Haihuwa Da Hanji Page 4 Hausa Novel
A wurin ta cigaba da zama jiki a saɓule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har ya ɗuri ruwa saboda ƙuna daga gefe zuwa ƙasan idanunta, Allah ya taƙaita ma bai taɓa idanun ba ta ce “Har kin gama ci Afeefah?””Eh Aunty na gama”Ta faɗa a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.”Bari na ba uncle ɗinki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ƙunar kar ya zama miki damuwa”Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta miƙe ta shiga parlor zuwa ɗakin da ta ajiye mata kayanta daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana “Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika ɗauko ta za kiyi ba”Itama Auntyn a sama ta amsa shi”sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman””Zainabu…!”Da mamaki ya ƙira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta ɗaga mishi murya ba sai yau. Kuka ta fara”Haba Usman na fa faɗa maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah ɗiyar yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru…”Ya katse ta “Zainabu ba wai ‘yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki ɗauko ta ki kawo min cikin gida?”Tana kuka sossai tace”Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taɓa yarda Afeefah zata yi maita ba, babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ƙare idan ko don ka zauna da mutum kwana ya ƙare ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar da ita gidan labaran ba wallahi”Numfashi mai karfi ya sauƙe”shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana””Babu ma abin da zai faru sai alkhairi”A lokacin Afeefah ta sulale ta maƙale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta ɗago kai “Aunty don Allah ki yi haƙuri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina hankalina ba’a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba…”Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye “bawa baya taɓa wuce ƙaddarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taɓa iya sake barinki ki zauna wurin ‘yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je”Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ƙuna a wurin kan suka dawo.Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke maƙotaka tana saya kuma ta sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba tela akan zai ɗinka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar yadda zata so mahaifiyarta.Da kaya sossai suka dawo niki niki, a ɗakin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu ɗan dama suka tafi da su kasuwa aka rarrage mata yadda zai ƙarbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo, natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen shekara za’a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee ɗin ke nuna ta matsayin ɗiyarta.Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag ɗinta, fuskanta ya fito fess a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin ɗinta har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga ɗakin uncle usman ta samu ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta ɗan duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa “Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?””Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci”Afeefah tayi murmushi “Toh shikenan na wuce makaranta””karɓi”Ta matsa ta karɓi ɗari biyu da yake miƙa mata”Sai kin dawo a mayar da hankali”Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe. Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu programs na makarantar, bata da ƙawa har yanzu don duk ajinsu ba sa’annin ta shirin exams ake don haka yau revision ƙarfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.Sai dai ta samu babu kowa, ta karɓi key a maƙota ta shiga sai da ta zare uniform ɗinta ta sauya da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta ɗaura dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta ɗora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san suna da dangin nesa nesa ta ɓangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee ɗin ba ta su take ba abinda ke gabanta ma ya fi karfinta.Tana sauƙe faten doyar sai ga su sun shigo “wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?”Aunty zee ta leƙo kicin ɗin tana tambaya Dariya Afeefah tayi”Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?”Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta miƙawa Afeefahn, Afeefah ta karɓa ta shiga saka mata kan tace “Eh Afeefah ban jin daaɗi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ƙani”Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee ɗin sai ta hau hawayen murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin ‘ya’yanta a duniya?Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace”duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle ɗinki da ma ɗayar Auntyn taki da suka tasa ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana yasa”Tana murmushi ta ƙarasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai ni’ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa a cin abincinta.Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term ɗin don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee ɗin ba, ko tsinke in ta ga zata ɗaga za ta karɓe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani ɓangare, kishiyar Aunty zee ɗin ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haɗu da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba tunda babu abin da ya haɗa su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan so bata damu ba sam.Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta “Aunty ki taya ni murna”Result ɗin ta miƙa mata”Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri”Kai ta gyaɗa tana ta dariya.****Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha’awar shi ta tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa Aunty zee ɗin hira kaɗan kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huɗu kenan.A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah ɗin tana da matuƙar buri a kan rayuwar Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu’a yadda ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah “Wai kuwa kin san kamanninki har ya ɓaci da Yaya Aisha?”Afeefah ta ɗago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin Aunty zee ɗin “Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)”Miƙewa Aunty zee ta yi ta shiga ɗaki ta ɗan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da cikinta har ya turo sossai ta zauna.”Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin bikinta ne da babanki”Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na ɗan rawa ta sanya ta karɓa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar ta irin na mamanta ne, baƙin fatarsu mai sheƙi, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su, karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda ɗaya da maman nata ke dashi a gefen hagu itama tana da shi.Raɗaɗin maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici? Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk duniya idan da za’a ce me take buƙata ayi mata ko da abu na ƙarshe ne za ta zaɓi su yi rayuwa na har abada amma ake mata Ƙazafin kashe su, anya zuciyarta za ta taɓa warkewa? Anya za ta iya yafewa masu alhakinta? Ɗago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee”Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaɓi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuɗi ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba? Yanzu wannan pure soul ɗin ni na kasheta ko?” Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwo da raɗaɗi…


