basu amsa. “Kenan kun sani amma saboda son karya doka sai kuka fito?�? Wani daga cikin sojojin dake kan motar ya sauk’o yana k’are musu kallo. Sai a lokacin Laila ta d’ago kanta daga bayan Haydar tace, “Don Allah sir kuyi hak’uri, nice na matsa masa zan je duba d’an uwana.�? “Kin jawowa kanki da k’aninki fushin doka.�? “She’s my wife.�? Haydar ya basu amsa. “Woah, ka d’auko mai zafi my friend, amma dole zaku yi tsallen kwad’o goma-goma. Saboda gobe in tace ku fito ba zaka biye mata ba.�? “Zan yi da nawa da nata domin tana d’auke da k’aramin ciki.�? “Haydar ka bari zan iya.�? Laila ta fad’a tana dafa kafad’unshi. Sassauta muryarshi yayi yace, “Su kalli bayanki? No! Na gwammace in zaga unguwar nan duka da naga hakan ya faru.�? Zata yi magana ya d’aura yatsunshi saman la66anta yana murmushi yace, “Shhh. Ni na jawo, kuma ni zan kar6i duk hukuncin.�? Gyad’a kai tayi domin tsoro da fargaban ya fara fita a ranta, tunda ba duka zasu masa ba ai da sauk’i. Haydar ya mik’a mata food flask d’in ta k’arba tana murmusawa tare da jin tausayinsa da k’aunarsa duk a lokaci d’aya. “In kun gama soyayyar ka fara, guda talatin zaka yi, mun k’ara maka goma.�? Haydar ya tattare jallabiyarsa sama ya kama kunnensa ya fara tsallen kwad’o, ai Laila bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba. Juyowa yayi yana kallonta da mamaki shimfid’e a fuskarsa domin baiyi tsammanin koda wasa zata masa dariya ba. “Kaga Madam ma dariya take yi, kayi sauri ku gama ku shiga gida.�? Sojan ya fad’a yaci gaba da binshi a baya. Haydar da kyar ya k’arasa tsallen kwad’on Laila ta matso gurinshi tana masa sannu ya harareta. Da haka yayi gaba ta bishi a baya tana k’unshe dariyarta. “Haydar yaya dai? Kayi shiru baka ce komai ba.�? “Na ceceki shine kike mini dariya ko? Kici gaba.�? Da haka suka shiga gida, ita dai Laila hannunta na kan bakinta tana son daina dariyar. Yana shiga falo ya kwa6e jallabiyarsa ya mik’ar da k’afafunshi kan kujera yana dannawa. Laila na ganin haka ta cire hijabinta ta matso ta fara mishi tausan tana murmushi. Kallonta yayi yaga ta k’ara masa kyau, yasa hannu ya cire kallabin kanta yace, “Masha Allah.�? Ya rik’o hannunta wanda aka yiwa k’unshi jaa mai kyau yana juyawa. “Kinyi kyau sosai.�? A kunyace tace, “Nagode.�? Kana ta mik’e tana cewa, “Ya kake jin k’afar?�? “Wallahi kaman an k’ara mini na mutane uku a cikin nawa nake ji. Da kyar na iya isowa gida amma ke dariya kike mini.�? “Kayi hak’uri amma abun ne da ban dariya, bayan ka gama cika baki sai gashi Allah ya had’aka dasu. Bari na had’a maka ruwan zafi ka gasa jikinka ko zaka ji sauk’i.�? Kad’a mata kai kawai yayi ya kwantar da kanshi kan kujeran yana rufe idanunshi. Shi kad’ai yasan yanda yake ji a jikinshi, baya son tayi masa dariya da yawa ne yasa bai langwame mata kamar yanda zai langwamewa Ammi ba. Minti d’aya da haka Laila ta fito tace, “Na had’a maka ruwan zafi a bathtub, ka shiga kayi wanka ka gasa jikinka.�? Sauk’e k’afafunsa yayi k’asa amma yana mik’ewa yaji sun badashi zai fad’i, ai da sauri ya koma ya zauna ya kalli Laila da sai yanzu abun ya fara bata tsoro tace, “Haydar yaya dai?�? “Bani minti biyu in huta tukun.�? Da haka ya k’ara komawa ya kwanta ya rufe idanunsa. A hankali yaji Laila ta fara masa tausa sai dai data ta60 muscle d’in da yafi jikk’ata sai ya d’age k’afar yana cewa ‘wash�?. K’arshe ma hanata yayi yace kamar k’ara masa take yi. Zama tayi a gefenshi tana kallonshi tayi zugum, can tace, “I’m sorry.�? Idonsa d’aya ya bud’e ya kalleta yaga yanda ta marairaice yace, “Ba wani sorry zan rama, zaki ji abunda naji.�? Yayi kwafa ya k’ara rufe idanunsa. Cinyarshi ta matsa inda yake masa zafin yayi saurin tashi zaune yana kallonta, “What was that for?�? “Inji da kyau.�? Ta tashi tsaye. “Trust me zaki yi bayani.�? “Kai kad’anka.�? Da haka ta shige d’aki ta barshi a gurin amma har ta fara tausaya mishi. “Ya Salam, mutanen nan sun lahantani.�? Ya furta a hankali yana komawa ya kwanta. Laila sai da tayi wanka ta saka kaya sannan ta fito ta samu Haydar na bacci. A gefenshi ta zauna tana kallon fuskarshi sonshi na fisgarta. Bakinshi da yake a bud’e kad’an ta rufe masa da yatsunta, tana cire hannunta ya k’ara bud’ewa yana jan numfashi ta nan. Dariyan da tayi yasa Haydar farkawa ya dubeta, yana ganin itace ya k’ara rufe idanunshi ya gyara kwanciyarshi. “Yalla6ai a tashi ayi wanka ayi sallah isha.�? “Ba yanzu ba.�? Pillow da ya kwantar da kanshi ta zare kana ta tallafo kanshi ta zaunar dashi amma yana neman k’ara komawa ya kwanta. “Haydar bana son musu, ka tashi muje kayi wanka.�? “Bazan iya ba tashi ba.�? “I will help you. Tashi.�? Da haka ta taimaka masa ya tashi amma duk ya sakar mata nauyinshi tana k’ok’arin fad’uwa dasu. “Nasan da gangan kake haka.�? Suna shiga d’aki ya saketa ya zauna a bakin gado yace, “Ki k’ara mini ruwan zafi a ruwan wankan.�? Ba musu ta shiga band’aki yayi saurin ciro tsarabarsa ya jefa a jakar Laptop d’inshi. Kana ya tu6e sauran kayan da yake jikinshi. “Na had’a maka.�? Fad’in Laila tana mai fitowa daga band’akin. Ganinshi haka yasa ta koma ta d’auko masa towel ta jefa masa. “Bazan iya wankan ba Laila, it’s like hannuna ma sun gaji.�? “Don’t do this to me Haydar.�? Ta fad’a tana kad’a kanta zata fita daga d’akin ya kamo hannunta. “Ko ki mini ko in kwana haka�? Kallon-kallon suka tsaya yi, k’arshe dolenta ta sake ajiyar zuciya tace, “Yanzu kam nasan yaro na aura.�? “Ni ba yaro bane.�? “Seriously kamata yayi ka k’ara shekara biyar a gaban Ammi kafin ta maka aure.�? “Kici gaba. Allah ya bani lafiya.�? Dariya tayi har tana rufe bakinta tace, “Kaga yanda kayi kyau kuwa da kake tsallen kwad’on nan? Tausayinki naji amma daa na maka video.�? Bai k’ara cewa komai ba ya tashi da kyar ya shige band’akin tabi bayansa. Bayan sun yi sallah sun ci abinci ya koma d’aki ya kwanta, sai data kashe komai ta kulle gidan sannan ta shiga. A gefenshi ta kwanta kana ta d’aura kanta saman k’irjinshi tace, “Sojoji basu kyautawa d’an Ammi ba.�? Murmusawa yayi yace, “Laila kenan.�? “Yanzu shikenan kenan?�? “You know I can’t. Kiyi shiru kiyi bacci. Good night.�? Washegari Haydar da kyar ya tashi yayi sallah asuba ya koma ya kwanta. Tun abun na bawa Laila dariya har ta fara jin tausayinshi da kuma haushin sojojin da suka aikata masa haka. K’arfe tara na safe ya farka, daga nan ya wuce band’aki da kyar yayi wanka ya fito yana jin maganar Laila a falo kamar tayi bak’i. Su waye suka samu fitowa a cikin wannan lockdown d’in? Yana bud’e k’ofar d’akin ya hango Mas’ud, ai kuwa ya juya zai koma Mas’ud ya kira sunanshi. “Haydar. Ina kuma zaka koma?�? Ya tuntsire da dariya. “Mas’ud bana son haka fa, na fad’a maka ne don ka jajanta mana ba wai ka sakashi a gaba kana mishi dariya ba.�? Haydar na jin hakan ya gane Laila ta fad’a mishi. Tun jiya yaso warning d’inta amma sanin cewa babu mai iya kawo musu ziyara yasa yayi shiru. Juyowa yayi ya tako cikin d’akin cikin dauriya ya zauna. “Sannu kaji?�? Fad’in Laila tamkar zata zubar masa da hawaye. “Wai ya akayi hakan ta faru ne? Baki bani full detail meya faru ba tun daga jiyan zuwa yau.�? “Na fasa fad’i.�? “An tashi lafiya? Ya iyali?�? Haydar ya gaishe da Mas’ud. Duk da yana auran Yayarsa yasan ya girmeshi. “Lafiya kalau. Ya naka iyalin.�? “Gata nan lafiyanta kalau.�? “Ashe abunda ya faru kenan?�? Mas’ud bakinshi a washe yake maganar. Koda Haydar ya lura tsokanarshi yake yi sai yayi murmushi ya tashi ya nufi dinning Laila ta biyo bayanshi. “Irin wannan warayya da bani da mata sai naji haushi.�? “Wai meya kawoshi ne?�? Haydar ya tambayi Laila wacce ke zuba mishi abinci. “Wai yazo dubani ne. Da ire-iren maganganunshi dai.�? “Kuna ta gulmana ina jinku.�? Ya fad’i hakan shima yana hawa kan dinning chair d’in. “Tunda kana iya jinmu ba gulma bane Mas’ud. But seriously baka tsoron had’uwa da sojoji ko?�? Fad’in Laila ba tare daga kalleshi ba domin had’awa Haydar tea da take yi. “Haydar ne yace kinyi kitso shine abun ya bani mamaki nazo in gani.�? Haydar ya kar6i kofin tea yace, “Mallam ba don kai tayi ba.�? Mas’ud bai kulashi ba ya dubi Laila wacce itama ta zauna tana kare masa kallo tace, “Seriously abunda ya kawoka kenan?�? Gyad’a kai yayi kana ya dubi Haydar yana dariya yace, “Wai meya faru ne.�? Haydar ya bashi labarin yanda aka yi ya k’arishe da cewa, “In zaka je pharmacy don Allah ka dawo mini da maganin ciwon jiki.�? “Akwai a gida, ai dana sani da tun jiya na baka kasha, watak’ila da abun yazo da sauki. I’m sorry.�? Tana fad’in hakan ta tashi ta shige kitchen inda first aid box d’insu yake ta d’auko masa magani ya sha Mas’ud ya mik’e yana cewa, “Zan koma gida, a tayani da addu’a kar na had’u da mutanen nan. Ai daa na san sun cafkeka jiya da ban fito ba wallahi.�? “Allah yasa ku gamu. Gulma ya kawoka ai.�? Fad’in Haydar yana dariya. “Kalti bakiyi sa’an miji ba.�? Mas’ud ya harareshi cikin wasa. “Nagode.�? Ta amsa masa tana tura plate d’in abinci gaban Haydar wanda ya turo tsakiyar table d’in. “Laila na k’oshi.�? “Babu abunda kaci Haydar, ka k’ara kad’an ko loma biyar ne.�? “Kalti kina sakalta yaron nan.�? “Nikam ba cewa kayi zaka tafi ba? Meya tsayar da kai?�? Ta tambayeshi tana zarewa Haydar ido wanda ya k’ara turo mata plate d’in, murmushi yayi ya jawo yaci gaba da cin abincin. Wannan karon ita ta raka Mas’ud waje suna tattaunawa na tsakanin ‘yan uwan juna. “Abul ya sake kiranki ne?�? Girgiza kai tayi kana tace, “Bai sake ba, yanzu da aka shiga lockdown ko ya yake ciki sai Allah.�? “Allah ya kyauta. Sai munyi waya.�? Da haka yasa kai ya fita bayan ya lek’a waje ya tabbatar babu sojoji. Laila na dawowa ta samu Haydar akan gado yana danna Laptop d’inshi gefe guda kuma yana waya. Sai daya gama ya juyo ya kalleta, kashe Laptop d’in yayi ya yafutota da hannu ta iso wajenshi. “Yau ban fad’a miki cewa kinyi kyau ba ko? Kin fi koyaushe kyau amma a cire kallabin nan.�? Yasa hannu ya cireshi, gashinta data 6oye ya zubo ta goshinta da kuma bayanta “Kinfi kyau a haka.�? “Yawanci wannan ne kitsona a wancan lokacin, last kitson da nayi irinshi nayi shiyasa daka ce inyi banyi musu ba. Ina son wannan memory ya gushe a zuciyata ya zamana duk lokacin da zanyi kitso bazan tuno wancan ranar ba.�? “Insha Allah. Shi kuma Allah yaji kanshi ya mishi rahama.�? “Ameen Ya Rabbi. Kana k’ara burgeni, baka da halin wasu maza na kishin mazajen matayensu da suka mutu.�? “In kinga namiji na kishi da marigayin mijin matarsa ki tabbata tana had’asu wajen halayya ko kuma na rayuwar yau da kullum. Babu namijin da zai so yaji matarsa tana kusheshi sannan tana yabon wani namijin ko da kuwa matacce ne. Sai dai bana son a yawaita yin maganan saboda gujewa fitina.�? Gyad’a kai kawai tayi kana ta kwantar da kanta kan k’irjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa. Wayarsa ce ta fara ringing ya d’auka ganin sunan Amminshi ne. Sallama ya mata kana yayi shiru yana sauraranta amma yanayin fuskarsa kad’ai ya isa a gane ranshi ya 6aci. “Gaskiya hakan bai mini dad’i ba Ammi. Bai kamata ki gayyaci mutane su zauna a gidanki ba tare da munyi shawara ba. Baki san daga ina suke ba, baki san halinsu da manufarsu a kanki ba. Ammi yanzu ba lokacin da zaka bari tausayi yasa kayi gaggawan yanke hukunci bane. Su koma inda suka fito, idan na samu fitowa jibi zan zo in gansu sai a san me za’a musu.�? Da haka ya k’ara shiru yana sauraronta, can kuma ya kama kanshi da yatsunshi biyu yace, “Allah ya taimaka. Sai anjima.�? Ya kashe wayar. “Yaya dai?�? Laila ta tambayeshi tana tashi zaune. “Matar can da kwanaki suka je gidan Ammi neman abinci shine yau suka sake dawowa wai an koresu a gidan hayan da suke ciki basu da gurin zuwa. Damuwata a nan shine; Ammi bata san mutanen nan ba, bata san nufinsu a kanta ba. Sannan meyasa suka tsallake duk gidajen dake unguwar suka sauka a gidanta? Ba wani gida mai kyau bane balle ace sun ga alamun tana da wadata ba. Bana jin dad’in saurin yanke hukuncin da take yi.�? Shiru Laila tayi har na tsawon minti biyu, sai data tabbatar ya fara sauk’owa sannan tace, “Mu mata haka muke da tausayi da kuma rauni. Kayi addu’a Insha Allah babu abunda zai faru sai alkhairi. Idan Allah ya kaimu ka samu fita sai ka biya ka dubasu, in ka yarda dasu sai su zauna da ita, in baka yarda dasu ba sai a nema musu wani gidan hayan su koma can. “Hakan zai fi, hankalina zai fi kwanciya.
Mum Fateey 👌




