Mallama Juwariyya

Yadda Zaki Gyara Budurcinki Cikin Sauki.

YADDA ZAKI GYARA BUDURCI KI:

 

MENENE BUDURCI?

 

Assalamu Alaikum Warahmatullahi wabarakatuhu.

 

Wannan wani darasine mai muhimmanci da ya kamata mutane su sanshi musamman samari da yan mata, amma da zaran an fara irin wannan sai a kama jin kunya, ko shi mai koyarwar ya ji kunya ya ki yin bayani yanda ya kamata ko su masu sauraro su sa kunya su qi nutsuwa su koya. Don haka ya kamata mu gane wurin neman ilimi ba a jin kunya.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Nana Aisha (RA) tace: “Madalla da matan madina wadanda kunya bata hanasu tambaya game da abinda ya shafi addininsu ba. ”

 

Sannan a wani hadisin Ummu Salamah tace ma Manzon Allah (SAW ) “Lallai Allah baya jin kunya game da gaskiya. Shin akwai wanka kan macen da tayi mafarki?” sai yace “Eh! idan ta ga ruwa (ma’ana idan ta fitar da maniyyi)”. [Bukhari da Muslim].

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Indai wurin neman ilimi ne musamman ma na gyaran ibada da rayuwa to ba a jin kunya. Wannan dalilin ne yasa naga ya kamata na yiwa yan’uwana wasu bayanai akan budurci, bayani ba irin na posts na rashin kunya da batsa ba da suke yawo a social network. A’a bayani akan yadda budurci yake da darajar budurci don yan mata su san me suke dauke dashi.

 

Allah cikin ikon sa da tsari na halitta Irin naSa Yasa kowace mace da budurci ake haifanta, shi ake kira da “HYMEN” A turance.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Ita dai HYMEN wata fatace mai dauke da jini a cikinta tana farjin kowace mace amma ba tada wuyar fashewa. Sannan ba wai hymen bane kadai a cikin farjin mace ba a’a. Akwai fata biyu sune LABIA MINORA da VESTIBULE Su wainnan sune suke farjin mace amma shi ainihin budurcin yana daga ciki, ma’ana kenan sune suke kare miki ainihin budurcin ki na ciki.

 

Shi wannan zafin da ake ji lokacin jima’i na farko sune suke budewa suke fitowa da jini, Sune idan babu su to zaki ga babu wannan jan jinin a jima’in farko saboda sun rigaya sun narke ne a gabanki, sai ya zamana koda kin yi aure mijin ki ya sadu dake to zai ga baki fitar da jini ba sai ya dauka ko kin taba bin maza ne, bayan kuwa ke baki taba yi ba, kuma mata dayawa suna shiga cikin matsala saboda mazan su suna jin su a bude yayin da suka shiga gidajen auren su.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Sannan su wainnan fatan uku ba makawa idan daya ya yage a cikin su to dukkan sauran zasu yage, don ita ba tada karfi, kuma yawan kai hannu wurin zai bude shi. Mafiya yawan yan mata suna loosing virginity nasu ba tare ma da sun sani ba, saboda wasu abubuwa kamar haka:

 

1. Guje guje da tsalle tsalle, da tafiya da sauri kamar gudu koda yaushe.
2. Rawa mai karfi ko motsa jiki mai karfi.
3.Bude kafa, ya zamana mace tana zama da karfi sosai, kuma kullum in ta zauna zata bude kafa, bata kama jikinta.
4.Hawa bishiya, da keke, da daukan abu mai nauyi.
5.Tsallake rami mai fadi sosai ko yin abin da zai sa sai ta bude kafanta sosai.
7.Nishi mai karfi.
8.Magana ko ihu mai karfin gaske, don akwai mata shashashai, ita mace tana magana ne with class da kamala irin ta mace.
9.Yawan saka hannu a wurin na rashin dalili.
10.Dadewa ba aure da yawan shekaru ma yana sa mace ta rasa budurcin ta.
11. Mikewa tsaye da karfi, idan zaki mike tsayema ya kamata a matsayinki na macce ko matar aurece ki yishi a nutse balle budurwa da tasan darajar ajiyar ta.
11.Wata kuma budurwar yawan cushe cushe ko matse matsen abubuwa da yawan sit bath ba tada aure zai iya kawo kaucewar budurcinta.
12.Sannan wasa da kansu da wasu mata ke yi saboda matsanancin sha’awa gashi ba su da aure, yana kawar musu da budurci. Dama sauran su.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Kenan dole ne ki fahimci matsayin ki na mace budurwa, kuma ki dauki aniyar gyarawa, Idan ka tattauna da matan aure da dama zasu ce wallahi idan har namiji ya sami mace budurwa to ta riga ta gama amsan ma kanta girma da daraja, kuma duk lokacin da yaso ya ci mata mutunci zata tashi tsaye tace kasan dai yanda ka same ni, ni ba mutumiyar banza bace, suka ce sai ka ga sun shiga hankalin su, saboda sun San ke mai mutunci ce.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Back to top button