Karfe A Wuta Chapter 58 By Ayshercool
Cikin matsanancin tashin hankali, Nabila tana kuka ta ce “Viper zuciyarka fa, dan Allah ka nutsu zata daina aiki, idan ta cigaba da bugawa a haka, ka cigaba da istigfari da maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji’un” tayi maganar cikin damuwa, ƙara danna hannunta yayi a kan ƙirjinsa, yana wata irin shaƙuwa mai haɗe da haki, numfashin sa na fita sama-sama.A jejjere zuciyarsa take bugawa da ƙarfin gaske.Cikin tausayawa take kallon sa, Al’amin yana buƙatar kafaɗar da zai kwanta yayi kuka, babu wanda ya fuskanci ainihin matsalar sa, kowa ɗora masa laifi kawai yake yi, iftila’in da ya faɗa masa, kowa ya dare ya bar shi, sai abokansa duk da suna iya ƙoƙarin su a kansa, amma ba abun da yake buƙata suke yi masa ba.Ji tayi ina ma tana da damar, da zata rungume shi, ta bashi dama yayi kuka yadda yake so, ko zai samu afuwa a zuciyarsa, tsawon shekaru shida, yana dakon baƙin ciki da damuwa, kuma ya kasa zubar da hawaye sai a wannan lokacin.Haka yayi shiru ya sunkuyar da kai, sai dai bai saki hannunta ba, hawaye ne kawai yake zuba daga idonsa, taya shi take yi, sai dai ta rasa me ma zata kuma ce masa, a tsorace take da kar zuciyarsa ta buga.A hankali ya saki hannunta, ya goge hawayen sa, ya tashi zumbur, ya tattare kayan ya mayar ɗakin, hatta kayan jauhar suna nan, lokaci lokaci, su Walid ne ke zuwa su karkaɗe gidan su share, dan idan ya bushi iska yana zuwa cikin dare, yayi ta tuna irin rayuwar da suka yi.Yanzun ma yana shiga ɗakin, ƙwaƙwalwarsa ta nuna masa ita zaune a kan gado, tana shirin dutse, gefe ga boti a kusa da ita a kwance, ya mimmiƙe yana ta goge jikinsa.Ta ɗago ta kalleshi tana murmushi ta ce “Manya gatan wasa, me ake so ne ake ta kallona? Ko fankar ce?” Tayi maganar tana kashe masa ido.Gadon ya nufa da hanzari ya kai hannu ya riƙe ta, amma ya ga pillow ne kawai a wurin.Ya dafe hannunsa a wurin, daga baya ya fito jiki a sanyaye ya ce “Mu tafi” Nabila ta saki niƙabinta tana ta kuka, suka nufi hanyar fita, ya gyara facemask ɗin sa suka fita.Yana fita yaga wasu daga magidantan layin, a ɗan tsaitsaye, suka yi ido huɗu da malam lawan, ya zura da gudu ya shige gidansa, ya rufe ƙofa.Ya danƙi hannun Nabila ya din ga sauri da ita, maimakon su bi titi, lunguna suka din ga bi, suna tafe yana haki, yana dafe ƙirjinsa.A dai-dai wata kan kwana, ya saki hannunta, ya danƙo wani mutum da yake zaune yana jin radiyo, yana cin karas, zuwa wani lungu.Nabila ta ce “Me yayi maka shi kuma?”Ya zaro iraƙi a ƙugunsa, ya saita masa a maƙoshinsa, ya ce “Bani wayarka”Jiki na rawa, ya ciro wayar, ya miƙa wa Viper.”Ka janye mini mutanenka, zan yi walƙiyya, idan ba haka ba, zan yi maka rami a maƙoshinka”Mutumin ya diririce, ya ce “Ban gane me ka ke nufi ba”Ya ɗaga mutumin ya haɗa shi da bango da ƙarfi, ya ce “Ka janye mini mutanenku zan tafi, idan na kuma magana, hanjinka zan naɗo da wuƙar nan”Mutumin ya ce “Ya aka yi ka gane ni, ka san identity ɗina?””Saboda tsohon mai laifi ne ni, ba yau na fara aikata laifi ba” yana ƙoƙarin zira hannu a aljihu Viper ya riga shi, ya ciro bindigar da take aljihun mutumin ya ce “Ka yi abun da na ce, ko na harbe ka”A razane Nabila ta ce “Viper bindiga ce fa, dan Allah kar ka yi wani laifin mu shiga uku” bai kulata ba, ya sake saita mutumin da bindiga.Ya saka wayar a kunnensa ya ce “Zaku iya tafiya, we missed the target” ya katse wayar ya ce “Sai ka bani bindigata na tafi”Viper ya ce “Ɗaga hannunka, ka wuce mu je” ya tasa mutumin a gaba, tamkar ya kamo mai laifi, yana gana suna bin sa a baya, da ya motsa sai ya ji Viper ya ce “Idan ka waiwayo zan fasa kanka da bindigar nan” haka suka yi doguwar tafiya a haka, sai kuma ya ji shiru.Ya waiwaya, ya neme su ya rasa, a rikice ya bi hanya, saboda bindigar sa da take hannun Viper.Yana shan wata kwana, ya ga abokin aikins a tsaye da bindigar a hannunsa.”Gata, tun da ya ritsaka nake biye da ku, a hanya ya yar da ita, suka yi wani wurin, nayi ƙoƙarin bin su, amma ban cim musu ba”.”Ohh shit, meyasa ba ka yi making wani move ba, wannan ai shirme ne kayi””No, kar ka gargaɗe mu a kan haka, ka ce sai abun da ka ce, kai ka ke son ka kama shi da kanka”Ya fesar da iska ya ce “Kuma haka ne, amma gayen nan ya bani mamaki, na rasa ya aka yi ya gane ni a cikin fararen kaya.Kaga fuskarsa?””A’a sir, fuskarsa a rufe take ai, ban ganshi ba, ni bayansa ma kawai na gani”.”Na so naga kammaninsa, ko wataran zamu sake haɗuwa, suma informer’s ɗin banzaye, da ba su sanar da wuri ba. Yi shiru ga oga Nasir yana kiran waya”Ya saka wayar a kunnensa ya ce “Hello sir””Ya ake ciki ne?””We miss the target sir”Nasir ya ce “Kamar yaya?””Kafin mu je, ya bar unguwar, bamu tarar da shi ba”Nasir ya numfasa ya ce “Shikenan, ku dawo mu haɗu a office, sai mu sake shiri””Ok sir” ya kalli abokin aikinsa ya ce “Mu je,ya ce mu koma office”Viper kuwa wata hanyar ya bi, suka ɓulla can wata unguwar daban.Sai dai suna tafe yana ta haki, yana haɗa hanya.”Viper mu tsaya ka huta, kalli halin da kake ciki, ko mu samu wani asibiti a duba ka, kar numfashinka ya ɗauke” bai ko nuna ya san da shi take ba, sai da suka fita titi ya saki hannunta ya ce “Ki koma gida”Cikin damuwa ta ce “To kai kuma fa?””Ki tafi nace” yayi maganar da kyar, kawai ya tare wani mai napep ya shige ya tafi.Jiki a matuƙar sanyaye, ta koma chamber ta ɗauki motarta, ita kanta ta san ikon Allah ne ya kaita gida, amma kusan gaba ɗaya ba ta hayyacinta, tarin damuwa ce kawai cunkushe a ranta.Ba ta san yar madara ba, ba ta taɓa ganinta ba, amma ƙarshen labarin ya tsaye mata a rai, da wayonta ba a taɓa yi mata mutuwar da ta gigita ta ta ji ta ba, sai dai jin wannan mutuwar ta gigita ta, ta ɗaga mata hankali. A cikin zuciyarta take jin ƙaunar matar da ba taɓa gani.A wannan karon ma tayi kuka mai isarta, ga uwa uba, tausayin mai gayya mai aikn wato Al’amin, dan ita yar madara ta mutu ta huta, amma shi da blame ɗin ya dawo kansa, shi ne babban abun a tausayawa. Wayoyinta suka isheta da ringing, ta kashe su gaba ɗaya ta ajiye.Ta din ga fatan Allah ya mayar da Viper maɓoyarsa lafiya, dan ta tsorata da mummunan yanayin da ya shiga.Sannan haryanzu labarinsa da saura, ba duka bane ba, amma tana fargabar sake matsa masa son jin ƙarashen labarin, dan gudun kar ya sake shiga mawuyacin hali kamar yau.Tana ta saƙe-saƙe, sumayya ta yi sallama, ƙasa-ƙasa ta amsa, sumayya ta shiga ɗakin tana mita. “Malama kin ce mini zaki zo, amma kin shanya ni, bayanai ne suke ta fitowa a kan mutuniyar ki, ina son ki gana da mutanen direct, na haɗa ku, amma ki ka ƙi zuwa”Ji tayi Nabila tayi mata shiru, ta ce “Arfa meyafaru ne? Kamar kuka ki ka yi fa””Kuka nayi sumayya”Cikin rashin fahimta ta ce “Kukan me kuma? Ko duk a kan shari’ar ne?””Sumayya komai ma, yakamata nayi kukan ne kawai””Arfa yakamata fa ace kin san kin girma, haba abu kaɗan sai kuka, ki din ga miƙa wa Allah lamuranki mana haba Arfa”.”Arfa, Arfa” suka jiyo muryar Nasir yana ƙwala mata kira.Tayi shiru bata amsa ba, ya shigo ɗakin, ya tarar da ita a zaune, ta jingina da gado.”Ina magana ki ka yi mini shiru?”Ta ce “Kaina ne yake yi mini ciwo”Sumayya ta ce “Yaya ina wuni?”Ya amsa da “Lafiya ƙalau sumayya, ya aiki?””Alhamdilillah”Ya sake mayar da idonsa kan Nabila ya ce “Waye mutumin da ya zo wurinki ɗazu a Office ɗin ki?”Ta ɓata fuska ta ce “Na gaya maka client ɗina ne ai””A’a arfa, na tambayeki wani irin case ne zaki tsaya masa, kin ce is confidential ban san lokacin da muka fara ɓoyewa juna abun da ya shafe mu ya shafi aiki ba. Mutumin nan yayi kama da masu aikata miyagun laifuka, duk da ban ga fuskarsa ba”Ta girgiza kai ta ce “Allah ya kiyashe ni hulɗa da masu aikata laifuka, sai dai ko da mai laifin ne, a matsayina na lawyer babu ruwana da laifin sa, zan bashi kariya ne kawai. A wurinku ne ku ke kama mai laifi, a wurin lawyer babu ruwansa da mai laifi ko akasin haka, client ɗinmu ne a gabanmu ba laifinsa ba”.Ya tsaya yayi shiru yana kallonta “Ban gane me ki ke nufi ba”Tayi murmushi ta ce “Ba wani abu da nake nufi yaya, aikinku kamo mai laifi, mu kuma namu aikin binciko gaskiya komai ɗacinta”Ya jinjina kai ya ce “I see, ɗazu informer’s ɗin mu sun sanar da mu Viper ya je gidansa, da shi da wata da ba a san ko wacece ba, sai dai kan jami’anmu su je, ya bar unguwar” duk da ƙirjinta yayi dumm. Amma cikin iya siyasa ta ce “Ikon Allah, lallai wannan Viper akwai shu’umi, ya cika macijin gaske, wato lokacin da ya ga dama, sai ya baro raminsa ya fito shan iska, to Allah ya shirye shi. Amma ya batun abokinsa da kake bibiya?”Nasir ya ce “Nothing much, ya daina zuwa unguwar ma kwata-kwata, abun har mamaki yake bani, da mun hari wani abu da muke son mu kama shi, sai abun ya kuɓuce mana, amma muna nan muna ƙoƙari”Nabila ta ce “Gaskiya abun da mamaki, Allah ya yi jagora”Ya amsa da “Amin, Sumayya ki din ga yi wa yar uwar nan taki faɗa, bata ji ko kaɗan tana neman zunguro mana sama da kara, kasadarta tayi yawa sosai”Sumayya ta ce “Ana yi mata fa yaya, ka san halinta da kafiyar tsiya ne, amma zata daina in sha Allah”Ya jinjina kai ya ce “Allah ya sa” bayan ya fita Sumayya ta ce “Arfa, waye yaya yake magana a kai, ina fatan dai ba wani mai laifin bane ba, ko kuma wani abun ki ke shirin ɗaukkowa ba”Nabila ta kalleta ido cikin ido ta ce “Kina son na ce miki viper ne, ki je ki ji daɗin gaya wa waɗanda ki ke ba wa information a kaina?”Gaban sumayya ya faɗi ta ce “Information a kan ki kuma?””Eh mana sumayya, ana bibiyata ta hanyarki, kina bibiyar duk activities ɗina kina sanar musu. To ki gaya wa ko suwaye suka saki, wallahi babu yadda suka iya da ni, gaba da gaba za su yi da ni, su karɓi abun da suke so daga wurina, ba wai su fake da ke ba kina ba su information a kaina ba””Nabila waye ya gaya miki haka?”Nabila ta ce “Jira ki ke yi a gaya mini? Ni na ganoki, sai dai na kasa yadda saboda ƙauna ba ƙarya ce ba, kuma wanda ya gaya mini ba zai yi mini ƙarya ba, dan bai sanki ba, balle ya san alaƙarmu da ke. Please sumayya You can leave, ko ganinki ba na son yi wallahi” Sumayya ta ce “Nabila, ki tsaya mu fuskanci juna dan girman Allah””Babu wata fahimtar juna da ta rage tsakanina da mai fuska biyu, ni da gaske na yarda da ke, ba zan bari a cutar da ke ba, mussaman ayi amfani da ni a cutar da ke ba, amma ke gashi ana ƙoƙarin cutar da ni ta hanyar ki. Koma waye yake bibiyar tawa, ki ce masa ya fuskance ni ya gaya mini abun da nayi masa. Idan kuma a kan ayyukan da na saka a gaba ne, babu wani mahaluki da ya isa ya hana ni abun da nayi niyya, ki tashi ki tafi”Sumayya ta miƙe tsaye, kawai ta ɗauki jakarta ta fita, tana tafe a hanya tana kuka, sam ba ta san da wasu kalamai za ta yi amfani ba, wurin fahimtar da Nabila ba, sai dai tayi mamakin gaske, a kan wanda ya gaya wa Nabila cewa ana bibiyar ta, da Nasir ne ya gaya mata, to da tabbas sai yayi zancen yanzu a gabanta, kuma sai ya tuhume ta, amma sai dai bai yi hakan ba.Bayan tafiyar sumayya kuwa, Nabila ƙanƙame pillownta tayi, tamkar ta samu viper, ta cigaba da zubar da hawaye.Viper kuwa a galabaice ya ƙarasa gidan da suke, gaba ɗaya nema yake ya fita hayyacinsa, haki kawai yake yi, zuciyarsa na cigaba da wannan matsanancin bugun.Ɗan mama ne kawai a gidan, ya tashi ya riƙo Viper cikin tashin hankali, ya shiga da shi ɗaki, ya kwanta a kan katifarsa, ya cigaba da ajiyar zuciya, yana haki, ga wani abu da yaƙi gaba yaƙi baya a tsakiyar ƙirjinsa.”Oga Viper, meyafaru ne? Baka da lafiya ne? Meyake damunka?” Ya jejjerawa Viper tambayoyin, amma babu guda ɗaya da ya iya amsa masa, ya lumshe idanunsa ya na ta sauke numfashi.Cikin sauri, ɗan mama ya kira Walid a waya, ya sanar masa halin da Viper yake ciki.Walid ya ce “Ka kula da shi, kar ka bari ya sake fita, gani nan zuwa”***Madaki ne zaune a cikin dokar daji, a gaban wani mutum da shi da yaronsa lakwari.Ya miƙe ƙafarsa da ciwon jikinta yayi rami, mai zurfi, sai wani irin kore ruwa ne yake fitowa, wurin ciwon ya kumbura suntum babu kyawun gani ko kaɗan.Mutumin ya ƙare wa ƙafar kallo sannan ya ce “Ya riga ya yi maka illa, tabbas yana da makarin asirinka, dan kuwa ya karya shi ɓara, wuƙa da kaifi, za su din ga tasiri a jikinka. Cikin tashin hankali da damuwa madaki ya ce “Yanzu babu wani abu da za ayi a kai, idan ya so a kuma bani wani asirin?”.”Gaskiya babu, yanzu dai magani zan baka, aje a haɗa shi da diddigar maƙera, ka yi kwana arba’in ana sakawa ciwon, sai ya warke sai kuma mu ga da abun da zamu ɗora”.Madaki ya yi shiru, saboda baƙin ciki, lokacin da aka bashi asirin, an tabattar masa da babu wani wanda yake da laƙanin karyewar asirin, sai shi wanda ya bashin, wanda yanzu ya mutu sai ɗan sa yanzu dan kuwa shi kansa ɗan ma bai san makarin asirin ba, dan haka sun yi mamakin yadda aka yi Viper ya samu.Sun kamo hanyar dawowa kano, madaki ko iya magana baya yi, babu tunanin da yake yi, da ya wuce wani mataki zai ɗauka a kan Viper, dan kuwa karya asirin nan, dai-dai yake da karya alkadarinsa baki ɗaya.Kiran P.A ne ya din ga shigowa wayar Madaki, sai da yayi da gaske sannan ya ɗaga, domin kuwa gaba ɗaya ransa a jagule yake saboda tashin hankali, da fargabar halin da zai shiga, idan aka fuskanci Alkadarinsa ya karye.”Madaki, ina ka shiga ne, yau kwanaki kusan huɗu wayarka ba ta shiga, distinguish ya bayar da muhimmin aiki da kai kaɗai ne zaka iya yin sa”Madaki ya yi ajiyar zuciya ya ce “Aikin menene?””Idan kana gari ka shigo”Madaki ya ce “A’a, na ɗan yi wani balaguro ne””Duk in da ka ke ka dawo, honorable ya matsa a kan lallai a kama viper, yarinyar nan yake so a ɗaukko masa”Madaki ya ce “Wace yarinyar kenan?””Wata lawyer ce, wadda na fara yi maka zancen nan”Madaki yayi wani huci, ya ce “Bari na shigo garin, zan yi maka magana”P.A ya ce “Wai madaki lafiya kuwa? Kamar ba ka da karsashi, meyake faruwa ne?””Basar ka ɗauke tunaninka a kan hakan, zan faso idan na shigo gari” ya katse kiran yayi shiru yana tunani, tabbas ta bakin Al’amin daga lokacin da suka ga ya daina yi musu amfani zasu watsar da shi.***Nabila ta kira layin Viper ya kai sau biyar, dan ta ji halin da yake ciki, amma ba a ɗagawa, har ta fitar da ran zai ɗaga ta ji an ɗaga wayar.”Haba master, ka barni cikin zullumi da tunanin halin da kake ciki, ka ƙi ɗaga wayata”.”Walid ne” “Oga walid, yana ina dan Allah?””Gashi muna ta fama, jiki ya rikice gaba ɗaya”.Cikin tashin hankali ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wani abun ne ya same shi ne?””Ke zamu yi wa wannan tambayar, dan babu yadda bamu yi da shi ba, ya ce sai ya fita, wurinki zai zo, zai yi wani aiki, mun yi iya ƙoƙarin mu mu hana shi, amma ya ƙi saurarenmu, ko kin yi masa wani abu ne ki gaya mana dan Allah””Wallahi Allah kenan, ban yi masa komai ba, office ɗina ya zo ɗazu….Walid ya katseta ya ce “Office kuma? Ya ce kiranki zai yi a waya ku haɗu””A’a zuwa yayi, yayi amfani da wayata da computer ta ta, daga nan ya ce zai ƙarasa mini labarin da ka fara bani, har gidansa muka je” ta yi wa walid bayanin yadda aka yi.Walid ya ce “To ki tayamu addu’a, jiki ya rikice, ɗan sakewar da yayi kwana biyu, ta gushe ya koma yadda yake a da. Salla kawai yake yi a kwance tun da ya dawo, sai dafe ƙirjinsa yake yi yana haki”.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Oga walid da ka ƙarasa mini labarin nan, duk da haka bata faru ba, da na san halin da zai shiga kenan, da ba zan takura masa ya gaya mini ba. Ubangiji Allah ya kawo masa mafita, Allah ya bashi lafiya, ba zai yiwu na fito yanzu ba, dan Allah ku kula da shi sosai. Zan zo in ga jikin nasa in sha Allah””Shikenan, Allah ya kawo ki” ya kaste wayar, yana kallon in da Viper yake kwance, hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa, yana ta sauke numfashi.***Duk wasu kalamai da Abdul yake tunanin idan yayi amfani da su, zai shawo kan ramma, yayi amma fafur taƙi saurarsa, ya kaɗa ya raya, amma taƙi saurarsa. Da ya addaba mata cikin tsawa ta ce “Wai me kake so ne Abdul, ai ban yi zaton mugun zaluncinka ya kai haka ba, ka yi mini fyaɗe an ɗora wa mutanen da suka taimaka mini sharri, wannan wace irin rayuwa ce?”Ya sake kwantar murya ya ce “Ki fahimce ni dan Allah, zan yi duk iya ƙoƙarina a kan mutumin nan ya fita a sake shi, dan Allah ki daina ɗaga hankalinki””Dama dole ka ce haka mana, tun da kana ganin ko ta halin ƙaƙa, kuɗi zasu ƙwatar maka komai, baka tunanin mawuyacin halin da zaka jefa zukata, baka yi dacen hali ba ko kaɗan” taƙi sauraronsa, sai uban miyagun maganganu da ta din ga yaɓa masa.***Bacci ya gagari idanun Nabila, ta ga tamkar an ƙara wa daren tsawo, gashi ta kasa bacci, ƙarshe ta tashi tayi alwala ta tayar da nafila.A gaggauce ta hana baba magajiya aikinta, ana idar da sallar asuba, ta shiga kitchen ta dafa abun da take buƙata, da duku-duku, ta ɗauki motarta ta fita.Jin ƙarar mota ya sanya Nasir ɗaga labulensa ya duba, ya ga babu motarta, ya kalli agogo, hari sam bai gama waye ba, ya fara tambayar kansa ina tafi da wannan duku-dukun?.Gudu ta din ga yi a titi, gani take yi tamkar kafin taje, wani abun ya same shi.Gari yayi haske sosai tana hanya, ta ajiye motarta a wani wuri, ta fito ta tsaya ko zata samu abun hawa, amma bata samu ba, dan haka ta cigaba da tafiya da ƙafa, gabanta na ta tsananta faɗuwa sai addu’a take yi.Ta sha tafiya sosai, sannan ta samu abun hawa ta hau, ya ƙarasa da ita.Kasancewar da tafiya daga titi zuwa gidan da yake, haka ta din ga haɗawa har da gudu, har ta ƙarasa tana ta haki, ta shiga da sallama, ta ƙarasa ƙofar ɗakin, ɗan mama ta hango zaune a gaban Viper, yana ta rarraba ido, daga shi sai shi a gidan.Ƙwayoyi ne a hannun Al’amin, gefe ga allura a cikin sirinji, amma sai haki yake yi mai ban tsoro.Da sauri ta ƙarasa ɗakin, tana cewa “Wannan ƙwayoyin na menene?”Kafin ta ƙarasa ya watsa su a bakinsa, babu ruwa yake ƙoƙarin haɗiyewa, ba ta san lokacin da cikin tsawa ta ce “Viper meye haka? Ƙwayoyin meye wannan kashe kanka ka ke son ka yi?”Bai kulata ba, ya cigaba da ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai ya kasa saboda abun da yake ji ya tokare masa a wuyansa zuwa ƙirjinsa.Matse bakinsa tayi iya ƙarfinta, tana girgiza masa kai “Kar ka haɗiye, wallahi hakan ba mafita ba ce ba, dan girman Allah ka zubo su daga bakinka” hankaɗeta yayi yana ta huci.Ɗan mama ya ce “Ki daina zuwa in da yake, zai yi miki illa, wallahi aiken su Walid yayi, ni kuma yayi mini barazana da wuƙa, na samo masa kuma wanda ya watsa a bakinsa sun yi yawa, sun yi masa ƙarfi””To waye ce ka kawo masa, ba sai ka gaya wa Oga walid ba, ai ka san ba zai taɓa iya kisan kai ba”Ta sake tunkarar Viper, sai haki yake yi mai haɗe da huci, tamkar kumurcin, yana motsa bakinsa a hankali, yana son haɗiye ƙwayoyin.Bakinsa ta sake matsewa, idanunsa sai buɗewa suke yi suna lumshewa, wanda suka fara narkewa a bakinsa, sun fara rikita masa lissafi.”Kalleni nan, ka fito da su na ce” tayi maganar tana zare masa ido.Ya ɗago a hankali ya kalleta, ta ce “Ka zubo da su, kar ka haɗiye. So kake ka kashe kanka, idan ka kashe kanka, ɗan wuta zaka mutu, kuma ko ka je lahira ka mutu ɗan wuta, yar madara kuwa muna saka mata ran tana aljanna, kaga ba zaka ganta ba”A galabice, ya buɗe bakinsa, yana zubo da ƙwayoyin da suka rage a bakinsa, yana ta haki.Shammatarta yayi, ya ɗauki sirinjin da yake gefensa, ya caka mata a hannunta, wata irin ƙara tayi, cikin razani, dan ba ta yi tsammanin hakan ba.Ɗan mama ya rikice, ya nufo su da sauri, Viper ya kalli in da ya caka mata sirinjin, ya kalli fuskarta yadda ta fara kuka, sai kuma ya ankare da abun da yayi.Sai ya rikice, ya zare sirinjin ya jefar ya riƙeta ya ce “Zahra, me nayi miki? Yi haƙuri, na daina shan komai, ai nayi miki alƙawari” yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta, ya share mata hawaye.Walid ne suka shigo tare da liti, suka nufo su, liti ce wa yake “Me ki ka yi masa?”Viper ya yinƙura ya tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi.Suka rufu a kansa, suka ɗaga shi da kyar, Nabila ta gaya wa Walid a halin da ta zo ta same shi.Walid ya kalli ɗan mama, cikin tsananin ɓacin rai, ɗan mama ya ce “Nifa bani na kawo masa ba, wallahi ɗaukko masa kawai ya saka nayi, ban san a ina ya samo abun sa ba”Suka mayar da hankali a kan Viper, sai dai ba maye kawai yake yi ba, suma yayi, ga numfashinsa iya ƙirjinsa yake.Nabila ta ce “Dole fa a kai shi asibiti, ko da hakan yana nufin a kama mu ne baki ɗaya, lafiyar sa ita ce mafi muhimmanci a wannan lokacin”Walid ya ce “Haka ne, amma wani asibiti zamu kai shi?”Liti ya ce “Akwai wani asibiti a can bayan gari sosai, sai dai na kuɗi ne, ina ga kamar can zai fi zama safe”Nabila ta basu mukullin motarta, ta gaya musu a in da take.Liti ya karɓa ya tashi ya fita.Nabila kallonsa take cike da tausayawa, namijin gaske ne, sai dai ta wata fuskar yana da raunin zuciya sosai.Da liti ya kawo motar, suka yi kama kama, suka ɗauke shi, suka shafo tafiyar nan da shi, suka fito titi.Liti ne yake jan su a motar, ɗan mama da Viper da walid suna baya.Asibiti ne mai kyau, sai dai ya yi nisa da gari sosai da sosai.Ganin halin da yake ciki yasa suka karɓe shi da gaggawa, Nabila ta tambayi ya tsarin Asibitin yake, da payment ɗin, aka ce su bari, a fara ceto ransa tukuna.Da aka tambayi sunan Al’amin, sai Walid ya ce “A saka masa Muhammad Nura”Liti ya ce “Meyasa baka bayar da normal sunansa ba”Ya bashi amsa da “Saboda tsaro”A kan oxygen aka fara ɗora shi, saboda numfashinsa, sannan aka fara sauran ƙoƙari a kansa.Walid kallonta kawai yake yi, yadda take a rikice cike da tashin hankali, babu ma alamar tana fargabar a kamata ko wani ya ganshi, ta uzzurawa likita da tambayoyi.Likitan yayi mata bayanin yadda Jinin Al’amin ya hau, ga bugun da zuciyar sa take yi, fiye da kima kamar yadda ECG ɗin sa ya nuna, he’s at very risk of having heart attack.”Subhanallah, dan Allah doctor kayi ƙoƙarin ka, na san Allah ne mai komai, amma dan Allah ka taimaka””In sha Allah zamu yi iya a ƙoƙarin mu a kai”Tayi masa godiya, ta tafi reception ita da litu, suka gaisa da cashier ta tambayi, me za su yi depositing, na patient ɗin su da aka yi admitting?.Ya tambayi sunan mara lafiyan, liti ya gaya masa, ya duba cikin system ɗin gabansa ya kalle su ya ce “Ai an biya”Suka kalli juna da ita da liti, liti ya ce “Malam ka duba sosai, ɗazu muka shigo fa, aka ce mu bari a fara bashi taimakon gaggawa, ka duba ko masu irin sunan biyu ne”.”Shikaɗai ne me irin sunan da aka yi admitting yau, Al’amin Ibrahim”Suka kalli juna da Nabila, liti ya ce “Mu sunan mara lafiyanmu Muhammad Nura””Wanda ya biya kuɗin, sunan da ya bamu kenan, ba shi ne na ɗaki mai lamba 2 ba? Al’amin Ibrahim ya ce mana, ya turo kuɗi ya ce ayi masa duk abun da yakamata”.
Ayshercool 08081012143


