Halysaah Page 184 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 184…Jay ya fito daga cikin banki wajen karfe goma looking so confuse, rabonsa da shiga irin wannan confusion din da anxiety da yake ciki zai yi 2 years yanxu, duk da sanyin safiya dake kadawa wani mugun zafi yake ji a duk jikinsa, ya ma rasa takamaiman abun yi a wannan moment din don sai kai komo yake a bakin bank din ba tare da ma yasan yana hakan ba, kawai yayi saurin komawa inda yake zaune daxu kafin a bude banki cause he was breathing at a very fast pace, ya zauna kan dakalin wajen ya dafe kirjinsa trying to calm the blood rushing through his body as a result of anxiousness, da yana da hawan jini babu abinda zai hanasa tashi a wannan lokacin, at a point sai yaji kamar it’s one of his numerous dreams, it feels like he is dreaming, amma sai yayi saurin bude ido to be sure he isn’t dreaming and everything is real, wayarsa ne ya fara ring which made him jerked immediately, yayi saurin ciro wayar yaga Mami ce ke kiransa, daga kiran yayi da sauri ya kai kunne, daga daya bangaren Mami tace “Jawwad” Ya runtse ido ya kasa amsawa at first, har sai da ta sake kiran sunansa, cikin karfin hali trying hard to control his emotions yace “Mami wallahi shi ne ya zo bankin yayi ATM card ya cire kudin, Mami Ajay ne….” Mami sai da ta mike tsaye a tsorace without knowing she did so, she was soo shock and completely lost of words, can ta juya a hankali tana kallon Khaleesat dake kwance kan gado idonta a lumshe, ko minti sha biyar ba ayi ba take bata labarin abubuwan da Ajay ya gaya mata a mafarkin da tayi jiya, kuma tun da gari ya waye take tambayar Mami yaushe za su koma Bauchi, ita tana son komawa gida don akwai abinda zata yi, Mami ta zame wayar daga kunnenta bayan taji alamar Jay ya katse kiran, kofa ta nufa da sauri ta fita daga dakin ta koma inda babu mutane ta sake kiran Jay, yana dagawa da wani expression tace “Jawwad ban gane Junaid bane yaje ya ciri kudi a bankin? Su suka gaya maka haka? Ta yaya suka san shi? Did they check der CCTV camera?” Jay ya kasa ce mata komai at first, har sannan numfashinsa yaki komawa dai dai tsabar irin anxiety din da ya shiga, cike da kaguwa Mami tace “Speak to me Jawwad, ta yaya kasan shi ne yaje bankin” Da kyar Jay yace “Mami they confirmed he came to the bank yesterday morning, sun ce shi da wani mutumi suka zo bankin, he was even sick and they had to attend to him fast without letting him join the queue, har hotonsa na nuna masu suka tabbatar min shi ne wallahi, har Atm fa yayi Mami….” kasa ci gaba yayi cause he was getting so emotional, Mami da taji zufa na karyo mata tace “Yanxu ina suka ce ya tafi?” Jay ya girgiza kai ya hadiye wani abu da ya tokaresa a throat da kyar yace “Mami how will they know suna cikin banki?” Mami tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, is this real or i am dreaming Jawwad? Kana nufin Ajay ne ya ciri kudin?” Cike da karfin hali Jay yace “Mami wallahi gani nake kamar mafarki nake kuma zan iya tashi a mafarkin nan at anytime, this is seriously going to break me, i am feeling it’s not real, I will be so heartbroken Mami idan ba da gaske bane, I don’t think i can take it, shi yasa naki barin nan kar ma in tashi baccin nan” Muryarsa na rawa ya kare maganar, Mami tace “Ba mafarki kake ba Jawwad, ka tashi ka tambayi mutanen dake surrounding din ko sun san whereabout dinsa, show them his picture” Da sauri Jay ya mike kamar wanda wani strength ya zo masa, kwata kwata bai yi tunanin yin haka ba sai da Mami ta fada, yana gyada kai yace “Ok, ok I will do so Immediately Mami” katse wayar yayi ya nufi wajen securities din bank dake zaune ya fara nuna masu hoton Ajay duk suka ce basu ganesa ba, barin wajen yayi da sauri ya tafi jerin shaguna dake kusa da bank din su ma zai nuna masu hoton Ajay sai ga Message ya shigo masa daga IG, message biyu yaga sun shigo one after the other, tun daxu da sassafe yaga shigowar message from same sender, sai dai bai bi ta kai ba don har ya mance rabonsa da bude IG din, but wannan sakon da ya shigo na karshe yayi capturing attention dinsa saboda Dsp Bilyamin Muhammad da ya gani as the last content of the message, cikin hanzari ya shiga message din wondering who the Dsp is, nan yaga an masa sallama sau biyu tare da introduction tun jiya da daddare, daxu kuma aka yi requesting yayi dropping number sa if he sees the message, sai kuma yanxu da aka sake masa wani message din, ya dinga kallon sunan me masa sakon babu ko kiftawa, can ya tura reply yace “Good morning, but ban gane me magana ba” Immediately sai ga reply daga user din with phone number aka ce masa ya kira layin, Without hesitation Jay yayi copying number yayi pasting ya fara kira, Bilyamin ya daga kiran tare da yi masa sallama. Sai bayan kusan 40 mins Jay ya isa address din hospital din da Bilyamin ya basa bayan sun dau minti sha biyar suna waya, shi kansa bazai iya kwatanta irin anxiety din da yake ciki a wannan lokacin ba, he was more than nervous and uncertain, kawai jan kafa yake kamar mara laka a jiki, sai zufa yake a goshi yaji throat dinsa was completely dry, babban fargaban sa kada kawai ya farka yaga mafarki yake duk wannan abun, his heartbeat rate is increasing as each minute passes, duk wanda ya gansa yasan baya hayyacinsa, kawai dai yana biye da Dsp Bilyamin da ya fito ya taresa a reception din asibitin ne, Babban asibiti ne me tsada, suna isa kofar wani ward Jay yaga ɗan sanda a zaune kan kujera, cike da karfin hali ya gaida ɗan sandan da ya mike ganin Ogansa, Dsp Bilyamin ya bude kofar ward din gently, he even have to speak to the Doctors kafin suka bari har ya shiga ward din tare da Jay, Jay ya kasa shiga ciki bayan Bilyamin ya shiga, bugun zuciyarsa ya tsananta, his legs were very weak, Bilyamin ya juya ya kallesa yace “Come in Jawwad” Da kyar Jay ya daga kafa ya shiga cikin ward din idonsa ya sauka kan Ajay dake kwance idonsa a rufe kan gadon ward din an sa masa drip har biyu at once, kallonsa ya dinga yayi babu ko kiftawa, yana jan kafa da kyar ya isa har kusa da gadon, bai san sanda ya duka ya dora kansa a jikinsa ba, and he couldn’t control his tears, likitan dake tsaye kan Ajay ya dago Jay yace “It’s fine, he need much rest, Kar ka tashe sa….” Jay ya kasa cewa komai ya hade kansa da bango with more tears flowing down his eyes, Bilyamin dai na tsaye gefe daya a ward din, likitan ya kallesa yace “Tun da ya gansa za ku iya fita Officer” Bilyamin ya gyada masa kai, sannan ya tafi ya dafa Jay a shoulder dinsa calmly yace “Mu fita mu bar likita yayi aikinsa” yana fadin haka ya kama hannun Jay da ko ganin gabansa baya yi, a haka suka fita daga ward din, Bilyamin na nuna masa kujeran dake gaban ward din yace “Ka zauna can ka samu nutsuwa, You need to calm down, ka kira gida ka sanar masu abinda ke faruwa….” Jay bai iya ya ce masa komai ba don baya ma gane abinda yake cewa, yana tafiya da kyar amma at this point ya dena ganin gabansa da kyau, hakan yasa yayi saurin dafe bango, Bilyamin da Police officer dake wajen suka nufesa da sauri ganin he was crumbling to the floor suka yi hanzarin rikesa…. Khaleesat na zaune kan darduma bayan ta idar da sallahn azahar, ta juya tana kallon Mami dake ta dialing call tun daxu amma da alama wanda take kiran baya picking call din, zaka iya ganin damuwar dake kwance fuskarta a wannan lokacin, Khaleesat ta mike daga kan darduman da take ta koma kusa da ita ta zauna a hankali tace “Mami is everything alright? Naga kamar kina cikin damuwa” Mami ta kalleta, sai kuma tayi murmushin karfin hali tace “Ba komai Khaleesat, baza ki je ki leka su Inteesar ba, duk yau fa baki shiga wajen su ba, gashi har an daura auren” Khaleesat ta sauke idonta tace “Yanxu nake son zan shiga Mami” Mami tace “Ya kamata, in ma baza ki zauna ba kiyi congratulating dinta sai ki dawo nan” Khaleesat ta gyada mata kai, sai kuma tace “Amma wa kike kira tun daxu baya picking Mami?” Mami tace “Jawwad nake kira zai amso min sako, to har yanxu ban samesa a waya ba” Khaleesat tace “Kilan a silent ya sa wayar” Mami tace “Kin ma yi magana da yan gidan ku kuwa Halysaah?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Wayar ba caji sai na kashe tun da safe, kuma na manta ban zo da charger ba” Mami tace “Na ce ki dena kashe waya Halysaah, ba sai ki tambayi Hadiyah ta baki nata ba tunda naga wayar taku iri daya ce” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “To zan tambayeta Mami” Mami tace “Baki san yau ake daura auren Faridah ba ko?” Khaleesat ta dinga kallon Mami babu ko kiftawa, da mamaki tace “Aunty Faridan mu?” Mami na murmushi tace “Ai har an daura ma, shi yasa nace baki yi magana da yan gidan ku bane yau” Khaleesat was very very surprise, tace “Wallahi ni ban sani ba, bari in kunna wayana” Mikewa tayi ta dauko wayarta da sauri, ko shekaranjiya da safe sun yi waya da Aunty Farida amma bata gaya mata komai ba, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, yanxu Aunty Farida zata yi aure shi ne babu wanda ya gaya mata balle taje Kanon, Mami dai tayi using wannan opportunity din ta mike ta fita daga dakin tana sake dialing number Jay, tun wajen karfe sha daya da yan mintuna take kiransa har yanxu he is not picking his call, sosai hankalinta yake a tashe daurewa kawai take, what could have happen da zai ki daga kira for almost 3 hours now, she was so worried…. Jay ya bude ido a hankali yana bin ward din da yake kwance da kallo, da sauri ya mike zaune kamar me son recalling abinda ya faru har ya zo asibiti, was he sick? How did he get here, ga dai shi ba ƙarin ruwa ake masa ba, lokaci daya abinda ya faru suka fara dawo masa daya bayan daya a kai, sosai gabansa yayi mugun faduwa, could it be he was only dreaming ba Ajay ya gani ba, could this be one of his many dreams, ji yayi zuciyarsa ya fara bugawa da karfi, in dai duk wannan abu da ya faru mafarki ne yasan da kyar idan Heart attack bazai kamasa ba, sauka yayi daga kan gadon ko takalmansa bai sa ba ya nufi kofa da sauri ya bude ya fita, ward din da Ajay yake ya nufa zuciyarsa na tsananta bugawa, Police Man din dake bakin kofar dakin a zaune ya mike, tun bai ce komai ba Jay yayi saurin bude kofar ward din ya shiga ciki without waiting to listen to him, lo and behold he still saw Ajay lying on the bed sleeping, sai a sannan ya yarda ba mafarki yake ba it’s real, Jay ya jingina da kofa ya runtse idonsa trying to calm himself down, yasan har ya bar gidan duniya babu wani abu da zai sa shi jin kwatankwacin abinda yake ji a ransa yanxu da ya ga Ajay, nothing will ever make him be this grateful to God in this life like his reunion with Ajay, gani yake kamar an gama masa komai a duniya, Police Officer din ya shigo ward din yayi masa alamar da ya fito, Jay na jan kafa ya fito daga ward din, Officer din ya jawo kofar gently ya kulle, Jay ya fara duba wayarsa a aljihunsa amma bai ji sa ba, Police officer din dake kallonsa yace “Oga ya tafi da wayar ka, yaje masallaci sallahn juma’a bai dawo ba har yanxu” Jay ya jingina da bango yace “Ka ɗan bani aron naka wayar, ina son zan yi waya” Police din ya basa wayar yace “Amma da ka nemi waje ka zauna, tunda kai ma ba lafiyar ce da kai ba” Jay ya gyada masa kai ya tafi ya zauna kan kujeran dake wajajen don bai ma son yin nisa da ward din da Ajay yake, ya jinginar da kansa da kujeran ya lumshe ido har sai da yaji numfashinsa ya fara dawowa dai dai, godiya ya fara yi ma Allah, getting his brother back is just the best thing that had ever happen to him in life, bude idonsa yayi a hankali yana kara yi ma Allah godiya, yayi dialing number Mami a wayar hannunsa sannan ya kai kunnensa, yana fara ringing Mami ta daga, cikin sanyin murya yace “Mami” Mami dake zaune ita kadai a daki ta mike da sauri tace “Jawwad, me ya samu wayar taka? Kana ina yanxu?” Jay ya kasa cewa komai, cause he don’t want to be emotional, hankali tashe Mami tace “Ka min magana mana, kasan yanda ka daga min hankali kuwa yau? Where are you now?” Da kyar yace “Mami na ga Ajay, I found him Mami” Sai da gaban Mami ya yanke ya fadi tace “Junaid din?” Jay ya kasa ce mata komai cause he is really getting emotional, hawaye suka cicciko idon Mami cikin rawan murya tace “Ina ka gansa Jawwad? Yana ina yanxu?” Da kyar Jay yace “He is sick, we are at the hospital, har yanxu ban kira Mai martaba ba” Hawaye na zuba idon Mami tace “Alhamdulillah, Alhamdulillah Allah mun gode maka” Katse wayar tayi ta zauna kan kujera ta dafe kanta tana kuka sosai, sai yanxu ta fahimci dalilin da yasa Khaleesat taki ɗangana, ashe tana ji a jikinta mijinta na nan da ransa, duk suka dinga mata kallon ta samu matsala ne a kwakwalwarta, lallai ta kara tabbatar da cewar tsakanin miji da mata sai Allah, ko yaya Khaleesat zata ji da wannan abun farin cikin, shekara biyu taki barin dakinsa tace yana nan zai dawo, kuka sosai Mami take tana imagining shi kuma Sarki yaya zai ji, ji tayi baza ma ta iya jira ba, kawai tayi booking ride da zai kai ta car park, ta mike da sauri ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta dau handbag dinta da ATM card ta fita daga dakin, babu wanda Mami tace ma ga inda zata a gidan, bata ma sallami kowa ba ta fita kofar gida ta jira ride din a can har sai da ya karaso ya dauketa, tana isa car park ta biya motar da zai kai ta Benue ita kadai don bata ma son bata lokaci wajen jiran sai mota ya cika, tafi shekara talatin rabonta da zuwa tasha ta hau mota sai yau, babu bata lokaci dreban motar ya dau hanya, Mami couldn’t control her tears, har ana ta mata gaisuwa a tasha an zata rasuwa aka mata… Bayan Jay ya gama waya da Mami number Mai martaba ya kira har sau biyu bai daga ba, dama yasan bazai daga ba don ba kasafai yake picking bakuwar number ba, zai yi masa text message yace shi ne sai ga Dsp Bilyamin ya karaso wajen yana kallon Jay yace “Maa sha Allah, hope you Had enough rest, don likita yace you are stressed shi yasa kayi collapsing”




