Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 18 Book 2 Complete Novel

Jalila da kyar take fizgo numfashi, nufota yacigaba dayi, yana zuwa seya wuceta yatafi gurin Tv yanata shan tabarsa, yaje yasaka wayarsa a caji, Jalila kuwa se binsa take da kallo, yagama sa cajin ya taso yakuma dawowa harya wuceta ya dawo ya zauna a gabanta ya kura mata ido, dauke nata idon tayi, “naga kina son kallona ne shiyasa na zauna kigama karemin kallo” ya busamata hayakin sigari a fuskarta, da sauri ta dago tareda toshe hanci, ta dan fara tari, “wai meye haka, Allah ya sawwake inzauna ina kallonka, kato da kai kazomana gida tube sekace dakinka” “dakin Jawwad dakina ne, dan haka ko tsirara naga dama zanyi yawo” yunkurawa tayi zata mike, ya maida ita kan kujerar ya kafeta da ido, yasa kafarsa daya a gefenta, ta kalli inda yasa kafarsa aranta tace kalli jikinsa duk gashi kaman wani dan biri, lighter ya jefomata yasa wata sigari a bakinsa, yaimata alama ta kunna masa, wani mugun kallo tayi masa ta dauke kanta “Allah ya kiyaye ya rufamin asiri, nikabani hanya in wuce, kalleka dan Allah” hannunta daya yakama cikin mugunta ya murde mata yatsu, ihu tayi saboda zafi, take tafara zufa cikin tsawa yace “Kunnamin ko tarihi ya maimaita kansa, inkuma duramiki sigari yanzun nan” jiki na bari ta kunna lighter ta mika hannunta ta kunna masa, “dan Allah ka sakarmin hannuna, yatsuna zasu cire” a hankali yasakar mata hannu, idonta har yayi ja, yacigaba da busa mata hayaki, gashi ya tareta da kafa bazata iya guduwa ba, hannu ta kai zata toshe hancinta, “wallahi kika toshe hancinki sena wanka miki mari, sena baki mamaki da hannunki zaki shata” bashiri ta ajiye hannunta yana busa mata hayaki, se tari takeyi tana dauke numfashi “gaskiya Jalal dan iskane bashida mutunci, yanzu inna matsa da rashin kunya ze iyayimin akuya” seda ya shanye tabarsa tsaf sannan yadubeta “nine Namiji mara daraja ko? Ni Jalal nikike zagi ko?” shiru tayi tana kallonsa, daka mata tsawa yayi “ba dake nake ba kike wani kallona mara kunya” cikin dakewa tace “karya nayi, aiba kadyanayi ba namiji me daraja baze abunda kake ba” “hakane Amma kin bar kari tun ran tubani, kinyi sake namiji mara daraja yamiki Illa, wadda bazaki ganetaba a yanzu, idonki kawai ya nuna a tsorace kike kar in miki wani abu, ba abunda zan miki a yanzu, amma kisani bana yafiya, bana mantuwa, sena hukunta ki akan cin mutuncin dakikemin bazan kyaleki ba, sena gwada miki abunda nakeji idan kika ci zarafina, kidena shishshigi akan abunda baki saniba” Yayi ajiyar zuciya “tashi ki tafi kibani guri kuma kar inkuma ganinki a part din Jawwad dai 2 wannan lokacin, dan kinsan baya nan inkuma kika kuma zuwa to nasan abunda kikazo gani” 

Sumi2 ta tashi, taje bakin kofa ta tsaya ta kalleshi “to me zanzo gani, kaikanada abun kallone jiki duk gashi ba kyan gani sekace jikin biri, kokuma wannan jijiyoyin zanzo kallo, jiki kamar dan wrestling aikai ko kyan gani baka dashi, kasa wannan katon hannunka ka matsemin yatsuna Allah yasakamin dan ban yafeba kuma duk barazanar ka bazan dena fadan gaskiya ba, sannan kayi kadan kayimin Illa ko a yanzu ko a gaba, mugu kawai “tai ficewarta, Jalal kam yana jinta tana banbaminta ko dago kansa beba balle ya kalleta. 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ta wuce cikin gida tana yarfa hannu saboda zafi, tana zuwa daki taga Nana ta shirya da alama fita zatayi

” Ya dai naganki kin hade rai, me akayi miki ne? ” Jalila ta yamutsa fuska “Bakomai” “Shikenan dama kenake jira kizo ki rakani gidan, Yaya mairo, tace tana son ganina” 

“Tab amma badani Jalilan bako?” 

“Kamar yaya?” “kamar yadda nagaya miki mana, haka kurum ketace tana son gani baniba, dan haka ba inda zani, banje gidanta ba ma cimin mutunci take, inaga innaje mata gida, kitafi kawai, ba inda zani” “Shikenan tunda bazakiba, dama banason tafiya nikadai ne” “sauka lafiya ki gaishesu” 

      

Bayan Jawwad ya dawo daga school suka zauna domin cin Abinci rana shida Jalal, Jalal ba karamin dadi yajiba ganin wainar shinkafa ce, sunci Abincin nan sosai, Jalal yace “Jawwad dan Allah in da sauran Abincin nan ka zubamin in kaiwa daddy, kasan yana son wainar shinkafa” “Hakane Allah yasa akwai, bari inje cikin gida in duba” Jawwad ya tafi domin dubawa koda Abincin, Jawwad na fita aka kirashi waya, Jalal ya daga wayar ya duba, seyaga sunan Hanan, Murmushi yayi ya daga wayar

“Jawwad ka manta dani ko? Baka daga wayata, nashiga wani hali banajin dadin abunda kakemin” gyara murya Jalal yayi

“ba Jawwad bane, Jalal ne” “Jalal kaine yakake ya gida” “lafiya kalau ya Abdallah, kodayake muna waya dashi” “Yana lafiya, Jalal kaga abunda Jawwad yakemin ko? Banajin dadin hakan, dan Allah kasa baki, Jalal inason abokin ka da wasa na dau abun amma yanzu serious nake sonshi, Jalal help me, so masifa ne, da ban yadda da hakanba se yanzu” “kinaji Hanan, kiyi hakuri Jawwad inyace baya Sonki karya yake, kawai yana duba alkar dake tsakaninki da kanwarsa, amma karkidamu zamuyi magana dashi” (🙄🙄🙄 nikam nace su Jalal dama an iya rarrashi haka) Ajiyar zuciya Hanan tayi “to nagode sosai Jalal, agaida su Ilham” 

Jawwad ya shigo da food flask a hannunsa, ya ajiye ya kalli Jalal, “gashi nan Abincin Baby ne tace abawa daddy, amma dawa kake waya haka a wayata” 

“Jawwad” “Na’am ina jinka” “Meyasa kakewa yarinyar nan hakane” “Wace yarinyar kenan?” “Hanan mana, ta damu da kai, kamanta kaikake min fada akan Ilham segashi kaima kanayi, meye marabar Hanan da waccan fitsararriyar banzan, ba gara Hanan din bama tafita nutsuwa da saukin kai” “Haba Jalal, Jalila da soyayyar ta na tashi, banason yin abunda zan bata mata rai, tarayyata da Hanan baze haifar da da me idoba, kuma Hanan da kake ganinta itama rigimammiyace, kaikewa Jalila wani kallo dan bakwa jituwa” 

“Jawwad yakamata kakoma hankalinka, kayi wani abu akan yarinyar nan mana, kana ganinta so classic nasan da wanine ba kaiba zata sauke ajinta tace tana sonsa ne? Kayi wani abu mana” tsaki Jawwad yayi

“Ina tsawon shekaru Ilham ta dauka tana nuna maka so, kai mekayi akai” 

“Jawwad kasani nasani, nida Ilham bamu dace ba, kuma kasan dalili, kuma bari in sake jadadda maka, kokuma in tunamaka wani abu, mahaifiyarka bazata taba bari ka auri Jalila ba, musamman in wannan magananniyar matar tana nan, kaima kasani, kayi tunani Jawwad kafin al’amura su kwabe maka” yana gama fadin haka ya kwashi food flask din yai ficewarsa, yabar Jawwad a zaune yana tunani. 

Jalal yana zuwa gida ya tafi part din daddy da fara’arsa, “daddy ina fatan bakaci Abincin rana ba? ” “banciba ina shirin ci dai” “Abincin daka fiso nakawo maka” Jalal ya turawa daddy flask din ba karamin murna daddy yayi ba daganin Abincin da Jalal ya kawo masa, “Jalal inaka samo wannan Abincin?” “a gidansu Jawwad” “yaushe rabon da inci masa” daddy ya dan kalli Mummy “Madam kindenamin Abincin gargajiya, mussaman favorites dina” “hmm ba gashi danka yakawo maka ba sekaci ai” daddy yai murmushi “Jalal wayayi girkin nan yayi dadi” “nima bansaniba” Mummy tace “nasan baze wuce Jalila ce tayishiba, dan Maama bata fiye yin girki ba Nana kam dama ba a maganarta akwai son jiki” daddy yace “Jalal inka koma ka turomin takwararka, kafin inkoma England inason inkuma cin irin Abincin nan” hade rai Jalal yayi “daddy waibaka san sunanta bane zaka dinga cemata takwarata” murmushi daddy yayi irin na manya “hmmm to ko in tunamaka tarihin yadda aka samata sunan ne? Dan naga kaman ka manta” “Wai daddy meyasa kake son yimin haka, abune yafaru shekaru da suka wuce kuma kuruciyace baya wuce ba” murmushi daddy yayi “kaji tsoro kenan” “niba wani tsoro danaji” “hmm Jalal kenan, a shikenan tunda kaki yadda” ganin daddy yana neman takura masa yasa yatashi ya fice, bayan fitar Jalal ne Mummy ta kalli daddy “daddyn Jalal, inason muyi magana da kaine” “to ai gani ina jinki” 

“Dama gani nayi lokaci yayi daya kamata mucika muradin yaran nan, ina ganin Jalal idan akayi masa aure ze samu nutsuwa, ze rage abubuwan dayakeyi” Ajiyar zuciya daddy yayi 

“to yanzu wace yarinyar kike gani zata auri Jalal a wannan halin dayake ciki?” “to ai Jalal yanada wadda yakeso, ga Ilham nan suna son junansu, yakamata kawai ayi magana asaka rana” “kin tabbatar da duk su biyu  suna son junansu” “Eh mana sun son junansu, yakamata ayi magana kaje kasamu baban Ilham ayi maganar auren nan” “Kina ganin ba matsala a yin hakan, sunada banbancin halayya, kaman zamansu bazeyi dadi ba” “kaga tunda dai suna son junansu a haka ai shikenan” “Amma ni Jalal be taba yimin wannan zancen ba” “to aini gana nagaya maka” daddy yayi Ajiyar zuciya, be kuma cewa komai ba”. 

Jalila kwance akan gadonsu ta dakko wayarta ta kira Alhaji Kabiru amma be daga ba, dan haka ta sauka tafara chatting, tana what’s app tana hira da zahra, setaga Alhaji Kabiru yakirata, ta daga wayar amma batace komai ba, setaji yana cewa

“Jabir Nakiraka bata shiga, se yanzu tashiga, kayan sun taho daga kudu, munyi waya sunkusa karasowa kano za a sauke a gidan gonata, kaje ka karba se ka rarraba musu cikin dare, kayiwa Jeje magana shima yazo ya karbi nasu” shiru Jalila tayi, wane irin kayane wannan? ta kashe wayar , ta maimaita “Kaya a rarraba cikin dare, kuma hada Jeje” what’s app ta koma da sauri tai masa sallama, amma beyi reply ba, ajiye wayar tayi tanata tunani, besan lambar waya kiraba kenan, “Allah nagode maka nafara samun hint akan mutumin nan, Allah kabani mafita” wayarta takuma dubawa setaga ya amsa mata sallamar 

“barka da rana, ranka ya dade yakake ya harkoki” 

“lafiya kalau, wake magana?” shiru Jalila tayi tana tunanin wani suna zata gayamasa, kawai setace masa “Halima ce” “Wace haliman?” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“hmm duniya da gaskiya kuwa? Wadda kabawa complementary card a banki” “ohhh am so sorry, kuma seda na kawo kece dan na dau muryarki, sedai dan bansan sunanki bane, ina fatan kina cikin koshin lafiya, Gimbiya Halima” “Ina lpy” “Amma nayi mamaki, dakika nemeni, danaga kin yaga card din banzaci zaki nemeni ba, nayi farinciki gaskiya” Jalila ta biye masa suka dinga chatting, daga baya ta sauka ta rufe data dinta, 

Jinjina kai tayi, “lallai wannan mutumin zakayi saurin fadawa tarkona, Kuma abun mamaki, wani kayane ake rabawa cikin dare, ga sunan Jeje ya ambata, to me hakan ke nufi, wannan ya tabbatar da yana hulda da Jeje, to wace irin hulda Alhaji Kabiru yakeyi da JeJe haka, wanda yasashi zuwa gurin birthday din Jalal a boye, kai akwai lauje cikin nadi” tana tsaka da wannan tunanin still aka kuma kiranta a waya, koda ta duba tagane lambar Dan sandan nan ne, tsaki tayi harta ajiye wayar sekuma ta yi wani tunani ta daga

“Salamu alaikum” amsamata yayi sanna yace “beauty barka da wannan lokacin ya kike seda ta dan tura baki gaba “Lafiya kalau” “dama cewa nayi bari inkiraki inji lafiyar ki, sannan inaso inzo gidanku in ganki” 

“What gidanmu kuma mezakayimin” “Meye abun tashin hankali, inasonki ne aurenki nakeso inyi, please” ture wayar gefe tayi takama dariya sannan ta maida wayar kunenta “Ni wallahi kabani kunya yar baby dani yaushe na isa aure, kuma ya za’a yi Abbana ya aura maka ni, ni gaskiya yarinya ce” yadda take shagwabar ba karamin birgeshi takeba

“Haba yar baby wayace miki baki isa aure ba sannan kuma babu kunya a soyayya” “Babana bazemin aure yanzu ba kuma yariga yabadani, amma nima bansan wayabawa ba” Ajiyar zuciya yayi “bayarwa ba aure bane dan haka zancigaba da neman aurenki” 

“Hmm shikenan se anjima, zanyi karatu yanzu” “To Baby tunda kinki gayamin sunanki, ayi karatu da kyau, inkinki mu hadu zannemo gidanku inzo gurin Abbanki da kaina” “Sekazo” daga nan ta kashe wayarta “tab ina zan kai wannaan mutumin” 

Bayan sallar la’asar, Jalal yakoma gurin Jawwad, koda yaje ya tarar dashi wani iri kaman mara lafiya, Jalal bebi takan tambayar meyake damunsa ba, saboda yasan akan maganar dazu ne, 

“Jawwad daddy yace yana son ganin kanwarka” 

“wacce daga ciki?” “wadda ta yi Abincin yau” 

“Jalila ce tayi, Allah yasa ba laifi tayiwa daddy ba” “nima bansaniba yace dai taje yanason ganinta” 

“zangaya mata Insha Allah” “yayi kyau bari in tafi in kyaleka naga kana cikin damuwa tunda mukayi magana dazu, karka bata lokacinka gurin dogon tunani, maganata itace gaskiyar lamari, duk inda zaka juya kayi tunani kasani maganar dayace mahaifiyarka da yan uwanta basa som wadda kakeso kuma bazasu bari ka aureta ba, dan haka mafita kacireta a ranka ka maye gurbinta da Hanan”

“Jalal tayaya wannan abun ze yuwu, ni Jalila nakeso, Kuma maganar Maama nasan zata amince ne in na lallabata” murmushi Jalal yayi “Shikenan Allah yabada sa’a, amma karka manta da batun kiran daddy” yana gama fadin haka ya fice. 

Tunda Jalal yafuta tunani ya damu Jawwad, wayarsa ya dauka ya kira Jalila suka dinga hira, har ya manta da abunda yake damunsa, daga nana yagaya mata daddyn Jalal yace taje yanason ganinta. 

Jalal yana komawa gida, kozama beyiba kiran Hannah yafara shigowa wayarsa, tsaki yayi ya ajiye wayar ya shiga sabgoginsa amma tacigaba da kiransa, takirashi yafi sau goma, a fusace Jalal ya dau wayar 

“Hannah kina bina bashine? Wannan kiran haka meya faru?” 

“Niko nake binka bashi Jalal, meyasa kake wahalar dani hakane? So seya koma kiyayya bana sukuni idan banganka ba, Jalal dan Allah ka tausayawa zuciyata, Jalal kasan Masifar So kuwa? Na tabbatar dakasani dabakaimin haka ba, Jalal ka dubi girman Allah ka tausayawa zuciyata” murmushi Jalal yai kaman Hannah naganinsa 

“Hannah kenan, ina mamakin sanda soyayyar da kikemin ta rikide zuwa ta gaskiya abun akwai mamaki gaskiya, but don’t mind me akan abunda na fada kinji, nagaya miki gaskiya tun farko, baze yuwu ace nayi yawon club sannan ace matata ma tsohuwar yar club bace, dukda zuwa club dinmu yanada banbanci, kiduba a samarin club dinnaki kisamu wani ku daidaita amma ba Jalal ba”

“Amma Jalal ai nace maka na tuba wallahi inka aureni zandena” 

“Ni ABDUL JALAL nafi karfin ragowar garorin bariki, ki kiyayeni” yana gama maganar ya kashe wayarsa. 

Daddy sam yakasa yadda da batun Mummy gameda Jalal, shidai yasan Jalal ko zancen mata bayaso ayi masa, amma ya akayi haryake soyayya da Ilham besaniba dukda yana dadewa baya nan, amma yasan da zeyi masa zancen, dan haka ya yanke shawarar kiran Jalal yaji tabakinsa. 

    Hanan na kwance akan katafaren gadonta, tayi zurfi a tunanin ta, taji an turo kofar dakinta, dan daga kai tayi taga mum dintace, batace uffan ba tai shiruu tacigaba da tunani, gefenta Mum tazo ta zauna ta dafata “Auta meyake damunkine, yan kwanakin nan kullum cikin damuwa kike meyake damunkine” a hankali Hanan ta tashi zaune “Mummy na ba wata damuwa, damuwar school ne kawai kinsan akwai tension na makaranta” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

“Hakane Hanan, amma yusuf yakawomin kararki fa” dan ya mutsa fuska Hanan tayi “Meyace miki?” 

“gaba daya kin canza masa yakasa gane kanki, meyake faruwa ne?” 

“mummy kinsan tun farko dama ni bawani yimin yaya  ba kinsani, Mummy kinsan wani abu kuwa” 

“A ‘a sekin fada” 

“tun farko kinsan ba son Yusuf nakeyiba, Mum zuwana kano naga Yayan Jalila cousin dinta wanda takeso, da saboda in tsokaneta nace ina sonshi, amma daga baya abun yakomamin Gaske, Mum ina son Abunda Jalila takeso ne, kuma yazama dole tabarmin dan basu dace ba”. 

Wani irin Kallo Mum tayiwa Hanan

“I don’t think you are in your senses, Hanan, kawartaki dukda yarinyar ba wani yimin tayiba, amma son da kike mata yasa na kyaleku tare, amma hakan bazesa inkasa gayamiki gaskiya ba, Hanan inkikayi haka baki kyautaba, hakan ba daidai bane, Jalila taana kaunarki meyasa zakiyi mata haka” kwalla ce ta taru a idon Hanan

“Mummy ki fuskanceni banyi haka dan cin amanar Jalila ba, Mum wallahi makauniyar soyayya nakewa Jawwad, Mummy he is very nice and gentle, gashi salihi, Mum soyayyata da Jawwad mafita ce kuma ceton Jalila ne, inajinta a zuciyata kamar yar uwata ta jini, dan haka bazan iya cutar da itaba all i know is that inason Jawwad ” 

“Kamar yaya kenan, tayaya kike son maida karya gaskiya” 

Labarin abunda ke tsakanin Jalal da Jalila tabawa Mummy, ta nisa tace 

“Mum ko bankuma cewa komai ba kinsan Jalal is her e destiny, ita kadaice zata iya sadaukarwa domin ceton sa, Mum mahimmanci Jalal a rayuwarta ne yasa ake mata nuni da halin dayake ciki a mafarki, Mum kibani karfin gwiwa, zanyi meyuwuwa in dauke hankalinta daga kan Jawwad, sannan zan temaketa akan rayuwar Jalal” Jikin Mum ba karamin sanyi yayiba dajin labarin da Hanan tabata, 

“Shikenan Auta, zancigaba dayimuku Addu’a Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi”. 

     Jalal cikin gida ya tafi domin samun yin hira da daddy, yana zuwa ya tarar da Ilham a babban palour da waya a hanunta tana waya, kotakanta bebi ba yanufi part din daddy, bayansa Ilham tabi da kallo “muje zuwa Jalal zakaga tsiya” Jalal yana zuwa ya tarar da daddy a  palour dinsa suna hira da mummy, daddy na ganinsa yai murmushi “dan halak kaki ambato, zancenka nakeyi a a raina karaso Dama inason ganinka dan gidan daddy” 

“to gani mezaka bani, Jalal yafada yana zama akan kusa da daddy” 

“Jalal magana nakeso muyi da kai, Mum dinka tazomin da magana nayi murna da jin hakan shine nakeson ji bakinka” Mummy tai farat tace 

“Ba dai maganar da mukayi dazu bane, ai mungama magana dakai, meye kuma na tada wannan zancen, kayi abunda yakamata kawai” daddy yace

“A a Madam karmuyi gaggawa, dole mubi komai a sannu sannan inji ta bakin kowannensu” “A’a fa ai mungama magana wannan kawai maida hannun agogo baya zakayi” 

  Jalila da sallama ta shigo palourn, Ilham na palourn amma tai mirsisi taki amsawa, “Aminiya Ilham amsa sallamar ma seyazamo miki aiki, amsa sallama dabi ace ta kyakkyawan musulmi, karki zama irin yayanki nan mana” tsaki Ilham tayi tareda fadin

“meye hakane wai? Ke kullum in baki shiga sabgata  ba bakyajin dadi ko? Ina ruwanki da nida danuwanane mayya” 

“Aini indai a irin sha’anin nan ne to nafi uwar mayya naci, mayya in akayi magani ana samun nasara nikuwa babu abunda zakiyi kiyi nasara akaina, sannan duk abunda ba’aso ni shinakeyi dan aji haushi, and the most craziest part of me is that bana riko, yanzu zamuyi fada yanzu zan manta, duk abunda na rike a zuciyata nake fushi akansa to yanada mahimmanci a gurina, dan haka nibana gaba dake Ilham dan bakikai inyi hakan ba dake, sannan kuma bazan fasa bata miki raiba in har kikayi abunda yaci karo da Ra’ayina sedai kiyi hakuri “

Lallai Jalila tacika yar rainin hankali, wulakanci goma da ashirin. 

Duk yada Mummy tayi a wayance kar Jalal yaji zancen nemamasa auren Ilham daddy yaki, karshe a fusace Jalal yace” waini meye hakane daddy, afadamin komene mana, inbaza ayiba meye na dakko maganar agabana, nibanason irin haka fa”

“Ohh ka kwantar da hankalinka yaron kirki, aiba abun tashin hankali bane, maganane me dadi akanka, maganane nacika maka burin rayuwarka, Mummy dinka tagama yimin bayani akan komai, nagame da abunda ke tsakaninka da Kanwarka Ilham, dan haka zanje muyi magana da mahaifinta asa rana, nayi farinciki da har kafara tunanin aure Jalal, cigaba yafara zuwa a rayuwarka kaga…… 

“Enough daddy” Jalal yai maganar a fusace, “Wannan maganar daga ina? Duk matan duniya in rasa wadda zan aura se wannan, in har farinciki kake nafara maganar aure, to da saurana, wait wai wama yagaya maka wannan maganar, kodayake base ka gayamin ba nasani,” ya kalli mummy “Ke kika gaya masa nasan haka, nidake na taba cemiki ina son wannan yarinyar ne? Meyasa kikemin hakane, meyasa kikeson kuma rusa al’amuran rayuwata, ke a ganinki Ilham ta dace da zama matata, kimin adalci kiyiwa kanki mana, akoda yaushe kidena duba maslahar kanki kawai, kuma Ilham tunda Ubanta na raye se ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane ba, akanme za a dinga batamin rai haka, wallahi sena kakkarya yarinyar nan inga uban da ze tsayamata” daddy yai gaggawar mikewa da nufin tare Jalal amma Jalal ya kauce ya nufo hanyar fita, 

Ilham taiwa Jalila wani mummunar kallo “ai dama da ganinki base an fada ba ke mayyace, bari inkuma jadadda miki, duk maitarki kurwata data Jalal tafi karfinki haka kika ganmu haka zaki kyalemu, nidashi mutu ka raba” “to dan kincemin mayya ai ba haushi zanji ba, ko ina cin kurwa bazanci taki data Jalal ba saboda bazanci kazamar kurwa ba, kuma kina bani mamaki, dakikancinki yayi yawa Ilham bansan lokacin dazaki gane cewa niba abunda zanyi da wannan dan giyar ba, kuma kema dakike ta wahala akan se ya aureki don cikar burinki, ABDUL JALAL baze taba aurenki ba Ilham, tunda yace baya sonki baze sokiba, kuma kinsan daddyn sa yana goyon bayansa, nasan hanya dayace dake dazakibi ki aureshi hanyar sihiri kuma wannan hanyar bata bullewa” da sauri Ilham ta kalli Jalila tanaso tayi magana amma takasa,

“Karya kikeyi, Yaya Jalal yana sona kuma bani da wani mugun nufi akansa, ubanwa yagaya miki saboda wani dalili nakesonshi, munafuka duk masifarki wallahi haka zaki kyalemu, dan banga uban daya isa ya hanani auren Jalal ba” 

“Eh kinyi mamaki ko? Ya akayi nasani, da bakinki kika fada, ba a gurin wani naji ba sannan….. 

” A gidan ubanwa na taba gayamiki ina sonki meyasa ba kya ganewa, sa’anki neni, mahaukaciyar inace ke dakike tunanin zan aureki? Yau zaki tattara kibar gidan nan tunda bana ubanki bane, akanme zaki dage cewar nikikeso nace bana sonki bana sonki meye haka wai, mekike nema a gurina ne Ilham” Jalal ne yakewa Ilham magana cikin fada, da sauri daddy ya fito tareda Mummy, daddy ya karaso inda Jalal yake “haba Jalal ai duk abun be kai hakaba, koba komai kanwarkace, kayi hakuri” 

“Daddy wace irin magana kakeyi hakane, seta bar gidan nan koni inbar muku gidan, akan me za a takurawa rayuwata, for what reason dad, ace kullum mahaifiyata batada buri se ganin bacin raina” Jalila rasa abun cewa tayi, ta kalli wannan ta kalli wannan, 

“Haba Jalal ya ina matsayin mahaifiyarka zakace bana son cigabanka, Aurenka da Ilham alherine ni banga aibun Ilham ba, a tunanina komai ya wuce” wani mugun kallo Jalal yaiwa Mummy duk ya birkice idonsa yai jawur “Kikace komai yawuce, karki yaudari kanki mana, kodayake son zuciya baze barki kidinga ganin gaskiya ba, nayi dana sanin kasancewarki mahaifiyata, kullum bakida burin daya wuce gayyato matsala cikin rayuwar dan dakika haifa, haka sauran iyaye sukeyi” Jalila kasa jure abunda Jalal yake tayi , wanda hakan yasa ta mike ta fice daga palourn jikinta a sanyaye, tafito ta jingina da bango tai shiru tana tunani “meyake damun Jalal ne? Dole nasan dalilinsa na cin zarafin iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina tausayawa Jalal ya mutu yana sabawa iyayensa, zanso inji dalilin hakan kozan iya temakamasa, wulakanta iyaye ba abune me sauki ba” 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ilham se kuka take, duk yadda daddy yaso ya shawo kan Jalal ya kasa, seda yai me isarsa sannan ya bude palourn ya fito a fusace, yana fitowa Jalila tana gurin a tsaye akan hanyar daze wuce, hannu yasa ya hankadeta gefe yai gaba abunsa ya nufi part dinsa, mamakine yacikata, kodayake ba abun mamaki bane kadan daga aikin giya. Jiki a sanyaye ta baro gidan, sedai me tana fitowa taga motar  Hannah a kofar gidan, ta fito tana ta kiran lambar Jalal amma yaki dagawa. Jalila a ranta tace “lallai Jalal kana cikin iftila’i” dayake duhun magariba yafara yi, Hannah bata gane wacece ba, dan haka tace “Dan Allah baiwar Allah naga kaman daga gidan kika fito Jalal na ciki ne?” 

Karasawa Jalila tayi gabanta “kalli da kyau baki gane wacece bane?” se yanzu Hannah taganeta “dama kece? 

” Eh nice, meyasa bakyajin kunyar zuwa neman Jalal ne? Mace da aji akasanta abunda kike zubarda mata kike” “Ke kome nakeyi beshafeki ba kingane bana son surutu, Jalal yana nan ne?” 

“Eh Jalal yana nan, amma kaman yanda nagaya miki kwanaki yauma hakanne baze zoba, huwaila kike kowa, ni mamaki kike bani meyasa bakida kunya ne, me yayi miki haka kika uzzurawa rayuwarsa” 

“Ke dakata, ba abunda yadameki, Ko agaban uban waye zan fada son Jalal nake, nan da kankanin lokaci ze aureni” murmushi Jalila tayi “to Ilham dinfa? Kokina tunanin zuba miki ido zatayi ki aureshi, naga kaman tafiki sonshi dan tafiki himma ina tunanin za’asa sa ranar aurensu” zare ido Hannah tayi “dagaske kike?” “nasankine dazan tsaya ina miki wasa” 

“Ni Jalal zewa haka wallahi basu isaba dagashi har kanwar tasa, Nikadai zan aure Jalal in rayu dashi sena lalata komai, in bahakaba sena masa sharrin da nan duniya babu wanda ya isa ya fiddashi, nayi wannan alkawarin” “kaman ba yanzu kika gama cewa kina son aurensa ba, kin dade kina cutar da rayuwarsa, ranar birthday dinsa kun shirya yimasa wani abu, ni nasaka aka dauke shi daga gurin bayan kin bashi kwaya kin bugar dashi, a wannan lokacin nakara tabattar da bakinku daya da da wannan dan iskan, sannan kisani babu wani sharri dazakiyi masa yayi tasiri akansa Allah yana tareda shi, dan haka wannan ba soyayya bace, ba kyasonsa dan Allah, ku saurari yadda karshenku ze kasance ” Jalila ta juya tai gaba, da sauri Hanna tabi bayan Jalila tana mata magana akan dan Allah ta tsaya, amma Jalila taimata banza tai wucewarta zuciyarta cike da tunani. Ba karamin mamaki Hannah tayiba, gaskiya Jalila tabata mamaki ya akayi haka, dama ita tasaka aka dauke Jalal, ita ta turasa wannan shirin da suka dade sunayi, to meye manufar Jalila akan Jalal. 

Jalila kam Tana zuwa gida  ta tarar da Nana ta dawo daga gidan Yaya mairo, ta tarar dasu a palour Nana tana kuka, Maama tana rarrashinta, kaman ta wuce seta fasa ta tsaya “Nana lafiya kuwa” 

“ke bana son gulma ina ruwanki, wuce kitafi inda zaki, uwar tsegumi kawai” ba Jalila ba hatta Nana seda taji babu dadi abunda Maama tayi. 

Dakinsu ta wuce taje tai alwala tai sallar magariba, tafara tilawar al’qur’ani, wayarta se ringing takeyi amma bata dauka ba harseda ta idar da karatunta, tana duba wayar bakuwar lamba ce da akayi ta kiranta da ita ranan, dan haka ta ajiye tacigaba da sabgoginta, har bayan sallar isha’i Nana bata shigo dakin ba Jalila kuma bata nemeta ba, wayarta ce takuma daukar ringing, a fusace Jalila ta dauka “Wai ya hakane ankira ban daga ba kuma se kuma kira ake, haba inkuma ina wani uzurinne fa?” 

“Tuba nake, adon gari, nakasa samun sukuni ne amin afuwa” 

“waima wake magana?” 

“Suleman ne” “waye kuma Sulaiman ni bansan wani suleiman ba” “yi hakuri, wanda kuka hadu shekaran jiya kika bashi lambarki” seda Jalila ta dan yamutsa fuska dan ita ta manta dashi, 

“ohh nagane sannu yakake?” “lafiya amma ba lauba, nakira nakira baki daga ba, inata kewar muryar nan taki” “Hmm to ai yanzu gashi kaji” “Hakane nayi farinciki fatan kina lafiya” “eh lafiyata kalau” haka sukayi waya da Jalila kaman ammata dole, ita kunya ma yake bata da haushi inyayi wani abun tsoho dashi se wani tabara yake mata. 

Nana ce ta shigo jikinta a sanyaye, Jalila bata kulata ba taje tazubo abincin dare tanaci, bayan tagama tai shirin bacci ta haye gado tana chatting dinta, Hanan tana online, suka fara hira kaman abun arziki, har Jalila take bata labarin Alhaji Kabiru, dakuma wannan dansandan, Hanan tabata shawarwari, Jalila tagaya mata abunda yafaru yau agidansu Jalal, Hanan ta fara kunna Jalila “queen gaskiya Jalal is destined to be in your life, dan haka ki kauda wata Ilham da Hannah gefe kisa kai dan kun dace sosai, ke kadaice zakiso shi tsakani da Allah ki temaki rayuwarsa” 

“Ke bana son shirme Allah ya kiyaye meye abunso a gurinsa, meye abun birgewa a gurin mashayin giya” 

“A’a adena zakewa dai, kar nan gaba azo a gigice akan sa ehee dan bazan bawa mutum shawara ba” 

“Narasa meyasa kike likamin wannan sakaran, inada Yaya Jawwad ba abunda zanyi da wani Jalal” 

“Ke dakata, Jawwad nawane kuma ni kadai, gara ki rungumi Jalal tun lokaci be kuremiki ba, Jawwad baze aureki ba nina gayamiki” rufe data Jalila tayi, dan hartaji wani bacin rai yana tasomata” Nana ta kalli Jalila tace

“Jalila bazaki tambayi meyasameni bako? Kina kallo ina cikin wani yanayi” tashi Jalila tayi takoma kusada Nana “Nana hawayen nan naki jinake kaman ni nake zubar dashi, kinji abunda Maama tace dazu, shiyasa ban takuramiki inji meyasaki kuka ba bansaniba kobe shafeniba” 

“haba Jalila har akwai abunda ze sameni dabe shafekiba?” “to yanzu kiyi hakuri gayamin meya faru?” Nana ta share hawayenta sannan tace

“Jalila wai kiran da yaya mairo tayimin, waiso take ta hadani da Nura waiya aureni” 

“Waye kuma Nura” “babban danta ne, wallahi Jalila inda abunda natsani na bude ido ingani be wuce wannan Jakinba” “Amma Nana meyasa?” 

Wasu hawayen ne suka kuma zubowa Nana “Jalila dan dabane fa, mugun tantirine har prison yayi, ga shaye shaye na masifa, ba ilimin addini bokon ma secondary ya tsaya, wai dan zalunci shi takeso ta hadani aure dashi, wallahi akace sena aureshi sena kashe kaina, inkuwa aka kaini gidansa sena ksheshi na kashe kaina”

Da sauri Jalila ta rufemata baki tareda fadi “subhanallah, Nana karki kara fadin hakan, wannan maganar tayi tsauri, amma me Maama tace?” “cewa tayi inyi hakuri, zatasan matakin dazata dauka, nikam hakan beminba kawai ajanye wannan maganar, inbahakaba gara in bar gidan nan” “Nana nace kidena irin wannan zantukan mana, kiyi amfani da kwakwalwarki, kina tunanin Abba ze yaddane, baze yadda ba dan haka kiyi hakuri, ba abunda zesa ki aureshi Insha Allah mutumin kirki zaki aura, zan tayaki addu’a kinji My Nana kidena kuka, banaso” gyada kai Nana tayi sannan tace “Saboda tsabar son zuciya irin na matar nan waishi kuma Yaya Jawwad da Naja za’a hadasu, wallahi inshi ya yadda nibazan yadda da auren dan daba ba, gara in kashe tsinanne in huta”

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Seda gaban Jalila ya fadi, kirjinta ya buga da karfi, amma ta dake ta maze, ta lallaba Nana suka kwanta, amma bacci ya gagari Jalila, gaba daya abubuwa sun cunkushe mata ta rasa menene mafita, dan haka ta tashi taje tayo alwala ta tada salla. 

Washegari da safe seda Jalila takusa sasu su makara sannan suka tafi makaranta, yauma sir hafiz yashiga ajinsu Jalila, har yayi lectures yagama hankalinsa yana kanta, ita kam ko a jikinta, abubuwan dasuka dameta kawai take lissafawa, na farko damuwar Jalal, ga abunda Hanna tace, Hanan ma ta dage akan son datakewa Jawwad tana lika mata Jalal, ga abunda Nana tagaya mata jiya da daddare, gaba daya zuciyarta a cunkushe take tanason sanin waye Alhaji Kabiru ta hanyar yarsa dake ajinsu wato saleema, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, sir hafiz yana monitoring din duk moves dinta sam attention dinta baya kansa, dan haka yace ta tashi tsaye, ba musu ta mike, ya dinga yimata tambayoyi amma taki kulashi tayi masa shiru, lamarin yarinyar nan ba karamin daure masa kai yake ba, daya dameta ma kawai seyaga idonta ya cika da kwalla, tana nema tafara kuka. Dan haka ya kyaleta yacigaba da lectures dinsa ba tareda yace ta zauna ba, yagama tsaf sannan yace ta biyoshi office, banza tayi masa, tanemi guri tai zamanta ta kifa kai, tarasa meyake mata dadi, hawaye tafarayi tanayi tana gogewa, zahra ta dafata tace “Kiyi hakuri kidena kuka, nikaina banajin dadin abunda lecturer din nan yake miki, nasan ba dadi amma dan Allah kidena kuka kinji” sam zahra batasan meye damuwar Jalila ba dan haka tabita a haka, zahra tace “bari inje in siyo miki ruwa kisha ki wanke fusakarki” Jalila ba tace komai ba, zahra tafita taje siyo ruwa, a hanyarta ta dawowa, Su Samira suka datseta, suka sha gabanta, samira ta kalleta sama da kasa sannan tace “A tunaninki tarayyarki da wannan dakikiyar yarinyar zesa in fasa bibiyarki ne, wallahi yazama dole ki amince da bukatata, komai kike bukata na more rayuwa zanbaki shi, amma muddin kika cigaba dabin yarinyar nan, ina tausaya miki abunda ze biyo baya, saboda rayuwar taki dakike takama da ita, ita zansa a tarwatsa yadda sekin wulakanta a idon duniya ” a firgice Zahra ta kallesu, Saleema tace “Zahra dama ce a gareki kina ganin su zee da salma duk asirinsu a rufe sunata hutawa, keme yasa bazaki yadda ba, waike ta Allah ko, wallahi duk matakin data dauka akanki kekika jawa kanki, sannan yazama dole kiyi gaggawar rabuwa da wannaan dakikiyar yarinyar. Daga nan suka wuce suka batta a gurin, a hankali ta furta” Nashiga uku, Allah ka tsareni daga sharrin wadannan mugayen” jiki a sanyaye tafara motsa kafarta

“Ke! Ke!!” taji ana mata magana a baya, tsayawa tayi ta waigo, setaga sir Hafiz, “kigayawa kawarki kice mata bataji kiran danayi nata bane” jinjina kai kawai tayi, ta tafi aji ta kaiwa Jalila ruwa ta sha ta wanke, fuskarta Jalila ta kalleta, a sanyaye zahra tace “sir hafiz yace meyasa bakije kiran da yayi miki ba” jin maganar zahra a sanyaye yasa tace “lafiya naganki wani iri, me yafaru” zahra bata boye mata komai ba tagaya mata, “Jalila inaga dole mudena hulda tunda suka sakoni gaba, inacikin tashin hankali” ran Jalila ba karamin baci yayi, ta kalli zahra “har yanzu babu uwar datayi nakuda ta durkusa ta haifi wata shegiya dazata sa inyi wani abu ku indena wani abu dan ina tsoronta, dan haka nasiyi wannan rigimar koni kosu, musamman Saleema, bada ita zanyiba sa makyankyashinta zanyi” mamakine yacika zahra kaman ba Jalilan da take kuka ba yanzu abun tausayi amma yanzu itake masifa haka “Jalila meye kuma makyankyashi?” “ba ruwanki, kuma bazan dena hulda dakeba sedai kibar department din nan, in yaso ba tarwatsawa ba in sunga dama susakawa rayuwartaki bom, ba abunda ya shafeni bane tunda kedai bakida wayo bakusan yancinkiba, seki zauna wasu yan kwaya suna raina miki hankali saboda bukatarsu” tanagama fadin haka tatashi ta dau Jakarta tabar ajin, tabar zahra baki bude. 

Office din sir hafiz ta tafi, tana zuwa su samira na fitowa, kallon Samira tayi ido cikin ido tace mata “Kiki yayi shiga hurumina, karki yadda kisanni a ainihin kalata” ta juya ta nufi office din, tayi knocking yace ta shiga, yana zaune yana breakfast yana shan tea, dan kuramata ido yayi ya dauke kai yacigaba da abunda yake, har kasa ta durkusa ta gaisheshi dan dagowa yayi ya amsa mata, bata jira izininsa ba ta haye kujerar dake fuskantarsa ta maze hada jujjuyawa, aransa yace “Ikon Allah wanna yarinyar ba dai mulkiba” seda yagama abunda yake yayinda still yanzuma tunani take tanayi tana kokarin maida kwallar data taru a idonta, ya dan dubeta yai nazarinta nawasu seconds sannaan yace “Wayabaki damar ki zauna?” bata kalleshiba tace “bana son tsaiwa dazu ma daka tsayar dani a  aji kafata ciwo take” “Kodayake bakiyi kakar wahala ba, amma Meyasa kike kokarin boye baiwar da Allah yayi miki, meyasa kika zabi kidinga dizga kanki agaban yan ajinku? Kika fi maida kai akan tunani kullum?” shiru ta danyi idonta taf hawaye tace “ai kai ka janyomin, nagaya maka kadena tambayata agaban yan aji amma kullum seka tambayeni danka wulakantani, ni bazan bada amsa agaban yan ajiba, bana son sa ido” 

“Wayece miki dan in wulakantaki nake tambayarki?” “Zuciyatace tagayamin” murmushi yayi “tagayamiki ba dai dai ba, amma meyasa kike boye baiwar da Allah yayi miki, ga yawan tunani a class, you are too young ace kina tunani dayawa?” 

“Akan me zan nuna ni watace? A hakanma wasu sun tsaneni a ajinmu nibansan menayi musu ba,” 

“Suwaye suka tsaneki?” 

“Samira da gangs dinta mana, kuma wallahi in basu fita sabgata ba senayu maganin yarinya “

Kallonta yayi “I like your confidence, amma kidena wannaan maganar, yarinyar nan tanada manya karki sa kanki a matsala kinada kwakwalwa me ban mamaki, ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai” Jalila a zuciyarta tai murmushi “tab aikuwa bazan bar gurin nan ba senaji Labari sosai akansu, bari inbi da mutumin nan a sannu” 

Dan zumbura baki tayi “ni ina ruwana da wasu manyanta akan me zata takuramin, nima inada Allah kuma babana yana sona dan haka ba wanda zemin komai” 

“No bahaka bane, yarinyar tasan manyan yan siyasa, gata fitinaniya har yan daba ne da ita karkije tasa a miki Illa” Zare ido Jalila tayi ta lura yanajin dadin hirar dasuke dan haka tace “to sir amma aka kyaleta a cikin school din nan haka kawar nan tata tafi tsanata taana cemin dakikiya fa,

They are terrorist in har mace za’ace tanada yan daba tazama hatsari a society” “Hakane amma ya zamuyi, hukumar makaranta bata dau mataki ba ance babu kwakwkwarar hujjar data tabattar dahakan kinga se hakuri, dan haka ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai kidena wannan tunanin” 

“To nagode sosai Insha Allah zan kiyaye, amma tunani yazamemin dole, anyway am very grateful with your advice nagode, Allah ya jikan mahaifa” murmushi yayi yace “Nima nagode Allah ya wuce mana gaba” ta dakko Jakarta ta fito. 

Jalal jiyake kaman inyayi kykyawan yunkuri zuciyarsa zata fasa kirjinsa dan bakinciki da bacin rai, daren ranar kasa bacci yayi, yasha giyar amma batayi masa komai ba, haka Jawwad yazo yasameshi da safe, juyin duniya yaki kula Jawwad balle yagaya masa meyake damunsa, haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi makaranta, yana nan zaune a palour yaji bacci ya sace shi, kira’ar Karatun Jalila ya dingaji a mafarki, wadda yagani a gidan telabijin shekarun baya koda ya farka daga baccin se yaji babu damuwar a taredashi, yai ajiyar zuciya yai shiru yana tunani wayarsa ce take ringing, kallon wayar yayi, sunan Hannah yagani, tsaki yayi yaki daukar wayar. 

Ilham hankalinta yagama tashi jin abunda Jalal yace jiya, kwana tayi batayi bacci ba, aiko sama da kasa zata hade bazata bar gidan nanba ba tareda ta samu abunda take soba, dan haka da sassafe ta tafi dakin Mummy, 

Kuka sosai tasakawa Mummy, “Mummy kingani ko, baya sona kinga wulakancin dayayumin, betabamin goriba se jiya dan kawai ance asa ranar aurenmu nikam nashiga uku Mummy, wallahi inban aureshi ba mutuwa zanyi” 

“Ilham meye hakane, kibi komai a sannu mana, kiyi hakuri bazaki bar gidan nan ba shima bacin raine yasashi fadin abunda yafada amma kiyi hakuri zan shawo kan matsalar” 

“Mummy nan da yaushe to? Nifa gaskiya na damu, bantaba tunanin Yaya Jalal zemin haka ba, anya kuwa ze yadda da aurena”? 

“Nace kiyi hakuri nasan abunda zanyi, aure keda Jalal ba fashi, kigoge hawayenki kidena kukan haka ya isa, tashi muje palour” 

Ilham ta goge hawayenta suka fito itada Mummy. 

Hannah tarasa meyakemata dadi, dagaske Jalal za’asamasa ranar aure da Ilham, aikuwa da Ilham ta tafka mafi girman kuskure a ratuwarta, to amma Jalila fa meye nata manufar, amma yakamata in gayawa Jeje wadda ta rusa masa shiri, amma yakamata inyi magana da Wannan yarinyar yana da kyau insan meye manufarta, wayarta ta dauka tayiwa Jalal message 

Jalal ya shiga yai wanka, message ne ya shigo wayarsa, ya dauka ya duba

“Wallahi Jalal inbaka amince da aurena ba, narantse maka sena nuna maka ni cikakkiyar yar bariki ce, wallahi sena maka sharrin da harka mutu ba wanda ze yadda bakai kayi ba, ka rubuta ka ajiye gara tun wuri kanemamana mafita karka kuskura kayi ganganci auren wata, dan wallahi bakai ba kwanciyar hankali 

“Hmm bakida hankali” Jalal ya furta a hankali, yafito ya tafi cikin gida dan yunwa yakeji, a palour yaga Mummy da Ilham, be kulasu ba yaje ya dakko abunda ze dakko ya nufi part din daddy, Ilham ta zata yanzuma zemata masifar yace tabar gidan amma taga be kulata ba, yaje part din daddy ya zauna yaci Abincinsa suka sha hira, a haka daddy yaita masa nasiha akan hakuri dakuma yadena kyamar Ilham, se Jalal yaji kaman yai masifa danshi baya son adinga dangantashi da Ilham wai ya aureta, se ya tuno abunda Jalila tagaya masa akan baya yiwa mahaifinsa biyayya, haka yayi shiru daddy yaitai masa nasiha, Jalal yana gama cin Abincin sa ya kalli daddy “daddy kaga naji nadena, yanzu inason in dan fita ne”

Daddy yace “ba dai kasaon fadan danake maka Seka dawo Allah ya kiyaye” “Ameen” ya tashi yabarwa daddy kwanukan Abincin a palour, Ilham tanata fargaba da Jalal yafito amma taga still be kulata ba ya fice daga palour, dakinta ta koma ta dauki wayarta takira yaseera, bugu biyu ta dauka

“Hello yaseera kinajina?” 

“ina jinki Ilham lafiya naji muryarki a haka” 

“Yaseera ina cikin matsala” “matsalar me kuma?” 

Nana Ilham ta gayamata dukkan abunda yafaru jiya akan ance za’ayi maganr aurensu da Jalal. 

“tabdijan lallai Ilham akwai katuwar matsala, gaskiya yayan nannaki akwai taurin kai, dole musake shiri amma kunyi waya da ummane?” 

“A’a yaseera amma zanje anjima, wallahi banaso ingaya mata ne hankalinta ya tashi banaso ta karaya akan bazan iya cika mata burinta ba, gani nake bazam gayamata ba, gara mubari ranar Sunday muje gurin malam” 

“to shikenan yadda kika gani, amma abun da damuwa wallahi, ace duk wani kissa taki tasiri akansa sekace ba namiji ba, anya ba mata maza bane ba

Ace mutum zuciya kaman karfe” 

“Hmm kema dai kyafada yaseera, bari ranar ki shirya da wuri muje” 

“to shikenan Allah ya kaimu” “Ameen yaseera nagode sosai”. 

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Y’an kwanakin nan, Jalila ta dan sakewa Sulaiman suna gaisawa saboda tasamu damar daze temakamata, amma sam taki yadda yazo gidansu ko susake haduwa, dama ba koyaushe yake zama a kano ba se lokaci2 yake zuwa, aikinsa yafi a Lagos, anan yake gayamata shi kakakin rundanar yansanda ne na jihar Lagos, amma iyalalinsa suna kano, suna hira sosai da Jalila yana bata labarin nasarori da hatsarin ayyukansu, amma daya dakko batun daya shafi soyayya seta kashe wayarta, hakama Alhaji Kabiru Jalila ta sakar masa sosai gani yake kaman sonshi takeyi, a nan takara tabattar da Saleema yarsace ta cikinsa itada faruk. 

Yanzuma waya suke da Alhaji Kabiru 

“sweet heart wai yaushe zaki farantawa masoyin kine, kinki yadda mu hadu” 

“tab waikai bakajin kunyane yarka fa daka nunamin hotonta zata girmeni kawai sesuga ka auri yar yarinya?” 

“to meye a ciki gidanki daban zan ware miki, ita Saleema tanacan karatunta tanagama karatu zan aurar da ita, Faruk yana ABU, sukenan yarannawa fa, kuma basuda damuwa da aurena, please my sweet kibari mu hadu mana, yakamata kinunamin soyayya ina Sonki fa” shi sam besan Jalila tasan Saleema department dinsu dayaba, Jalila aranta tace me mutumin nan yake nufine? Amma ta maze tace

“yaushe zakazo ku gaisa da Abba na?” 

“Ai wannan ba wani abun damuwa bane, kibari mugama fahimtar juna mana kinki bari inzo gidanku balle mudan dinga fita chilling din nan, bakya wani nunamin soyayya” 

“Banda wannan danake maka wacce kakeso kuma?” 

“yakamata ace kinkawomin ziyara gidana mu gaisa mana” “haka kurum matarka ta zaneni” “wayace miki nan zakije, gidana danake ganin special guest dina zakizo” murmushi Jalila tayi “hmmm special guest, ashe nima special ce” “sosai makuwa please my sweet yaushe zakizo?” 

“karka damu kabari in mungama exams zanzo, ba dai zuwa kawai zanyi shize tabattar maka da inasonkaba karka damu” 

“Kai amma naji dadi sweet, Allah ya kaimu kugama” 

“Ameen se anjima” koda sukayi sallama Jalila ta kalli wayar ta takunna recording gaba daya wayar datakeyi tana recording dinta, tana saving a Gmail dinta “Azzalumi kawai, shiyasa abunda kakeyine yasa yarka take can take watsewa a makaranta bakasaniba Jaki kawai, zakuga abunda zan muku kaida yartaka sena kunyataka agabanta in nuna mata nafita iya rashin mutunci”. 

Sosai Zahra ke gudun cigaba da mu’amala da Jalila sedai ta waya saboda kashedin dasu sameera sukayimata, gashi suncigaba da uzzuramata akan lallai ta amince da bukatar sameera, tarasa inda zatasa kanta abun ya isheta, dan haka ta samu Jalila tagayamata halin da take ciki, “Zahra yazama dole ki amince da batun su Sameera” 

“haba Jalila so kike rayuwata ta tarwatse ne yazakice haka?” 

“basonake rayuwarki ta tarwatse bane, taimakonki zanyi” 

“to tayaya Jalila, kinsani nasani dukkansu ba mutanen arziki bane da sharri suke nufina” 

“Nasani ai tarko zamuyi musu nasan yadda zanyi dasu” Saleema ce tazo har inda su Jalila ke zaune ta kalli zahra “wato zahra bakiji kashedin da Sameera ta miki bako? Har yanzu kina biyewa wannan yarinyar ko” 

“Ke wai dakata, suwaye dinta ku, ana dolene ko angaya muku kowa sakaraine dabba irinku” “Ke shiga hankalinki, bana son shishshigi muna daf dasawa amana maganinki yadda ko hanya muka hada sekin kauce” 

“Allah ko? Dama waze hada hanya da kazamai jakuna marasa tsoron Allah, aini base kunsa anyi maganina ba, nizanyi maganinku daga ke har kawartaki ba sameera ba ko langa ce kukiyayeni musamman ke” ta nuna Saleema, 

“Asararu ko kunya bakwaji kaf school din nan kowa yasan mekukeyi” kafin Saleema tayi magana Jalila ta dau jakarta tayi gaba tabarsu Zahra a gurin. 

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah su Jalila suka fara exams din first semester, kowa yana abunda yaga ze fisheshi, wasu sun dukufa karatu, wasu ko sharholiyarsu kawai sukeyi, itakam Jalila ta maida kaine akan lissafin yadda zata bullowa al’amuran ta dasuka dameta, 

Yau karfe tara zasu shiga exams, ita Nana sun gama tasu Jarrabawar dan hutu ma sukeyi, gashi Manu direba baya nan Maama ta aikeshi, da karambani Jalila tasaka Manu yakoya mata mota, da mukulli na nan da dakanta zata tafi yau, dan haka ta yanke shawarar tafiya ta hau napep, 

Tana fitowa daga gidataga Daddy da dansa Jalal a jikin motar Jalal, durkusawa Jalila tayi “daddy ina kwana?” “Lafiya kalau Jalila makaranta za’atafi ina direban naku?” 

“daddy baya nan, napep zanje in hau karfe tara zamu shiga exams” 

“kai Masha Allah, Allah yabada sa’a, takwarar Jalal, Allah ya temaka” Jalal ya tsani yaji ance takwarar nan tasa, yawani hade rai, “Ameen daddy nagode sosai Allah yasaka da alkhairi bari in tafi kar in makara” “A’a tsaya, dama Jalal fita zeyi, Jalal kuje seka ajiyeta a makarantar tunda duk hanyace” kallon daddy yayi, ya kalli Jalila ya dauke kansa

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

Back to top button