Uncategorized

Maciji Ne Page 65-66 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 65/66

________________”Ki sanar dani dalilin da yasa  baki son zuwana gurin yarinyar nan?

Me alaƙarki da ita ?ko ince me ta tsaremiki uktee?

Sarauniya suhaimat ta fada cikin haɗe fuska ,dan tasan kadan daga aikin ammi ta hanata zuwa gurin fattu.

Zaro ido ammi tayi tana mai kallon suhaimat ,dan sai lokacin ta fahimci tana kokarin bada kanta,cikin in-ina ta fara magana “su…hai..mat,wane dalilin ne zaisa kuwa in hanaki zuwa gurinta?kawai ina gudun ace ko wata munaƙisar muka ƙulla yasa kike ta zarya,kinsan tunda wannan abun ya faru to komai ma laifi zai zama , amma bayan wannan bani da wani dalili”ammi ta fada tana kafe suhaimat da idanu.

Download>>> The Governor Wife Book 3 Complete Document

Murmushi suhaimat tayi ,kafin tace “Indai dan wannan ne karki damu ,ai kowa yasan Ni likitar matace,kuma ba laifi bane idan naje duba marar lafiya,kuma ma mace”suhaimat ta fada cikin yanayi na rashin damuwa.kafin ta juya ta bar ɗakin.

Harara ammi ta biya da ita ,kamar idanunta zasu fado ,haushin suhaimat takeji fiye da tunanin mai tunani,wllh badan tana tsoron faruwar wani abu ba ,data gama da suhaimat ,dan itace silar shigar ta ko wace irin damuwa.amma ba komai muje zuwa sannu sannu bata hana zuwa,saidai dade ba’ajeba.

koda sarauniya suhaimat ta koma bangaren Adeeb, kwance ta tarar da fattu adaki, idanunta alumshe kamar mai barci,yayinda Adeeb ke falo yana amsa waya.

Bayan sun gaisa yake sanar da ita fattun tana cikin daki, dan sosai yake jin dadin yadda take kula masa da fattu.

Tana shiga fattu ta buɗe idonta,da sauri sakamakon jin muryarta,dan dama tana kwancen nan, tunaninta  Sarauniya suhaimat kawai take.

Da murna ta tashi zaune tana murmushi,tare da kallon suhaimat,

Itama cikin farin ciki ta karasa gareta ta zauna.

Ahankali fattu tace “inna nayi tunanin bazaki dawoba,ina ta tunaninki araina”ta fada fuskarta ɗauke da annuri.

Shafa fuskar fattu tayi kafin tace “ƴata kenan ,tunda nace zan dawo ,ai dole na na dawo naga kaykykyawar fuskar nan taki,ya jikin naki”suhaimat ta fada cikin murmushi.

“Da sauki “cewar fattu.

“Masha Allah,haka ake so ki kula da shan magungunanki kinji”cewar sarauniya suhaimat.

Jinjina kai fattu tayi kafin tace “ina yan biyu “

Murmushi suhaimat tayi kafin tace “suna can suna shiryawa ,Basu san nazo nan ba da kin gansu sun biyoni, dan sun damu dake sosai” ta fada cikin murmushi.

Fattuna murmushin tayi, tana wasa da ƴan yatsunta.

  Sun jima suna hira da fattu,duk da tana  ɗan jin kunyar sarauniya suhaimat din,amma zakayi mamakin yadda ya sake suke ta hira ,harda dariya .

Anan ne take sanar da ita cewar yau zasu tafi garinsu.

Lokaci guda fattu ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka,

“Ayya inna meyasa zaki tafi?dan Allah ki zauna anan,bana son ki tafi “fattu ta faɗa tana mai kallon sarauniya suhaimat.

Ahankali suhaimat ta kamo hannun fattu ta rike cikin nata tana ɗan murmushi,duk da itama sam batason rabuwa da Fattun,amma dan ta kwantar mata da hankali sai tayi murmushi tace”karki damu my princess ai zan rinka zuwa ina ganinki,kuma wataran zance yarima ya kawomin ke muyi hutu,ko bazaki zoba”?ta fada tana kallon fattu.

Download>>> Kwarata Complete Document

“Zanzo mana inna dama bana son zama agidan nan tsoron wannan mai kama da hamman nawa nake”ta fada cikin yanayi na damuwa, idanunta har ya kawo kwalla.

Cikin damuwa itama suhaimat ta tallafi kumatun fattu,tana mai cewa”ki kwantar da hankalinki ƴata, ba abinda zai miki kinji,ki daina tsoronsa,yanzu haka yana can akwance cikin halin mutuwa da rayuwa,kuma hammanki yana tare da ke”ta fada cikin salon kwantar da hankali.

Jinjina kai fattu tayi tana mai kallon suhaimat ɗin.

Murmushi suhaimat tayi tana mai kallon wayarta dake ringing ,lokaci ta duba taga harta kara minti biyar akan time ɗin da zasu tafi,dan ma private jet ne.kuma mijinta bai sami halartar gurin ba saboda wani meeting da suke mai muhimmanci.

“To ƴata zan tafi saina ƙara dawowa zan dawo mutafi tare dake ,kinji”suhaimat ta fada tana jin ba dadi cikin ranta,ji take kamar zata rabu da abu mafi muhimmanci arayuwarta.

Ahankali fattu ta daga mata kai, idanunta na zubda kwalla,sam bata son suhaimat ta tafi,”Allah ya tsareku,ya kaiku lafiya inna ,saikin dawo”fattu ta faɗa tana ɗan kwantar da kanta jikin suhaimat.

Rungumeta suhaimat tayi cikin alhinin rabuwa da ita .Adeeb ne ya shigo dakin da sallamarsa,da alama wanka yayi dan ya cire kayan dazu ya sanya riga da wando blue  and white yayi matuƙar kyau sosai,sai ƙamshinsa yake kamar kullum.

Kallonsu yayi yadda ko wanne ke zubda kwalla ,lallai lamarin Allah abin kallone,dubi yadda lokaci ɗaya shakuwa ta shiga tsakanin bayin Allahn nan?kamar sunsan juna.murmushi yayi yana kallon suhaimat kafin yace “anty suhaimat har yanzu kina nan da tausayi da  kuma  saurin kuka ” ya faɗa yana kallonta.shikam tun sanin da yayi mata haka bakinta yake ,akwai tausayi da son mutane bata da kyamar dan adam.

Share hawayen idanunta tayi kafin tace “prince wllh da zaka bani yarinyar nan dana tafi da ita can Ghana munyi zaman mu ,dan Allah ya doramin kaunarta cikin raina sosai” ta fada tana shafa kan fattu.

“In baki ita ku tafi?Ni kuma inyi yaya,haka kawai ,ki tafimin da mata?inaaa”Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa.amma zahiri saiyace “karki damu watarana zata zo “

“Allah yasa da gaske kake,yanzu dai kayi mana hoto dan tarihi”sarauniya suhaimat ta fada tana mai janyo fattu jikinta.

Luuuf!! fattu tayi ajikin suhaimat tana mai jin wani irin sanyi acikin zuciyarta.hotuna Adeeb yayi musu kusan kala biyar awayarsa, hakama yayi musu awayar Sarauniya suhaimat ɗin.

Da gyar suka rabu da juna cikin kewa da kaunar juna, fattu sai kuka take ta rungume Adeeb lokacin da suhaimat ta tafi rarrashinta yayi tayi da gyar ya samu tayi barci.

Ammi kuwa sosai taji dadin tafiyar suhaimat,dan hankalinta sam bai kwanta ba ,gani take kamar zata iya gano wani abu game da fattu

Yanzu damuwarta daya shine yadda ,zata bullowa lamarin Adeeb.

Download>>> Matar Makaho Complete Document

Rashad ya farfaɗo ,saidai gaba ɗaya ankasa gane  kansa ,dan kullum haka zaka ganshi shiru baya magana saidai kallo,abin yana matukar damun amma,haka zatayi ta kuka tana kallonsa,saidai kawai kaga hawaye yana bin fuskar Rashad din,ya rame sosai,dan baya wani cin abinci,ga karaya ajikinsa ta ko ina likitoci suna ta binciken kwakwalwarsa dan suna tunanin tanan ya sami  matsala.saidai muce Allah ya bashi lafiya.

Sam yanzu Adeeb baya  kula tareeƙ ,haka zai zo yayi ta bashi haƙuri amma Adeeb bazai ce masa ko ci kankaba.duk da yadda yayi kewar tareeƙ ɗin cikin zuciyarsa.

Abin yana yiwa tareek ciwo ,haka zai je gurin nanny yayi ta kuka ,saidai tabashi hakuri.

Alhamdullah jikin fattu ya warke sosai,dan duk tabon ciwukanta ma babu,sosai shakuwa ta kara shiga tsakaninta da Adeeb,dan kuwa ya dawo da ita bangaren sa gaba ɗaya ,ya siyo mata sabbin kayan sawa ,da duk wani abu datake bukata.

Yayin da gefe guda yake ci gaba da bincikensa akan al’amarin su Nazli da kuma sarƙar nan ta fattu,akan ammi ,saidai har yanzu ya kasa samun wata kwakwkwarar hujja da zai kama ammi da ita .dan haka ya kara yarda cewar hadin bakine na amma da nanny ,suke son hadashi da ammi.

Bangaren rashad kuwa ,abin ba’acewa komai,dan har yanzu yana nan jiya iyau, baya uhhhm bare uhm -uhm .magani ta ko ina yi masa ake ,mai martaba da kansa abin yana damunsa,.

Haka ma Adeeb yana jin ciwon abinda yayiwa ɗan uwan nashi,saidai koma menene shiyajawa kansa.kuma hakan bai hana shi neman masa magani ba .

Shaikh lateef ya bawa Adeeb magungunan da zai rinka amfani dashi,kuma yana amfani dasu yadda ya kamata.zamu iya cewa yanzu abubuwa sun dan lafa agidan.

Yanzu haka fattu ana mata lesson kullum ,zakuyi mamakin yadda fattu ta iya Yaren larabci sosai,tana ji kuma tana iya mayarwa, dan fattu akwai ƙwaƙwalwa,shikansa mai mata lesson yana mamakin hazaka irin ta fattu.

Adeeb kullum yana kara nuna mata abubuwan da bata game ba.tayi kyau sosai ta goge idan ka ganta bazaka taba cewa itace ba.

Kullum saisunyi waya da sarauniya suhaimat,sun shaku da juna sosai.

Gimbiya Zulaihat ma tana nan tana nata shirin,dan yanzu kam tana ganin fattu na neman zama wata abar alfahari agidan,dan ta kereta ta ko ina,Shegiyar yarinya kyau kamar yar aljanu.

Download>>> Bankada Complete Document

Wannan kenan.

Ammice zaune ƙaton falonta tana waya,dawowarta kenan daga gurin mai martaba,tana masa maganar ya dace ace zuwa yanzu Adeeb yayi aure ,dan shekaru na tafi kuma shine magajin fada.

Dan haka abie yace ta zaba masa matar da zai aura ,tunda itace amminsa ,kuma yasan Adeeb bazaiki zabin ammin nashi ba.tun da dai shi ba kula yan mata yake ba.

Cikin farin ciki kuwa ammi ta dawo ɗakinta ta kira kawarta.

“Ƙawata ,albishirinki?

Ammi ta fada cikin ɗoki.

Bansan me akace mata ba ta dayan bangaren naji dai taci gaba da cewa”ai mai martaba ya bani damar zabawa Adeeb matar da zai aura,kuma ba kowa na zaba masaba face yar wajenki,maryam.kinga mun sami hanya cikin ruwan sanyi,da zamu cika burinmu akansa” ta fada cikin doki tana murmushi.

Shiru na ɗan wani lokaci kafin taci gaba”ki rabu dashi, kawai ,nasan barazana ce yake min,amma kinsan bazan taɓa yarda Zulaihat ta auri Adeeb ba,dan kuwa ubanta zatayi wa aiki ba muba,

Batun yarinyar da yazo da ita kuwa,na boye duk wata hanya danasan zai gane suwaye iyayenta na asali,kuma nasanya boka ya hana uwarta zuwa gasar nan ma gaba daya , Kinga har abada bazasu taba haduwa  da junaba.

Abu na gaba da zamuyi shine ,da zarar anyi auren nan,zamu sa ta kashe dan banza kowa ma ya huta, zan san yadda zanyi in shawo kan wancan mugun ya yarda ayi auren saimu kashe Adeeb din”

Shiru ammi tayi tare da sauraron abinda ake fadi aɗaya bangaren.

Kafin taci gaba”wllh ƙawata Ni kaina yarinyar nan na tsaneta ,bana don ganinta,Aduk lokacin dana ganta fuskar uwarta  nake gani ,kuma ina tunano abinda ya faru abaya,dan haka itama kawar da ita zanyi kowa ya huta ,duk dana ɗauke sarƙar nan Tata,amma na nemeta na rasa ,kuma banganta awuyan yarinyar ba,dan haka ina tunanin bata koma gareta ba,ƙila dai nice na sauya mata gurin ajiya na  manta”

Shiru ammi ta sake yi ,kafin tace shikenan sai kinzo ma karasa maganar.

Jikin fattu banda rawa da bari ba abinda yake ,zuciyarta sai neman tarwatsewa take , innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!!wanann wace irin masifa ce haka,yanzu ammi tasan su waye iyayena dama ?kenan kashe Hamma zasuyi?me hakan ke nufi? kenan ammi ba itace mahaifiyar Adeeb ba?dan kuwa tasan ba ta yadda  za’ayi uwa tayi yunkurin  kashe ɗan ta,  wai meke faruwa ne?wannan ɗin wane irin badakala ce kuma?

Tsabar rawar da jikinta yakeyi bata san lokacin data buge wani flower vase dake ajiye agefenta ba , ya fadi kasa ,jikake toshshs!! Ya fashe.

Download>>> Fahimta Fuska Complete Document

Cikin tsoro da tazana fattu ,tayi sauri buya ajikin ƙofa tare da runtse idanunta.

Ammi kuwa da sauri ta taso Dan ganin waye yayi mata labe ,har yaji sirri ta.

Da mugun ƙarfi aka fizgi fattu akayi waje da ita ,buɗe baki fattu tayi da nufin kurma ihu,taji an toshe mata bakinta…..

Waye ya dauke fattu?

Me zai faru nan gaba?

Muje zuwa anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

Karanta Labarin>>> Maciji Ne Hausa Novel

More comment

More typing.

Back to top button