Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 54 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E54

Hawayene suka cicciko idanuwanta, ta soma girgiza kai tana ja da baya, kafin ta juya da gudu ta koma É—aki ta haye saman gado, hannayenta toshe da bakinta, gudun kada masu bacci su farka sakamakon jin sautin kukanta, gani take kamar amafarki komai ke faruwa, zuciyarta har wani tafarfasa take yi, wai haka ma don batasan me, su ka yi ba acikin toilet É—in, kawai ranta ne ya bata cewar wani abu ya shiga tsakaninsu, Zuciya ta gama tunzurata, Atare suka shigo cikin dakin, Unaiza ta wuce saman gadonta, ta haye ta kwanta tana faman sakin murmushi, Danish kuwa Yana tsaye bakin Æ™opar sashen toilet dinsu, Wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarshi, Sam baison angel tace za ta yi fushi dashi, baisan dalilin dayasa take yi mishi wani irin kallo ba, DaÆ™yar ya motsa ya nufi gadonta, A hankali ya zauna daga gefen gadonta, muryarshi na rawa ya ambaci sunanta”Angel” kamar jira take yi, ta É—ago idanuwanta jawur ta shaÆ™i wuyan rigarshi, ta runtse idanuwanta, taci burin ta zazzaga mashi masifa harma ta mare shi amma sai ta kasa, Numfashinta na fita da hucin zafi ta ware gray eyes É—inta akan fuskarshi, muryarta adisashe ta furta”me namaka Danish? dana cancanci irin wannan Æ™untatawar, ka faÉ—a min me ku ke yi acikin toilet tsawon lokacin nan kai da ita”?
Muryarshi na kerma ya furta”koda bazaki yarda dani ba, zan faÉ—a maki gaskiya, ta nemi alfarmar tana so ta kwanta ajikina tayi bacci saboda tana tunanin zata samu relief na zazza6in da take ji, shine nace mata bakomai, tsawon time da muna a toilet tana kwance ajikina, tana bacci, sai yanzu tafarka…….’ daÆ™yar ya Æ™arasa maganar ganin irin kallon da take yi mishi, acan cikin zuciyarta 100% ta yarda da maganarshi, saboda tasan halinshi sarai, bazai ta6a yi mata Æ™arya ba, ku ma koda ace sun aikata wani abu to kuwa tabbas idan ta tambaye shi zai faÉ—a mata gaskiya ne koda zata kashe shi,

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa a jere, batare da tayi tsammani ba, taji saukar hannayenshi saman fuskarta, Yana share mata hawayenta, harara ta É—an jefa mishi tare da cewa”kada ka yi tsammanin saboda kai nake zubar da hawaye na,” Æ™ayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, yace”nasani, amma faÉ—a min meyasa ki zubar da hawayen ki” yatsina fuska tayi still bata daina hararar shi ba tace”haushinka nake ji, É—azu kamar in shaÆ™e ka, saboda me zaka nuna ni da yatsa kana min faÉ—a akanta? Bayan itace bata da gaskiya bani ba” cikin sanyin murya ya furta mata”Am sorry bazan Æ™ara ba” gyaÉ—a kai tayi kafin ta kuma cewa”daga yau idan har kana son zaman lafiya, kada ka Æ™ara yarda ta ta6a jikin ka, ko kallonta bana son yi,” mamaki akan fuskarshi yace”why”? Harara ta wurga mashi”saboda bana so Danish, bana son ganinka da ita, inaso kayi min alÆ™awarin hakan” shiru yae bai bata amsa ba, nan take taji gabanta ya É—an faÉ—i,

“Ba zaka Iya É—aukar min alÆ™awarin hakan ba ko”? Ƙura mata kyawawan idanuwan shi yae, ba tare daya furta komai ba, ta6e baki tae idanuwanta suka cicciko da Æ™walla tace”nasani dama ae, kana sonta ne shiyasa kake liÆ™e mata,” girgiza kai yai muryarshi a tausashe yace”Ki daina tunanin hakan, dalilin dayasa bazan É—aukar miki alÆ™awari ba, saboda ina son kowannan ku, mu tamkar Æ´an uwa ne, bazan iya raba alaÆ™a da waninku ba, sai dai inyi Æ™oÆ™ari wurin ganin na haÉ—a kanku, ke da ita,” fuskarta a daure tace banso, ka tashi ka bani wuri idan har bazaka min alÆ™awari ba,” Ƙin miÆ™ewa yae sai ma ya ruÆ™o hannayenta acikin nashi yadan matsasu, Yayin da idanuwansu ke kallon na juna, ya rasa gane dalilin dayasa take so ya yanke alaÆ™a da Ƴar gidan daddy, magana ya soma yi atsakane”Its okey, zan yanke alaÆ™a da ita, amma bazan iya daina kallonta ba, saboda ni tana burgeni, tana da abunda baki dashi, wanda yake jan hankali na, ” Ras! taji gabanta ya faÉ—i, shi kanshi baisan ya akai maganar ta su6uce mishi ba, a matuÆ™ar ruÉ—e take bin shi da kallon mamaki da Al’ajabi, Yau dai ta tabbar da cewar Danish mutun ne, ba kamar su haris fa, yasan me yake yi, kalamanshi sun tabbatar mata da hakan,

“Am sorry angel, am sorry bana nufin na fusata ki, na faÉ—a maki ne saboda kema kiyi irin nata, saboda in dai na kallonta” Kamar sakarya hake take binshi da kallo, Tsabar mamaki Ya hanata tayi motsi, ta koma kamar gunki, idanuwanta ko Æ™yaftwa basa yi, su kaÉ—ai suka rage acikin É—akin basu runtsa ba, Hatta Æ´ar gidan daddy ta jima da yin bacci abunta, ta baje saman gado tana sharar murshari, kamar jaki,

“Angel, kinyi shiru baki ce komai ba,” muryarshi a araunace yayi mata maganar, wani irin wahalallan miyau ta haÉ—iya, zufa ta ko’ina ajikinta duk irin sanyin da ke akwai, da Æ™yar ta daidata natsuwarta, ta kalle shi da kyau, damuwace Æ™arara akan fuskarshi, jinjina kai ta É—anyi muryarta Æ™asa Æ™asa tace”Shikenan, Amma ni bani da hanyar da zansa su fito a Æ™irjina, zan dai yi addu’ar Allah ya bani su, yanzun ma da kaga bani dasu saboda ban kai lokacin yin sun bane, tun da nima macace kamar ita, zasu fito minne,” ajiyar zuciya ya sauke jin abunda tace, hankalin shi har ya kwanta, don shi har ga Allah burge shi suke yi sosai,

Murmushi ya É—an saki, Yana kallonta yace”Yanzu zamu fara Æ™irga time da zasu fito miki kenan”? Girgiza mashi kai tayi”a’a, basai mun Æ™irga ba, Allah ya riga dayasan lokacin daya dace dani,” jinjina kan shi yae”i will wait for the time……” bai Æ™arasa maganar ba jin yadda ta kwashe da dariya, Har fararen hakoranta suka bayyana, mamakine ya kama shi, Ko me ya bata dariya? Tsagaitawa tayi da yin dariyar tace mishi”kaje ka kwanta, ka huta,” ya amsa mata da toh, ya miÆ™e ya wuce gadonshi ya kwanta suna fuskantar juna, kowa da abunda yake saÆ™awa acikin zuciyarta, bakomai ne yasa ta yin dariya ba face imagining da tayi wai gata nan da abubuwa manya manya fiye dana unaiza a Æ™irjinta ne, Shine ya bata dariya, Can kuma ta koma tana tunanin wai me yasa suke burge shi? Sannan kuma idan suka fito mata Æ™irjinta to mexai yi dasu? Ita dai a iya saninta Na baby ne da ake shayarwa, ”

Da wannan tunanin bacci yae awon gaba dasu, É—akin yae tsit baka jin hayaniyar komai saina sautin minsharin su parveen maji dadin bacci,

tsakar dare Angel tafarka, ta dinga addu’a tana roÆ™on Allah akan yabata abun arzikin nan wanda yafi na Unaiza, hada Æ´ar Æ™wallarta, itafa bilhaƙƙi so take itama su fito mata, ko dan saboda Danish ya daina kallon na Æ´ar gidan daddy, ya koma kallon nata,

ƙuruci dangin hauka🤣

tun lokacin da Danish ya É—aukar mata alÆ™awari bai Æ™ara kula Unaiza ba, gashi ta nace mashi, ko toilet ya shiga sai ta bishi, idan yana bacci sai dai yajita a jikinshi tana lalubarshi, ta zamar mashi masifa, Da angel ta lura da hakan saita koma tana bashi kulawa ta musamman, Ta sanya mishi ido sosai, Idan suna cin abinci unaiza tana kashe mashi ido, sai angel tace mishi ya tashi ya koma saman gado zata kawo mishi abincin shi yaci acan, da yake yana son farin cikin ta, ga kuma alÆ™awari da aka yi mishi na abubuwa idan sunfito, shiyasa yake bin umarninta sau da Æ™afa, idan dare ya yi zasu kwanta bacci, Angel bata runtsawa gefen gadonshi take zama tana bashi labarai masu daÉ—i har sai bacci ya É—auke shi, kafin ta koma tana Yin addu’o’inta na dare da saba yi, Idan ya tashi zuwa toilet da kanta take raka shi ta tsaya abakin Æ™opar har sai ya kammala ya fito tukunna su ke komawa É—aki atare, hakan ba Æ™aramin Æ™ona ma Unaiza rai yake yi ba, angel ta toshe duk wata Æ™opa da zata haÉ—a ta da Danish, taÆ™i samun yarda take so kamar tayi hauka, yarinyar ba Æ™aramar jarababbiya bace, Idan abun ya motsa da kanta take Amfani, Saboda tsabar shaiÉ—anci, hatta su Haris saida taso su bata haÉ—in kai, a Æ™arshe taci ubanta hannun Naufal, saboda bai É—aukar raini, Ta addabi rayuwarsu, Wani sabon shaiÉ—ancin saita koma tana binsu Azeeza tsakar dare saman gadajesu, tun arana tafarko data fara yi musu hakan suka tarar mata, dama angel ta faÉ—i musu cewa mayyace kuma idan suka bari ta ta6a jikinsu to zata shanye musu Jinine har sai sun mutu, tsoro ya kamasu, shiyasa aranar su kayi mata bugun mutuwa, a Æ™arshe suka kulleta Cikin toilet, Ta dinga kuka tana faÉ—in su buÉ—e mata Æ™opa bazata Æ™ara ba, amma suka Æ™i buÉ—e ta, babu ci babu sha Yinin ranar, sai tsakar dare ne suka je suka buÉ—e mata Æ™opa, a Æ™asa suka sameta kwance tana fitar da numfashi sama sama, Angel ta ciko bokiti da ruwa suka sheÆ™a mata shi a jikinta, sharkaf su ka jiÆ™a ta, ta dai ci baÆ™ar wahala awurinsu, dama masu lallashinta haris da Danish ne to duk sun fita sabgarta, shiyasa su angel suka samu damar koya mata hankali, Sai gashi tafara yin hankali ta koma tana jin shakkarsu, bata Æ™ara gigin ta6a wani acikinsu ba, Sai dai har yanzu bata daina yi musu gorin Æ™irji ba, idan rashin kunyar ta motsa haka zata dinga yada musu habaici acikin É—aki babu mai tanka mata, kuma duk da haka bata hakura da Danish ba, dama kawai take jira da zata ke6e dashi.

idan muka koma 6angaren Majnun, Babu abunda ya sauya, Mahaukaci ne na gaske, 6arnar daya Æ™ara yi musu wadda ta gigitasu, Aranar sun taru aÉ—aki Gabriel Yana koya musu rawa, da yake ya iya sosai, Ba Æ™aramin daÉ—i suke Ji ba, sun dage suna ta tiÆ™ar rawa iri iri, Ashe Yaron nan Ya gudu Zuwa toilet É—insu bai nufi ko’ina ba, Sai Wurin tukunyar fulawar nan, Yasa Hannu Ya tsige furen Batool dana daddynta, Hada Na aneelerh, ba zato ba tsammani sai gashi ya faÉ—o É—akin hannun shi ruÆ™e da su Yana FaÉ—in Wai su kalli Ya curo musu shukokinsu, hankalin su yae matuÆ™ar tashi, musamman angel, gani suke kamar ya kashe rayukan masu Furennin ne, ransu ya 6aci sosai, da gudu suka nufe shi da niyar su buge shi, da sauri ya juya shima ya watsa a guje Ya shige Cikin toilet É—in, da yake mahaukaci ne, Ya buÉ—e murfin trash can É—insu, Ya faÉ—a ciki ya 6oye yana haki, gudun kada su buge shi, koda su ka shigo basu same shi ba, kuma ba su yi tsammanin ya 6uya acikin abun zuba sharar ba, Kaf suka bincika kowani sashe na toilet basu gan shi ba, Danish ya basu haÆ™uri akan su Æ™yale shi, yace musu ae ba wani abu bane don ya cire furen zai iya fitar da wani tsiran, jin hakan yasa hankalinsu ya kwanta aranar saida ya sake tsuro wasu flowers É—in masu kyau, sak irin wanda Majnun ya cire musu, sukai ta murna sam sun manta da yaron nan, Ashe bayan ya shige cikin trash can É—in Bacci ya É—auke shi, ga bola duk da babu wani abun datti sosai 6awon kayan marmarin da suke sha ne wani harya fara ru6ewa, Har dare yayi babu chinonso, Hankalinsu yaÆ™i kwanciya, Suka soma nemanshi saÆ™o da lungu har Æ™arÆ™ashin gado, har toilet suka koma neman shi tsakar dare amma basu ganshi ba, saboda su ba son cewa ana Iya cire murfin abun zubda sharar ba, shiyasa ba su yi tunanin yana aciki ba, Arufe saman shi yake sai dai Æ´ar Æ™opar da za’a zubar da shara ciki, da suka gaji da neman shi É—aki suka koma kowa ya kwanta, tsakar dare Chinonso Ya farka daga bacci, ya ganshi acikin trash can, Yasa hannu zai É—age murfin yaÆ™i curuwa, Ya dinga kurma ihu yana faÉ—in su zo su taimake shi, dodonni zasu cinye shi, babu wanda ya iya jinshi saboda sun nutsa cikin baccinsu, Tun yana kuka da Æ™arfi har muryarshi ta disashe, Hada fitsari ya saki aciki, Jikin shi duk zufa, sai kerma yake yi, wani irin tsoro ne ya mamaye shi, saboda bai Æ™aunar duhu, saboda sun manta basu kunna Æ™aramar fitilar dake acikin toilet É—in ba.

bari dai in taÆ™aice mu ku zance sai da Chinonso yae kwana biyu acikin Abun zuba sharar nan, basu san dashi ba, ba komai yajawo hakan ba face rashin kawo musu fruit, dama shine ke kaisu zubda shara acikin trash can É—in, Aranar da zai Cika kwana Uku cuf aka kawo musu fruit, Bayan sun gama Cin abinci Parveen ta tattara 6awon taje zata zubda, sai da ta tsaya ta lashe na lashewa, Don har 6awon wani lokaci tana Ci, Bayan ta gama É—an kingin da ta rage irinsu 6awon lemu da bata sha, ta buÉ—e murfin zata zubda nan take idonta suka sauka akan hurhurar gashin kan Majnun, Ya sandare aciki Ya Æ™ame, babu alamun yana motsi, wata irin gigitacciyar Æ™ara tasaki saboda ta tsorata sosai, Da gudun gaske su Angel suka faÉ—o É—akin suna tambayarta lafiya hannunta na kerma tadinga nuna musu abun zuba sharar tsoro yasa kowa yaÆ™i zuwa ya duba, Sai da Azeeza taje ta kira Danish Ya taso daga saman gadon shi, ya shigo toilet É—in Ya buÉ—e murfin trash can É—in, yayin mamakin ganin yaron nan, Hannu biyu yasanya ya tsamo shi daga Ciki ya sauke shi Æ™asa, yaji jiki kuma idonshi biyu amma baya motsi, ko magana ya kasa, Jikin shi sai wari yake yi, gefen bakin shi hada 6allin ganyen furennin daya cinye lokacin da yunwa ta addabe shi, ‘ Su parveen sun sha mamaki, Wai harya iya buÉ—e murfin gaba É—aya ya shige, kuma ya maida murfin Ya datse amma Ya kasa fitowa daga Ciki.

Ba tare da 6ata Lokaci ba, Hanna da hibba suka taimaka wurin cire mashi kaya, Yasmin ta kar6a tasa abokiti ta wanke mishi su, Wankan tsarki su kayi ma jikinshi, da sosa da sabulu suka wake shi, Bayan sun gama Aka É—auko bargo É—aki suka Æ™udundune shi aciki, suka kaishi É—aki saman gadon shi, Allah yaso sun rage sauran abincinsu da aka kawo musu, Yana daga kwance suka dunga cusa mashi abaki daÆ™yar yake wuce wa, Sai da yaci ya Æ™oshi cikin shi yae Æ™ato, tukunna ya dawo hayyacin shi, ya fashe musu da kuka yana faÉ—in wai basu Æ™aunarshi yana ta kiran sunansu akan suzo su taimake shi amma suka Æ™i zuwa,’ dariya kamar zata kashe su, parveen tace ashe kasan sunayen mu? Nayi tunanin baka sani ba, Cikin shessheÆ™ar kuka yace”nasani mana, ba wanda bankira ba, hada Angel da danish da hanna, amma kuka Æ™i zuwa, dodo yae ta tsorata ni” saboda tsabar dariya hada dafe ciki, Tun da suke dashi bai ta6a nuna yasan fuskokinsu ba balle sunayensu, Amma yau ya zaÆ™e yana zazzaga musu masifa, tass saida ya lissafa musu sunayensu, Sun sha mamaki, Angel hada yi mishi nasiha akan ya daina rashin ji da 6arna, ya dinga kwanciya saman gadon shi yana bacci, kamar mutumin kirki ya amsa mata da toh, suka ce to ya kwanta, yanzu, Batare da yayi musa ba, Ya gyara kwanciyarshi, sai gashi bacci ya É—auke shi, hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi musu ba, duk da sunsan zaiyi wuya ya daina 6arna tunda abun daga kwakwalwarsa ne.

(Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇)

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button