Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 28 Book 2 Complete Novel

“Wakenan?” ya tambayi Mummy yana kallonta

“eh da ita yarinyar daka dawo dan ita mana, tunda tana maka abunda bana maka, wallahi kaji tsoron Allah, ba irin Magiyar da banyi maka ba, Amma kayi biris amma yanzu dayake tafini ai gashi kadawo” 

Tsyawa yayi ya zubawa Mummy ido tagama, Yayi tsaki ya tashi ya fice yana masifa. 

Haka yakoma dakinsa yana mita yana tunanin meyasa ma yaje inda take. 

Jalila tanata lissafi gobe su Abba zasu dawo, dan haka ta tsananta Addu’a Allah yabata sa’a yasa Abba ya janye batun Aurawa Jawwad Naja. 

Yauma Jalila taje school, sun kammala lectures, sunfi to itada Zahra, Zahra tace

“Yawwa nikam Jalila naji Wata suna hira tace wai jiya wani hadadden gaye yazo yasaki a mota ya tafi dake, amma wai dagani dan shaye2 ne dan wuyansa hada sarka, ga wani irin Aski akansa, ina fatan lafiya ba wata matsalar bace?” 

Dan karamin tsaki Jalila tayi aranta tace” 

dan jaraba da masifar mutane komai kayi idonsu akanka

“Eh haka akayi, seme kuma?” 

“A’a ba komai dama nayi tunanin ko mutanen baban Saleema ne” 

“basu bane, Yayana ne” Jalila tabata amsa a takaice, Dan zare Ido Zahra tayi

“dama kinada yaya dayake shaye2, na zata Yaya Jawwad ne kawai Yayanki” 

“Akwai wani to, kuma akansa nayiwa Alhaji Kabiru baban Saleema, abunda yanzu yana daf da zuwa prison shida ‘yan tawagarsa” 

“Amma Jali…. 

” Ke zahra kin isheni wallahi, nagaji ga yunwa ina ji se faman tambayoyi kikemin, sekace wata likita, haba se Allah ya kaimu gobe”

Inda sabo Zahra tasaba da halin Jalila, tanada saukin kai Amma tanada tsari a komai nata, in bakasan halinta ba zakace batada kirki ne kawai, bata da san yawan tambaya. 

Mummy ta bawa Ilham kudi tace ta kaiwa Nana ta ajiyewa Maama in ta dawo a bata, Ilham ta karba harta shiga gidansu Nana wani tunani ya fado mata a rai, dan haka tayi murmushin mugunta tashi. Tana fitowa hakan yayi dai2 da dawowar Jalila daga makaranta sukayi karo a kofar gida. Ilham ta tsare Jalila da ido tana mata kallon zaki gamu dani ne. 

Jalila tace “Ilham wai kin manta maganar danayi mikine? Ki dawomin da Al’qur’anina tun muna sheda juna dake” 

Ilham ta rike kugu ta kalli Jalila “idan naki fa? Me zakiyi?” 

“Aimeyi baya fada se dai kigani a aikace, zakiga matakin dazan dauka, ki kawomin abina na gayamiki” 

“ina jiran ganin matakin dazaki dauka din, amma kafin ki dauka ni ki saurari nawa” 

“banida lokacin saurarar duk wani shirmenki, ba abunda kika isa kiyi min, nagama magana Ilham” 

Jalila tasa kaii ta shige gida. 

Kwana hudu kenan basu kara haduwa da Jalal ba, haka nan yaji yana kewarta sosai. Koba komai yayi missing neman maganar ta. 

Sannan tunda abun nan yafaru tsakanin sa da Mummy be kuma shiga cikin gidan ba. Mikewa yayi yafito zetafi gidansu Jawwad. 

Yana kokarin fitowa daga part dinsa Ya hango Ilham a jikin mota tanata boye kudi a jikinta, yana ganin haka yasan bata da gaskiya amma bebi takanta ba ya fice. 

Jalila tana zuwa ta dire Jakarta ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar Azahar ta kwanta bacci, se la’asar ta tashi, tayi sallar la’asar sannan taji tana jin yunwa. 

Jalila tana zaune akan dadduma kafin tabar kan daddumar ta, Ahmad ya kirata suka dinga hira har kusan 40 minutes, Nana kallon ta kawai takeyi seda tabari tagama sannan tace

“Jalila wai dan Allah ina kika samo wannan Ahmad din, iya sanina ba kya son duguwar waya amma kalli yadda kika zage kina waya” 

Jalila tayi murmushi sanna tace

“Nana a Bauchi na samo shi, yanada kirki sosai” 

“kinga niba wannan ba magana nakeso muyi masu mahimmanci” 

“inajinki amma ki hanzarta inajin yunwa” 

“bawani in hanazarta, ki zauna kigama wayar se yanzu zakiji yunwa? 

Jalila dan Allah ki gayamin hakikanin meke tsakanin ki da Yaya Jalal?” 

Jin maganar tayi wani banbarakwai, batayi zaton jin wannan tambayar ba

“kamar yaya? Kinga wani abune da baki yadda dashi ba? Meyasa kikamin wannan tambayar” 

“Jalila ruwa baya tsami banza yadda Ilham ke takura tsanarki tabbas wani abun tagani, tana claiming kuna soyayya ne, nima da nayi wani nazari zancenta yana kusada gaskiya” 

“Mtseww niban san yakuke so inyi ba, da muna fada da shi, ance banida kunya inamasa rashin kunya, yanzu na dena ance ina sonsa to ya zanyi, Nana niba son Jalal nakeba, ina tausayinsa ne musamman danaji labarin waye shi, Nana a baya nikaina nasan na bata masa rai dayawa, yadda nake masa rashin mutunci da bakaken maganganu, naga ban kyauta ba sannam ba’a gyara da barna, muddin kanaso ka temaki mutum ya dena aikata laifi indai zakayi masa hayaniya baze dena ba, zaka kara tinzira shine, na fuskance shi yanada mataukar saukin kai, na gane hakanne a zuwan dasu Hanan suka danyi, Hanan gashi sa’ata ce, tafini tsiwa amma yana sakarmata fuska har yayi mata wasa, ita bata masa rashin mutunci kamar ni, shiyasa nima na sassauta yi masa wulakanci, 

Amma babu soyayya tsakanin mu, ina fatan kin gane”

Mikewa tsaye Nana tayi tana shirin fita ta waigo tace

“Naji amma ban yadda ba” Nana ta fice daga dakin, tunani Jalila ta dingayi kozata gano wani dalili ne yasa ake kallon soyayya ce tsakanin ta da Jalal amma bata ganiba share wannan tunanin tayi ta mike ta fito itama domin neman abunda zataci dan ba karamin yunwa takeji ba. 

Koda ta duba kitchen ba’ayi girki ba bakomai tayi tsaki ta fito daga kitchen din. 

Daki takoma ta hado goldenmorn dinta ta fito farfajiyar gidan domin shan iska, tasamu kujera ta zauna tana cin Abincinta, Abba takira a waya yakara tabattar mata da gobe Insha Allah ze dawo, ji take kaman ta Jawo gobe Abba yadawo dan ta kagu ta dau mataki akan Naja. 

Tanata wannan tunanin aka kira wayarta, A zatonta Ahmad ne amma se taga bakuwar lamba dagawa tayi tasaka a kunnenta tareda yin Sallama 

Caraf taji matar ta Ambaci sunan ta “Jalila yakike ya gida?” 

“lafiya kalau Alhamdilillah” 

“Antyn Jalal ce, nasan baki gane me maganar ba” 

Murmushi Jalila tayi tace 

“yi hakuri Anty ban dau muryarki bane, ya gida ya kukaje gida ranar” 

“lafiya kalau nasan baki dauki muryata bane, Jawwad nakira nace ya turomin lambarki mudinga gaisawa, ya mutan gidan naku?” 

“lafiya kalau Anty, yasu Mahmud?” 

“Ahha Mahmud Nana zaki tambaya shi, muntafi da kwana uku yakoma U.K”

“Allah sarki, aikam kullum suna tareda Nana a waya” 

“Aikam naga shi can nasa hankalin ya karkata, se fatan Allah ya tabattar da alkhairi” 

“Hakane Ameen ya Allah” 

“Jalila ya Amanata dana bar miki?” 

Dan murmushi Jalila tayi tace 

“Yana nan Anty” 

“Kundena fadan dai ko?” 

Murmushi Jalila takumayi tace “Anty kenan” 

“Au kunya na baki? Jalila bamuda kalaman dazamuyi Amfani dasu gurin gode miki akan namijin kokarin da kikeyi keda Jawwad akan Dan uwanmu mungode Allah yasaka maki da Alkhairi” 

“Haba Anty meye wani abun godiya kuma? Ni banga wani abu da nakeyi ba” 

“inke baki ganiba mu mungani ai, ko iya yanzu kin taka rawa gurin canza abubuwa dayawa a tareda shi, munyi waya dashi yacemin daze bar kasar nan kika hanashi” 

“hmm sa’a kawai nayi, nazata ma ze min duka, Allah yakara shirya shi, nima nagani ya rage Abubuwa sosai” 

“Ameen Jalila, haba baze iya dukanki ba ai, he respect you fiye da yadda kike tunani, ki kulamin da amanata Jalila, inaji a jikina abubuwan da Jalal yake zezama tarihi sanadinki” 

“Allah yasa, Munagodiya Jalila, Allah ya jikan magabatanki” 

Jalila ita bataga me tayi ake mata wannan godiyar ba, Jalal din da banda fada ba abunda ke hadasu, dan haka Tace

“Anty yaushe zanzo abani turaren maiduguri ne? ” 

“Kibari in Aurenki yazo har kano zanzo in hadaki, kamshi sekin gaji, Allah ya nunamin Aurenki” 

Dariya Jalila tayi ta kashe wayar, Antynsa tanada saukin kai, gata da abun dariya, Amma ita bataga me tayiba daza’ayita yimata wannan godiyar ba. 

Washegari da safe Jalila bata tafi makaranta da wuri ba, seda tagama gyara gidan dan kusan kwana biyu Naja bata gidan, Halima dama Maama ta dade da sallamarta, Manu direba be dawo daga kai Nana ba, tunda ita Nana da wuri ta tafi school yau, 

Taita gyaran gida, da kokarin dora girki saboda dawowar su Abba, be kamata abar gidan bakowa ba gashi ba’ayi girki ba.

ta fito ta leka part din Jawwad, taga inya tashi ta kaimasa Abinci, Amma ta hango Jalal yana shan sigari, Jawwad kuma baya palourn, da niyyarta ta fadawa Jalal bakar magana amma tafasa ta shiga palourn. Batayi sallama ba unexpected ya daga kai ya ga Jalila, hade rai tayi sosai taki kulashi shima be kulata ba, ta duba ta kalleshi tace “Ina Yaya Jawwad?” 

“ki duba mana” yabata amsa a takaice

“Ina zan duba?” ta tambayeshi a ransa yace “lallai yarinyar nan kyaleta yayi bekuma kulata ba yanata shan sigarinsa, tambayarsa takuma yi

” wai yana ina? “

“Zoki duba rigata kona sashi a ciki” 

Bude baki tayi tana kallon sa, Jalal dan rainin hankali ne, amma ta shareshi ta dakko wayarta takira Jawwad be dauka ba, tsaki ta danyi taje tayi knocking kofar bedroom din Jawwad amma ta tarar yana bacci. Mayarwa tayi ta rufe ta juyo zata fita, Amma Jalal bashida niyyar dena shan taba, gashi yana kallon boom TV ne music ne kawai yake tashi, yana shan sigarinsa yana lumshe ido, ya jingina a jikin kujera. Dan girgiza kai tayi tazo gabansa ta tsaya ta dauki remote ta mayar saudi qur’an, bude ido yayi ya kalleta sannan yace “Meye haka?” 

“Abunda ka gani” ta bashi amsa

“mayarmin inda take da farko” 

“Bazan mayar ba” dago Jan idonsa yayi yana kallon ta, wani tunani tayi a ranta, ta fuskanci fitsarar da rake masa baya sashi dena abunda yakeyi, dan haka tace 

“Ka karyane? Da safiyar nan kake shan sigari, kamanta me likita yace maka ne? Kobaka son lafiyar kane?” 

Shiru yayi ya dauke kai, ba karamin haushi takeji tana masa magana ya mata banza ba amma ta dake tace 

“Am talking to you, kamanta you said you want change, and i promise to help you out, please badanni ba a kashe sigarin nan please, na zata dena mu’amalarka da wannan jakin Jejen zesa ka canza kadena shaye2, amma meyasa har yanzu baka dena ba?” 

Juyowa yayi yana kallonta, tayi kalar magiya, a hankali yace

“ba lokaci daya nafara shaye2 ba, don’t expect me to stop it at once, Jeje ya dade yana cutar dani, na dade ina shaye2 bazan iya dena wa lokaci daya ba” 

Tausayinsa ne yakamata, dan haka tace “I understand, kadena sha dayawa, a hankali zakaga ka dena” gyada mata kai kawai yayi, ta dan kalleshi maganar zahra ta tuna, “wani handsome guy” 

Ba karya Jalal yanada kyau, inama ba ya wannan shaye2, da seyafi haka kyau, Amma tana fatan Allah yasa abunda ta shirya akansa yayi tasiri ya dena shaye2. 

“inaso kamin wata Alfarma” 

“fade ta Allah yasa zan iya” 

“zama ka iya, ba me wuya bace ba” 

“inajinki” 

“Dan Allah kadena saka sarkan nan, you are Muslim, bekamata ace kana yawo da itaba, da dinma nasan saboda Jeje ne kaima ka kwaikwaya please ka cireta” 

Kallonta yakeyi amma bece komai ba, can kuma ba tareda ya cire sarkar ba yace

“meyasa idan aka kirani da dan shaye2 kike jin haushi bayan kema kina gayamin? Dan shaye2 mara tarbiyya wanda ya raina iyayensa, idan wani ya gayamin kinajin haushi, Amma kekina gayamin” 

Gaba daya taji jikinta yayi sanyi, har bataso ta tuna irin bakaken maganganun datake masa abaya, musamman idan ta tuna labarin Rayuwarsa tabbas tayi wauta, amma tace 

“Waye ya kiraka da dan shaye2 naji haushi?” 

“mutane dayawa, bari in tuna miki daya, Oga KB mahaifin Faruk, ban taba tunanin yadda kika tsaneni a wannan lokacin ranki ze baci dan anci zarafina baa” 

“har yanzu kanajin haushin abunda nayi maka abaya ko? 

” ko kadan gaskiya kika fada ai, banida tarbiyya, ban cancanci zama

Abokin yayanki ba kaddararsa ce tareda tawa shi……. 

“Enough dan Allah, wannan abune daya riga ya wuce please” 

Kallonta ya kumayi sannan yasa hannu ya cire sarkar wuyansa yace “Insha Allah nayi alkawarin bazan kuma saka sarka a wuyana ba” 

Murmushi tayi “Are you serious” 

“dagaske nake miki” 

“kai gaskiya na yadda you want change, Allah ya shirye ka da gaggawa” murmushi yayi yace

“Ameen ya Allah” 

daga nan ta mike tayi waje a ranta tace

“da haka Insha Allah kafin inyi Aure seka dena shaye2 in Allah ya yarda” 

Yau fasa zuwa school tayi ta zauna ta shirya Abinci saboda dawowar su Mummy, bayan tagama ta kaiwa Jawwad nasu, ta gyra ko ina a gidan se kamshi yakeyi. 

Bayan tagama komai ta zauna tana tilawar Alqur’ani, wajen karfe daya Abba suka dawo gida, ta dinga murna tana musu barka da hanya, duk hassadar mutum yasan gidan nan ya sha gyara amma Abba ne kawai ya yaba, Maama nunawa tayi bataga ma me akayi ba. 

Bayan sunyi salla ta kawo musu Abinci. Takoma dakin su. 

se la’asar Nana ta dawo daga school nan ta dinga murna su Maama sun dawo, Jawwad seda magariba ya shigo cikin gidan yayiwa Su Abba barka da dawowa, wannan karon kamar kullum Abba yarabawa kowa tsaraba sunata murna, sun hadu a palour ana hira. 

Abba yace “Jawwad ranar Asabar Insha Allah za’akai kudin Aurenka kamar yadda Maamanka ta bukata, inda wani shiri da kake ganin zakayi to kaje kayi, Jalal yagama komai next month Insha Allah zakafara zuwa gurin Aikinka” 

Wani irin gumi ya dinga tsatstafowa Jawwad, yariga yagama karaya, sannan yana jin matukar kunya da nauyin ya bude baki yagayawa mahaifinsa baya son zabin da mahaifiyarsa tayi masa, Jalila ta kurawa Abba ido alamar bata gamsu da abunda yafada ba, Abba ya kalleta yace “ya dai ‘yar Baba? Kokinada magana ne?” 

Juyawa tayi ta kalli Maama data tsareta da ido, magana kam akwaita a bakinta amma ba’ a gaban Maama ba, girgiza kai tayi alamar A’a, ta mike ta tafi dakinsu tanata safa da marwa, tana tunanin ta ina zata fara yiwa Abba bayani, tasan kotayi Maama karyata ta zatayi. 

Gajiya tayi da sintirin datake taje ta bude wardrobe zata dau towel tayi wanka, ta bige wata jakar Naja ta fado kayan ciki suka zubo dayake bata zugeta ba, a sama inner wears dinta ta dora a kai, amma kwayoyi ne da kwalaban syrup a cikin jakara, binsu da ido Jalila ta dingayi yayinda tayi mutiwar tsaye. 

Da sauri ta durkusa ta tattare mata su ta mayar mata da jakarta yadda ta ganta, nan tunani yakara yiwa Jalila yawa bazata taba bari a Aurawa namiji kamar Jawwad wannan tanbadadiyar ba,ko Nana bata gayawa abunda ta gani ba, tayi shiru da bakinta. 

Wasa2 duk yadda Jalila taso ganin Abba personally Maama ta kankane, ta tattare a part dinsa bata matsawa ko nan da can, seda aka kai kudin Auren nan, naira dubu dari Abba yaje ya kaimusu, su Yaya mairo hada kira wayar Maama tana mita wai duk Arzikin da Allah yayi musu amma ace kudin Aure akawo dubu dari, mecec dubu dari a kudin da suke dashi, Maama taita lallabata tace tayi hakuri zasu hade a kayan lefe. 

Yayinda gefe abun duniya ya damu Jawwad, begayawa Hanan halin dayake ciki ba, ko Abinci baya iyaci, duk ya rame. Jalila da kanta taje ta dinga bashi kwarin gwiwar yacigaba da Addu’a komai zeyi dai2.

shikansa Jalal abun ya dameshi, meyasa za’ayiwa namiji Auren dole, ko mace be kamata ayiwa ba balle Namiji, shima Jawwad saboda nusaranci da kunya baze iya cewa baya sonta ba, wani lokacin kawaicin Jawwad yana batawa Jalal rai. 

Jalal yanata tunanin wani taimako ze iyayiwa Jawwad, dan shima baze bari ayi wannan Auren ba, tunda Jawwad baze iyaba zeje yasamu Abba da kansa yagaya masa Jawwad baya son yarinyar nan, yana wannan tunanin yaji message ya shigo wayarsa, 

Koda ya karanta, tsayawa yayi yanata juya message din shidai yasan tabass wannan message bana sa bane saba lamba akayi, dan haka ya barshi a matsayin anyi missing number ne aka turo masa, dan hukumar dasuka turo message din da sun san wayeshi sun san laifin dayake aikatawa da basu turomasa abunda suka turoba. 

Jalila ta yanke hukuncin yau zata samu Abba ko agaban waye, zata nuna masa illar abunda yake shirin yi

Kai tsaye part din Abba taje, ta shiga da sallama a bakinta, ya amsa sallama sannan yace “dama ina son ganinki, Baby ankaiwa yayanki kudi ze Auri ‘yar uwassa, kune’ yan mata kunfi sanin menene kuke so, kuma kuna tareda ita, maybe a kayan lefe akwai abunda takeso maybe ku tayi hirar daku, ba lallai tagayawa iyayen ta ba, dan haka inda wani abu da take bukata kokune tagayawa kota rubuto, saboda asan me za’a samata a kayan lefe”

“Abba wannan Auren fa bame yuwuwa bane?” mamakine ya kamashi yace “meyasa Jalila?” 

“Baya sonta fa” 

“Amma na kirashi na tambayeshi yace min ya yadda” 

“Haba Abba zuwa yanzu yakamata kagane halin Yaya Jawwad, tunda kake ka taba nuna kana son Abu yace bayaso? Wallahi Abba Auren nan tamkar kasa hannune da kanka ka rusa doguwar tsaftataciyar katangar rayuwar Yaya Jawwad ne, Abba please kayi bincike” 

“karya kikeyi bakar munafuka, ba wani bincike daza’ayi, yarinya ‘yar dangice, me tarbiyya da sanin yakamata suna son junansu, Amma dan munafunci shine kike bata mata suna a gurin sirikinta, kedai Azzaluma ce, ni ina kudina ma da Mummy ta bayar akawomin? Ilham tace tabaki amma dan son zuciya baki baniba seda na buga waya aka gayamin ke aka bawa”

Abba ransa ya baci dajin kalaman da Maama ke fadi dan haka yace 

“zainab meye haka kuma? Kibar ta ta fadi abunda yake bakinta mana, be kamata ki katse mata hanzari kidinga jifanta da wannan muna nan kalaman ba akanme? Na dade ina tunanin Jalila bata jin dadin zaman gidan nan, Allah ka dai yasan mekike mata inba na nan, nayi shiru ne dan bata taba gayamin wani abu akan irin zaman da take ba, kallonki kawai nakeyi zainab “

Se yanzu Maama ta shiga hayyacinta take tuna maganganun data fada idonta ya rufe ta manta shaf agaban Abba tayi su, cikin kokarin kare kai tace

” kayi hakuri Abban Jawwad, raina ne ya baci, iya sanina Naja batada wani aibu amma Jalila se kokarin kushe Auren take, kuma da ina cuzguna mata aida zata gaya maka tunda kasan bakinta baya shiru” 

Jalila kallon Maama kawai take, Abba yayi tsaki yace “Inajinki Jalila cigaba da maganar ki” 

Jalila tace 

“A’a Abba base muncigaba ba, Amma Maama ni Ilham bata bani kudinki ba, tsawon zamana a gidan nan ban taba daukan cokali da sunan ha’inci ba, kina aikena gurare da dama da kudi, har banki kike turani da ATM card dinki ban taba batar miki da ko kwabo ba abaya, wallahi ni Ilham bata bani kudi ba”

Yadda Jalila take maganar kasan zuciyarta a cunkushe take da bacin rai, dan har idonta yatara Hawaye, Maama kuwa fakar idon Abba tayi ta watsawa Jalila wani kafirin Kallo. 

Abba yace

“ke Zainab kikoma can kuyi maganar kudinku, ni ‘yata bata sata, bata ha’ inci na yadda da ita, Jalila tashi kije Allah yayi miki Albarka, karki sake ki zubar da hawayenki a banza” 

Jalila jinjina masa kai kawai tayi ta mike, tana fitowa taji hawaye nabin fuskarta wani bayan wani, koda Jalila ta koma daki Nana tana bacci dan haka ta samu guri ta takure ta fashe da kuka, hada sheshsheka tana kuka tana surutai

“Ummi kingani ko? Da tun farko kin tafi dani da kome zefaru tare ze samemu amma kinmin Nisa, kin barni inata fama da wahalar Rayuwa, banida matemaki se Allah” 

cikin bacci Nana taji kukan Jalila, koda ta bude idonta Jalila ce ke faman sharbar kuka, da sauri ta sakko daga kan gadon tazo gabanta tareda fadin

“Jalila lafiyarki kuwa? Gayamin me yasamiki?” 

Shiru Jalila tayi se kuka data cigaba, duk yadda Nana tayi Jalila taki gayamata me yafaru, Nana ta rumgumeta tana fadin 

“tunda bazaki gayamin ba bazan takuramiki ba, Amma dan Allah kidena kukan nan, Jalila banajin dadin ganin kina kuka haka dan Allah kidena in bahakaba nima zaki sani kukan” 

Jinjina mata kai kawai Jalila tayi, ta zame ta kwanta akan cinyar Nana, ta juyarda kanta hawaye na cigaba da zuba. 

Da Naja ta dawo gidan seda Maama tagaya mata abunda ta tarar da Jalila tana gayawa Abba, Naja ta dinga masifa taana zataga bayan Jalila, setasa ta bar gidan da kafarta, tunda ita mayyace, Maama ta gaya mata wai Jalila ta cinye mata kudi dubu tamanin Abba yace karta kuma daga maganar shi yasan Jalila bazatayi haka ba, suka kuma haduwa sukasa Jalila a gaba da gori, Maama ta hade kai da Naja suka cigaba daYiwa Jalila barin miyagun maganganu, Amma sam Nana bata san meyake wakana ba, zuwa makaranta ne kawai kesa Jalila samun raguwar pressure dake kanta, shima yanzu makarantar idan taje kuka takeyi bata jin lectures din. Jalila batayi mamakin abunda Ilham tayi mata ba dukda abun yamata ciwo, Amma a yanzu ita ba wannan ne ya dameta ba, maganar Auren nan ce yake damunta. 

Wasa2 Jawwad yayi rama ta ban mamaki, yana cikin tashin hankali an saka biki a kusa watanni shida, ko Abinci baya iya ci, nutsuwarsa daya idan yana waya da Hanan, kokuma Idan Jalila tana masa nasiha da bashi kwarin gwiwa, ko Abinci baya iyaci, duk haskensa seda yayi duhu, Jalila tarasa ta ina zata fara shawo kan matsalolin nan. 

Yanzuma gurin Jawwad ta tafi don ba karamin tausayi yake bata ba, taje ta kaimasa Abincin rana, ta tarar ya idar da salla ta jira Jawwad yayi Addu’oin sa ya shafa, sannan tace 

“Yaya Jawwad nasan kana cikin damuwa, amma kadinga kokarin kwantar da hankalin ka, ina nan inata kokari sannan ina Addu’a Allah ze kawo mafita” 

Murmushin yake  yayi wanda yafi kuka ciwo yace “ina Addu’a baby, ina fatan Allah yabani ikon cin Jarrabawa” 

“Insha Allah komai ze wuce sannan nace ya batun zuwan ku kaduna kuwa? Bana son plan dina ya tafi a banza”

“Ina sane Jalila, zamuje Insha Allah, kafin lokaci ya kure” 

“to shikenan, amma ka dena wannan damuwar kaji Yayana?” 

“Na dena babyn Ummi” 

Murmushi tayi masa

“yawwa haka nakeson ji, bari in dawo in gyara maka dakin nan, naga yayi kura” 

“to shikenan Autar Ummi nagode sosai, Allah ya sanyawa Rayuwar ki Albarka, Yadda kike kokarin faranta min Allah yabaki mijin daze kula dake ya soki ya rikemin ke Amana, a lokuta da dama kina sadaukar da farincikinki dan ganin wasu sun samu nasu farincikin, Allah yabaki wanda ze kulada ke, yabaki mijin marainiya, wanda ze kula dake da maraicinki”

Taji dadin Addu’ar yayan nata, Amma takasa cewa Ameen sema Hawaye daya taho mata. 

Tagama abunda take a cikin gida, taje domin gyara bangaren Jawwad, Jalal na kalmashe akan kujera yana game a system, sukaci Abinci shida Jawwad, yacigaba da game dinsa, tunda ta shigo ba wanda ya kula wani tsakanin ta da Jalal, Maama takira Jawwad a waya tace yaje cikin gida tana son ganinsa, jiki ba kwari ya tashi ya tafi, dan yasan be wuce akan maganar Naja ba. 

Jalila tasan babu alamun Jalal yayi sallar Azahar, ta duba taga system din a jikin caji take yake amfani da ita, tasa hannu ta kashe main socket na dakin, system ta dauke dama babu caji, kallonta yayi  a fusace ze masifa amma yakasa, ganin irin kallom da take masa, 

“Kayi sallar Azahar kuwa?” 

“ban Sani ba, ko innayi ke zanyiwa?” 

“Subhanallah karkayi sabo, ai ba fada bane, Salla fa, haske me girma ga tarin lada ga ma’abota yinta akan lokaci, kaga da kana bata mahimmanci sosai da yanzu Rayuwarka ta canza, da abubuwa dayawa kadaina aikata su, karfe uku ta wuce amma bakayi salla ba, wanda ya mutu baya salla kasan makomarsa wuta ce ta saqara, wadda ake sa wanda basa salla, Ai baka son shiga wuta ko dan gidan daddy? Ta tambayeshi kaman tana magana da yaro karami”

Be Amsa ba se kallon ta dayake, tasa hannu ta janye system din

“Yawwa abokin Yaya, kayi yaki da shedan, ka yaki zuciyarka ka daure, kaga in kayi sallah sekayi Addu’a, Allah na karbar addu’a bayan sallar farilla, kaje kayi salla” 

Mikewa yayi ya nufi bedroom din Jawwad ba tareda yace mata kala ba yaje yayo Alwala, yana shiga tayi Ajiyar zuciya mutum kaman wani dan karamin yaro, komai se an lallabashi Allah ya shirye ka, yanzu tagama gane halinsa, ba yasan fada ne sam, indai zaka gaya masa magana da fada, to zakuiyi fada dashi. Jalila tanata goge2 ta kunna TV takai sunna tv ana karatun Al’qur’ani, tana aikinta tanayi, sosai takejin dadin karatun suratul Yusuf,  dauke wuta akayi dan haka tv ma ta dauke, ta danyi shiru, kawai taji an dora daga inda ta tsaya, waigawa tayi ta ga Jalal yana karasa mata ayar, ya iya karatun qur’ani, bata manta randa ya kaita makaranta ba ranar data fara jin yana karatu, Murmushi tayi tace 

“cigaba mana” 

“A’a kedai kicigaba, na manta Aya tagaba, bana tilawa, bana tuna haddata duk na manta, kwakwalwar ta toshe” 

“Ahh waika manta, ba wani kamanta” 

“Am serious na manta, cigaba maybe inkin cigaba in tuna” 

Ba musu kuwa ta dora, tana cikinyi setaji yakama yanayi, 

“Amma kace ka manta? Dama ka iya karanta Al’qur’ani haka, inama kana yawanyi da ko a hanya kaga giya zaka dauke kanka ne, waye ya koya maka karatu haka?” 

“A islamiyya sannan kuma Ummi, bazan manta ba” 

Maama ta cazawa Jawwad kai akan Naja, yana zuwa dakin ta shiga yi masa fada “Wallahi Jawwad ka kiyayeni tun ban bata maka rai ba, shine ka hada kai da wannan makirar yarinyar take kokarin ziga mahaifinka akan Auren nan ko? To wallahi ka kiyayeni akan Auren nan zan iya cimaka mutunci, kuma in har muna raye baka isa ka kuskurewa Auren nan ba, indai zanyiwa yayata biyayya kai waye da bazaka yimin ba? “

Sunkuyar da kai Jawwad yayi yace” kiyi hakuri Maama, niba ina kokarin kuskurewa Auren nan bane, kiyi hakuri dan Allah “

“ni rufemin baki, se anyi magana kadinga wani ayi hakuri, Naja tagayamin wulakancin dakake mata, ka fifita waccan yarinyar akanta shima ka kiyayeni Aure zakuyi da Naja, dole ka dinga janta a jiki ku fuskanci juna” 

“to Maama yadda kikeso haka za’ayi insha Allah” duk abun nan Naja na gefe a zaune tana tauna chewing gum, tana hararsa, da Nana tana dakin Maama itama, amma bacin rai yasa tabar dakin. 

Har Jawwad ya yunkura ze fita yabar dakin, Naja tayi karaf tace “Yaya Jawwad dan Allah zan shirya zaka kaini anguwa” shiru yayi bece komai ba, Maama tace “kobazaka kaita bane?” 

“zan kaita bari inyi sallar la’asar” 

Haka ya taho ransa babu dadi, yarasa me yake masa dadi, gaba daya Maama ta canza yaya mairo kullum cikin zigata take kansa har wani sarawa yake yi, ya nufi dakinsa amma yana zuwa dakinsa abunda ya tarar ya bashi mamaki, kunnuwansa suna jiye masa kira’ar Jalal, yana karanta qur’ani , wanda rabonda Jalal ya karanta Al’qur’ani baze iya tunawa ba, to mutumin dabe damu da salla ba, ina zeyi karanta alqur’ani. 

Jalal yana cikin biyawa ya kakare, Jawwad yakarasa masa, tuni Jawwad ya manta da bacin ran dayake yi yace “Jalal yau kaike karatu haka? Amma naji dadi, yaushe rabo” 

“kanwarka ke kokarin ta kureni, nace mata na manta tace senayi shine nake tunowa naji ashe da saura, haddar bata gama zubewa ba” 

Jalila tace “niba kureka nake ba, aiba takura maka nayiba” 

Jawwad yace “Baby kinga Jalal, wallahi ba karamin kwarone ba da muna yara, kwakwalwar sa tana kawo wuta, duk lesson din daza’ayi a kansa yake daukewa, gaskiya yau kinciri tuta baby, yanzu dai mu cigaba da tilawar nima ayi dani” 

Murmushi Jalila tayi, Jalal yabata mamaki yau sosai, da Jalal yacigaba da karatu da al’umma zasu amfana yanada kwakwalwa sosai, Jalila tace “to kucigaba ni zanyi Alkalanci”

dariya Jalal yayi wadda take masa kyau dan be fiyeyiba yace “Jawwad kai zaka fara, nifa babu haddar ta zube, shekaru Ashirin baya da yin haddar kuma kaga bayi nake ba” 

Jawwad yace “hakan ma ka yi kokari fa, amma dan cigaba zan na tuna maka, nayi missing din karatun ka” murmushi Jalal yayi, yafara kokarin dorawa, yana cikinyi ne kawai yafara tari, jikinsa yana rawa, Jawwad yace “lafiya meyafaru Jalal?” 

Tari sosai Jalila ta dakko ruwa Jawwad ya karba yana kokarin bashi amma yasa hannu ya make ruwan, ya fadi kasa, nan take idonsa yafara juyewa jijiyoyin kansa dana fuskarsa suka mimmike, nan take fuskarsa tayi murtuk yakoma Jalal dinsa na ainihi dan shaye2 wannan murmushin da Annurin na fuskarsa ya dauke gaba daya, tashi yayi daga kan kujerar dayake yakoma kan doguwar kujera ya kwanta ya rufe idonsa. 

Jalila tace

“Yaya Jawwad meyasameshi kuma?” 

Ajiyar zuciya yayi yace “Jalila haka yakeyi wani lokacin, ko yana cikin nishadi inka fara masa nasiha gaba daya jikinsa ze hau rawa, ya canza Amma ze ware Insha Allah” 

Jinjina kai tayi takarasa aikinta tana mamaki sannan ta fice. 

Jawwad yayi mamakin yaushe suka shirya haka har take sashi abu yayi, Amma da ya tuna kokarin da Jalila ke tayi akan Jalal, da kuma Alkawarin data taba yi masa akan zata taya shi addu’a da kokarin ganin Jalal ya shiryu, murmushi yayi yace “lallai baby kinada sa’a mace ta farko daya ji maganar ta tun bayan lalacewarsa” 

Jawwad sam ya manta da batun wata Naja, seda Maama ta kirashi a waya, haka ya tashi ransa ba dadi ya dakko key din motarsa ya fito. 

Shigar data saba yice yauma tayi, jikin nan duk a matse se wani dan ficicin gyale, ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga gaba daya motar ta bule da kamshin turarenta dayake hawa ka, ya kunna motar yace “Ina zaki?” 

“Shopping zaka kaini zan sayi kayan kwalliya” 

Bekuma ce mata komaiba ya kunna motar yaja, ya kaita kofar wani store ya ajiyeta, ta kalleshi “to muje mana” 

“Ba inda zani, in bazakiba inada abun yi” yafada a hasale

Tsaki tayi ta bude motar ta fita, tana fita ya kashingida ya kira Hanan, seda ta kusa katsewa ta daga cikin muryarta na shagwababbu tace “My Haidar am sorry bana kusada wayarne” murmushi yayi yace

“gaskiya ban hakura ba, seda ta kusa katsewa za’a daga wayar” 

“ni gaskiya kayi hakuri ko inyi kuka” 

“No don’t cry, Ya kike?” 

“Lafiya kalau sedai ina missing dinka” 

“Insha Allah zan shigo Kaduna next week zanzo in ganki, na kusa tafiya lagos Daddy ya samo min Aiki a can” 

“masha Allah can’t wait to see you my dear, wallahi naji dadi Haidar, Allah ya kawomin kai lafiya, ina yayana kuma sirikina?” 

“Wake nan?” ya tambayeta

“Yaya Jalal mana” 

“Eh ina sa ran tare zamuzo dashi, Amma yaushe yazama sirikinki?” 

“Yacemin yabani kai yazama sirikina, nikuma zan masa tukuici da Jalila dan ita zan bashi shine tukuicin dazan bashi” dariya Jawwad yayi yace 

“ba ruwana kunfi kusa keda su” 

Sosai ya manta da batun Naja, yaketa murmushi, Kuruciyar Hanan tana birge shi, yanzu duk wata kunya ya ajiyeta, She’s so kind 

Har Naja ta dawo motar wayarsa yakeyi da Hanan. 

Naja ta fusata matuka a hargitse tace “wannan wane irin rashin mutunci ne? An samana rana Amma kana waya da wata wannan ai wulakanci ne kuma a gabana” 

Karaf a kunnen Hanan, Jawwad kashe wayar yayi dan yasan yanzu kome zece Hanan bazata saurareshi ba yanzu, dan taanada matukar kishi, ya kalli Naja yace

“Ke zabin Maama ce” wannan kuma zabina ce, dan haka ki kylaeni”

“ni kake gayawa haka ko? Wallahi zakaga rashin mutunci, kuma ko bakaso seka Aureni, kacigaba da yimin wulakanci, nikuma zancigaba da hadaka da mahaifiyarka” 

Bece mata komaiba ya kunna motar yatafi, shi gaba daya hankalinsa da tunanin sa yana kan yaze shawo kan Hanan. 

Suna zuwa gida yafita ya barwa Naja motar, daya koma daki ya tarar Jalal ya tashi, yazo ya zauna kusada shi yace “Sannu ka tashi kenan?” Jalal ya jinjina masa kai

Jawwad yace “Jalal dan Allah sati me zuwa, inaso inje kaduna” murmushi Jalal yayi yace “Zakaje gurin Hanan kenan?” 

“Eh amma tare zamuje da kai, zaka rakani” 

“meyasa sena raka ka?” 

“kaima naka zuwan yanada mahimmanci, dan Allah ka rakani” 

“to naji, amma senayi shawara” 

Jawwad yace “ba wata shawara da zakayi, Akwai damuwa ne?” 

Jalal yace “damuwar menen?” 

Nan yagayawa Jalal yadda sukayi da Naja, har Hanan taji, Jalal yace “tun farko bekamata ka boye mata halinda ake ciki ba, Amma yanzu ka kira kanwarka ka gayamata, tafara yimata bayani kafin kaje kaduna” Jawwad yace “Hakama za’ayi ka kawo shawara, kai Amma Inajin kunyar Jalila sosai” 

“meye kuma Abun jin kunyar? Kirata ni zan gaya mata” ba musu ya kira Jalila a waya yace tazo farfajiya yana kiranta. 

Befi 3 minutes ba sega Jalila tazo, Hannunta dauke da wani karamin teddy da kuma wayarta, bakinta kuma dauke da alawa me tsinke, Jalal kura mata ido yayi aransa yake zancen zuci in be manta ba, saura watanni shida Jalila tacika shekaru gome sha tara Amma har yanzu bata dena halin yarinta, kana kallon ffuskarta zaka san yarinyace, sedai Kwakwalwarta ba kowane babbane ze iya lissafin da kwakwalwarta takeba tasamesu akan fararen kujeru a harabar gidan, tayi mamakin ganin Jalal kaman bashine dazu ya canza gaba dayaba. 

Taja kujera ta zauna tace “gani Allah yasa ba lefi nayi ba?” 

Jalal yace “ke tunda kin saba lefi, duk lokacin da aka kiraki bakya kawo komai a ranki se laefi kikayi, kodayake ke ai aikata laifi a jininki yake” 

Bakinta yayi jawur saboda Alawar datake sha, kallonsa tayi ta harareshi ta dan murguda baki tace “Eh tunda kullum ‘yan sanda sesunzo sun tafi daniba, aidole kace laifi a jinina yake” 

Yadda bakinta yayi jawur din nan tana juyashi ba karamin birge Jalal yayi ba, Jawwad yayi murmushi yace “Allah yabaku hakuri, dazu gwanin sha’ awa naji dadin yadda naganku, Amma yanzu kuma zakuyi fada” 

Jalila cikin shagwaba tace “toba shine yace ina laifi ba” 

“to kice ba kyayi mana? Shekarun baya ina seda kikasa Abba zuwa kaduna kin tabo ‘yar gidan masu bullet”

gaba daya sukayi dariya, saboda Jalal da sigar tsokana yayi maganar” gaba daya Jalila mamakin Jalal takeyi, ya iya barkwanci da tsokana, Amma inbaka zauna dashiba bazaka gane hakan ba, kuma abun mamaki lokaci daya seya birkice yakoma Jalal dinsa mashayin giya. 

Jawwad yace “Baby wani taimako nakeson kiyimin” 

Ta gyara zama takara rungume teddy tace “with due respect, ina jinka babban yaya” 

Ya yunkura zeyi magana suka jiyo hayagagar Maama ta nufosu itada Naja, 

“saboda ka cimin mutunci kake gayawa Naja wai baka sonta kanada wadda kakeso, Jawwad yaushe kakoma haka? Yaushe kafara bijirewa umarnina? Ya koyamaka ko? Zama da Jalal yasa kafara bijiremin, har kake waya da wannan shedaniyar yarinyar a gabanta, na samaka ido tsakanin ku kar mahaifinka yakawo wani abu aransa amma duk baka ganiba ko? “

Jawwad yace” Maama nifa bahaka mukayi da itaba, kuma ba ruwan Jalila bada ita nake waya ba, na gayamata ita zabinkice, nima inada zabina”

Tas Maama ta dauke shi da mari, gaba daya sukayi tsit dan ba karamin mamaki abun yabasu ba, 

Shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai ko tari beyiba, cigaba tayi da zazzga masa masifa Jalila tace

“haba Maama, biyayyar da Yaya Jawwad yake miki in baki gode masa ba bekamata ki zageshi ba, kuma da ze canza hali da ya dade da canzawa dan Allah karki kuma dukansa” 

“rufemin baki kasurgumar munafuka kawai, bake kike zigashi ya bijirewa umarnina ba, jarababbiya wallahi zanyi maganinki, kuma baki isa ki hana Auren nan ba, jarababbiyar banza” 

“Kuma makira barauniya ba, mara usuli gata barauniya abun kunya itace ke kokarin kusheni wai kar a Aureni, ai garani da dangina uwa da uba, kekuwa fa, dangin uba babu, na uwarma ba wanda yasansu, kodayake ina wani dangi daza’a nuna tunda Arnane” Naja ce take wannan maganar tana jujjuya ido da kebe baki kamar uwatta. Jalila tace

“Naja, nina godewa Allah da yadda ajiyeni, da naso rushe Aurenki lokaci daya zan bata komai wallahi, Maama Niba barauniya bace ba, Ilham bata bani kudinki ba, akira Ilham din gani gata tafada miki lokacin data bani, sannan ni bazan ziga Yaya Jawwad ya bijirewa Umarninki ba, Amma kijawa Naja kunne wallahi takuma zagina, sena ambaci uwatta na zageta, nagaji da abunda kukemin Maama menayi miki, kullum ba damar inyi motsi se anciwa uwata mutunci? “

A fusace Maama ta daga hannu zata mari Jalila, Jalal da tun dazu beyi magana ba yai sauri ya shiga tsakani ya rike Hannun Maama, ya girgiza kai yace 

“A’a Maama, Jawwad ma dana san zaki mareshi bazan bari ba, gaskiya Jalila tafadi, uwa batafi uwaba, sannan in baki godewa Jawwad kiyiwa Allah godiya da samun da nagari ba, be kamata ki butulce ba, ya miki biyayya akan abunda bayaso amma baki ganiba, mahaifiyata misali ce a gareki, nikadai ta haifa amma nakasa yimata biyayya, karkiyi kuskuren da Mummy tayi a rayuwarta, kizo kina da nasani, dan Allah”

a tafi cikin gidan da yanzu takejinsa kamar prison. 

Nana batasan me akeba, tana can tana manne da Mahmud a waya, dan haka koda ta fito palour Maama ta tarar tana sababi, ita zuwa yanzu lamarin Maama har tsoro yake bata, kullum cikin fada take, takoma halin ‘yar uwatta na masifa ko gajiya batayi, Nana batabi kan maganar da Maama takeba ta wuce kitchen tadora girki. 

Jalila ta shigo palour, Maama na kokarin shiga dakinta se hararta takeyi tana tsaki, sannan ta shige Naja ma wani tsaki tayi tace

“hmm nidake naga wanda ze Nasara, duk wani iyayinki da iya munafurci da kinibibi na kafirai da kuka iya sedai kiyi kigama dan nafi karfinki wallahi kar nake kallonki nafiki iya tashanci, banza ‘yar Arna kawai, wadda uwarta ta yasar ta tafi gararinta” 

idon Jalila yayi jawur dan kuka, cikin matukar bacin rai da masifa Jalila tace 

“Naji nakuma yadda kinfini iya tashanci, tunda kin tsotsa a Nono mana, nagode Allah har mahaifina ya koma ga mahallicinsa ba’akamashi da ‘yar waniba, naki uban fa? Shekararsa biyar a prison da kyar aka karboshi, tashanci gashi nan ke kinayi yayarki da ďan uwanki nayi, sannan kinfini tashanci nikuma nafiki kai da iya wasa da hankali, ki kiyayi ranar dazan miki tonon silili, kuma Aure ne da yardar Allah baza’ ayi shiba, saboda nagama shirina akanki, lokaci kadan ya rage kifada tarkona”

Nana data fito daga kitchen bata taba jin wannan labarin na mahaifin Su Naja ba, itakuma Naja daskarewa tayi a gurin dan mugun mamakine yakamata, dan ta girmi Jalila kuma tun kafin a haifeta abun yafaru bakowa yasani ba, Amma ita ya akayi tasani. 

Jalila tuni ta shige daki, ta nufi bandaki ta dauro Alwala tazo ta hau sallaya tafara gabatar da sallar magariba. 

Jalal yanata rarrashin Jawwad 

“Jawwad tun asalinka me biyayyane da hakuri ba kamar niba, dan Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalinka, kasan iyayenmu mata daukar ziga baya musu wahala, ka kwantar da hankalinka kayi hakuri” 

Wata irin Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace “Jalal Abunda yafaru naji babu dadi, amma abunda yafi batamin rai halinda wannan marainiyar Allah keciki, Jalal hakurin Jalila yakai a yaba mata, duk fitinarta tanada kawaici da hakuri, kuma tanada biyayya, duk abunda Maama take mata bata taba nuna mata bacin ranta ba, akan Jalila nasan Abba ze iya rabuwa da Maama, amma bata taba gayamasa abunda ke faruwa ba, Jalal inajin tausayin yadda rayuwar Jalila ke kasancewa daga wannan se wannan, nasan yau kwana zatayi kuka, kuma Jalal abunda Ilham tayi bata kyauta ba, be kamata tayiwa Jalila hakaba, son zuciya ba halinta bane”

“Nasani Jawwad, komai zezo da sauki zan dau mataki akan hakan, kaji ka kwantar da hankalinka” 

“Shikenan Jalal, ka shirya jibi Insha Allah zamuyi tafiyar nan” 

“Allah ya kaimu” 

Jawwad ya amsa masa da Ameen, Jalal ya tashi ya fito, a harabar gidan yaci karo da teddyn Jalila da sweet dinta a kasa, yasa hannu ya dauka teddyn ya tafi dashi. 

Bayan Jalila ta idar da salla, Nana tace “Jalila dan Allah meya faru kikewa Naja wannan maganar? Abun yabani mamaki ni bantaba jiba fa, kodai fushi ne yasaki”? 

Jalila idonta Jawur ta kalli Nana tace “Nana duk bacin raina banawa mutum kazafi, kuma bana gori yauma raina ne ya kai makura a baci, sannan ba karya nayiwa mahaifin Naja ba, kuma na fada ne kozan samu sassauci akan bakanta min da ake, kullum aka tashi gori sedai ace uwata Arniya, kawai saboda…… Kasa karasawa tayi, maganar ta sarke saboda kuka

“Am really sorry sister, i feel your pain nasan ba dadi abunda yake faruwa dake amma kiyi hakuri dan Allah” 

Wayar Jalila ce tafara ringing Ahmad ne Amma bazata iya dagawa ba ta kashe wayar. 

Jalal na zuwa gida ya ajiye teddyn Jalila akan gadonsa ya tafi cikin gida, a palour ya tarar da Mummy amma ya shareta ya nufi dakin Ilham, tana kwance akan gado tana chatting ya fado dakin, zumbur ta mike zaune dan tasan indai taganshi a dakinta toba Arziki, ya kureta da jajayen idonsa yace “Tambayarki zanyi, idan kikamin karya sena shakeki, yaushe kika kaiwa Jalila kudi tabawa Maama?” hade rai tayi

“Na kaimata kudi, nace ta ajiyewa Maama inji Mummy” 

“karya kikeyi” 

“niba karyanake ba” 

“zan tattakaki wallahi, karya kike” 

“wayyo Allah mummy, kizo ki temakeni” ganin tana ihu ya harzuka Jalal jikinsa yafara rawa ya janyota daga kan gadon ya zuba mata mari

“Nizaki rainawa hankali? Nizakiyiwa ihu uban me nayi miki?” 

Mummy kam a sukwane takaraso dakin

“lafiya meye haka metamaka?” 

Banza yayiwa Mummy yace “waike wace irin dabbace ne? Ranar akan idona kike soke kudi a jikinki, naganki da idona amma saboda baki da mutunci kin dorawa yarinya kinsa se kuka take, wace irin zuciya ce dake haka?” 

Se yanzu Mummy tagane inda ya dosa dan haka tace  “to mara mutunci, dama saboda waccan yarinyar kazo kake wannan zare idon kake kokarin shaketa, kaji kunya wallahi ka fifita wata banza can bare akan ‘yar uwarka” 

“Karki kara dangantani da wannan shedaniyar niba’ yar uwata bace ba, tanemi ‘yan uwanta can baniba, kuma kicigaba karki fasa, indai wannan yarinyar ce you know what she’s capable of doing, ba’ a tabata ta hakura, kuma wallahi kika kuma yi mata wani abu makamancin haka sekin bar gidan nan tunda ba gidan ubanki baneba”

Mamakine yakama Mummy suka bude baki suna kallonsa gaba daya,

A fusace Mummy tace “kai ka kiyayeni, akan waccan banzar yarinyar zaka ci zarafin Ilham, kuma har kake nema ka gayamin bakar magana haka? Jalal kanayiwa kanka hisabi kuwa?” 

“Karki kara ce mata banza, ga banza nan agabanki” ya nuna Ilham 

“tayimin abunda ko raina nabata bazan biyata ba, bashida amfani yimiki wani bayani tunda son zuciyarki kawai kikasani, amma lokaci ze bayyana komai” har ya juya ze fita daga dakin idonsa ya sauka akan Alqur’ani nan a saman rio, zuwa yayi yasa hannu ya dauka ya duba tabbas Alqur’anin ne, Amma me yakawo shi hannun Ilham? Be tsaya tambayarta ba yai waje abunsa. 

Yana fita Ilham ta dora hannu aka tace “Nashiga uku mummy, wannan wace irin masiface? Wace irin kiyayya yaya Jalal yakemin haka?” Mummy tace

“kinga dan Allah darene, kidena min ihu, hankalina ya karkata wani gurin, tabbas yaron nan yana sonta, kenan seta juyamin ďa, yadda yake wannan masifa kanta, har yana wannan kumfar bakin akanta ina baze yuwu ba wallahi, ba’a haifi yarinyar dazata juyamin ďa ba, koya fifitata akaina ba”

(su Mummy amanta lokacin da ake juya ďan wata🙄) 

Ilham cikin kuka tace “Wallahi bawani sonta dayake, tana bashi kanta ne kawai, nikuma bazan iyaba shiyasa baya sona se ita dan Allah Mummy kiyi wani abu”. 

“ke rufemin bakini, yanzu ba wannan issue dinne agabana ba” ta juya tabar Ilham da sakakken baki. 

Koda Abba ya dawo beji motsin yaran nasa ba, dan yasaba yazo yatarar da Nana da Jalila suna kallon ko wani abun a palour, dan haka yake tambayar Maama

“wai ina yaran nan ne? Banga kowa a cikinsu ba, Jawwad har ya rufe kofarsa, sukuma ‘yan matan banga kowacce ba lafiya dai ko?” 

Maama tace “lafiya kalau, sun kwanta da wurine kawai” dahaka suka bar zancen. 

Washegari da safe yakasance Asabar, Jalila tana baccin dole, dan kwanakin naan bata iya bacci, ga matsanancin ciwon kai saboda kuka, wayartace tafara ringing Hanan ce dan haka ta daga, amma da mamakinta taji Hanan tana kuka, nan da nan hantar cikin Jalila ta kada tace “Hanan lafiya kuwa?” 

Cikin kuka Hanan tace “Jalila dama Haidar Aure zeyi kuka boyemin?kuka kyaleni naketa masa wannan makauniyar soyayyar?” 

“Haba Hanan, waya gaya miki haka?” 

“ya zakice waya gayamin? Jiya muna waya da kunnena naji, muna waya dashi wata tana cewa wai ankusa bikinsu yake waya da wata, Jalila am so disappointed, meyasa kukayumin haka?” 

“Hanan bazaki ganeba, yanzu haka cikin rikici muke dagani har Yaya Jawwad” 

“Jalila duk rikicin da kuke ciki bekamata kumin haka ba, amma nagode”

Jalila na kokarin yimata bayani amma Hanan ta kashe wayar ta, dafe kai Jalila tayi ta marasa dame zataji, Hanan, Jalal, Jawwad kokuma wannan tashin hankalin. 

Jawwad ya gayawa Abba zeje kaduna, Abba be hanashi ba, ya fuskanci Jawwad baya walwala, amma Abba yabarshi a stress ne na shirye shiryen biki da kuma tunanin rabuwa da gida ze tafi wani gurin aiki. 

Jalal yakira yagayawa Abdallah cewar zasuzo, 

Hanan kam tasha kuka, Abdallah yazo mata da labarin Jawwad zezo, amma sam batayi murna ba, Mummy se rarrashinta take, amma kuka kawai takeyi. 

Daddyn Hanan yasan da zuwansu Jawwad dan haka befita  ba yana gida. 

Shabiyun rana su Jalal suka iso kaduna garin gwamna, sunsami kyakyawar tarba a gurin iyayen Hanan. Har cikin gida Abdallah ya kaisu Jawwad suka gaida Mummy, Abunda ya daurewa Mummy kai be wuce yanayin abubuwan Jawwad sak Yusuf dake bauchi, boye mamakin ta tayi suka gaisa sosai, har cikin ranta ta yaba da hankalin Jawwad, har ranata takw Addu’ar Allah yasa Jawwad ya auri Hanan. 

Abdallah yaje dakin Hanan yasameta a daki idon nan jawur ta sha kuka, yace mata “to uwar kishi gashi can yazo, yakamata kije ya ganki tunda danke yazo, amma fa naga shima kaman bashida lafiya ne, naga ya rame sosai” 

Da sauri ta mike zaune tace “dan Allah bashida lafiya?” 

“hmm magulamaciya, da kikace haushinsa kikeji, keda a rayuwarki ba kya uzuri, inkin ga dama kicigaba da kukan karkije” ya fice yabar mata dakin, bayansa tabi da harara, tayi zamanta taki tashi, seda Mummy ta biyo sahunta taita mata mita sannan ta mike, jallabiya tasaka baka se mayafinta ta tafi palourn da aka sauki su Jawwad. 

Kallo daya zakayi mata kasan tasha kuka, tana zuwa tasamu guri ta zauna ta takalli Jalal tace “Yaya Jalal sannu da zuwa ya hanya?” 

Murmushi Jalal yayi yace “lafiya kalau Hanan, ga Jawwad din na kawomiki” 

Kallon Jawwad tayi kawai tafara kuka, Jalal yace “Ikon Allah, su mata komai nasu na kukane, hakama Jalila takeyi, mikewa yayi yafita yabasu guri. 

Jawwad ya tashi daga inda yake yazo gabanta ya zauna ya dan zuba mata ido sannan yace ” dama zaki iya fushi dani haka? Haba My i don’t expect this from you, Hanan bakiga na rame ba, ina cikin damuwa komai yayi min zafi narasa ya zanyi” nan ya kwashe komai ya gaya mata, gaba daya tausayinsa yakamata tace 

“Am sorry Haidar kishinka yasani nayi maka haka, dan Allah kayi hakuri, Amma yaya Jawwad bazan iya jure ganin ka Auri wata baniba, Jawwad zan iya hakura ka auri wata ka hadamu amma banda wannan yarinyar” 

“Meyasa?” 

“sister dinkace, nibazan fadi komai ba, Amma zancigaba dayi mana Addu’a” 

Jawwad yaayi ta rarrashinta harta saki jikinta suka fara hira

Koda Jalal yafito Abdallah ya janye shi dakinsa suka dinga hira, bayan sunyi Sallar Azahar, suka tafi part din daddyn su Abdallah. 

Daddy ya karbesu da fara’a ya kalli Jawwad yace “barka da zuwa sirikina ashe kuna tafe” 

Sunkuyar da kai Jawwad yayi saboda kunya kodan karamcin nan da sukayi masa zenemi alfarmar Abbansa ya barshi ya auri Hanan. 

Matsana suka zauna a kujerun dake palourn suka gaisa, ya tsaida idonsa akan Jalal ya lura da yadda bayason magana sosai, sedai in anyi abu ya danyi murmushi 

Daddy yadubi Jalal yace “My son, Kaine Jalal kenan?” Jalal yayi mamaki dan yasan daddyn Hanan besanshiba, amma ya akayi yakama sunansa haka? Jalal ya gyada kai yace “eh nine” 

Daddy yace “Ai ina ganinka naganeka, ammm nace bakaga tex message da’aka turamaka ba?” 

Jalal ya dan dirirce yace “Wane message?” 

Daddy yace “Eh akwai hukuma dasuka turomaka message na daukar aiki mana, zakaje screening” 

Shiruu Jalal yayi sannan yace “Ammafa daddy nima ina shaye2, tayaya NDLEA zasu daukeni aiki?” 

Tausayinsa ne yakama Jawwad yace “haba Jalal aiba a haka, ka amince mana, sun san kanayi suka daukeka ai” 

Daddy yace “ABDUL JALAL don’t mind kaji, ai munsan kana shaye2, karka damu you are my son dukda bansanka abaya ba amma yanzu nasamu ďa, dama yaran sunmin kadan, nayi magana da daddynka ma, An riga an baka aikin, ba wani abu ai zaka iya, Jajircewarka akeso sannan kaikuma kayi kokarin denawa, zaka temakawa hukuma, ni yadda naganka din nan with good body structure aida a soja nasaka kaima”

Gaba daya sukayi murmushi tunda daddy cikin sigar zolaya ya karasa maganar banda Jalal daya shiga tunani yayi shiru, 

Daddy yakuma cewa “Am sorry munmaka laifi nida diyata ko? Tasani nasa an soke maka visa, tuba muke bamuyi hakan dan bata maka ba” 

Murmushi Jalal yayi ya sunkuyar da kai suka cigaba da hira, bayan Azahar suka daura haramar komawa gida, sukayi sallama dasu sannan suka nufo kano, daddyn Hanan duk ya lurada yadda Hanan take nan nan da Jawwad ya yadda ba karamin so takewa Jawwad dinba. 

Bayan tafiyar su Mummyn Hanan tace “Daddy ka lurada yaron nan Jawwad kamarsa daya da Yusuf, wallahi hatta murmushinsa irin na Yusuf din Baba sagir ne” 

“Na gani nima, Amma kamnin twins girl dina yafi fitowa, tun lokacin dana ganta nakeji ajikina kaman akwai alaka tsakaninmu, Amma ni yanzu abunda yake raina inason tuntubar mahaifinsu, indai Jawwad yana sonta yafito kawai, tunda naga hankalinta yafi karkata gareshi”

Kaman Mummy tayi masa bayanin yakusa Aure, amma tafasa tace “To Allah ya tabattar da alkhairi amma gaskiya ni na yaba da hankalin sa, gashi nutsatse” 

Tunda suka taho hanya Jalal yayi shiru yakasa magana, Jawwad ya dubeshi yace

Jalila sosai take rashin lafiya, bata ko cin Abinci zuciyarta a cunkushe bata sha’awar komai, ga wani matsanancin ciwon kai dayake hanata bacci, ko makaranta bata iya zuwa, Nana tayi2 taje Asibiti tace mata ba wani matsala bane damuwa ce kawai take damunta, 

Ta yunkura ta mike zata shiga toilet, kawai taji jira gaba daya garin yayi mata baki kirin, aikuwa ta fadi a gurin tana fidda numfashi da kyar, Naja na kan gado tana kallon Jalila tace ” ahaka bakinciki da mugun abunki zasu hadu su kasheki, ki barmu a duniyar nida Jawwad muyi Aure, Allah yasa ki mutu shegiya” 

Jalila tanajin Naja amma bazata iya motsa ko dan yatsanta ba Nana data dawo dauke da kofin tea ganin Jalila a kwance yasa ta jefar cup din tazo kanta da sauri tana girgizata, Jalila tasa hannu ta dafe kanta tace “Nana kaina ze fashe” 

“Sannu Insha Allah ze dena ina zuwa” 

Taje ta dakko youghurt a fridge tazo tana bawa Jalila danta fuskanci hada yunwa ke damun Jalila, 

Naja ta kallesu tayi tsaki “Aikin banza wahalallu” 

Tunda su Jawwad suka nufo kano, Jawwad yakejin faduwar gaba dan besan meze tarar ba dan shi yanzu ko zuwa gidan baya so, shikam Jalal se sakawa yake yana warwarewa, shi meye amfanin yin wani aiki, Jawwad yaji shirun yayi yawa dan haka yace “ya dai naji kayi shiru haka? Ko har yanzu baka yadda da aikinbe?” 

Jalal ya danyi tsaki sannan yace “Jawwad nifa kaina yagama daurewa a ina Baban Hanan yasanni da harze bani aiki, kuma yana cewa sungama magana da daddy, yaushe akayi wannan zancen bansaniba? Tayaya zan fara hana wasu sha da fataucin miyagun kwayoyi bayan ni inayi? Ka gayamin tayaya?” 

“wannan ba abun damuwa bane bafa, kaiba ruwanka da wani tone2 na meyasa aka baka aiki, kuma ai ansan kana shaye2 akabaka ko?” 

Shiru Jalal yayi baya tunanin ze iya wannan aikin, tayaya za’ace me hana laifi yana aikatawa. 

Haka suka cigaba da shiru kowannensu yana sakawa yana kwancewa har suka iso kano. 

Jalila tunda ta danci Abinci tasha magana tasamu nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. 

Koda su Jalal suka dawo, kowa gidansu ya nufa, Jalal ya tafi gida, shima Jawwad ya tafi gidansu. 

Kwana uku da zuwan su Jawwad kano, tunda suka dawo Jawwad baya shiga gidan saboda gudun fitina sam baya wuni a gidan. 

Jalal yayiwa teddyn Jalila guri akan gadonsa, yana son yaganta yabata abunta sannan ya tambayeta ya akayi Alqur’ani daya bata yaje hannun Ilham? Har yayi wanka ze kwanta yaji kamar ana hura masa wuta a zuciyarsa da kansa gaba daya jikinsa ya dau zafi a sukwane ya nufi fridge dinsa ya ciki cikinsa da giya sannan yaji daidai. 

Da safe Jalal yasamu daddynsa a daki yana bacci dayake saukar dare yayi, ba tunanin komai Jalal ya tasheshi, koda daddy ya tashi Jalal yafara jeramasa tambayoyi 

“daddy da saninka aka samomin aiki a hukumar sha da hana fataucin miyagun kwayoyi?” daddy yace

“Dafarko dai ban saniba sedaga baya, General Abdurrashed ya kirani a waya, yacemin ‘yarsa tanemi ya sama maka aiki a wannan hukumar inbazan damuba in turamasa CV dinka, shikenan na amince” 

Jalal yayi saroro yana kallon Daddynsa “Wace’ yar tasa?” 

“kai zan tambaya ai” 

Shiru Jalal yayi, kawai ya mike ya sakko daga kan gadon daddy yafice daga dakin. 

Jawwad yana dakinsa, Nana tazo tace masa Abba yana kiransa, haka ya tashi gabansa na faduwa, yana fatan Allah yasa ba wani laifin yayi ba, yana zuwa, ya tarar da ‘yan gidan a palour banda Naja, Abba yayi shirin fita, Abba yace masa “Jeka ka canza kaya, Bauchi zamuje yanzun nan” 

Cikin mamaki Jawwad yace “Bauchi kuma Abba?” 

“Eh bauchi mana, kayi sauri a yau nakeson mudawo” 

Cikin Mamaki Maama tace “Abban Jawwad ni nakasa gane meke faruwa haka, tun jiya kake bacin rai, kaki saurarata yaukuma ba zato ba tsammani kace bauchi zaka tafi, mezakiyi a bauchi ne?” 

Kallon ta ya danyi yace “ba dole inki saurararki ba, ki shirya munyi magana da baban Jalal, ranar Lahadi shida ‘yan uwansa zasu kawo kudin Auren mahmud da Nana, sannan zanje bauchi inne mawa ďana Auren’ yar mutunci, sannan karki kuskura in dawo in tarar da yarinyar nan Naja a gidan nan, tabarmin gidana a yau” 

“Amma meyasa?” 

“in mun dawo kyaji meyasa” 

Jalila dake gefe tace “Abba Allah ya kaiku lafiya, ka gaishemin dasu, kuma akwai wani albishir dana boye banyimaka ba sekaje bauchi zaka gani” 

Abba yayi murmushi yace “to shikenan Baby, kema inason kafin lokacin bikin Nana ki fidda miji ku karasa karatun a dakinku” Jalila ta sunkuyar da kai tana murmushi,  Abba kuma yasa kai yabar palourn. 

Mummy tana zaune suna hira daddy a babban palour Jalal yashiga da sallama, suka amsa masa gaba daya, yaje kan Mummy ya tsaya fuskarnan babu alamar walwala ya jefa mata wata jarida a hannunsa yace “ga shi nan yanada kyau ki duba Labari na uku a cikin wannan jaridar, yanada mahimmanci agareki” 

Ina yinku ABDUL JALAL group da sauran masoya wannan Novel irin sosai din nan fa 😍😍😍 inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing, gashi nan na muku dogon page, in banga ruwan comments inna shura takalma na posting se rana ita yau 😂😂😂

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool.

Back to top button