Uncategorized

Matar Makaho Part 4 Complete Hausa Novel

MATAR MAKAHO

Chapter 4

By Rukayya Ibrahim

Cikin tashin hankali Khadija ta nufi kofar gidan tana isa taga an fitoh da inno Akan kadon asibiti da ake daukan gawa Koh Mara lfy tana kwance Koh motse batayi aka shigar da ita Ambulance sai su Inna asabe da baba lami suke ta rusan kuka Kamar ana yankasu,

Khadija Kam iyya rudewa ta rude ganin Yan matan gidan duka kuka suke harda wasu mazan ma

Bappa Dayyabu da bappa sulaiman harda kawu  tafawa suka shiga motar Yan sanda da gani dai abin Case ne babba 

Ta rasa wama zata tambaya ga Goggo Amina sai kuka take ,

Ganin lokaci na tafiya tasan yanzun bazata samu amsar tambayar taba yasa ta wuce kofar yayan ta shanyar kayan dazun da safe takai d’akin jakar ta dauka da Abubuwan da ta lissafa Mata duka,ta rufe kofar  tayi kofar gida

Da sauri ta fita daga gidan ganin har yanzun jama’a na tare Tam,

Hospital ta wuce direct tana isa dakin ta baiwa Sumayya jakar,

Budewa nayi na zaro kudi  50k  na mikawa yayan khadija “ga kudin ka dau takardan khadija ta rakaka kuje ku biya”

…Toh Al’ameen yace  Yana laluben kudin ya karba hade da zaro dubu goma da dari biyar in safiya da Khadija ta basa ya hada da dari biyar in mangoron sa,ki cire dubu goma da dari biyar a cikin kudin sai na hada Dana wajena na ciki ta na biya,

“Ka bar na wajen Kan ai ba’a sallame niba zasu bukace  mu Sai wasu abubuwan irin su hand gloves Koh ruwa da allurai duka ai bamu Gama kashe kudi ba ba iyya aikin bane kawai ka rike kudin a gunka,”

Toh khadija Tashi mu tafi 

Toh yaya, ta basa amsa

**Fita sukayi nikam zuciyata tsinkewa ya ringayi da fargaba gani nake kamar bazan rayu ba,

Waya ta da khadija ta kawo mini na dauka number abie na Kira Amma Bai dauka ba,

Sake Kira nayi harna fidda tsammani naji  ya dauka cikin sanyin jiki na Masa sallama”assalamu alaikum abie”

Waalaikumu salam ke lafiya?

Lafiya Alhamdulillah abie Daman na kiraka ne nace maka za’a mini operation yau don Allah Abie in nayi maka ba daidai ba kayi hakuri abie ka yafe mini bansan Inna shiga operation room  xan fita da Rai Koh a mace ah ah shiyasa na kiraka naji muryarka abie ka samin albarka Koh xanga nasara a rayuwa ta Dan Allah”

Keeeeeee!!!! ce Miki akayi  in za’a ma mutum tiyata mutuwa yake ne kin wani kirani kina fadamin Zaki mutu ki mutum Mana keee!!!! bara ma na fada Miki daga yau karki sake kirana!!!!

 wallahih, tunda na aurar dake ki barni na huta mana,

***Hawaye ne keben fuskata Wai meke faruwa da rayuwa nane haka,,

Yanzun mahaifina in ma ya juyamin baya,

ganin shigowar Al’ameen da Khadija yasani share hawayen,

“Khadija kin biya”?

Eh Aunty…. Sunce 7:00 na dare za’a shiga operation room in,

“Toh bara nayi sallah mangariba Koh kafun Azo a dauke  ni” na fada zuciya takaraya sosai wallahih,

Shima masallaci ya tafi nida Khadija mukayi Sallah muna idarwa na sakasu suci abincin da ya rage tun safe Basu sake saka kome a cikin su tun karyawan safe na taliya da wake,,

Daker suka iyyaci Amma kadan nikam na kasaci tsabar fargaba,

Karfe bakwai akazo za’a dauke ni,

*** Da kafata na fitoh nurse suka sakani a gaba har nayi nisa Al’ameen ya k’wala mini Kira tsayawa nayi ya iso inda nake lalubar hannuna yayi ya rike cikin damuwa sosai nasan daurewa yake,

Sumayya insha Allah Zaki fitoh cikin nasara kinji ki cire tsoro a ranki kinji Allah ne ya jarabceki Kuma insha Allah shizai baki lfy kinji,

“Kukane ya k’wace mini yau wa’innan bayin Allah sune gatana a yau bani da kowa a kusa Dani sai su dame Zan biya su babu, Allah ne kawai xai biyasu” rungumar sa nayi cikin kuka nake  cemai “insha Allah insha Allah”

Lokaci fa na wuce wa ki shige mu tafi Naji muryan Nurse 

***Sakensa nayi na rungumi khadija wance tun tuni kuka take, 

***Na juya Ina tafiya a hankali Kamar wance k’wai ya fashewa a ciki sudai suna bin mu a baya har Muka Isa kofar operation room aka dakatar dasu tare da nuna musu su koma Kan kujirun d’ayan block in su zauna…… 

Bayan da Al’ameen baiyi ba Khadija ta koma gida taje ta kwanta Amma Taki tace anan zata kwana sai da ya nuna Mata Jan ido kafun ta yarda zata tafi 500 ya Bata ta hau nepep sauran change ta rike a hannun ta ,,,

. godiya ta Mar sosai ,ta dauki kula ta fita,…..

Zama Al’ameen yayi agun har akayi Kiran isha’i yaje yayi sallah yanata Addu’a Allah ya yasa aiyi aiki a sa’a ya Bata lfy(muma mukace Ameen) 

Bayan wasu hours Sumayya aka fitar akan gado tare da kayan tiyata da hulan duka Koh motse batayi aka kaita dakin da ake aje,wa’inda akama tiyata Basu farfado ba shima binsu yayi har dakin ya shiga sun dauke ta sun daura akan gadon dakin,

 kujira ya samu  a Gefen gadon ya zauna ganin an shanja musu daki ba dakin emergency bane tashi yayi yaje ya tattara kayansu na dakin emergency ya dawo dashi dakin da take yanzun, zama yayi a Kan kujira,

Har dare yayi sosai Bata farka ba,  sai karfe 2 na dare ta farka tana fizge fizge bakin ta dauke da salati tana ambatan sunan abie yayi hakuri karya gujita itama,,

Abirkice ya mike Yana kakamata ganin irin girgiza da take ya tsorata da sauri ya k’wala ma nurse inda ke dakin a zazzaune Kira ganin inyace zai tashi Sumayya zata iyya raunana kanta,

Da gudu suka yi kanta suka kakamata surutai tayita Yi Akan Abie da salati sai Shan anjima kadan Sumayya ta koma bacci,

Likita lafiya kam meke faruwa ne da Matata?ya fada hankalin sa a mugun tashe,

Ka kwantar da hankalinka ana samun haka Daman in dai mutun zai farfado sai yayi ta sambatu,..

Toh doctor yace Yana komawa Kan kujiran ya zauna hannunta ya laluba ya rike yanajin wani irin tsoro a ransa,

Har asuba Yana zaune sai da yaji ana Kiran sallah kafun. Ya Mike ya fita yaje yayi ya dawo  ya cigaba da zama…

Khadija Taki fadawa yayanta abinda ta gani a gidansu gudun kada hankalin sa ya tashi ta Sansa da saurin birkice wa gashi Yana fama da Sumayya tazo ta Kara Masa da wani Kuma,

Keke napep tahau  ta wuce a kofar gidan su Goggo Amina ta sauka ta biyasa kudinsa ta shiga gida da sallama. ……

Goggo Amina ta samu  zaune sai rusan kuka take Kamar wance ake yanka namar jikinta,

Da sauri ta karaso gareta cikin tashin hankali tana cewa Goggo Amina lfy menene ya farune wallahih tunda na tafi hankali na yaki k’wanciya?

Wallahih Khadija kedai ki bare kawai mutanen gidan mu sun dawo kashe junansu,

Kamarya Goggo ban gane ba?

Toh dazun bayan la’asar iro ya dawo daga aiki yazo zaici abincin ranan sa ashe suwaiba( yar baba lami) ta dauka taci shine da yazo dauka yaga babu yake tambayan inno ya abincin sa babu  a kula shine fati tace masa suwaiba ne taci, 

Tashin sa ba wani tunani ya zaro wayan wuta ainahin na bol ya zuba mata ita kuma da taji zafi tana ihu ta zari tabarya zata muka Masa,

Inno Kuma ganin za’a bugawa iron ta tabarya tazo zata k’wace kawai tabarya ya sauka a kanta,shine fa Kika ga ta mike Koh motse batayi, 

Ni tsorona ma yanda naga Kan Bai fitar da jini ba kinsan akwai babban hatsari ka bugu irin wannan ace jini Bai fitoh ba,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Shine iro ganin inno a yashe a kasa yaje ya ibo Yan sanda akazo aka tafi da suwaiba, gabaki daya gida ya hargitse su bappa nayinku duk sun bisu station wasu suna asibiti har hanzun ba’a San takamammen halinda inno ke ciki ba mutuwa Koh rayuwa😭😭😭 wayyo ni Aminatu,

ta fada tana sake rushewa da kuka ita dai Khadija Allah ya kiyaye na gaba tace ta Mike taje ta ajiye kulan Sumayya a kitchen sai gobe zataje kofarta da safe,wanka tayi, tayi isha’i ta kwanta don batajin yunwa taci a asibiti,haka tayita juyawa Amma bacci yaki daukan ta tashi tayi ta Kama lafilfilu tana nemawa Aunty Sumayyan ta lfy da nasaran aiki sai 1 ta kwanta

Bangaren Al’ameen bayan sallan asuba har lokacin yana zaune Dayake dakin da suke yanzun babban falo ne Mai dauke da majinyata masu yawa wa’inda aka ma operation shiyasa Basu kadai bane a dakin,

 sosai Yan dakin ke mamakin MAKAHON nan shin baida Yan uwane da zasu kula da wannan Mara lfy sai MAKAHO chap lallai Kam kowa gulma na cinsa( Niko nace gulma zai karku bazakuji kome ba) 

Tun asuba Khadija ta farka Bata koma. Bacci ba wanke wanken Goggo Amina ta fara ta hada harda kulan  aunty ta duka ta wanke tayi shara tana Gamawa ta daura dumame ganin yau Goggo Kamar Mara lfy haka da tashi ,tana Gamawa ta dauki key sai gidan yayan ta,

Yauma sai da tayi shara ta daura ruwan zafi Yana tafasa ta juye a flasks ta dafa indomie da kwai lokacin karfe 7:30 wanka tayi tasa kayan ta data dauko a gidan Goggon ta tadau abincin tayi hanyar FMC

****Da misalin karfe bakwai na safe na bude idona Wanda nakejin Kamar an zuba mini barkono a ciki a hankali na sauke k’wayan idanuna a kansa a zaune yake ya tasani a gaba Kamar wani Mai kallo yayi tagumi kallo daya zaka Masa kasan a cikin zullumi yake sosai…….

Aunty’ inno ta rasu tace tana Kara karfin kukanta,

“Innalilahih wainnailaihir rajuun”   Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta” nace 

Ameen Aunty tace tana mikewa tadau hijab inta ta nufi cikin gida,

**Banyi niyar zuwaba saboda jikina Amma ganin mutuwa ne Kuma Abu da  gida babba hakan zai iyya zama abin magana, yasa na mike na fita zuwa cikin gidan, 

Ai ban tashi sanin Yan gidan ba sai da Naga manya da yara Suna kuka harda na tashin hankali kuka suke ba manya ba yara Mai makon a ma mamaci Addu’a sai ihu da kuka nidai Ina zaune a Gefen matan makwanta da suke shishigowa Ina kallon ikon Allah

Al’ameen da wannan sanyin jikin ya iso kofar gida ya tarar da jama’a makil, inno ta rasu mutuwar ta dake sa sosai don alokacin sai da mutuwar mahaifiyar sa ta dawo Masa sabo,ganin yanda iro ke kuka Wanda yasan halin iro ba kome ke tsorata Sa  bama Amma yau kuka yake,

tabbas mutuwar iyaye akwai ciwo,(Allah kajikan iyayen mu)

Ankai inno gidan ta na gaskiya yau har anyi sadakar bakwai gida ya koma kamar yanda yake kowa na sha’aninsa sai yaranta da sukayi sanyi kadan na rashin uwa,

A tsawon satin nan na fahimci yayan Khadija baida aiki haka zaije yayi ta yawo Koh sisi bazai samuba ya dawo Yana kame kame taliya Koh Maggi Koh indomie nake iba  na bawa Khadija takaima masu shago su Saya da araha kafun mu samu na shifenen Miya,..

Duk da Al’ameen baisan Ina Saida garana ba,

karshe dai ajesa nayi nace ya fadamin me ke faruwa, dashine yanzun,duk lokacin da ya zauna baida aiki sai tunani,

Tukum yamin bayanin bashi da jari yaje tashan kayan marmari  sun hanasa bashi duk inda yaje su taimaka Masa sunki,

,”Amma   menace maka in Abu ya taso ta wajenka bance ka ringa fada mini ba”?

Hakane Sumayya Amma ni sai Inga Kamar ni ya dace in bukatar ki ya Tashi ki tambayi ni ba Zan ringa daura Miki nauyi ba,

“Au aini ma nufina bashi Zan baka Amma Ina ni Ina baka kyautar kudi sai dai bashi “

Duk da haka dai Sumayya….

Ban Bari ya karasa maganar Saba na tare sa “na baka bashin ne ka rufawa kanka asiri Koh na rike kudina ka cigaba da yawo ba aiki ga azumi saura wata biyu”

“Kuma bara na gaya maka in azumi yazo kayan Dadi zakana sai min Kuma kamin kayan sallah harda Khadija kaji dai na fada maka”  

Toh shikenan abani yace Yana gyara zama alamun dai baida mafita,

“Ka Bari sai gobe Zan baka”

Washe gari Khadija na tura yaro yace tazo, ba’a jima ba sai gata aikanta nayi   *say* *box* ta Kira mini Daya daga cikin yaran  masu shagunan sai da wayoyi da laptop’s suzo tare tace Masa amarya ce ni Kuma ban fara fita ba,

Don nasan in na Bata laptop innan za’a Mata cinikin wulakanci ne kawai Koh ma wani ya Mata wayo ya gudu da laptop in don nasan say box ba irin mutanen da babu a ciki,

Munyi ciniki da Mai sayan system in ganin  yanda Yama laptop in cinikin wulakanci yasa nace na fasa sayar wa,

Buhun flower na dauko a kitchen Daman ban taba bude Saba nace wa Khadija taje gun Haladu tace Masa xai Saya buhun flower Zan Masa sauki,

Bata jima ba ta dawo tace min yace ta kawo flowern ya gani, Bata buhun nayi taje shagon Haladu ta sayar mini shima naira dubu bakwai ya Saya ba yanda na iyya haka na sayar Masa Amma ni Karan kaina nasan ba haka kudin yake ba,

Yayan khadija na baiwa dubu uku yayi jari na rike dubu hudu na D’an Yi sayayyan abin bukata  nayi irin su pad omo sabulu na baiwa Khadija dubu D’aya, tunda har yanzun Basu gyara Mana NEPAn kofar muba  don sun biya ganin mu bamu biya ba sai suka yanke wayar kofar mu Khadija na baiwa dubu daya ta mikawa bappa sulaiman kudin wutan NEPAn mu aranan sukasa aka hada mana wayar aka gyara, na baiwa Khadija dari biyar itama  😉

Haka rayuwa tayi ta tafiya Rana ya wuce sati ya shude yau Dadi gobe Akatsen sa  har Muka cika wata Daya da sati biyu da aure, ba abinda ya taba shiga tsakanin mu Koh da kuwa hada gado ne, in munkwana waje D’aya toh ana zafi munyi kwanan waje ba nepa,

A y’an kwanakin nan na  fara fuskantan matsen rayuwa Wanda ban Saba ba,

Dole sai abinda ya samu zamuci wani sa’in ma in Bai samo kome ba haka zamuci indomie d’anye wani a dafe da ruwa, in ya samu D’an ciniki Kuma muci shinkafa da Mai da yaji,Inda Allah ya sumuma garana Bai kare ba akwai taliya Mai Maggi kefe shinkafa, Amma duk da haka na D’an fada  na chanjin yanayi,  saboda yanzun ya hanani Saida Kayana don har Yan unguwa sun fara gulman ya kasa rikeni Kayana nake sai dawa,maganan har kunnen da yashiga shiyasa ya nuna mini baya so ,

yau na shirya da niyar zuwa gidan Goggo Amina, da gidan mu tunda safe na kammala aikina yau mun Sami kudin kayan shaye mukasha da safe’ bayan ya fita na kammala aikina dake na sanar dashi Zan fita gidan Goggo Amina ( marikiyar Khadija ) Zan bi gidan mu d’uka Bai Musa ba saboda mun Riga munyi maganar dashi, dari da hamsin ya bani kudin Keke,

 Khadija zata rakani kasancewar yaune Zan fara fita, unguwa tunda nayi aure bayan asibiti ba inda naje,

Sai goma Khadija tazo lokacin na fitoh wanka, Muka gaisa ta shiga Wanka Dayake tun jiya ta zo ta guge kayanda zatasa d’aya Daga cikin Wanda nake Bata,

Shiryawa nayi cikin lufaya Mai tsada fari Mai Flowers brown NASA riga long sleeve brown NASA takalmi fari na dau jakama fari fuskata ba kome sai powder da man baki, Khadija dake gefe na tsaye baki bude tana kallona,

“Rufe bakin ga guda zai wuce ciki”nace Mata cikin murmushi Mai karawa fuskata kyau,

Hmm Aunty na gaskiya ke Mai kyauce Allah ne kadai yasan dalilin da yasa ya bawa yayana wannan k’yakk’yawar hallintar nan Ina ma Yana kallo yaga yaran da za’a Haifa Masa 😅

Murmushi kawai nayi bance kome ba  don na lura ita ta yara ma take,

” Khadija kiye sauri kisa kaya don Allah na masu na ganni a gidan mufa Naga abie na”

Toh Aunty tace tana saka dogon riganda na taba Bata,tayi shafe shafen ta tana Gama shiryawa, Muka  fita”

Yaune rana na farko Dana taba karewa unguwan sintali kallo unguwa ne da ya hada ruwa biyu masu kudi da talaka wa Yan kasuwa da ma’aikata da masu zaman banxa unguwan nada kyau sosai da fasali,..

Gidan Goggo Amina mukaje da kafa ,

Mun samu tarba Mai kyau ba laifi matar nada kirki sai dai na Lura ita mace ce da Bata shiga abinda Bai shafe taba Sam babu ruwanta,mun D’an jima a gidan kafun Muka Mata sallama na aje Mata laidan Turare Wanda na d’auka a kayan aure na,

ta rakomu har waje Muka tare keke napep ,

Hajiya Ina kukayi? Ya tambaye ni

“Specialist” zaka kaimu,

Ku hau muje yace,

Dukan mu Hawa mukai yaja machine insa muka nufe  unguwan specialist,

Muna shiga unguwan mu  na Masa kwatancen inda zai sauke mu,

“Yana sauke mu na tambayi sa “nawane kudin ka”  

Naira dari da  hamsin kudin ku kubiyu,

Sai a lokacin na tuna dari da hamsin inne a jikina kacal Wanda yayan Khadija ya bani Allah dai yasa abie na gida nasan zamu samu na dawowa don karyan mu taka da kafa daga specialist zuwa sintali,

biyansa nayi muka  nufi kofar gidan mu

Khadija mutuwar tsaye tayi ganin wani irin gida Mai bala’in kyau Wanda Koh a mafarki Bata  taba ganin irin Saba Daman ita ba yawo take ba iyya kacinta kasuwa sai unguwowin kusa da sintali  irin mafindi unguwa gadi da sauran unguwowin kusa da unguwan su,

Amma Bata taba zuwa unguwa Mai nisan nan ba sai dai tanaji a bakin Asma’u sunje unguwan specialist Koh millionaire’s sweet in suna Bata lbrn gidajin unguwan sai taga Kamar tatsuniya suke Bata bata taba zaton haka gine ginen unguwan yake ba Wai duka wannan a cikin Jala yake?

***Harna nufe get Amma sai naji Kamar ba Khadija a gefena juyawa nayi me Zan gani Khadija an sake hanci baki ido ana kalle kalle zuwa kawai nayi na jaho hannunta, sai a lokacin ta farga da kauyancin da ta nuna 

Cikin Jin kunya tace Aunty wallahih unguwan nan yayi kiga gidan da zamu shigan nan Kamar aljannan duniya,

Kai Khadija kin cika shirme wallahih mu tafi nikam,

**Get Muka nufa Mai girman gaskiya kamar get In gidan prison haka ma ginin gidan dogayene sosai anyi penti fari get in ma farine k’wank’wasa,makeken kofar get in,nayi

Wani farin buzune ya leko ganina yasa ya washe bakinsa cikin hausar sa da baya fita yake cewa laaa Amarya Kaine hajiya Sumayya wallah nayi kewanka shannu  da zuwa lale lalema barkama lale ya fada Yana bude mini get muka shiga,

Shiga cikin gidan mu ya sake ruda Khadija ganin filin gidan mu filine babban bana Wasa ba  Wanda yakai girman wani karamin unguwa,ga shuke shuke na Flowers ya kewaye gidan Wanda ya kara haska gidan sosai ga parking space babba Mai dauke da mototi na alfarma wanda akalla zasu Kai talatin duk ciki bamai araha,

Nidai Ina rike da hannun Khadija Muka nufi wani  babban part Wanda duk fadin gidan part inne kawai ba wasu Amma daga ganin part in kasan ba karamin duniya bace a ciki ganin shima ginine na gidan sama Mai Hawa uku,babban kofar falon NASA hannun na na bude da sallama a bakine duk da banida tabbacin za’a ji,saboda girman falon,

Khadija Kam mutuwar tsaye ta sake tayi ganin cikin falon gidan mu,

Kusa Kai mukayi cikin falon falone Mai girman gaskiya Wanda ke dauke da kujiru set biyar ga babban plasma na alfarma Kai fadar tsaruwar falon gidan mu Bata lokaci ne na barwa readers su keyasta,

Babban falon gidan mu Yana dauke da d’akuna kusan Sha biyar haka upstairs shima dakuna  goma Sha biyar ne Hawa na uku ma haka,Amma duk yawan d’akunan gidan munan falon mu dayane shine falon kasa, Wanda Koh a Hawa na uku kake kana hango falon,

 d’akunan kasa na samarine sai kakarmu dake zaune dasu a kasan Wai tana saka musu ido injita, dakunan Hawa na biyu na iyaye ne Hawa na uku shine na Yan Mata da d’akunan yaran gidan da sukayi aure maza,suna zaune da iyalansu ,..

duk yanda Zan fasalta muku gidan mu saifa na  rage wani abin,

Kaf gidan mu da colour D’aya aka kawatashi da white colour sai surkin baki Kama daga kujiru labule  Abubuwan da aka kawata gidan kome farine daga sama har kasa abin sai Wanda ya gani,

Jama’ar gidan mu duk Muka samu a falo da yake yau weekend ne ba aiki ba makaranta kowa na zaune wasu na kallo wasu na Danna waya wasu na Danna laptop yara na wasa wasu abinci suke ci ganin mu yasa dukansu barin abinda suke suka zuba Mana ido Kamar yau suka fara ganina,tunda Khadija ce Basu sani ba,

Idanuna ne ya sauka a Kan kakata dake zaune tanacin kefe sai uncle’s nawa dake zazaune wasu na cin abinci wasu na Hira wasu na duba takardu,

wani abune ya tsayamin a makoshi Mai kamada Takaici sun aurar Dani Basu damu da rayuwar da nake ashan ba gasuna suna zaunen su Kamar Basu San wata Sumayya da aka bawa MAKAHO ba Basu neme sanin ya rayuwa ta kare ba waima me dalilin auran Dani ne tunda gasu Aunty miemie sun girme ni nesa ba kusa ba Amma saini kadai aka aurar auren ma da MAKAHO ba lafiyaye ba,Koh don anga mahaifiyata Bata gidan ne Kai Koh mahaifiyata Bata gidan ai ubana nanan

Koh da kowa zai nuna Mini kiyayya dada zata sassauta tunda ita ta haifi babana amma Ina abin ba sauki,

“Ina kwana dada,”nace Ina zama a cikin Daya daga cikin kujirun falon,

Toh matan miskinai ne agidan namu yau Koh idonane,?

Ah ah Kaka ba idon ki bane kinsan azumi ya karatoh anzo amsan zakkah ne,

Hhhhhh Kai miemie baki da dama Amarya ce fa tazo ganin gida mutun da gidansu kece yazo karban zakkah,kubra ke fada tana dad’a tunsirewa da dariya

Waiku yaran nan wasu irin Yan iska ne me yasa baku da mutunci shegu kawai ai gwara ita tayi aure Koh?

Keee koh miskini kin samu yazo wajen kine da sunan aure, a cikin ku waye ta samu miskinin na zuwa wajenta,Yaya Abdu ya fada ransa a bace,

Ai itama ba zuwa yayi ba lika Masa akayi,miemie ta basa amsa,..

Rufe mini baki karna ci ubanki Yar iska Abdul yace Yana mikewa,

Ai duk laifin  dadane Sam bansan me yasaba, Dada (kakar mu)  itace babba Amma ita ke sasafo Mana bala’i yaya kabiru yace Yana maijin takicin ahlin gidansu,

Abubakar kanajin abinda shegen yaron Kan nan kabiru yake  shimin mutunci kayi shuru kana kallonsa,,,

Kiye hakuri Dada Kai kabiru zanci kaniyarka fa inka sake shiga abinda ba ruwanka uwarka aka zaga Koh me da zaka saka bakinka a ciki,

Mikewa Kabir da Abdul sukayi sukabar falon,

Ganin yanda aka Mai Dani Kamar kashi ba Wanda yabi ta kaina kowa na Harkan gabansa

Ganin Banga Abie na a cikin falon ba yasa na mike nayi hanyar upstairs na nufi d’akin sa nabar Khadija a falo wance ke rakube Kamar ace kitttt ta ruga,

Bude kofar d’akin nayi nasa kaina na shiga   Abie nane zaune a kasan tiles Yana duke da Kai sai momy (yadikko na) zaune a bakin gado daga Gani dai magana suke………………

Bayan fitar Ammar Khadija ta kirga kudin dubu goma ne,Mika min tayi, Aunty ga kudin

“Ajjye Khadija in yayanki yazo ki basa tunda shike fama da zirga zirgan asibiti” toh Aunty ta bani Amsa tana aje kudin a cikin ak’watin Kayana,

Al’ameen na fita daga asibiti da kafa ya koma har gida Dayake akwai sanda in Kuma yazo titi sai ya Kama yara su tsallakar dashi Yana Isa unguwan su(sintali) wajen shagunan bakin titi ta inda yake sai da mangoro a bakin su,

Shagon malam shu’aibu ya fara zuwa don shine yafi masu shagunan abin arziki sosai alayin da sallama a bakinsa ya shiga shagon,

Assalamu alaikum malam shu’aibu

Waalaikumu salam Mai mangoro ne?

Eh nine malam shu’aibu barka da jama’a

Barka dai lafiya Kam Naga yau tun safe danazo bude shago Naga hulbairon ka a rufe dazun na aiki yaron gidana ya karbo mini yako yake fadamin baka nan?

Eh wallahih malam shu’aibu iyalina ne ba lfy jiya na kaita asibiti,

Allah sarki ya jikin nata?

Da sauki Daman nace bara nazo ka taimaka mini da kudi dubu hamsin za’a Mata aikine appendix ya kumbura a cikin ta don Allah ka taima kamin,

Kutt lallai ma a karnin nan da kowa ke takai takai Ina Zan iyya daukan kudi har 50k na baka da sunan bashi, bayan anyi operation in Ina zaka samu kudina ka biyani, gaskiya bazan boye maka ba ni nan Koh biyar bazan iyya baka ba banaji ance Yar masu kudi aka aura maka ba me yasa danginta bazasu Mata jinya ba tunda sunsan baka dashi Daman suka baka ita

Shikinan malam shu’aibu na gode, ya fada Yana fita ba tare da ya basa amsar tambayar Saba,

D’ayan shagon Al’ameen ya shiga  shagon gwanja bayan sun gaisa shima ya rokesa Koh zai samu bashin kudi

Amma Kai dai wallahih D’an rainin wayo ne ya Ina Saida kayan Miya zakace na baka dubu hamsin duk kayan shagon nan aka sayar Ina zaiyi dubu hamsin,

Haka yayita bin shagunan makwantansa Amma ba Wanda ya basa Koh sisi wasu kamma da bakar magana suke binsa dashi,

A haka ya iso shagon Haladu shima yace baidashi,. Wajen bairon mangoron sa yaje ya bude ya tataba mangoron rabi duk sun lalace saboda yini da sukayi a rana Kuma a rufe, zabe masu kyau yayi Yana,

D’auka yana sawa  a k’wando ya shiga shagon Haladu dashi, Yana cewa,

 don Allah Haladu Koh zaka sayar mini da mangoro na zanje na zauna a asibiti  na kwana biyu daidai Matata taji sauki 

Gaskiya bazan iyya sayar maka ba sai dai na saya kawai na sayar Nima na samu D’an riba,

Ba damuwa Al’ameen yace Masa

…..Nawane mangoron?

D’ari takwas da hansim

…..Zan baka dari biyar  don Naga wasu sunyi laushi?

Ba damuwa Allah ya saka musu albarka

……Ameen

Kudin Haladu ya basa ya karba gida ya shiga ya bude kofar,

 da yake ya karbi key a hannun Khadija wanka yayi ya saka kayansa Jin ana  Kiran la’asar yayi Alwala ya lalube takalmin Sumayya ya fita dashi a hannunsa, masallaci ya tafi yayi sallah ya wuce asibiti duk zuciyansa ba Dadi ya rasa wajen wa zai tinkara da zancen kudi,, yasan Koh mutuwa zaiyi Yan gidansu bazasu taimaka Masa ba bare Sumayya matar sa,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


***Muna nan da Khadija har la’asar sallah mukayi dukan mu nurse tazo ta mayar mini da laidar ruwan a hannu na,

Na kwanta baccine ya dauken nabar Khadija na zaune,

Ya iso asibitin da sallama ya shigo dakin Khadija ta amsa masa.

Sannu yaya ka dawo?

Eh Khadija

Toh yaya ka samu kudin?

Wallahih Khadija sai addu’a naira 500 ne kadai na samu

Amma yaya ya kamata ka sanar da Aunty gaskiya don wallahih Yaya Ina Jin tsoro kaga ance appendix in ya kumbura fa tunda Allah Bai baka ikon samu ba, ka fada Mata ita sai ta biya?

Toh Khadija wallahih inajin kunya a matsayina na mijinta na kasa biya Mata kudin operation don samun lfyr ta,

Habba Yaya karfa ka manta Allah yaga zuciyar ka baka dashine Kuma ba abin kunya bane tunda itama tasan baka dashi,

Suna cikin Hira na farka a gigice Jin wani irin mahaukacin ciwon ciki ya tasarmin ” Innalilahih wainnailaihir rajuun wayyo Allah na cikina”

Subhanallah Sumayya cikin ne Al’ameen Daya Mike cikin tsananin tashin hankali yake lalubarta ,

Khadija ma da saurin ta ta iso ni,sannu Aunty take fada idon ta ya jika da hawaye

*****Nikam.na kasa Bata amsa kuka kawai nake hankali tashe

Khadija tashi kije ki Kira doctor eiiii sauri 

Toh yaya tace tana mikewa da saurin ta

Al’ameen Kam hannun Sumayya ya Kama sai sannu yake Mata a hakan likita yazo ya sameta a halinnan

Da sauri shida nurse suka rufu a kanta tare da K’ura Khadija da Al’ameen waje,allurai sukai Mata harda na bacci lokaci daya bacci ya dauke ta,

Khadija da Al’ameen na tsaye a  bakin kofa likita ya fitoh ya kira su zuwa office,

Malam Al’ameen majinyaciyar ka tana cikin condition Mai muni ya kamata ka samo kudin aiki nan da awa uku ba wallahih kome zai iyya faruwa,

 Innalilahih wainnailaihir rajuun kawai suke fada,

Suka mike zuka fita a office in Khadija Kam kuka ta fara abin Yama Al’ameen yawa ta Ina zai fara anya zai yafewa kansa kuwa in yar mutane ta mutu ata dalilin rashin kudin aikin da Bai samo ba,

Yaya ya kamata Aunty tasan abinda ke faruwa muje ka fada mata ta Kama hannunsa sukayi dakin 

Suna shiga suka samu Sumayya na bacci ……….

Yaya Ammar innan yazo baka nan  ya bawa Aunty kudi Amma Taki karba tace na baka 

Allah sarki Ammar yazo ne?

Eh yaya kana fita Yana shiga, yace ma Wai Daman Yaso kuyi sallama tafiya ne ya kamasa, na gaggawa,

Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari Yan kiyaye sa aduk inda yake,

Ameen yaya

 Khadija Miko min kudin na hada da dari biyar in hannu na naje na Basu Koh zasu mata daidai a Nemo sauran su bimu bashi,

Uhmm lallai yaya kadai San asibiti bata ma matum aiki ba tare da kudi bak’oh?

 Khadija bara dai naje na gwada Koh Allah zaisa a dace tunda kinga hour uku aka bamu kuma yanzun bacci take, bara naje na dawo ya fada Yana karban kudin da khadijar ke mika Masa,

Yana fita yaje wajen biyan kudi, 

don Allah Dan uwa kayi hakuri ga dubu goma da dari bayar a fara mata aikin in yaso za’a cikita muku daga baya Dan Allah ku taimaka min matatace ba lfy kuma hour 3 aka bani ake son mata operation?

Amma Kai *makahon* nan Ina ga baka zuwa asibiti ne taima?

Ina zuwa ranka shi Dade sai dai ban taba kawo majinyaci irin wannan ba

Toh gaskiya ka gannin nan Koh biyar naci a cikin kudin da nake karba wallahih Sai an daure ni

Kuma anan in baka biya kudiba wallahih baza’a Mata aiki ba Koh mutuwa zatayi gwara kaje ka Nemo duk in da kudi ya shiga ya fita shawara nake baka,Amma zance a taimaka maka toh hadai asibiti ba

Shikam tsabar damuwa har jiri yakeji yana ibansa ,a rayuwar yanzun in baka dashi kana ji kana gani harka mutu indai baka da kudin jinya ba Mai taimakon ka, zama yayi a bakin barandan pharmacy in yayi shuru cikin tashin hankali da alhini,

Bayan fitar Al’ameen khadija na zaune har lokaci hawaye baibar zuba ba sai ta gogi wani ya zuba, har  hour 1 yayanta Bai dawo ba,

*** A hankali nabude idona na sauke akan Khadija dake ta hawaye ido harya kumbura abinka da farin fata fuska tayi ja” khadija lafiya kuwa meya faru Naga kina kuka”??

Babu Aunty Daman na tsorata ne danaga cikin ki ya Tashi Ashe haka kike fama da Jin jiki sannu,

Murmushi nayi “haba Khadija Menene na kuka baki ga naji dauki ba” 

Toh Aunty,

“Yauwa khadija nikam likita ya fadi abinda ke damuna ne, Koh yake sani ciwon cikin nan”?

Kafun ta bude baki ma sai ga doctor ya shigo,Wai har yanzun baku samo kudin aikin ba Koh bakuji condition inda nace muku tana ciki ba Wai ina MAKAHON yake ne?

“Doctor ban gane mikake nufi ba” nace ina kallon sa?

Au baku fada mata bane? Yana kallon khadija alamar tambaya

Eh doctor bata sani ba khadija ta bashi Amsa,,

“Wai meke faruwa ne kun sani a duhu” waza’a ma aiki??

Kece appendix ya kumbura sosai tun jiya na sanar dasu Amma haryau shuru Basu biya kudiba yanzun haka  hour 3 na Basu su kawo kudin Dan kina bukatan aiki  gaggawa Amma an share hour 1  shuru, Banga alaman zasu biya ba

Da mamaki nake kallon khadija”yanzun khadija Ina fama da wannan babbar matsala irin wannan Amma kuke mini Wasa da rayuwa Ina da kudin da Zan iyya biya ba bandashi ba”

Kiye hakuri Aunty Daman Yaya ne yace shi yake son biya

” Koh ance lallai sai yayanki ne ya wajaba ya biya ai ni Karan kaina nasan Bai dashi don Bai biya ba ai bazai  zama wani abu na daban ba” menene riban ya fita yana neman bashi alhalin Ina da kudi”??

Kiye hakuri Aunty,ta fada jikinta a sanye ganin Raina ya baci

“Nawane akace kudin aikin”?

……50k ne

“Khadija tashi ki dauki key kije gida ki dauko mini jakana  wani yellow a cikin whtdp nawa ki dauko mini jakan akwai kudi a ciki”

Toh Aunty ta fada tana mikewa daukan key in tayi a jakan kayana ki hadamin da wayata ki dauko darduma babba da filo, ga kayan da nacire ma kikai mini gida kisa a basket in bayan kofa”

“Kihau nepep   ya kaiki kofar gida ki shiga in kin dauko kudin saiki shiga ya dawo dake ki basa 1k ya d’auki kudinsa karfa kice Zaki tafi da kafa”??

Toh Aunty ta d’auki  kayan nawa ta fita  a dakin, doctor Kam Dan kallo ya zama Daman tun da ya ganni yake ganin alamun Jin Dadi a tare Dani Amma abinda ya daure masa Kai mutanen da suka kawo ni asibitin abin yana bashi,mamaki harda Nurses Amma basuga fuskar tambaya ba

**komawa nayi na kwanta shima doctor fita yayi

 

Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Whatsapp Number 08138873799

Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents

Tsabar rudewa Khadija Koh yayanta Bata Lura dashi ba akan baranda ta wuce,

Shikam ganin lokaci na wucewa yasa ya Tashi ya shigo dakin,da sallama a bakin sa,

**Amsa Masa nayi Ina kallon sa yazo ya zauna a kujiran gefena,

 Sumayya,yakira sunana

“Na’am” na amsa Masa 

Kiye hakuri Sumayya na kasa kula dake wallahih nayi iyya kokari na Amma ban samu kudin ba Daman appendix ne ke damunki Kuma ya kumbura, shine ake son Miki aiki kuma……..

**Da nayi niyar rufesa da matsifa Amma sai jikina yayi sanyi Jin bayanin da yake mini” ban bare ya karasa ba na katse sa”ba kome, me amfanin Ina dashi kaje kana,.. baran attaimaka maka kazo ka biya mini kudin aiki”? Karka sake mini irin wannan banaso duk abin da zai taso a waje na Koh Khadija Koh Kai, in baka dashi  karka sake zuwa gun wani da sunan ya taimaka maka indai abin baifi karfina ba pls”

Kiye hakuri insha Allah bazan sake ba,

**Shuru na Masa

Jin Bata amsa ba ya sashi yin shuru

Khadija na Isa gida ta samu jama’a na cike a kofar gidan dam alamu dai wani  abinne ya furu don harda motar police ga jama’an unguwan makil……………

Shigowa d’akin nayi cikin hanzari na karasa kusa da abie na banyi wata wata ba na rungume sa na fashe da kuka maicin Rai,,,,

Ji kawai nayi momy ta dakawa abie tsawa,

Kai Abdulsalam mainace maka akan yarinyar nan?,

Ai da sauri Naga Abie ya hankad’ani a jikinsa ya mike tsaye cikin wani irin hada fuska Wanda. Bansan abiena dashi ba Naga ya mike cikin hargage yake magana Sumayya fita a dakin nan banason ganin ki banace Miki bake bani ba Koh bance ki zauna a dakin kiba,

“Abie Kai nazo gani don Allah Abie Koh kowa zai juyamin baya Kai karka Bari a rabamu don Allah Abie,” nace Ina fashewa da kuka,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Waye uban naki?? keh daga yau niba ubanki bane bansan wata y’a Sumayya ba kaf zuriyan shugaba babu yarinya Mai suna Sumayya ki fita a gidan nan da zuriyan mu bake bani Koh mutuwa nayi banason ganinki akan gawata,yace idanunsa na taruwa da hawaye daga Gani dai maganar fatar bakine bana zuciya ba,

“Amma abie menene nai maka da har zaka yanke dukkan alakar ka Dani har haka atunani na Koh kashe mutum nayi bazaka yanke alaka Dani ba abie ka rabani da mahaifiyata tun bansan kaina ba yanzun Kuma ka sallamawa duniya ni” wa nake dashi in ba kaiba kaf duniya nan abie why Abie why”😭😭?? 

Nafada Ina kallonsa gani nayi hawaye nabin fuskar sa,ya daga ido Yana kallon momy,

Toh munafuki kallon me kake mini,Ke Kuma wuce ka sata a  gaba tabar Mana cikin gida yanzun,

Nikam mutuwar tsaye nayi nashiga uku yaushe abie ya zama haka zaushe ya koma  yaron momy,abie da na  sani ne kuwa kafun na bar gidan nan Koh maganar banxa momy Bata Isa tamin a gabansa ba bare yau har tana basa umurni  ya koreni,

Ban farga ba naji an janii kiiiiiii!!! Anyi hanyar steps Dani,

Cikin mamaki nake kallon abie yau ni yake ja Kamar wata saniya zai koreni a gidan sa lallai fa,

Jana yake tayi har Muka sauko falo abin gwanin tausayi,nikam kuka nake Kamar Raina zai fita gabaki d’aya naji duniya tamin zafi,

Ganin abie ya nufi kofar fita falo Dani yasa Khadija tasowa ta biyomu a baya Yan falonka da ido suka bimu wasu na dariya ganin yanda uba ke fincikar yarsa 

Fincike hannuna nayi na dawo cikin falon na tsaya a gaban babuji  (kanin babana) ” babuji abani ducument Ina, Ina bukatar su,”

Don ubanki lokacin da uwarki ta haife ki da results ta haifiki ne,,,,,

Don haka baza’a bayar ba koma bara ma kiji daga yau Koh a kasuwa ne karki sake hada sunanki da family shugaba,

“K’warai  kayi gaskiya babuji ba’a haifini da results ba Amma da kudin ubana na same su in Kuma hassadace yasa kuka k’wace karfa ku manta arziki nufin Allah ne in Allah ya tsaga da rabonka  sai kayi arziki ruwa da iska Koh guguwa bazai Hanaka samuba”,

“Ba karatu bane kadai abinda ke sa bawa arziki rabonsa baya wuce kansa”

“Baiwa ta jarina”sannan wannan tsinannen gidan naku wallahih ku rubuta ku aje sai yafi muku prison ganin………………

Tassss naji saukar wani azabebben Mari  a kumatu na Wanda yasani sumar wucen gadi,ba kowa bane yamin Marin nan sai sahabi yaron babuji,

Ke karamar Yar iska watoh kema harkin zama Yar bariki irin mutanen gidan da kike Koh zakizo nan ki gwada Mana kin falle toh baki Isa ba ki tsaya kina gayama ubana magana in barki ya fada Yana fincikata juyawa nayi Ina kallon abie Wanda ke tsaye kansa a duke,

 Bai tsaya aku Ina Dani ba har Saida ya dangana da get turani yayi waje Yana ma Mai gadi warning daga yau in ya sake barin Mai Kama Dani ya shigo gidan nan a bakin aikin sa,Yana fadan haka ya juya abinsa yayi cikin gida, ya dauko jakana da takalmi ya watso mini a jiki,

Baba buzune ya fitoh yazo inda nake zaune tunda ya jefoni ban matsa ba mamaki tsoro da kuma wani irin tsana naji ya tsargan mini na family mu duka ban cire kowa ba, aciki nayi alkawari daga yau na yanke duk wata alaka da shugaba family house,

Kayi hakuri yaro haka rayuwa take kaji,

 kayi zaman auren ka ka rike mijinka Allah zai baka mafita kaji hajiya Sumayya,kayita addu’a kaima Allah ya tsareka gidan nan yanzun sai abinda matar babanka yace,

ya fada cikin tausayi,nidai Ina duke dakai sai kuka nake inda Allah ya Soni ma unguwan mu ba irin sintali bane nan kowa na cikin gidan sa Babu mutane a waje,

Jin ana kamani anason mikar Dani yasa na daga kaina Khadija ce wance bansan yaushi ta fitoh ba ,Ashe tun Marin da aka kwada mini ta ruga tayi waje tazo ta Saya,…

*******””””

Banyi musu ba na nike tsaye Kayana ta hau karkade mini nidai sai kuka nake Kamar zararriya gashi bamuda Koh sisi da zamu tare abin Hawa ya kaimu gida gashi Koh a gidan  ma bani da kudin da Zan biyasa Kuma banda tabbacin yayan Khadija na dashi, yasa na Kama tafiya da kafa Ina kuka,

Dukawa Khadija tayi ta dauki jakana Dana Bari,sai hakuri take bani Amma nai Mata banza a haka muka fara fasa hanya,

Mota na gani Tasha gaban mu tayi packing Abdul ne ya fitoh a ciki ya nufe mu,

 don Allah Sumayya kiye hakuri da abinda kikaje Kika tarar a gida wallahih yanzun gidan mu sai addu’a abin sai gaba gaba yake, Kuma na rasa me yasa duk gidan mu ke suka tsana,

*****Kala bance Masa ba don shima wani tsanar sa nakeji a Raina Sam yanzun naji banason ahalina kwata kwata na yanke duk wata alaka dasu daga yau Kamar yanda Suma suka yanke Dani,

***Kaucewa nayi na fara tafiya bance Masa kala ba,

Biyo ni ya sake Yi Yana mini magiya, Sumayya don Allah badon ni ba kizo ki hau na kaiki gidanki Kinga yamma yayi bazaki samu Keke napep ba anjima anan,

Wallahih Abdul Ina Ganin kimarka Inka kuskura ka kaini bango Zan maka abinda bazaka manta Dani ba Kai asuwa zakazo ka tsaya kana bani umurni wallahih daga yau Babu ni Babu Kai Koh a hanya ban sanka ba na tsaneku mugaye kawai azzalumai wallahih ku jira karshin ku,

Habba Sumayya menene laifina in sun Bata Miki ni meyasa Zaki had’a Dani,..

“Ai Wanda suka Bata mini su waye ne a gunka”?na tambaye sa Ina kallon sa ido cikin ido,

Iyayen  mune da Yan uwan mu,ya bani Amsa,

“Iyayen kadai da Yan uwanka daga yau bana D’aya daga cikin family shugaba  in baka sani ba ka sani yanzun ka fita harka ta “

Sumayya kada bacin Rai yasa ki ringa furta maganganu da Basu dace ba,

“Na furta Abdul Koh kaima dukana zakayi” na fada Ina wuce sa

Shikam mamaki ne yake son kashesa Anya Sumayya da ya sani ce wannan shuru shurun ashe haka take ganin bazata yarda tahau motarba yasa ya zare kudi a Aljuhunsa ya mikawa Khadija gashi Yan Mata kuhau Keke Koh ya fada Yana duban Khadija,..

“Wallahih Khadija Kika karbi kudin nan sai na nuna Miki true colour na”

Khadija Kam ta tsorata da sauri tayi gaba kamar yanda taga nayi,

Muka barsa a tsaye kamar gunki,

Tafiya muke har lokacin hawaye baibar zuba a. Idanuna ba wani irin zafi nakeji a Raina a haka muka ringa fasa unguwa unguwa muna wucewa tafiyarda tunda nake. Bantaba yin irinsa ba yau shi nake kafafuna duk sun kumbura na rashin sabo, Amma yanda zuciya ke cina Bai bare naji wahalar ba, Khadija kam Koh a jikinta,

Har mangariba yayi bamu ma kusa Isa sintali ba

   Aunty Koh zamu tare kekene in munje gida Yaya ya biya Kinga fa mangariba yayi ga hadari sosai? Khadija tace

Kala bance Mata ba tafiya kawai na cigaba dayi don nasan Koh na hau munje bazamu samu kudi ba tunda cinikin nasa duka ya hada ya bani Ina zai samu wasu dari da hamsin,

Tafiya mukaci gaba dayi ga yunwa don rabona da abinci tun ruwan shayen safe Amma bacin Rai baisa naji ba har aka Kira Isha adaidai lokacin aka fara yayafi sai ruwa ya sauko Kamar da bakin k’warya ganin mun iso bakin kasuwa yasa ban tsaya wani labewa ruwa ya dauke ba tunda dare ne Babu Wanda zai gane mu gashi NEPA sun dauke a haka ruwa na dukan mu muka shiga sintali hanyar gidana muka nufa tun daga nesa Muka hangesa 

Al’ameen ne a tsaye a kofar gida ruwa na dukansa daga ka gansa kaga Wanda hankalin sa yake tashe,

Muna Isa Khadija ce ta fara Masa magana nikam cikin gidan na nufa don bana bukatar Jin kome,

Yaya ya Naga kana tsaye a cikin ruwa haka gashi duk ka jika lafiya Kam?

Ina Naga lfy Khadija baku dawo ba Ina Aunty take Allah dai yasa Yan gidan su basuce bazata dawo ba wallahih naji tsoro Khadija karsuce zasu rabamu?

Hhhh habba Yaya bafa wani abu da zai rabaka da matarka insha Allah sai mutuwa Kama daina mugun tunani irin wannan,

maganan dadewa Kuma abin hawane bamu Bamu ba da wure, shiyasa naso ma mu kwana Amma Aunty tace mu dawo kar hankalin ka ya Tashi(Tamar karya don ya kwantar da hankalin sa)

Shap in kuka kwana ai nashiga uku kenan ,

Amma me yasa baku Kama hanya da wure ba kuka bare sai yamma kuka fitoh,gashi ruwa ya muku duka,

..Kai Yaya abinci fa muka tsaya muka ci,

Yauwa Yaya kasan me yau ran aunty a bace yake don Allah ka bita. A hankali inda Hali ma karka Mata magana yanzun ka Bare sai da safe ka Mata magana in ma kaga change a tare da ita ka Mata uzuri,

Meya faru Khadija?

Ba kome Yaya kawai dai sun D’an samu matsala da yaran gidansu ne sai Randa ya baci,

Bai yarda ba don yasan halin Khadija akwai surutu akwai boye abinda ba’a sata fada ba,shiyasa kawai ya shanja zancen,

Toh khadija muje ciki in ruwan ya tsakai ta sai na raka ki gida

Ah ah Yaya dare yayi fa yanzun ana neman 8:00 na dare nikam Zan koma Goggo zatayi fada,

Muje na rakaki gida  sai nama  Goggo bayanin dalilin jimawar ki karta Miki fada,

toh yaya,ta fada tana Kama hannunsa suka nufi layin su Goggo Amina,

Nikam Ina shiga cikin gidan da yake ana ruwa ba kowa a tsakar gida shashen mu na nufa,aje jakana da  takalmi nayi a baranda na kwabe lufayar jikina da yajika jakaf da ruwa na makala a igiya,

 dakin na shiga nadau towel na daura na zame  dogon wando da NASA   da under wear na makala a igiyar kofa ,

Kitchen na shiga na kunna gas na daura bojuwa (tukunya) na zuba ruwa a ciki,boket na dauko na ibi ruwa a Randa na tsaya a cikin kitchen in ruwan na tafasa na juye a boket in daidai yanda zanyi wanka na dauki boket in nayi bandaki,wanka nayi  na fitoh,har lokacin ruwa ake Alwala nayi,jakana na dauka a baranda na shiga dakin,

 Jin dis dis Kamar panfo yazo daukewa yasa na lalube  wayata  a jaka na haska dakin idona ya sauka akan kujiran da yayan khadija ke k’wanciya  ya jika jakaf da ruwa  saitin wajen na yoyo fita waje nayi da sauri na d’auko baf nazo na tare ruwan,kaya na dauka na bacci na saka da hula harda socks don wani irin sanyi nakeji har cikin k’ashina sallaya na shinfida na Tada sallah mangariba da Isha nayi shafa’i da wutire ,

blanket na dauko nahau gadon na lullubu abina na kwanta da wani irin ciwon Kai da zazzabi nakeji gashi kafafuna sai zuge suke mini nama rasa meke mini Dadi 

Al’ameen suna tafiya da Khadija Chan dai Khadija ta kasa hakuri tace ,Yaya nikam na tambaye ka Mana?

Allah yasa na sani dija,

Kai Yaya ni banason dijan nan ai sunan tsofine,

Toh hadixa Ina jinki,

Habba yaya ta fada tana hada fuska,

Sorry toh kanwata Ina jinki

Yauwa Yaya nikam Aina ka hadu da Aunty Sumayyan ne harkace kana Sonta?

….Dam dam haka gabansa ke bugawa , Khadija meyasa Kika mini wannan tambayar,?

Ba kome Yaya kawai na tambaye Kane ,

Ah ah Khadija fad’amin gaskiya nasan baki tambayar Abu banza,

Am Yaya Naga baka taba bani lbrn kana da budurwa ba kawai sai naji Wai kayi aure za’a kawo Amarya,

Toh Khadija ke abokina ne da saina fada Miki Ina da budurwa,

 auren Kuma yazone a bazata ban dauka iyayen ta zasu bani ita lokaci d’aya ba, 

Amma yaya kaga gidansu aunty kuwa Mai azaban kyau ga Yan gayu k’yawawa  a gidan Kuma Aunty ma kyakkyawa fa Yaya toh ma  Ina kake zuwa daga Tashar kayan marmari sai wajen sana’ar ka Ina kaga aunty har kuka fara soyayya?

Ikon Allah Khadija Wai tambayar nan Kam na lfy kin sani a gaba da tambaya sai kace wani sa’anki ,

Kayi hakuri Yaya dai dai lokacin suna iso kofar gidan Goggo Amina,

Muje Khadija na rakaki cikin gidan nama Goggo bayanin dalilin yin darenki ,

Toh Yaya ,

shiga sukayi cikin gidan tare,

Goggo Amina ce ta amsa sallaman tasu tana fama da icce a runfar girkin ta

Isa sukayi ya gaishe da ta Yamata bayanin dalilin yin Daren Khadija,..

Wallahih Muhammad Nima sai da na tura yaro yajimin lfy Khadija har dare Bata dawo ba ga aikin dare da tace zata dawo ta Kama mini, ya dawo yace min ba kowa a shashen ku,

Kiyi hakuri Goggo, Basu dawo ba sai yanzun Al’ameen yace Yana mike wa,

Ba kome muhammad  shine ka tasata a gaba a ruwan nan Maimakon ku bare Sai ya tsakaita,

Goggo Nima haka nace Mata Amma tace Zaki Mata Holo itakam sai gidan Goggo shine na rakota

Gggo ruwan da yawansa bansan karfe nawa zai dauke ba  shiyasa nace gwara na dawo

 

Hakane Kam  da gaskiyar ki Khadija

Toh sai da safe, Goggo Allah bamu alkhari

Ameen suka amsa ita da Khadija shikam fita yayi ya Kama  hanyar gida,

Ina kwance Amma ba bacci nake ba tunani kawai na fada  nayi zugum gabaki daya gari yamin zafi,

daidai lokacin ya shigo kofar duk ya jike Daman jallabiya ne a jikinsa ,,

 hauro wa dakalin  Yayi ya zare jallabiyar sa ya aje a cikin boket in wanka dakin ya shigo daga shi Sai gajirin wando, da sallama a bakinsa

Ina kwance cikin duhu don na kashe hasken wayana naji buruntu ana kokarin shigowa dakin  don ni Sam banji sallamar ba, hasken wayata na kunna me Zan gani yayan Khadija ba Kaya, murd’adden damtsen hannunsa naci Karo a waje ga fafad’an kirjinsa mai cike da yalwan gashi,baki sitik kwance akan farar fatarsa kafarsa farare tas sai gashi ke kwance a lallausar fatar kafar tasa ai bansan lokacin da na k’wala ihu ba na dirko a saman gadon,na Kama hanyar waje don ni sai ma gani nake kamar ba wando a jikinsa don ajike wandon yake tsabar birkita hanyar kofa na nufa zanfita na bar Masa dakin,

Jin ihunta sai ya birkitasa ya dauka Koh wani abune ya sameta Jin ihun take  akai akai hakan yasa ya gigice shima ya fara neman hanyar kofa cikin lalube,da D’an saurin sa Jin itama kofar ta nufo tana  ihu har lokacin,

Ji kake gauuuu! sun garu da juna a kofa daga shi har ita ihu suka saka a tare, sai kawai suka kuma zubuwa ji kake timmmmmmm…………

Back to top button