Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 73 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SEVENTY-THREE📍

A gigice ya karasa kan stage din, sai a lokacin yaga ainihin abinda ke wakana a gurin, wanda yafi kona masa rai shine wanda yake ta bayanta, jikinsu har gogon na juna yake, ran deen in yayi dubu ya baci, jijiyoyin kansa sun fiffito kamar zasuyi magana, kwayar idonsa har chanzawa tayi tsabar takaici, kallo daya zaka masa kagane irin bacin ran dayake ciki saboda yanda ya hade fuska kamar wani kumurci…
Shako wuyar wanda ke bayanta yayi ya wurgar dashi a kasa sannan yayi ball dashi sai gashi akan table din masu cin abinci, nan da nan kallo ya dawo kansu, sauran mazan dake mata liki na ganin haka suka dakata da likin rai a bace, dayane ya tabo kafadar deen yace;
“Mallam ya zakazo ka katse mana jindadi, in kaima ka kyatsa ba sai kayi joining cue din ba ko Allah zesa ka samu rabonka kaima, abu ne fa kowa naso ya dandana”……
Ai deen ji yayi kamar an sokeshi da mashi, wato duk wannan gayyar da sukayi akanta so ake ayi passing passing da ita kenan, irin ga karuwa sun samu?….
Naushi ya sakar masa akan hanci sannan ya saka kafarsa ya daki wandonsa, wani irin kara mutumin yayi yana rike gurin, deen ko a jikinsa yace;
“Sai inga ta inda zaka dandana ai, yan iska kawai masu lalata yaran mutane, kuna zaune kannenku zasu kawo muku tsarabar abinda kuka shuka”…
Karap wani yace;

“Kai dakata mallam! Meye a ciki dan yace kowa ya dandana? Ince kaima ba kayan aikin ka gani kazo ba?”…..
“Okay kaima sai na maka asarar abun dandanen kenan”….
Deen ya fada yana kai masa naushi a saitin gurin, sauran na ganin haka suka kwasa a guje kowa yayi takansa….
Juyowar da deen zeyi yaga babu baby tee a gurin, tini ta tsere daga hall din, tinda taga yayi ball dana farkon ta tsorata ta fita a guje, kicibus sukayi da eesha data tafi shigo da wasu friends dinta, baby tee na ganinta ta rukoto ta fashe da kuka tace;
“Eesha na shiga uku! Eesha dan Allah ki boyeni karya kasheni, dama kinyi inviting dinsa ne?”……
Dafa kafadarta eesha tayi cikin tashin hankali dukda batasan abinda yake faruwa ba tace;
“Ki nitsu teema, waye wannan?, me kikayi da ze kasheki?”…
“Nima bansan abinda nayi ba, eesha yanata dukan wanda sukemin liki, sai da nace miki bazan tsaya a gurin rawa ba kikace sai nayi”….
Ta karashe kuka yana cin karfinta, dagaske ta tsorata dan bata taba ganinsa a irin wannan yanayin ba, babban abinda ke damunta shine batasan abinda tayi ba bare tasan me zata kama….
“Teema ki fadamin waye wannan dan Allah, kawai daga kin danyi rawa shine me?”…..
Bata dire ba taji an dauketa da wani wawan mari da saida taga stars, baby tee na ganin haka ta dora hannun aka tace;
“Shikenan ya kamamu, wayyo Allah na”….
Kokarin gudawa tayi yayi saurin rukota da hannu daya sannan ya fuskanci eesha cikin bacin rai yace;
“Daga ta danyi rawa a gidan ubanki! Dama ke kika sata rawa ko wani kare da doki yazo yana shafarta da sunan liki, bayan lesbian din da kikayi claiming bakyayi dama ke yar iska ce? Toh daga yau babu ke ba ita, nonsense kawai!”…..
Yana fadin haka ya fuzgi hannun baby tee yayi inda yayi parking motarsa da ita, bude back seat yayi ya wurgata a ciki sai da hannunta yayi bugu, ta dan saki ihu tana yarfa hannun, ko kallonta beyi ba ya shiga yaja motar suka bar gurin a guje…..
Suna barin gurin daya daga cikin kawayen eesha tace;
“Eesha wai ba wannan kika nuna mana a matsayin wanda zaki aura ba? Bashi kike posting kullum ba?”….
“Nima shi nagani, naga kamar kuma kishi yake wannan tayi rawa, ko kunyi break up dashi ne eesha?”….
Daya daga cikinsu ta sake jeho mata tambayar….
Banza tayi dasu ta fita daga gurin bikin gabadaya hawaye na zuba a idonta, tabbas yau ko makaho ne ya shafa yaji yasan deen son baby tee yake, ya akayi bata gane ba? Ya akayi yanda baby tee in tayi dare a gidansu zezo da kansa ya dauketa yana fada bata gane sonta yake ba?, ya akayi yanda baby tee ke masa rashin kunya ya kyaleta bata fahimci duk a cikin so bane? Ya akayi yanda ya rungumeta ya dauketa a cikin mutane kanta be kawo cewa lallai sonta yake ba, abu daya ne batasani ba shin itama tana sonsa ko kuwa? Sannan in yana sonta meyasa be fada ba tinda iyayensu bazasu hana ba? Gashi yanzu maganar aurenta akeyi da khaleel, koma dai menene yau taga kishin baby tee muraran a idon deen kuma babu abinda zesa ta yarda deen ba sonta yake ba….
Suna barin gurin ba dadewa motar yan sanda ta fara jiniya, wasu daga cikin yan bikin ne suka kirawosu lokacin da sukaga abu ya koma action film, saidai babu wanda ya iya bada information akan wanda ya hargitsa taron, dole taro ya watse kowa ya koma gida….
Yana shirin danna mahaukacin horn yaga gate din gidan a bude, fitar su mami kenan me gadi ya hango motarsa ya barshi a bude, danna kan motar cikin gidan yayi har gaban part dinsa, securities din gidan nata mamaki amma babu wanda ya isa ya tanka……
Fitowa yayi ya zagaya ta inda take ya bude motar ya damko hannunta ya fito da ita, a fusace ya fara janta har suka shiga cikin parlournsa sannan ya maida kofa ya rufe….
Wurgar da ita a kan kujera yayi ya dora kafa daya kan kujerar sannan ya sunkuya daidai saitin kanta yana wuci yace;
“Wani dan iskan telan ne ya miki wannan dinkin?”….
A tsorace tace;
“Wallahi nima bansani ba, eesha ce takai mana dinkin”….
“Da eesha ta kai muku dinkin sai ba’a aunaki ba aka miki fitted kaya?”…..
Girgiza kai tayi tace;
“Wallahi ba’a aunani ba, hotona kawai ta tura masa”…..
Ai gani tayi kawai yana zaro belt din wandonsa, ba shiri tayi sliding ta sauka tayi hanyar kofa a guje, saidai me? Tana taba kofa tajita a garkame, da gudu ta juya tayi hanyar bedroom dinsa, ta tura kofa tana kokarin sa lock, amma ina kofa taki rufuwa, tama rasa ta ina ake rufe kofar, tana cikin kokarin rufe kofar taji ya banko kofar ya shigo, a rikice tayi kan gado sabon kuka na balle mata, sai kawai ta nannade kanta a cikin bargo tayi lup kamar beran da aka kusa kamawa ya tsira da kyar, takowa gabon gadon yayi ya tsaya akanta yace;
“Kin gama guje gujen ko kuwa?”….
Leko da kanta tayi hawaye shape shape akan fuskarta, dama dankwallinta ya dade da fita tun a mota, make up kuwa ya zazzago ya bata mata fuskar sai tayi kamar wata jaririyar aljana, cikin shessheka tace;
“Dan Allah kayi hakuri, eesha ce tasani”…..
Da ace ransa ba a bace yake ba babu abinda ze hanasa tuntsirewa da dariya saboda yanda make up din fuskarta yayi nashi gurin itama tayi nata gurin, gimtse fuska yayi yace;
“Idan eesha tace kisa hannu a wuta zakisa kenan?”…..
“Dan Allah kayi hakuri”….
Daka mata tsawa yayi yace;
“My friend answer me!”…..
Murya na rawa tace;
“A’a..aa”….
“Yaushe akayi planning duka wannan shirmen banda labari?”…..
“Eesha ce”….
Belt din hannunsa ya zuga mata guda daya yace;
“In kika kara karamin eesha a gurinnan sai na fasa miki jiki”….
Wani kara ta saki dukda ba wani shiganta dukan yayi ba saboda bargon dake jikinta, amma dayake a tsorace take sai taji zafin abun sosai….
“Cire bargonnan ki mike tsaye!”….
Ya sake daka mata tsawa….
Kuka ta fashe dashi ta tashi da sauri tare da bargon…..
Ze sake mata magana kenan tayi saurin cire bargon ta fada jikinsa ta kankamesa ta sakin wani kuka me ban tausayi….
Wani abu ne ya fadomasa a rai yaji lallai yanaso ya gwadata, yana chan yana gwada ya’yan wasu besan ya kanwarsa take ba, besides baby tee abun a dasa mata ayar tambaya ce, idan tana wani abun kamar mara hankali, gashi zuwa gidan khaleel datayi haryanzu abun be fita ransa ba, haka kawai yakeji wani abu ya fara a lokacin ko yayane, sai kawai ya yanke shawarar gwadatan…
Zareta yayi daga jikinsa ya cillata kan gado, wurgar da belt din yayi ya haura gadon ya doshi inda take, baya ta fara ja yana kara matsawa inda take, sai da takai karshen gadon sannan ta rintse ido tana kankame jikinta…..
Janyota yayi ya kwantar sannan ya kifata ta baya, hannunsa ya dora akan zip dinta ya fara kokarin kai shi kasa, ihu ta saki baki na rawa tace;
“Wayyo Allah me zakamin?”….
A nitse yace;
“Na fuskanci da’ na miji kike bukata shine zan baki abinda kikeso ba sai kina rawa wasu na shafaki ba”….
A razane ta juyo jikinta na rawa tace;
“Wallahi banaso, ni banaso”….
Sake maida ita yayi ya fara zuge zip din a hankali yace;
“Baki isa ba, ai nasan kina so”….
Be kuma sauraranta ba ya kai zip din kasa, dama a tsakiyar bayanta ya tsaya sannan ya juyo da ita, hannu daya yasa yana kokarin zare rigar, dayan hannun kuma ya fara shafa wuyarta…..
Wani mahaukacin ihu ta kwalla ganin dagaske yake, toshe kunnensa yayi saboda yanda ihun ya karade ko ina yana addu’a Allah yasa su umm basuji ba, ganin ya cire hannunta daga jikinsa ta dira ta dayan barin tayi toilet a miliyan, tana shiga Allah ya taimaketa ta rufe kofar, kwanciya a kasa tayi tana maida numfashi hawaye na sauka akan fuskarta, ko damuwa da yanayin gurin batayi ba, ita dai godewa Allah take ta tsira….
Bin kofar yayi da kallo yana sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, ko a iya haka hankalinsa ya kwanta ya kuma tabbatar da baby tee batasan komai ba saboda yanda jikinta kadai ke rawa kasan na wanda besan harkar bane, shareta yayi azuwan zaman toilet din shine punishment dinta da zuwa gurin biki, baze ce mata ta fito ba sai nan da awa biyu, a haka wani daddadan bacci ne ya kwasheshi cikin kwanciyar hankali…..
Ba shi ya farka ba sai karfe sha biyu na dare, lokacin a kalla tayi awa hudu a toilet din, tashi yayi ya isa ga toilet din yayi knocking, a hankali yace;
“Zahrah taso ki bude ba abinda zan miki”..
Shiru kamar babu kowa a ciki, murda kofar yayi ko ta gudu sanda yake bacci amma yaji kofar a garkame alamun mutum na ciki….
Cije lebansa yayi ya lumshe ido yace;
“Ki bude mana baby girl, ba abinda zan miki”….
Motsi yaji anyi amma batayi magana ba….
Haka ya karaci magiyar ta bude ta fito amma taki, haka suka kwana a jikin kofar dagashi har ita, ita tana jingine da kofar ta ciki, shi kuma yana ta waje, a haka bacci barawo ya sace su…..
Kiran sallar asuba ne ya tashesa, ya danyi knocking yace;
“Zan fita sallar asuba, ki fito kiyi sallah”….
Sai da ta bada tazarar minti ashirin kafin ta fito sadap sadap jikinta na mata wani mugun ciwo, kalle kalle ta farayi taga babu shi a dakin, haka ta cigaba da raba idanu harta karaso parlor, tana ganin bayanan ta fita tayi part din mami da sauri dukda yanda take jin jiki amma bazata iya tafiya a nitse ba, Allah ya taimaketa sun bude kuma basa parlor, a sidade ta samu tashige dakinta batareda sunji motsinta ba, saidai kawai insun ganta da safe tace musu da sassafe ta dawo daga gidan su eesha, dama sunyi a chan zata kwana shiyasa basu nemeta ba……
Yana dawowa daga masallaci ya samu toilet din a bude kamar yanda yayi expecting zata wuce kafin ya dawo, murmushi ne ya subuce masa tuno da yanda ta rikice daga zuge zip, sai kuma ya fashe da dariyar da be samu yayi ba na make up dinta…..
Da safe suka tashi da abinda ya saka wasu farin ciki, wasu kuma ya daga musu hankali irinsu deen, wato sa ranar bikinsu nan da wata daya, kuma ko gayamasa da wacce akasa ba’ayi ba, baby tee dai ansan khaleel ne…. Ita dai baby tee kasa gane halin da take ciki tayi, ta dai yi kuka ta roki umm a daga bikin umm tace bata isa ba ai ita tace tanaso saboda haka babu wanda ze tunkari bappa da batun daga biki, haka ta gama koke kokenta ta hakura….

Two weeks later…….
A cikin sati biyunnan shirye shiryen biki ake ta ko wani bari, kadama side dinsu khaleel suji labari saboda kasancewarsa jika na farko a familyn, gashi kuma bappa yasa an maida daddy gida saboda ayi hidimar biki a gabansa, baya dai iya komai daga tashi sai kwanciya amma a haka farin ciki yake sosai da bikin, bugu da kari kuma momma ta dawo gidan gabadaya, takanas momma da aminiyarta suka tafi dubai suka hadowa khaleel kayan lefe nagani na fada, satinsu daya suna siyayya suka dawo amma a haka sai da suka kara siyan wani abu a Nigeria, har abdul sai da ya dawo daga Malaysia, yana dawowa yaje suka gaisa da baby tee cikin mutunci dama shi ya fita daban da jama’ar gidan shiyasa take ganin mutuncinsa, bayan abdul kuma yan uwan khaleel da sukazo ganinta sun fi a irga, abun har ishen su mami yayi, umm tace ko a kansa za’a fara biki sai haka….
Satin baby tee daya abby na zaga dangi da ita, sai da ya karade ko ina da ita sannan ya barta a gidan mahaifiyarsa wato hajiya kasancewar mahaifinsa ya rasu, abinda ya dauke hankalin baby tee kenan ko samun damar tinani batayi, kwananta hudu babu irin gatan da hajiya bata nuna mata, ko abinci taci ta dauke kwanu da kanta hajiya ta dinga fada kenan, tsabar yanda baby tee ta samu sake har cewa tayi bazata koma ba, umm tacewa abby lallai a dawo da ita saboda shirin biki da suke, haka hajiya da baby tee suka rabu cikin kewar juna, hajiya harda kwallanta…..
Baby tee na dawowa hajiya huraira matar abby ta diro kasar tare da me gyaran jiki tindaga saudiya, nan aka fara dirza baby tee kamar za’a chanza mata fata, kasancewar tana da kyan jiki tun a ranar farko ta chanza, kafin sati daya kuwa yanda kasan an chanza mata halitta, tayi wani shegen kyau fatarta ta kwanta kamar ta jarirai abunka da farar mace, kamshi kuwa duk inda tashiga sai ya kama kamar wacce aka dafa da turare, gabadaya part din mami ya dauki wannan kamshin, kayan mata kuwa anan gidan aka hada dan su mami cewa sukayi basu yadda a bawa yarinya abinda basusan yanda aka hada ba, a idonsu aka hada komai kuma saida umm ta tabbatar da ingancin komai a matsayinta na likita kafin ayi amfani dashi, sannan gabadaya hadin natural abubuwa ne dan kayan fruit sunfi yawa a ciki, a cikin sati daya baby tee taji komai na jikinta ya chanza, ba dai zata iya fassara abinda take ji ba amma tasan ba haka take ba, koda yaushe cikin chanza pant take, sai hakan yasa ko zama tayi a tsarge take, ita dai ta kasa gane abinda yasa hakan…
A washe garin da akasa ranar biki deen ya sanar musu da zeyi tafiya na kwana uku, kamar mami ta hanashi saidai ganin yanda be nuna komai ba akan lamarin bikin ta barshi yayi tafiyar, tayi niyar karban daya daga cikin credit card dinsa da niyar hada lefi umm tace ta barshi ita zata hadamasa….
Tinda ya tafi suke kiransa a waya basa samunsa har akaci kwana ukun dayace amma shiru be dawo ba, sosai hankalinsu ya tashi amma basu sanar da kowa ba, ita kanta baby tee batasan bayanan ba saboda tafiyar datayi, sai da ta dawo take tambayar mami, mami tace mata yayi tafiya, kasa jurewa tayi bayan kwana uku ta kira wayarsa amma a kashe, sosai itama hankalinta ya tashi har kuzarinta ya ragu…..
Yana sane yace musu zeyi tafiya badan zeyin ba, sai dan yana tsananin bukatar space, so yake ya zauna a part dinsa shi kadai yayi tinanin abinda ke damunsa, daga lokacin da mami tace ansa rana yaji komai na duniyar na juya masa, yaji kamar numfashin dayake shaka ya chanza, a lokacin da ze iya kuka da yayi kodan ya samu saukin abinda yakeji aransa, ba zece ga abinda yake damunsa ba amma yana cikin tsananin damuwa, damuwar da ya kasa gane ainihi ta mecece, ko abinci ya kasa ci in banda energy drink dayake durawa kansa, haka ma bacci ya gagaresa sai yayiwa kansa allura har allurar tazo ta daina masa aiki, gabadaya ya zare SIM cards dinsa saboda bayasan kowa ya dameshi, hotunan daya mata ne kadai suke debe masa kewa ya kuma mai dasu abincinsa koda yaushe yana rungume da wayarsa yana kallonta, karshe zana fuskarta ya koma yi a duk abinda ya samu, a haka ya lalubo wani drawing book daya taba ajyewa wani lokaci, sai ya koma yagan paper ya zanata, inya kalla ya kalla sai yaga kamar be zanata da kyau ba sai ya sake yago wani, a haka a haka har ya hargitsa dakin da pepopi, a cikin sati biyunnan ko gyara part dinsa be gani ba deen dayake mutum me mugun tsafta sai gashi ko ina a hargitse kamar anyi barin makauniya a part din, gashin kansa da gemunsa sunyi mugun taruwa kamar wani mahaukaci sabon kamu amma ko damuwa beyi ba……
Satinsa daya a kulle shi kadai kafin ya gano auren baby tee dinne bayaso, bayaso tayi nisa dashi yafiso yayita ganinta yana jindadi, a yanzu haka ma shi kadai yasan yanda yake missing dinta, so yake kawai yaji muryarta ko zeji saukin abinda ke damunsa a rai amma ya kasa samun kwarin gwiwar fita daga part dinsa, wata zuciyar ma cewa take ya zauna a haka har ranar bikin, kila in ba’a gansa ba a fasa daura nasa auren, haka ya cigaba da zama a cikin gidan har na tsawon sati biyu batareda kowa ya sani ba….
Gama wayarta keda wuya taji kamar motsi a part din deen dake windown dakinsa na center garden ita kuma anan ta zauna tayi waya, kasa gasgatawa tayi ta karasa jikin window ta kasa kunnenta, karar tattara abu kamar kwalba taji hakan ya tabbatar mata da akwai mutum a ciki, batareda tinanin komai ba ta nufi part din, hannunta ta dora akan handle din kofar da niyar knocking kawai taji kofar ta bude, da mamaki tashiga bin parlor da kallo ganin ko ina kacha kacha kamar anyi dambe a parlorn…
Karar bude kofa deen yaji ya fito da sauri gabansa na faduwa, kawai yayi ido hudu da umm da take kallonsa kamar wanda bata taba gani…..
Zaro ido umm tayi a mamakance tace;
“Me zan gani haka, waye wannan? Saif kaine kuwa? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”….
A sanyaye ya sunkuyar da kai yace;
“Umm ni ne, stop panicking please”…
“Stop panicking fa kace saif? Kaganka kuwa, hasbunallahu wa ni’imal wakeel meya sameka? Yaushe ka dawo, why is everywhere so rough including yourself?”….
“Babu abinda ya sameni umm, jiya na dawo”…..
Kamo hannunsa tayi suka fita daga part din har lokacin bata dena mamaki ba, she just can’t believe saif ne haka kamar wani mahaukaci, part din mami suka shiga daidai mami na sakkowa daga sama…
A razane itama tace;
“Jam ina kika samosa, mun shiga uku ciwo kayi ne saifuddeen? Ina ka tafi, meya sameka? Kaga yanda ka rame kuwa?”……
Zama yayi akan kujera yace;
“Babu abinda ya sameni mami”…
“Babu abinda ya sameka fa kace? Yaya kina ganin abinda nake gani kuwa? Saif wallahi baka cin abinci, waye anan zo nan”….
Shi dai kallonsu kawai yake ganin sai exaggerating suke dan shi kwata kwata bega chazawar dayayi ba…..
Hussy ce ta fito tace;
“Nice umm, gani”….
“Je ki hado abinci ki kawo yanzu”….
Babu jimawa sai gata ta dawo da abinci a hade akan faranti, nuna mata kan table umm tayi ta ajye sannan ta tafi tana ta satan kallon deen….
“Saif ka gayamana gaskiya dama dai kana cikin gidannan ko?”…..
“A’a umm”…..
“Toh meya sameka haka, ramar nan da kayi bata lafiya bace wallahi”….
“Banda lafiya ne amma naji sauki yanzu”……
Ya fadamata hakanne saboda ta kyalesa dan yasan inba haka yace ba umm bazata yarda ba….
A hakanma be tsira ba dan cewa tayi;
“What’s the cause of the illness? Kayi tests? Where is the result? Wani drug kake sha?”…..
“Umm please, wallahi I’m fine”….
Ya fada yana marairaice fuska….
“Hmmm I will treat you again, ko menene zan gano”….
Dariya yayi yace;
“Haba umm sai kace ba likita ba”….
“Well we shall see, yanzu dai bari na baka abinci because you look like someone that has been starving”….
Bece komai ba ya dibo abinci ta kai bakinsa, karba yayi niyar yi ta zare masa ido wai ya cire hannunsa, babu yanda ya iya haka ya bari ta bashi abincin a baki kamar wani yaro, bata kuma kyalesa ba sai da ya cinye tass, kasa kasa yace alhamdulillah yana irga kwanakin da yayi be ci abinci ba…..
Lokacin da hussy ta shiga baby tee na wanka, zaman jiran fitowarta tayi dan ta mata gulma yaya saif ya dawo, tana fitowa kuwa ta fada mata, baby tee na jin haka ta shirya a gurguje ta fita parlor, saidai tana zuwa ta kasa karasawa tuno da last encounter dinsu, sai taji kunyar hada ido takeyi dashi, kamar dazu da hussy tazo wucewa haka umm ta sake jin motsi tace waye wannan yazo saboda tasa a fita da kwanu….
Kamar wata munafuka haka baby tee ta fito idonta a kasa….
Wani masifaffen kamshi ne yaji ya daki hancinsa, dagowar da zeyi ya ganta a tsaye a gaban umm, zaro ido yayi yana tashi daga kishingiden dayayi yana kallonta, kamar wacce aka chanzawa halitta haka ya ganta, shi sai yaga kamar ba ita bama, ta kara girma ta kara cikowa uwa uba fatarta na wani mugun kyalli me daukan ido, kamshi kuwa kamar anyi barin turare a parlourn…..
Kasa jurewa yayi yace;
“Ke zonan”….
Ajye kwanukan da umm tasata ta fara kwashewa tayi ta karasa gabansa tana mamakin ramar dayayi, kallonta ya farayi tindaga sama har kasa yaga kamar an kara mata tudun jiki, kada ma kugunta yaji labari dan gani yayi kamar an kara mata fadi ta nan sosai, kallo daya yayiwa samanta yaga shi kuma kamar anyi pomping dinta, wani mugun bacin rai ne yazo masa tuno da duk saboda wanchan banza ake mata wannan gyaran, amma uban me suka bata haka ta chanza dayawa a cikin sati biyu? Kasa dannewa yayi ya daka mata wani mugun tsawa yace;
“Bar nan!!”…..
Diddira kafa tayi ganin su mami a zaune sannan ta turo baki tabar parlourn, ai ji yayi kamar an buga masa dutse akai ganin yanda komai yake motsi a jikinta, babban tashin hankalinsa kuma khaleel za’a kaima duk wannan abun, a fusace ya juyo yace;
“Me kuka bawa yarinyar ta kumbura haka?”….
“Me kuwa zamu bata? Saboda ka rame ne kawai kake ganin kamar tayi kiba amma yanda take haka take”….
Cewar mami tana daure fuska….
Tashi yayi saida ya kai bakin kofa sannan ya juyo yace;
“Inma wani jikejiken kuke bata saboda zatayi aure gwara ku dena dan be dace ba”…..
Yana fadin haka yayi part dinsa…..
Sakin baki umm da mami sukayi aka rasa me magana a cikinsu…..
Sai da ya koma part dinsa yaji kamar zuciyarsa zata fita daga gangar jikinsa, hangowa kawai yake khaleel ya haike mata dan yasan babu lafiyayyen namijin da za’a kai masa zahrah ya barta ta kwana without deflowering her, shi yana nan tinaninta kamar ze kashesa ashe ana chan ana pomping dinta ma wani, mere thought of khaleel ya tabata sai yaji kamar ya zare, hargitsa bedroom dinsa yayi ya nemo SIM card dinsa yasa a waya, wayar na kawowa ya kira number sudais dan shi kadai ze iya juyewa kadan daga cikin damuwarsa….
Ko sallamar da sudais ke masa be amsa ba cikin daga murya kamar wani zararre yace;
“Sudais shikenan zata zama tasa, sudais kaga yanda ta chanza kuwa?, sudais yanzu in aka kai masa ita shikenan sai yace ze sadu da ita ko?, sudais an min adalci kenan?, meyasa lallai sai sun aurar da ita? Sudais da in zauna inyi witnessing ranar da za’a kaita dakin wani kato gwara in sha poison in mutu hankali kwance”…..
Sake duba sunan me wayar sudais yayi dan ya tabbatar da shi din yake magana dukda yanajin muryarsa, be taba ganin deen in a weak state irin haka ba da har yake sambatu da kanaji kasan na kishi ne, sai wani maimaita sunansa yake kamar shi ya rada masa, yanajin maganar poison ya dakatar dashi da fadin;

“WACECE ITA?”…..
Karar faduwar abu yaji hankali tashe ya dinga maimaita;
“Saif! Saif! Bro talk to me! Bro can you hear me! Broooooo”…
Amma yaji shiru gashi ba’a yanke wayar ba, hankali tashe ya chanza akalar motarsa zuwa gidansu deen dama akan hanya yake yaga kiransa….
Yana zuwa gidan be tsaya ko ina ba sai part din deen, be samu kowa a hargitsattsan parlorn ba ya karasa bedroom dinsa, yana shiga me zai gani? Deen ne a kwance a kasa baya numfashi!!…

Domin sauke cikakken Littafin sai ku danna inda aka saka Download

Back to top button