Hausa novels

Halysaah Page 208 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 208…Ajay ya kai hannu ya debi roasted ground nut da aka ajiye masu kan tabarman da suke zaune yana ci a hankali abubuwa da yawa na dawo masa kai na rayuwar da yayi cikin gidan da duk dawainiya da hidimar da suka dinga yi masa without knowing him, he could remembered ya bude idonsa ya tsinci kansa a gidan nan although he was semi conscious for a very long time amma yana tuna abubuwa da yawa, after a while Jay ya debi gyadar ya fara ci shi ma yana bin karamin tsakar gidan da kallo, Khaleesat dai na zaune kan wani tabarma daban ita ma ga gyadar a gabanta an zuba mata amma ko kallon gyadar bata yi ba wayarta kawai take dannawa fuskarta babu yabo babu fallasa, lokaci lokaci take daga kai ta kalli Amisoh dake gaban murhu ita da mahaifiyarta tana tayata fifita wutan girkin da suke yi, fara’a ce sosai shimfide fuskar yarinyar kana kallonta kasan she is very happy, Ajay ya juya ya kalli Khaleesat a karo na hudu tun zamansu a compound din gidan, duk da basu fi minti goma ba amma taki kallon inda yake, calmly yace “Baki son gyadan ne Jeeddah?” Ko kallonsa bata yi ba balle ta basa amsa sai ma daure fuska da tayi tana ta danna wayarta, Ya dauke kai bai sake ce mata komai ba, Ozhi ya gama fasa kwakwan da yake gyara masu ya wanke kwakwan a cikin earthen bowl ya kai masu kan tabarman ya ajiye sannan ya zauna shi ma, zaman shiru suka yi a wajen, kowa da tunanin da yake a rai, Ajay ya ɗaga kai yana kallon Ozhi yayi breaking silence din, ya nuna masa Jay a hankali yace “Wannan ɗan uwana ne na jini, sunansa Ahmad shi ma” Ozhi yayi murmushi yace “Na gan ku iri daya sosai, nayi tunanin haka a zuciyana” Ajay ya kalli Khaleesat yace “Matata ce wancan” Ozhi na gyada kai da mamaki yace “Dama kana da aure ko sai da ka tafi kayi yanxu?” Ajay ya ɗan yi murmushi yace “Ina da aure dama” Ozhi ya girgiza kai yana kallon Khaleesat yace “Allah sarki, sannu fa, sannu” Ya juya Ya kalli direction din da matarsa take yayi mata magana da yarensu, sai gata ta taso ta nufo Khaleesat da fara’a sosai fuskarta tace “Sannu fa, sannu da zuwa, sannu…” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “Yauwa nagode” Komawa matar tayi ta ci gaba da abinda take, Amisoh kuwa sai kallon Khaleesat take tana murmushi, Khaleesat dai bata kalli direction dinta ba, Ajay na kallon Ozhi yace “Ina mutumin nan me magani?” Ozhi yayi murmushi yace “Dochu kenan… Ya tafi wani daji jiya” Ajay ya sauke idonsa, they were all silent for some minutes, Ozhi yayi breaking silence din yace “Naji rashin dadi bayan da ka gudu, wannan ranan ban yi bacci ba, na damu sosai, haka ma family na, dama wasu mutanen garinmu suna ce min kai kana da lefi, don me lefi kadai ake yi ma harbi, suna ce min in bar ka ka mutu, amma ban ji kowa ba, saboda ina son in ceci rayuwar ka da na tsince ka cikin ruwa, ranan nan da ka gudu na dawo garin mu mutane da yan uwana suka ce dama suna gaya min ni ne ban ji magana ba, sun ce baka da gaskiya, ni da familyna mun ji rashin dadi sosai, amma kuma zuciyana bai yi believing kai me lefi ne, ina ta yi maka tunani me kyau a zuciyana” Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace “Bayan na bar garin nan mun tafi asibiti a America ne aka min aiki, 3 days ago muka dawo daga America, ko gida bamu je ba muka zo nan, saboda ina son in gan ku” Ozhi yace “Allah sarki, ni zuciyana yasan kai me gaskiya ne, yanxu ka warke sosai ko?” Ajay na murmushi yace “Na warke” Da ido Khaleesat ta bi Amisoh dake rike da babban clay bowl dauke da manyan kifaye an masu farfesu, yarinyar ta karasa har gaban su Ajay ta ajiye bowl din sannan ta mike ta tafi ta dauko wani bowl cike da shinkafa ta dawo ta ajiye tana murmushi ta kalli Ajay, murmushin ya mayar mata, Jay ya saci kallon Khaleesat yaga idonta na kan su, sosai hakan ya basa dariya, Amisoh ta mike ta bar wajen, a hankali Ozhi yace “Tun bayan da na dawo garinmu ni kadai babu kai sai yau ne Amee take yin dariya haka” Ajay dai kallonsa kawai yake kamar yanda Jay da Khaleesat ke kallonsa su ma, Ozhi ya girgiza kai yace “Ina ta damuwa halin da yarinyana ta shiga saboda ta saba da kai, kuma ita daya ne yarinyana da Yesu ya bani, bata son ta ci abinci da ka tafi, sai dai tana kuka da safe da rana da daddare, na zo na gane kai yaro ne da ke shiga cikin zuciyar mutum, don nima kana cikin zuciyana….” Ajay was quiet, Jay na kallon Ozhi yace “Sabo ne yasa ta shiga damuwa” Ozhi yace “Dama sabo ne ai, ita ne ke yi masa abinci fa idan mamanta ta tafi Benue zuwa program dinsu a coci, idan na tafi fishing ko tapping din Palm wine tana nan kusa da shi a zaune kullum don yana yawan bacci, har beard din fuskansa tana aske masa yanda taga ina yi, tana kulawa da shi sosai, ta yi sabo da shi sosai fa” Jay ya daga kai yana kallon Amisoh da ta nufo inda suke zaune ta ajiye kwanon da za su debi abinci ciki, sai cups biyu, mikewa tayi ta shiga cikin wani hut sai ga ta ta fito da calabash din palm wine ta karasa ta duka gabansu ta ajiye masu, Jay ya ɗan bude ido yana kallon palm wine din, ta dau cup duk ta zuba masu, Ozhi yace “Fresh Burkutu ne…” Ajay ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, Amisoh ta dau plate ta debi abincin da farfesun kifi ta kai ma Khaleesat ta ajiye mata a gabanta, hade rai Khaleesat tayi taki kallonta tana ta danna wayarta, Amisoh ta kalleta tace “Abinci” Kallon abincin Khaleesat tayi a takaice tace “Ohk” Ozhi na murmushi ya kalli Ajay yace “Tana yin Hausa kadan kadan yanxu, saboda yanda ta shaku da kai shine tana ta koyon Hausa wurin kawayenta bayan ka tafi” Ajay ya daga kai ya kalleta yana murmushi yace “Kin iya Hausa yanxu kenan” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta zauna kan tabarman da Khaleesat ke zaune, Khaleesat ta juya ta kalli Jay, sai kuma ta dauke idonta tayi dialing numbersa, Jay ya ciro wayarsa a aljihu yana ganin numberta ya daga kai ya kalleta, ta katse kiran sannan ta tura masa message wai zata yi magana da shi, mikewa tayi bayan ta tura message din ta fita daga compound din, Jay ya mike ya bi bayanta, Ajay ya bi sa da kallo, Khaleesat na kallon Jay bayan ya iso inda take tsaye, a hankali tace “Don Allah Ya jawwad yaushe za mu tafi, na gaji ina son in kwanta ne, naga kuma yamma yayi, ruwa fa za mu tsallaka” Yana kallonta yace “Halysaah, this is where ur husband spent 2 years taken care of by this people, basu san sa ba, basu san ko shi waye ba, but they stood by him and gave him all the care he needs, so now what is all this attitude you are giving for?” Lokaci daya hawaye ya cicciko idonta tana kallonsa tace “Shikenan sai aka ce ya rungumi wanda ba muharramarsa ba Ya Jawwad? Rungumarta fa yayi, kana kuma kallon yanda yake ta yi mata dariya kamar muharramarsa….” Kasa daurewa tayi ta fashe da kuka sosai, kiris ya rage Jay bai yi dariya ba don ba karamin dariya ta basa ba, ya dake yace “But Halysaah a gabanmu fa ta taho ta rungumesa ba shi yaje ya rungumeta ba” Cikin kuka tace “To ba sai ya koma gefe ba da sauri tunda yasan ba muharramarsa bace, ni wallahi na gaji tafiya nake son yi, ai Allah ne zai basu lada ba mu ba, in ma shi bazai tafi ba ni dai mu tafi Ya jawwad, wallahi jiri nake ji” Jay yace “Amma sai da nace ai kar ki biyo mu ki ka ki ji….” Ta kara fashewa da kuka ita kanta a zuciyarta tana mugun da ta sanin biyo su da tayi, cikin rawan murya tace “I am sorry for not listening, pls kar dare yayi Ya jawwad, mu tafi don Allah” Yace “We are not here to rush things Halysaah, we are not in a haste, they patiently accommodated ur husband and took care of him with no complain, so we have to be patient and show our gratitude without rushing” A fusace tace “To ni dai mu je ka dora ni a kwale kwalen da zai fitar da ni daga garin nan ko in tafi ni kadai” Jay yace “Ohk baza ki ji magana ta ba kenan?” Ta marairaice tace “Kwanciya fa nake son in yi Ya Jawwad, kuma zazzaɓi nake ji wallahi” Yace “In dai zan maki magana ki ji to juya mu koma ciki, and stop frowning ur face, in baki gode masu ba baza ki daure masu fuska ba” Ta kasa cewa komai tana jin kamar ta kurma ihu ko zata ji saukin zafi da take ji a zuciyarta, da kyar ta goge hawayen idonta ta juya ta koma cikin gidan, suka tarar da Ajay yana cin abinci Amisoh na zaune kan tabarman alamar ita ta zuba masa, Ko kallonsa Khaleesat bata yi ba ta tafi ta zauna, Ozhi na kallon Jay yace “Babu damuwa dai ko? Ko tana son wani abu ne?” Jay yace “Bata da lafiya ne, tana son zata kwanta” Ozhi yace “Ayya, sannu fa” kiran matarsa dake cikin bukkanta yayi sai ga ta ta fito yayi mata magana da yarensu, sannan ya kalli Khaleesat yace “Zata kai ki daki ki kwanta” Khaleesat ta kasa cewa komai, matar kuwa sai kallonta take tana murmushi, Jay na kallonta yace “Tashi ku je” Kasa yi masa musu tayi ta mike da kyar ta bi bayan matar Ozhi suka shiga Bukkan ta, Ajay dai sai cin abincin gabansa yake Jay na kallonsa, can ya daga kai ya kalli Jay yace “Ain’t you eating?” Yana fadin haka ya kalli Amisoh yace “Ki zuba masa shi ma” Tayi murmushi sannan ta dibar ma Jay abincin ta ajiye masa a gabansa, ko minti sha biyar Khaleesat bata yi a bukkan matar Ozhi ba ta fito ta nemi waje ta zauna, Ajay dai yaki kallonta sai hira yake yi da Ozhi. Wajen karfe biyar da rabi Ajay yace ma Ozhi za su koma Benue, Ozhi na kallonsa yace “Ina ce za ku yi bacci a nan ai tunda yamma yayi sosai yanxu” Ajay na murmushi yace “Zan dawo gobe….” Ozhi dai yayi shiru, lokaci daya hawaye ya cika idon Amisoh dake kallon Ajay, kuka ta fara yi kawai ta mike da sauri ta bar wajen ta zagaya can bayan gidan duk suka bi ta da kallo, uwarta dake zaune tsakar gidan ta mike ta bi bayanta, Jay dai mamaki ya sa ya kasa rufe baki, Ajay ya kalli Ozhi a hankali yace “Ka gaya mata ba tafiya zan yi ba, zan dawo gobe da safe” Ozhi ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru, Sai ga matar Ozhi ta dawo tsakar gidan tana kallon mijinta tayi masa magana da language dinsu, sannan ta tafi ta zauna inda take zaune, kana iya jiyo shesshekan kukan Amisoh, a hankali Ozhi yace “Tana tunanin idan ka tafi kuma shikenan” Ajay ya sauke idonsa bai ce komai ba, after some seconds ya mike, Khaleesat ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, ya nufi inda Amisoh ta zaga, ya tafi har gabanta ya tsaya yana kallonta yace “Zan dawo gobe Amisoh, ba tafiya zan yi ba” Cikin kuka tace “Zan tafi da kai” Ajay yayi shiru, sai kuma yace “To dena kuka, za mu tafi tare” goge idonta ta fara yi, ya juya ya bar wajen ta bi bayansa yana komawa cikin gidan ya zauna yana kallon Ozhi yace “Da ina son idan na koma garinmu za mu dawo tare da Babana ya gan ku, amma yanxu ina son mu tafi tare da ku garinmu tunda kun yarda da ni, Babana shi ne Sarkin garin mu, idan na kai masa ku zai yi farin ciki, ina son ku san garin mu da kuma gidanmu, da mamata da yan uwana gaba daya ” Ozhi yayi shiru yana kallon Ajay, Amisoh ta duka kusa da babanta tana masa magana da yarensu hawaye na zuba idonta, Ozhi ya sake kallon Ajay yace “Na yarda da kai abokina, amma a ina garin ku?” Ajay yace “Idan mun je Abuja za mu hau jirgin sama ne zuwa garin namu” Ozhi da matarsa duk suka bude ido sosai suna kallon Ajay.

Back to top button