Uncategorized

Maciji Ne Page 91-92 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 91/92

_____________Cikin wani irin salo wanda ke nuna tsantsar farin ciki da zaƙuwa,Adeeb ya bude hannayensa,alamun fattu ta taho gareshi.

 Da sauri fattu ta ƙaraso gareshi,cikin takunta mai jan hankali,tare da fadawa jikinsa tana murmushi.

Maida hannunsa yayi ya kulle tare da rungume fattu tsamm,ajikinsa.

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

Atare suka sauke ajiyar zuciya,wacce ke nuna tsantsar kewar juna da sukayi.

Banda ajiyar zuciya ba abinda Adeeb ke saukewa,kamar wanda yayi wasan tsere.

Ahankali cikin murya mai tattare da shauki yace “I miss You so much  Hulwa”ya faɗa yana kare matseta akirjinsa,kamar zai maidata cikinsa.

Kusan minti biyar suka dauka ahaka,kafin Adeeb yayi karfin halin ɗago da fattu daga jikinsa yana kallon kyakykyawar fuskarta.gani yake kamar ba fattunsa ba,kamar wanda aka sauya masa ita,tayi kyau matuka,ta kara gogewa kai kace acikin ƙanƙara tare rayuwa.

Fattu ma kallonsa take cike da jin zazzafar kaunarsa na ratsa jini da tsokarta,dan gani tayi yayi mata kyau sosai,ya ɗanyi kiba kaɗan ya kara fari,ga sajen da ya kara ajiye wa yayi matuƙar ƙawata fuskarsa.

Ahankali ta kai hannunta tare da shafa gefen fuskarsa,lumshe ido yayi yana mai jin sanyi cikin ransa.cike da son nunawa Adeeb yadda tayi kewarsa ta kai bakinta kan nashi,ta fara kissing dinsa,kawai sai jin bakin fattu yayi cikin nashi.

Ai kamar mayen karfe haka Adeeb ya karbe lips din fattu ya fara sha kamar ya sami lollipop.

Tun abun yana karami har yazama babba,dan sun kasa rabuwa da juna,ganin suna neman faduwa ne yasa su zubewa akan lafiyayyar kujerar dake kusa dasu.adeeb bai bar wannan dama ba ,saida ya kara angoncewa, sosai ya shiga ruɗu da gigita,ɗan jin fattu yayi kamar bai taba ma saninta matsayin ya mace ba,sosai ya nishadantu da ni’imarta,ya rikice mata sosai haka yayi ta sunbatu yana hawaye.albarka kuwa fattu ta shata ba adadi da kyaututtuka kala kala.

Saida suka sami nutsuwa kafin Adeeb ya samu yaci abinci.anan dakin sukayi wanka tare,gaba ɗaya Adeeb ya kara kwarewa fattu,ko yaya tayi motsi hankalinsa na kanta,wani irin so yake mata marar misaltuwa.fattu duk da taji zafi amma haka ta daure bata nunawa Adeeb raki ba.nan suka shantake suna nunawa juna so da kauna,dama tuni Adeeb ya mika gaisuwa ga Sultan Habib da innar fattu.

Dan haka salla ma acikin dakin nan yakeyinta. Fattu kuwa ranar ta yabawa aya zaƙinta,dan ta tabbatar da cewar Adeeb yayi kewarta,kuma shidin jarumi ne na gaske.

Washe gari suka tashi daga Ghana zuwa Nigeria,da tareeƙ akayi tafiyar,dan dama tare suka zo da Adeeb,shiya sauka a masauki na daban.

Kai tsaye a Jos suka sauka,kafin suka nufi kauyen su fattu cikin dalla dallan motocinsu.

 fattu da Adeeb cikin mota daya suke,yana rungume da ita ajikinsa,motar su ce agaba,ko kaɗan fattu bata manta hanyar kauyen nasu ba,dan haka tana lura da inda suke nufa.

Download>>> Matar Hariji Complete Document

Sai motar Sultan Habib shida innar fattu dasu zayyad.

Kauyen yana nan inda fattu ta sanshi, ba abinda ya sauya.gidansu ta fara hangowa,cike da doki take nunawa Adeeb gidan”Hamma ga gidanmu can,yanzu zanga baffana,Hamma bazan iya kwatanta irin farin cikin da nake ciki ba”fattu ta faɗa tana rike hannun Adeeb cike da murna idanunta ya cika da kwalla.

Murmushi yayi,dan shima saiya tsinci kansa cikin farin ciki, ganin yadda Hulwarsa ke farin ciki.

“Nima ina farin ciki Hulwa zataga baffanta,saidai anya kuwa zai gane ki?Adeeb ya faɗa yana kallonta da murmushi.

Cikin doki da dariya fattu tace “wllh zai ganeni,ko me nazama na tabbata baffana zai ganeni kuma zaka gani”ta fada daidai lokacin da sukayi facking akofar gidansu fattu.

Da hanzari fattu ta buɗe kofar motar ta fito,bata ko tsaya sauraron Adeeb ba,burinta kawai tayi tozali da baffa.da sallama ta shiga cikin gidan tana rarraba ido dan ganin ta inda zataga baffanta.

Ba kowa cikin tsakar gidan,gaba ɗaya gidan yayi datti,ko ina kazantace cikinsa.jin sallama yasa gwogwgo hansai fitowa daga cikin dakinta,tana ta soshe soshen kwarkwata.

“Waye yau agidan nan nawa?rabon da naji wani yazo gidan nan,harna manta,kodai Hau……maganar gwogwgo hansai ta makale sakamakon ganin wata balarabiyar yarinya da tayi tsaye fuskarta ɗauke da murmushi.

Cikin rawar jiki gwogwgo hansai ta fara fadin”maraba lalle baiwar Allah,daga ina?wa kike nema kodai gidan mai gari kike nema?”gwogwgo hansai ta fada cikin rawar jiki tana kallon fattu.

Dariya fattu tayi tana kallon gwogwgo Hansai,duk ta rame tayi baki sosai gashi ta tsufa,kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin wahalar rayuwa.

“Gwogwgo,baki ganeni ba ?nice fa,nice fattun baffa”fattu ta faɗa tana kama hannun gwogwgo Hansai ba tare da gyama ba.

Galala gwogwgo tayi tana kallon fattu,cike da ƙaryata abinda fattun ta fada,saidai kuma wa yasan fattun awani guri?bare yazo yayi mata wasa.cikin rawar murya tace “fa….t.t.tu,kece haka ?kece kika zama kamar balarabi?ina kika je kika zama mai kudi haka?ta fada tana shashshafa fattu.

Dariya fattu tayi kafin tace” nice gwogwgo tare muke da iyayena fa da hammana,suna waje bari nace su shigo,wai ina baffana ne tunda na shigo nake nemansa”fattu ta faɗa cike da doki tana nufar waje.

Download>>> Ana Dara Ga… Complete Document

Lokacin da ta fita atsaye ta tarar da itayenta da Adeeb,mutanen garin sun zagayesu suna kallonsu da shafa motar da suka fito daga ciki.

Bata damu da mutanen gurinba tacewa su Adeeb su shigo.

Murna take sosai kamar wacce akayiwa bushara da gidan aljanna.

Gwogwgo Hansai jiki na rawa ta shimfida musu wata rubabbiyar tabarmar kaba.ko kaɗan basu nuna mata gyamaba suka zauna.

Bayan gaishe gaishene, gwogwgo tayi ta kuka tana bawa fattu hakuri,itadai fattu burinta daya taji ina baffanta yake.

Nan gwogwgo Hansai ta sanar da ita duk abinda ya faru da baffa,ranar da suka bar garin.

Kuka sosai fattu ta sanya,tana jin wani irin kunci cikin zuciyarta,ina zata ga baffa?mutumin daya tallafi rayuwarta ,ya bata kulawa,wayyo Allah.haka fattu tayi ta kuka,ajikin Adeeb yana rarrashinta.

Gwogwgo Hansai cikin nadama take faɗin”bayan tafiyar malam,gaba ɗaya lamari ya lalace garin nan,kowa abinda yake so shi yakeyi,haka inaji ina gani,yarana mata sukayi cikin shege,yanzu haka bansan duniyar da suka shiga ba,shima namijin tuni ya zama rikakken barawo,yayiwa yar mutane fyade shine ya gudu,ya bar rugar nan.mai gari yana nan ya zama gurgu,jauro kuwa abarsa ta lalace har yanzu bata da amfani,haka haroji yana na da fuska kamar ta dodo,saidai yaje Bara cikin gari,dan Allah fattu ki yafe mana ,nasan hakkinkine ke bibiyarmu”gwogwgo Hansai ta fada cikin kuka.

Haushin ta sosai Adeeb yakeji,dan yasan kadan daga cikin mugayen halayenta.

Tashi sukayi domin barin rugar,dan bawani amfanin zamansu,tunda wanda suka zo gurinsa baya nan.

Kudi mai yawa sultan habib ya bawa gwogwgo hansai,sai murna take tana godiya,haka ya tabawa mutanen kauyen ma kafin suka bar garin.

Kuka sosai fattu keyi ajikin Adeeb,ta shiga damuwa mai tarin yawa,haka yayi ta rarrashinta,har suka iso cikin garin jos.

Download>>> Kwarata Complete Document

Wata babbar motace tayi faci akan tsakiyar kwalta,hakan ya haddasa go slow agurin,suna tsaye cikin mota,masu bara sai zuwa suke suna Bara.

Wani dattijone cikin shiga ta almajirai,kallo ɗaya zakayi masa kasan yana shan wahala yazo jikin motar su fattu yana Bara,kasancewar gilas din motar irin mai duhun nan ne,yasa na waje baya ganin na ciki.

Fattu ce tayi firgigit tatashi daga jikin Adeeb tana kallon tsohon dake barar.

Wani dan ihu ta sanya tana mai ƙoƙarin buɗe kofar motar.kira take 

“Hamma baffana,baffana”tana faɗa cikin rawar jiki tana kokarin buɗe motar.

Da sauri shima Adeeb ya kai kallonsa inda fattun ke nuna masa.

Tabbas baffa ne kuwa.gana ɗaya fattu ta rikice tana kici kici buɗe kofar Amma tsabar farin ciki tama kasa,budewar sai kira take”baffana,baffana”

Hannunta Adeeb ya riko yace “ki nutsu hulwa,karkije kiki ciwo kinji bari muje gurin baffan”ya faɗa yana bude kofar motar.

Da sauri fattu ta fito daga cikin motar ta nufi gurin mutumin da yayi dan gaba dan zuwa wajen wata motar ya sami sadaka.

Da sauri ta kamo hannunsa tana faɗin “baffana kaine,haka ?”cikin azama baffa ya juyo sakamakon jin Muryar da akullum saiyayi kukan rashin ta,kuma duk kuɗin da yake samu na bara tarawa yake,dan yayi ta zaga garuruwa yana neman fattu,yasan  watarana zasu hadu.

Jifa yayi da dan buhun dake hannunsa,wanda yake tara kudin barartasa ciki.

“Fattu,kece”baffa ya faɗa cike da shauki.

Kuka fattu keyi tana kallon baffa,kafin ta rungumeshi ajikinta tana kuka.shima baffa kuka yake cike da godewa Allah,yau gashi ga fattunsa,shikenan burinsa ya cika.

Sultan habib,da innar fatyu ma,fitowa sukayi,dan kobasu tambaya ba,sunsan wanna shine baffan fattunsu.

Adeeb kansa saida yaji kwalla ta cika masa ido,dan tausayin tsohon da yadda ya koma.

Horn din da motoci ke musu ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,dan tuni an janye motar data haddasa go slow ɗin,dan haka cikin hanzari suka shige mota dan ba mutane hanya. 

Motar su fattu baffa ya shiga,su Sultan ma suka koma cikin tasu ,sannan suka bar gurin.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Kai tsaye gidan da suka sauka suka koma,dan yau suke don komawa Ghana,

Fattu sai murna take daga ga baffanta.

Wanka kawai suka bari baffa yayi,aka bashi wasu kayan ya sanya,kafin suka daga sai Ghana….

Masu karatu bari muyi musu rakiya zuwa ghanar muma.

Ina kuke 

Masoya anty mammy?

Albishirinku,ina mai farin cikin sanar daku,sabon littafina mai suna RAINON DAWA,yana nan akan hanya,da zarar mun kammala MACIJINE,hmmmm

Daga jin sunan kinsan ba magana.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Karku bari abaku labari.

Ga mai bukata ,zai iya biyan kudinsa tun yanzu,domin nan da kwana uku zaku fara samun wannan kayataccen labarin na RAINON DAWA.

akan fashi mai sauki,

Normal group 300 

 

Special group 500

Sannan akwai manyan mata dake son atura musu private to kuma ga naku farashi,1000

 Dan haka saina jiku,

Acc. No.

Saratu kabir

A.u.b

2215749011

Saiku nuna shadar biya ta wannan no.

08148360851

Saina jiku,masoya.

Show ne your love akan novel ɗi Nan,

😍😍😍🥰🥰🥰🥰

Mrs babi ce💘💘

Back to top button