Page 71
Mummy ji tayi, tamkar an sanya mata dabaibayin ƙarfe an ɗaure mata ƙafafuwanta, ta kasa motsi, jikinta kuma yayi wani irin mugun sanyi, ta kasa motsa ko ina. Har rumaisa ta gama yi mata maganar, ba ta iya cewa uffan ba, mussaman ganin wannan layoyin a hannun rumaisa, kuma rumaisan ta ɓare fatar tsaf.
A tsakiyar garden ɗin gidan, ta bawa baba uwani ta binne mata, shi ne cigaban aikin da ake yi mata a kan Adam, akwai irin layoyin a gidansu, akwai a gidan da ya zauna da aisha, wannan karon ma an yi ta saka a gidansa, saboda ana son ya din ga shige da fice a kai a kai, a in da layoyin suke.
Kuma wannan laya ta bawa baba uwani jinin mage, da za ta din ga zubawa a ƙasar wurin sa’ai da lokaci.
Da safe rumaisa na ta sauri, ta kammala abun da za ta yi kar ta makara, dan haka ana idar da sallar asuba ta hau ayyukanta, sai dai kanta ya din ga sara mata, ta din ga kamar wani sauti, daga bayan ɗakinta, kawai ta sauka ta zagaya, wanda a nan ta iske baba uwani, ta gama binnewa, ta jira ta bar wurin, ita kuma ta tone ba ta sani ba.
“Ina sake roƙonki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daɗi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taɓa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake” ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita.
Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta.
Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba ɗaya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daɓas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta.
“Lallai wannan uwani an yi ƴar…….., ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?”
Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani.
Baba uwani ta fara koɗata, ta ce “Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?”.
“Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba”
“Ƙarya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ƙullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri”.
Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce “Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ƙoƙarina dan Allah kiyi haƙuri”.
Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba ɗaya ta gigice.
Ruƙayya ta shigo ɗakin, tana duban Mummy ta ce “Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?”
“Bakomai, jeki hutawa zan yi” Ruƙayya ta ɗage kafaɗa ta fice.
Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi.
Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa.
“Ammi sannu da gida”
Ammi ta ce “Yauwwa ƴar auta ta, ina ya baro mini ke ya shigo shikaɗai? Ai ban san tare ku ka zo ba”
Ta zauna ta ja yatsan takawa da ƙarfi ta ce “Tafiya yayi ya barni”.
“Ke baki san da zafi bane” ruma ta harare shi ta ce “To waye ya ce ka tafi ka bar ni?” Ta mayar da idonta kan Ammi ta ce “Ammi ina Anty Iman ne?”.
Ammi ta ce “Kin san ta sarkin ɗaki, tana can ko tana bacci ko tana karatu”.
Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Iman, Sabir ya biyota, ta tsaya ta ɗauke shi suka tafi tare.
Ammi ta ce “Yaya ake ciki, ai yanzu rigimar ta ta da sauƙi ko? Kuna sabawa a hankali na ga ta rage daru sosai”.
Yayi murmushi ya ce “Ba zata sauya hali ba, kawai na koyi zama da ita ne kawai. She’s simple at times wasu lokutan kuma ba a gane kanta”
Ammi ta yi dariya ta ce “Tun da ka iya zama da ita ai Alhamdilillah, Allah ya ƙara haɗa kanku”
Ya ce “Amin, sai dai Ammi akwai wani abu”.
“To, Allah ya sa ba matsala ba ce”
“Ba matsala ba ce ba, ta ce zata gaya wa mummy abun da zai saka a fasa kirana wurin mai martaba, ban san me ta ce mata ba”
Ammi ta ce “Wai yanzu daga can take?”
Ya ce “Eh”.
“Takawa meyasa ka barta? Idan kuma ta je sake hargitsa lamuran fa?”.
“Ammi, am testing her thinking capacity, tama Sharp brain fiye da tunani, kuma na fara yadda da abun da ta gaya mini a kan Jamil, idan har tayi nasarar sanya Mummy, ta janye ƙarata data kai wurin su mai girma wambai, duk abubuwan da rumaisa take faɗa gaskiya ne”.
Ammi ta numfasa ta ce “Takawa, kaifin basirar yarinyar da tarbiyyarta, su ne suka saka na zaɓa maka ita, ni na san tana da kaifin tunani tun kan ku yi aure, tana da basira. Dan haka a ƙara haƙuri, ka bi komai a hankali, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa kafin ka yi tafiyar nan, abun da hali zai yi”
“To shikenan Ammi, in sha Allah”.
Ammi ta ce “Amma zan so sanin me za ta gaya wa Jamila, da har zai sanya ta janye abun da ta je ta faɗa”.
Takawa ya ce “Nima na so sani taƙi faɗa, kuma mun yi da ita ba zan gayawa kowa ba. Idan na cigaba da matsa mata ba zata faɗa ba”.
“To Ubangiji Allah ya iya mana, ya sanya ita ce sanadiyyar warwarewar matsalolin nan”
“Amin Ammi”.
Ruma kuwa a kwance a ƙasa ta tarar da iman, a ɗan razane ta ƙarasa ta taɓa jikinta, ta ji yayi ɗumi.
“Anty iman, lafiya ko baki da lafiya ne? Ciwon kan ne ya dawo?x ta jero mata tambayoyin.
Iman ta tashi zaune, tare da yin yaƙe ta ce “Maman sabir, saukar yaushe?”
“Ba wani saukar yaushe, baki da lafiya ne?”.
“A’a lafiyata ƙalau, kawai dai kwanciya nayi”.
Rumaisa ta zaune sosai ta ce “Ke da papa wasu lokutan halinku ɗaya ma, idan ba rashin lafiya ba, akwai damuwa fuskarki ta nuna, dan Allah anty iman menene, bana son in ga damuwa a fuskarki, gaba ɗaya raina ɓaci yake yi. Ko wani ne yayi miki wani abun? zan iya rama miki”.
Cikin dauriya, Iman ta ce “Maman sabir, bana son ɓacin ranki nima, kasancewarki a tare da ni, yana bani ƙwarin gwiwa.
Zan gaya miki menene, amma dan Allah kar ki bari ammi ta sani, kin san bana son damuwarta”.
“Anty iman, duk surutun nan nawa, ina ɓoye sirri, gaya mini ko bani da maganin zan tayaki da addu’a”.
“Ammi ce ta ce mini, wai uncle J yayi mata maganar yana so na, wai zai je ya sanar da mai girma turaki, a zo a nema masa aurena, naga ammi tana murna, amma…..” Sai kuma tayi shiru.
Rumaisa ta ce “Amma ke ba kya son sa ko?”
Iman ta zubawa rumaisa ido.
“To wa ki ke so, dan ni ma bana son wannan jabir ɗin, babarsa ba ta da mutunci, wahalar da ke zata din ga yi”
“Ba na son kowa maman sabir, bana son sake yin Soyayya, na barwa Allah lamarina, amma wallahi bana son jabir”.
“Kin tabattar babu wanda ki ke so, tuna dai” ruma ta yi maganar tana basarwa.
Sai da gaban iman ya faɗi, tayi fatan, Allah ya sa ba ganota rumaisa ta yi ba.
“Na tabattar bana son kowa ni yanzu”
“Amma ya san ba kya son sa ya nace, kar ki damu ki yi ta addu’a, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, ba bari za ta yi ba. Ko kina son wani a yayyena, amma su talakawa ne?”
Iman kallon rumaisa take yi, tana son gano gaskiya, ko dai ruma ta gano ta ne. Ganin sun gaza haɗa ido, ya sanya ta ce “Kin manta nima talaka ce, ƴar fulanin tashi da aka tsinta a dokar daji, ai mutane masu asali kamar yayyenk……”
“Iman bana son wannan maganar wallahi, raina ɓaci yake idan kina gayawa kanki haka”
“Shikenan na daina”.
Ruma ta ce “Da dai yafi, yauwwa da muka je gida ranar, mai sunan baba ya tamabayeni kina ina? Na ce masa kina nan ƙalau”
Murmushi ne ya bayyana a fuskar iman ta ce “Allah sarki yaya umar” ruma murmushi kawai tayi, dan tuni ta harbo jirginsu.
“Kar ki damu anty iman, ba zan gayawa ammi ba kya son sa ba, amma in sha Allah ba za ki aure shi ba, dan nima haushin sa nake ji. Bari na je wurin papa” ta tashi ta koma falo, ta tarar ammi ta tashi.
Ta je ta zauna a kusa da adam, ta yi ƙasa da murya ta ce “Done, na gama aiki, ka zuba ido ka gani”.
Adam ya ce “Amma baki gaya mini me ki ka ce mata ba”.
“Zan gaya maka, amma sai ta fasa ɗin tukuna”
Ya ce “Shikenan, mu tafi ne, kin gama?”
Ta ce “A’a sai da daddare”
“Aliyu ya kirani, ya ce mini mama ta za ta yo miki aike, wannan yayan naki mara fara’a zai zo”
Ruma ta ce “Da mai sunan baba ka ke ko?”
“To waye mara fara’a idan ba shi ba”
“Hmmm, ai kusan halinku ɗaya, ina kallonku fa ko magana ba kwa yi, kowa yana ji da kansa ko, zan gani dai “
“Ke waye ya ce miki bama ma magana”
Ta kai bakinta kunnensa, ta kare da hannunta ta ce “Ina kallon duk abun da ku ke yi fa, idan ku ga juna ku wani din ga basarwa, shiyasa duk na iya zama da ku, amma gara kai ka fi sauƙin kai wataran, kai baka sakani punishment kamar mai sunan baba, tsakar dare zai sani kneeldown idan na yi laifi fa”.
Dariya Adam yake, hannu ɗaya yana danna wayarsa.
“Banbancinku, shi bai fiye magana ba, kai kuma idan ka ga dama, kana magana, wasu lokutan kana da wasa kamar yaya usy, jin kai kamar da son girma kamar yaya Aliyu, wataran sauƙin kai kamar yaya Abubakar, idan nayi wani laifin sai na zata zaka dakeni ne, amma sai na ga ka mini banza. Shiyasa wataran nake jin kunyar yi maka rashin kunya”.
“Ashe kina sane ki ke duk abun da ki ke mini”.
“Mama ta ce hali zanen dutse, ai ka ga bana tsokanarka sosai, kuma zuwa yanzu ba shiryu ba dan Allah, a makaranta fa ko ƙawaye bani da su, saboda kar a ɓata mini rai, a kawo maka ƙarata, bana son ka din ga ɓacin rai sosai, tausayinka nake ji” jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli rumaisa, har cikin zuciyarta, take maganar.
Ta cigaba da yi masa raɗa ta ce “Amma duk da haka fa, ban manta abun da ka yi mini ba, kuma zan rama”. Jabir ne yayi sallama a falon, sai zuba ƙamshi yake. Ya ɗan tsaya yana kallon yadda rumaisa ta daddane kafaɗar Adam, ta dafa kafaɗarsa take yi masa raɗa, a tsakiyar falo ma’aikata na kaiwa suna komawa.
Ya ƙaraso ba tare da rumaisa ta tashi ba, dan ba ta da niyya ma.
“Takawa barka da yamma”
Adam ya kalli Jabir ya ce “Barkanmu dai”
Rumaisa ta yi saurin cewa “Papa zan ƙarasa maka idan mun je gida, bari na kira anty iman mu tafi, da daddare sai mu rako su gida ko papa?” Ta yi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallon fuskar sa.
Ya ɗan ja hancinta ya ce “To mimi” ta tashi ta nufi ɗakin iman.
Tana shiga ta ga iman na ɓoye wayarta, kasancewar hoton mai sunan baba take kallo.
“Anty iman ta so mu je gidanmu, da daddare sai ku dawo”
“Maman sabir kiyi haƙuri, gobe in Allah ya kaimu sai mu zo”.
“Mai sunan baba ne zai zo, yana son zai ga sabir idan ya zo, shiyasa na ce mu tafi tare, sai papa ya dawo da ku, kuma ga wancan jabir ɗin ya zo, idan kuma zaki zauna ne shikenan”
Ba shiri iman ta tashi, ta shiga toilet, ta wanke fuskarta ta shirya a gurguje, suka fito tare har da Sabir.
Jabir ya ƙare ta da ido.
Ammi ta ce “Iman sai ina?”
Adam ya ce “Da ita zamu tafi, anjima zamu dawo”
Suka fita, Jabir ya biyo bayansu yana ƙwalawa iman kira.
Adam ya waiwaya ya ce masa “Ya aka yi?”
“Adam meyasa ka ke yi mini haka ne? Ka san wurinta fa na zo”
“Ai ka san yadda muka yi da kai Jabir, tun da ku ka nuna mini iyakata da kai da Jamil, nima dole na tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro. Ka fara nemo yardar mahaifiyarka tukuna, dan ba zaka auri iman ka ta wulaƙanta ba”
Rumaisa kuwa tuni sun yi gaba, Adam ya biyo bayansu, suka tafi.
Shiru Jabir ya yi ya tsaya yabi bayansu da kallo, ya jinjina kai tare da yin ƙwafa.
***
Iman har ta ɗan wartsake, suka cigaba da sabgoginsu tare da ruma.
Ta ce “Maman sabir, amma yaya umar zai ci abinci idan ya zo ko? Me za a dafa?”
Ruma ta ce “To, nima dai ban sani ba, sai dai idan ki ka saka shi wataƙila ya ci”
Gumm iman ta yi da bakinta, tare da gudun kar ta sake wata maganar da rumaisa za ta fahimci wani abu.
Mai sunan baba bai tashi zuwa ba, sai bayan sallar magariba.
Duk da ba sakin jiki zai yi ba, amma rumaisa ta yi murnar ganin sa sosai.
Babban abun da ya saka shi farinciki, bai wuce ganin iman ba, sai dai kallo ɗaya yayi mata ya san tana cikin damuwa.
Cikin sanyin halinta ta ce “Yaya Umar sannu da zuwa, ya mama?”.
“Alhamdilillah” ya bata amsa, a ganinsa yayi ƙoƙari ya amsa mata a sake, ba tare da sanin amsar ta sa ta taƙaice da yawa ba.
Ya kalli rumaisa ya ce “Ga saƙonki nan, na je katsina shekaranjiya, gwaggo ta bani kaya na kawo miki iya ma haka, zaku yi waya da mama”.
Ruma ta kalli kayan a manyan ledar viva, ta ce “Amma na gode sosai da sosai, amma mai sunan baba ba yanzu zaka tafi ba ko?”.
“Me zan zauna na yi miki?” Yayi maganar yana ƙoƙarin tashi.
Iman ta miƙe ta ce “Na ga kamar ni nake hana shi sakewa, maman sabir, bari in kira sidi a waya kawai, tun da takawa bai dawo ba”.
Umar ya ƙure ta da ido, da sai da ta kusa rasa nutsuwarta, duk da da mayafin abaya a kanta, wuyanta sai da ya fito, kuma ya nuna ramar da tayi.
“Na taɓa cewa zuwanki yana hanani zama? Gidan yayanki ne, ni kuma ƙanwata me zan zauna na yi mata?”
Iman ta girgiza kai alamar a’a.
“Mai sunan baba, har gida na taho da ita, ina murna ta tayani muka yi girki, kuma ka ce zaka tafi ba zamu ji daɗi ba, dan Allah ka zauna ka ci”
“In zauna in ci abinci a gidanki, Allah ya kiyaye” yayi maganar yana kallon agogon hannunsa.
Ruma ta ce “To bari na baka ka kaiwa mama”
“Saboda ni ɗan aikenki ne?”
Iman ma ta saka baki “Dan Allah yaya umar, ko ba yawa ka ci” ta faɗa a ɗan raunane.
Ji yayi idan har bai ci ba ta ji ba daɗi, babu lallai ya iya yafewa kansa.
Ya kalli rumaisa ya ce “Spoon biyu kawai”.
Iman ta miƙe da sauri, ya ce “Ba ke ba ita”
Yayi maganar yana kallon rumaisa.
Ruma ta tashi a zuciyarta tana cewa son kai.
A zahiri wasa yake da sabir, amma a ɓoye iman yake kallo, yana jin ina ma ta zama mallakin sa, ace kullum gata yana kallonta.
“Ina Mahmud” yayi mata maganar ba tare da tayi tsammanni ba.
“Yana gida” ta bashi amsa duk da ba ta ɗago ba, dan ta san da ita yake.
“Bai koma school ba kenan?”
Iman ta ce “Eh, ina ga ya gama ai”
Bai kuma ce mata komai ba, Ya cigaba da wasa da Sabir, kamar ba shi ba.
Ruma ta dawo da kwano a hannunta, ta ajiye a gabansa, alkubus da miyar taushe, favorite food ɗin mai sunan baba.
“Zuba na tafi da shi kawai”
Rumaisa kamar ta fasa ihu, mai sunan baba akwai wulaƙanci, ba yadda ta ita, ta kwashi kwanukan, ta sake komawa kitchen, ta sake bashi damar kaɗaicewa da iman.
Ya samu ya kalleta sosai yadda yake so, sannan ya yi musu sallama ya tafi. Ita kanta iman tana cikin farinciki, atleast sun yi doguwar magana da shi yau.
Tafiyarsa babu daɗewa, takawa ya kira iman, ya ce su fito ya mayar da su gida. A kayan da mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, har da uban fura da nono, kaya guda da su mazarƙwaila, sai addu’oi a rubuce, da wasu saiwoyi da ba ta san ko na menene ba. Ga su ƙuli da man ja da fari, kayan kuka da kuɓewa har da su wake abun ka da mutanen karkara.
Haka ta keta kayan biyu, ta ce wa Iman ta kaiwa Ammi.
A lokacin da Adam ya dawo daga kai su iman gida, ya tarar tuni ruma ta yi bacci.
Ya ci abincinsa, da ya tarar a kan dining, dan yanzu idan ba makaranta ta tafi ba, shine su barira suke dafo abinci.
Ya leƙa ɗakinta, ya tarar tana kwance a ɗakinta da kayan baccinta, ɗan mini skirt, da riga vest, ga jigidar da ke ƙugunta tayi mata cif.
Ya taka ya ƙarasa ya tsaya a kanta, amma baccinta kawai take yi, ya zauna a kusa da ita, ya zubawa ƙafafuwanta ido, daga ƙasa dai ga ta da hips, amma sama kam, yanzu ne ma dai suka ɗan tasa.
Murmushi yayi da ya tuna wasiƙar da ta aika masa, da ya yi ta yi wa Allah godiya babu wanda ya ga takardar ya karanta.
Ya kai hannunsa kan jigidar, yana ɗan ja a hankali, yana zancen zuci, abu kamar wasa ya koma shafa cinyoyinta.
Duk da nauyin baccinta, caraf ta riƙe hannunsa, ta buɗe ido “Meye haka?”
Ko a jikinsa ya ce “A ina?”
“Papa bana so” tayi maganar tana tura baki.
“Ni ina so ai” yayi maganar yana janyota ya haɗata da jikinsa yana kallon idonta.
Mutsu-mutsu take tana hararsa za ta ƙwace, amma ya saka hannunsa ya ɗaya ya ɗago haɓarta ya ce “Can we try it now?” Tayi masa ƙuri da ido tana kallonsa.
“Are you ready for it? I want kiss you mimi”.
Girgiza masa kai ta yi ta ce “Dan Allah bana so” tayi maganar idonta na cikowa da hawaye.
Bai kuma ce mata uffan ba, yayi abun da rumaisa ko da wasan wasa, ba ta taɓa kawo hakan ba. Kissing ɗin ta yake yi sannu a hankali.
Ta rirriƙe jikinta, tare da jin abun wani banbarakwai a duniyar ta, abun da aka ginata a kan cewa abu ne da bai kamata ba, yau ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin sa.
Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta ji Adam yana ƙoƙarin yin wani abu daban da ya tayar mata da hankali.
Ihu ta din ga yi, tana riƙe rigarta, har da kiran su baba uwani su zo su rabata da Adam, zai yi mata abun da bai dace ba.
Ba ihun rumaisa ne ya tayar masa da hankali ba, illa jin sa da yake yi kamar ba shi ba, kamar an canza shi.
‘Me hakan yake nufi?’ ya tambayi kansa a ɗan tsorace.
Jikinsa ne yayi sanyi sosai da sosai, ga rumaisa a hannunsa na ta ƙoƙarin ƙwacewa.
Kwantar da kanta yayi a ƙirjinsa, ya ɗora kansa a nata, a ransa yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wace irin masifa ce kuma wannan ya sake tsintar kansa a ciki?
Yana jin yadda rumaisa ke ta zubar da hawaye, tana alwashin sai ta gaya wa kowa na duniyar nan, ya saka mata hannu a riga.
“Yi mini shiru, ni ki ke yi wa wannan ihun ko?”.
“To waye ya ce ka yi mini abun da ka yi mini, bayan ni a gidanmu an ce mini ba kyau. Wasan banza fa kenan, kuma saboda a daina ce mini ƴar iska na ƙara yadda muka yi aure”.
Halin da yake ciki bai hana shi yin murmushi ba, ya ce “Duk wani mai aure ɗan iska ne ai, wannan sirrinmu ne, ba a faɗa”
Rumaisa ta tashi zaune ta ce “Sai na faɗa, kuma kowa na duniyar nan, duk wanda na sani sai na gaya masa”
“Idan ki ka faɗa, cewa zan yi ke ki ka ce ayi, gara ma ki yi shiru”.
Share hawaye take ta ce “Wallahi ni ba ƴar iska ba ce, bani na ce ayi ba”.
Takawa ya ce “Oho dai, idan ki ka faɗa abun da zan ce kenan, yarinya ki adana hawayenki ma, ba yanzu yakamata ki yi kuka ba. Sai an zo making baby”
Ba ta gane me yake nufi ba, ta cigaba da kuka.
“Gobe in Allah ya kaimu zan fara shirin tafiya, in dai Mummy ta janye maganar ta, ina son zuwa wurin mai girma turaki ma”
“Kai ta tafiya, ni ba sake shiga harkar zan yi ba, kuma sai na tambayi mama, in dai duk mai aure kallon ɗan iska ake yi masa, sai na koma gida”
“To ki tambayo, idan kin tambayo sai ki bani amsa. Banda tsiwa ina abun yake, meye a rigar da ki ke mini wannan bankaɗar, da kururwar, abun da bai fi murfin jarkar faro ba”
Banza tayi masa tana sake kawar da kanta gefe.
Ya tashi tsaye, ya bar ɗakin.
Duk son baccin rumaisa sai ɓarawo ne ya ɗauketa, tana jin tsoron ta rufe ƙofa, kuma tana tsoron takawa ya sake dawowa.
Adam kuwa hankalinsa a tashe ya koma ɗakinsa yana safa da marwa, yana tunanin wa zai tunkara da wannan matsalar, matsala ce ba ƙarama ba, da take buƙatar ya samu mafita, kan rumaisa ta gama fahimtar menene aure, kar ya cutar da ita.
Iman kuwa bayan ta koma gida, ammi kallonta kawai take tana son nazartar ta, za ta fita, ta ganta a damuwa, ta dawo ta ganta cikin annashuwa, ba tare da ta san menene ya sanya ta cikin farin cikin ba.
Sai da ta je kwanciya sannan ta janyo wayarta, ta shiga what’s app, cikin fargaba ta turawa mai sunan baba saƙo “Yaya umar ya ka je gida?”
Kallon message ɗin ya din ga yi, yana shafa kan message ɗin amma yaƙi reply.
Kusan mintuna talatin, tana ganinsa online, amma bai reply ba.
Tunani tayi meyasa ma ta tura saƙon, sai ta yi sauri ta goge.
Ta na gogewa ya yi replying da ‘Me ki ka goge?’
“Bakomai” ta bashi amsa.
“Send it again”
Tsuru-tsuru tayi kamar tana gabansa, sannan ta sake rubuta masa ya ka je gida.
“Wayata yakamata ki kira, idan kin damu ki ji ya na je”
Ta yi masa replying da “Yi haƙuri”
“Kin yi laifi ne ki ke bayar da haƙuri?”
“A’a na ga kamar ka ji haushi ne”
“Ba haka nake ba, masifaffe kamar yadda waccan yarinyar take baki labari ba”.
Iman ta ce “Eyya ba haka ta ce mini ba wallahi”
“Umar ba masifafe bane, na dawo lafiya ƙalau, na gode sosai” tashi zaune iman ta yi tana yarfe hannu cikin murna.
Offline mai sunan baba shi ma yayi, ya na murmushin da bai san dalilinsa ba.
Yau juma’a akwai makaranta, amma ruma ta ƙi shiryawa, ta sha baccinta.
Takawa ma bai takura mata ba, bai ce sai ta je ba.
Sai sha ƙarfe goma na safe, sannan runaisa ta fito, ta shiga kitchen ta haɗa abinci ta dawo falo ta zauna.
Ta zauna ba jimawa, sai ga shi ya shigo, ashe ma ba ya gidan ba ta sani ba.
Ta wani sake tsuke fuska, ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce “Ba gaisuwa yau?” Ta matsa daga kusa da shi. Ya sake matsawa ya ce “Mun yi faɗa ne?”.
“Gaskiya papa bana so, Allah ka taɓa ni sai na yi ihu da ƙarfi”
“Me zan taɓa?” Yayi maganar yana kallon ta.
“Oho ai ka san me kayi mini”.
“Ba wannan ba, tun da yau kin ƙi zuwa makaranta, zan je na ɗan yi bacci ne, an jima zaki tayani haɗa kaya, gobe in Allah ya kaimu zan tafi”
Da sauri ta ce “Haba dai?”
“Ba kya so na tafi ne? Ai gara na tafi, na je na yi aure, tun da ihu ki ke yi mini. And turaki ya ce mini Mummy ta samu mai girma wambai ya ce magana ta wuce, Weldon little Mimi, aikinki yayi kyau”
Kallo ta bi shi da shi, har ya shiga ɗakinsa.
Ta kalmashe ta kunna Tv, tana kallo, ta ji sallamar wata mata, wani irin ƙamshi ya daki hancinta.
Ta ɗaga kai ta kalli matar, matar fara sol kamar ka taɓa jini ya fito, wata ƴat gayu, ta sha baƙin glass, da English wears.
Ta nemi wuri ta zauna, ta kalli rumaisa ta ce “Hey, ina mutanen gidan?”
Rumaisa ta kalleta, tare da jinjina rainin wayo irin na matar, ta ce “Mutan gida kamar wa kenan?”.
Matar ta ce “Matar gidan, da kuma takawa”
Cikin rainin hankali ruma ta ce “Matar gida ni ce, takawa kuma is not available”
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.